Showing 150001 words to 153000 words out of 157081 words

Chapter 51 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

28

tayi tana mai barin parlourn, ta ce mana. "Ban da renin wayo kasan zaka dauki maganar manta, kazo ka saka ni gaba da niman shawara, duk abinda ka gadama kayi mana ina ruwana. Na sani dai duk abinda ake yi ana yi ne don kada na samu damar shiga jikinka." Ta kama masifa da ihu, babu wnada ya kulata karewa tashi muka yi muka barta a wurin. Waye zai iya da masifa irin na Nadiyyah.

Ranar sha takwas ga watan Disamba aka mai da Yaya matsayinsa, inda a sauke duk wani wanda ya haura shekara hamsin a fada, abin nan yayi masu ciwo. Daga cikin waɗanda suka rage matasa ne, da basu kai arba'in ba, ya shiga tsara yadda yake so, amma wani ikon Allah. Sai ga shi cikin abinda bai wuce wata guda ba Gwamnan Zanzabira yazo har fada tare da yiwa Yaya hannunka mai sanda. Kuskuren da yayi kenan Yaya ya tanka mi shi. Ai kuwa aka sauke tutar Muslunci na masarautar, sannan ya hana Yaya zuwa masallacin juma'a, saboda kawai Yaya yayi magana. Kai karewa ba a cika wata shida ba aka yiwa Yaya borin ba a sonshi. Wanda kawai yan siyasa da wasu dattawan fadar suna son kawai yaya ya sauka ya bar mulkin, a lokacin Ijlal ta haifi Yara maza biyu, haka mai babbar daki ta dauko Hajiya Karimah daga Kano Yayar Hajiya Mardiya, ta zauna a jikin Ijlal. A lokacin kome na Yaya sai da ta tsaya cak, manyan da ya sani yanxu basu kan muƙamin siyasa. A lokacin yaya ya shiga depression sosai don ta kai baya iya barci sai karfin Addu'a.

A haka muka samu wata bakwai a dan tsakanin Nadiyyah ta haihu, yadda take kaf-kaf da Yaronta yasani fahimtar Nadiyyah tsoron da take ciki na kada ta rasa Yaronta ba iya ita ba hatta ni da Ijlal muna dan razane da Haihuwar ko zuwa bangarenta bamu yi ba, shima kamar sauran Yan uwansa ya rasu. Innalillahi wainnalihir rajoun, yadda ta yanki jiki ta fadi, wani irin kuka take da dukkan zuciyarta, tana faɗin. "Ko wanka zan yi nasaka ana duba min Yaron me yasa sai ni? Me yasa sai ni sai ni!" Sai na tuna lokacin da nima nayi wannan maganar, haka muka yi ta rarrashinta nayi mamaki da bata yi mana fassaran mune ba, amma fa, a ranar na tsinci wani gaskiyar da Ijlal ta fada min ta ce min.

"Mammyn Yara, ko wancan Yaron da ake tunanin na kashe wallahi ban tab'a kisan kai ba, idan akwai kuskuren da nasan shi zai farauce ni, tow sai na driven da muka saka ya binne asirin da muka miki, shi kaɗai na san nayi miki wallahi Billahi azmin ban kashe dan Nadiyyah ba, akan me xan kashe shi? A ranar da na kira na gaya mata abinda ya faru, sai na fahimci kowani mutum yana da hanyar da zai iya amfani da kowa, kafin ya dauki wayar naji tana faɗin. Nayi amfani da Zainab na samu abinda nake so sai na kara da Ijlal domin biyar bukatana, a ranar kin san me naji? Jakadiya suke magana da mai aikinta cewa ai ko zata shekara dari tana haihuwa matukar maza ne sai ta ga bayansu, tunda ta amshi ragamar shiga kungiya, na shiga rud'ani dama can itama yar wata kungiya ne, a hankali na fahimci ita kawai tana zaune da Yaya ne domin ta haifi namiji da shi, ta ga bayan shi sannan akwai abinda tayi da yake bibiyarta, domin haka kawai ba zata kasance haka ba, duk da akwai Jarabawa amma abinda yake faruwa da Nadiyyah akwai wata a kasa. Ban zafaffa ba haka muka mata jajje da Yaya ya zo aka yiwa Yaron jana'iza aka kaishi makwancinsa wannan mutuwar ya sakata cikin wani irin tsoro wanda lokaci guda ta tattara rigimarta, gefe.

A haka har azumi ya zo mana, muka yi azumi da sunan Yeemar da ta kara haihuwar Da namiji aka saka mishi sunan Yaya, ai kuwa ya ga soyayya da gata ƙarshe sai da aka dawo da ita Zanzabira. Bayan sallah Yaya ya shirya mana tafiya aikin Hajji har da Yaran bakiɗayanmu har da Faruq, muka fara shiri kenan Aneesah ta dawo gidan ba wnada ya kulata, ashe sun yi rigima da Mai Babbar daki ta mata faɗa wai na mallake Yaya da ita kanta Mai Babbar daki, sai yadda nayi da su. Mai Babbar daki ta ce mata. "Eh Macen da ta isa take mallakar kowa, wacce bata isa ba kowa gudunta yake " iya abinda ta faɗa kenan yarinyar ta kwana tana kuka, haka ta bar gidan ta dawo gidan, muna ta shiri ana saura sati zamu tafi aka ce an soke visa Yaya da Ni, wayyo ranar farin cikin da Aneesah ta shiga na iya ka ba, har a gaban idanuna take rawa da murna, ni dai bai dame ni ba, Nadiyyah ma jin mijin ba zai tafi ba ta ce ta fasa Ijlal da Yara da Faruq da Yeemar da Yaranta suka tafi har da Khairat.

Ya rage gidan daga ni har Yaya, a bangaren Yaya yace ya san me yasa suke mishi haka, a bangarena kuwa na ji ciwo domin dai da aka yi ta program akan Mijina kasar Saudiya ta kore shi. Wani tudu wani gangare, ana jibi arfa, hukumar gwamnatin Saudiyya ta kira shi, ban san me ya faru ba, ina lazimi cikin dare sai gashi, ina ganinsa na shafa addu'a. "Allah ya amsa Addu'arki, kin ga hukumar Saudiyya sun nime ni, har an turo min. " "Alhamdulillahi Ubangiji ya amsa Addu'armu. Na gaya maka idan baka da hakki kana zaune zasu kira ka. Don haka ka kwantar da hankalinka, yanzu kai da waye zaku tafi?" "Ni da ke mana!" Yadda yayi maganar kai tsaye na kara yarda mutumin nan ya sauya, sannan bai gayawa Nadiyyah ba, sai da asuba ya dawo masallaci aka zo aka fitar da kayanmu. Sannan ya leka dakin a gurguje ya gaya mata ai bata san lokacin da ta dirko daga gadon ba, ta fara masifa ya ci amanarta ya munafunce ta bai gaya mata zai tafi ba sai kawai ya zo ya ce tafiyar ta tashi! Bala'i da masifa babu wanda bata yi ba, daga ni har shi babu wanda ya kulata kamar ta rufe mu da duka babu wnada ya ce mata ki yi hakuri.

Muna barin gidan ya turo aka tura Aneesah gida, duk yadda suka zo zaman shirya fita Yaya ya raba wannan al'amarin yadda kowacce ta ji babu dad'i, haka muka hadu a Saudiyya ashe babban dalilin kiranshi da suka yi Faruq ya shigar da korafin haka Mai gidansa shigowa tare da niman manyan lauyoyi daga Amirka su shiga lamarin saboda ai Salmanu Faris ba bako bane, sannan shi ɗan ƙasar Amurka ne yana da katin zama ɗan can, kasancewar larabawa sun zama yan amshin shatan Yamma sannan suka duba korafinsa, sannan aka hada wani zama da shi din akan akwai wani bukatar da ake ya shiga ma wani aiki da ya shafi ƙwaƙwalwa ana bukatar shi a wannan aikin. Amma sai an gama aikin hajji.....

(Ku yi hakuri bani da lafiya ne idan na ji sauki xan yi kokarin karkare labarin nan! Amma bana jin dadi bakiɗaya)

[8/30, 6:50 PM] Ramlat Manga41: 58

Bamu wani zauna ba domin bamu samu yin umara da ziraya ba, kawai mikati muka dauka tare da nufar filin Arfa, tuni muka rabu da Yaya na tafi niman su Ijlal, a hankali nake tafiya wuri ne da Allah ya hada mutane da jinsin Aljanu, tun daga tantinmu na ga yadda Allah ya tsara halittarshi kawai. "Tsigai ki ce an barku kun zo?" Kallonshi nayi na ce mishi. "Kasan Allah zan maka rashin mutunci!" "Na nawa kuma ke da mijinki ai Allah kawai ya kara min hakurin maza da ku." "Sayyid!" Juyawa yayi wata kyakkyawar matashiyar aljana ce da bata wuce a siffar dan adam ka kira ta yar sha bakwai ba, kallona tayi fuskartar a daure ne. Juyawa yayi ya kalle ni sannan ya kalleta, ta ce mata. "Haba Ashnur wannan ai ita ce Zainaba Mamar Ayaan ce." Take na fahimci shima dai a bangaren soyayya rago ne, nad'e hannu nayi a kirjina na ce mata. "Ke dube ni da kyau nayi miki kama da wacce take kutse a rayuwar wasu? Ni mijina Yaro ne danye jagab mai dauke da kuruciya da yarinta, ba irin wannan matsolon mai shekaru aru-aru ba!" Ita kanta sai da tayi dariya tana kallonshi, yake yayi amma yasan na caka mishi magana, duk yadda yaso hadiye takaici ya kasa wani uwar harara ya watsa min. Yana cizon bakinshi irin na ci mutuncinsa nan, na wuce abina na barsu gaba kaɗan na hadu da Ayaan yana tafiya shi ɗaya. "Tauhid dina!" Juyowa yayi da gudu ya rungume ni, na riko hannunshi muka nufi tantinsu, inda Ijlal take bawa Yaronta Nono, yaran suna zagaye da ita, Ayaat tana cin Abinci Princess tana waya. Amiratul Zaitunah tana zaune a kekenta. Sai Nana A'ishah da take matsa mata kafa. "Sannu da dawainiyya!" Tana d'ago kai hawaye na ga ya zubo mata. Nima hawayen ne ya zubo min. "Ki yi hakuri kin ji, Allah ya nufa zamu samu aikin hajjin gamu nan!" "Kin san yadda na gaji!" "Na sani Allah ya taya ki ai!" "Ban san me zance ba, amma Allah ya taya ni domin kuwa ba iya mutane na ta taimaka min ga Yeemar itama Yaronta ba lafiya! Sai kome ya kwabe min." "Ki yi hakuri gani nan!" Haka na fada mata na tayata rungume Amar ita kuma ta cigaba da bawa Amir Nono, Baba da Faruq aka saka kasancewar ya saka sunan Babanshi Ayaaz. Sai na cigaba da bashi Madara har ta gama bawa Yaron nono shima na karbe shi ta dauki Amar ta gyara mishi kaya ni kuma na bashi madara, ina faɗin.."ruwan garin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya wanke Yaran nan baki ɗaya!" Na kalli Yaran da suka yi wani shar da su. Sai da suka gama muka kara fitowa bakiɗaya zuwa filin Arfa, muna tsaye Yaya yana zuwa ya saka mata lema ni kuma ya mika min, Yaran kuma ya mikawa Nana A'ishah da Princess, suka rufe sauran. Saboda ana zafi, tana ganin shine ta fara kuka tare da kwantar da kanta a kirjinshi. Tana kuka. "Ba gani nan ba!" Ya faɗa yana murmushi, fadawa tayi tana kuka tare da cewa. "Kun bar ni, anan ni ɗaya." "Gamu nan mun zo Wifey!" Ya fada, murmushi nayi na dan matsa kaɗan na basu wurin. "Namiji munafiki, nan yake rawan jikin an koro ku ya ji dadi zai kasance da ke, yanzu ya dawo yana kiranta Wifey!" Kallon Aryaan nayi cikin takaici na ce mishi. "Yaushe ka fara zama munafuki ban sani ba?" "Allah ya baki hakuri, ai na zata gwaninta zan miki, amma sai ki yi." Ya fada yana kallon yadda nake tasbihi da kabbra, can ya ce min. "Anya babu ciki?" Gabana ne ya fadi na juya ina kallon Aryaan. "Kasan Allah zan maka rashin arziki, ka fita idanuna da maganar cikin nan!" Dariya ya fara yana faɗin. "Kina son Yara amma kina tsoron haihuwa." Ban kula shi ba ya ce min. "Mutanen da ya sauke a fada suka gwamnatin Zanzabiran ta saka aka soke visarsa da naki." "Me nayi kuma?" Na tambaye shi. "Kace kashin bayan Mijinki, sun fahimci idan yana tare da ke ba zasu tab'a nasara akansa ba. Ke babu yadda ba ayi don ku rabu ba." "Sai su kara himmae!" Na faɗa ina murmushi, taya zan rabu da Yaya a wannan lokacin bayan tarin Alkhairinsa a gare ni, Alkhairin da yayi min ya hanani hango sharrinsa.

Wunin arfa da muka yi, ya sani jin sauki da sassauci a rayuwata. Washi gari aka tashi da idin babban Sallah. Haka muka yi duk wani ibadar da za'ayi sannan bayan mun yi ibadar da ta dace muka wuce Madina muka yi ibada, daga ya hadamu bakiɗaya muka yi sayayyar tsaraba, kwananmu goma sha bakwai muka dawo, muka bar shi a can yayi aikin da zai yi.

Muna dawowa aka kawo mana abinci daga gidanmu, da fada muka ci a lokacin Ilham ta zo muka sha hira, da goyonta Yarinyar mace gwanin ban sha'awa. Dawowar Yaya ya samu wani irin nutsuwa. Ya koma fada. A hankali na fara fahimtar sauyi daga Matar gidan nan, wato ta zama wata mai sanyi tana amfani da Yarta tana shigowa cikinmu, Ijlal ta fara min magana take cewa. "Yar Malam da alamu wannan karon kishiyarki ta dauko magana tana son ayi wani abu kenan!" Murmushi nayi na ce mata. "Na lokacin Saadiyyah ma ban sha da dadi ba, balle yanxu da take mana kallon makiyanta." Tsarin yadda muka hada kanmu da Ijlal shi kanshi mijin sai da ya yi magana a gaban mu, ya ce mana. "Yadda kuka haɗe kanku nan Ubangiji ya saka na tashi da ku har gidan Aljanna, sai a kara min da huruul a'in!"

Haka yasa shi kanshi yake mana hidima, kamar me ina jin kamar kome ya zo min yadda bana zaton. Ana haka kwatsam sai ga shi ana tuhumar Yaya da wasu abubuwan da mu ba mu zata ba, sannan aka ce dole yayi murabus, tuni Faruq ya shiga lamarin aka yi ta shiga da fita kafin nan an ci zarafin Yaya, haka muka yi ta fama kamar yadda ake jan Yaya a kasa so ake ya amsa laifin yana da hannu a cikin wani mutuwar da aka yi asibitinsa, shi kuma ya ki amincewa har Fada gwamna Ashiru Mahmud Farin ƙasa, ya zo kada ku manta mutumin nan mu muka mara masa baya ya kai ga nasara, sai gashi, wai shine yake niman hanyar da zai ci zarafinmu saboda Alhaji Nafi'u da Rilwanu Yayari sun turo shi.

A cikin aka kawo min Yaya ya fadi, sai da naji kome ya tsaya, a lokacin Faruq da Salim ne a gefenmu, hatta dattawan fadar sarki sun juya mishi baya, haka ya sha jinya ya koma, shawarar da Salim ya kawo min, na samu Faruq da Mai Babbar daki, sai Maluma da Umma, muka tattauna sosai kafin muka yi ta bin wasu daga cikin yan siyasa. Amma babu nasara. Sai dai a lokacin na kara yarda Uwa tana iya mantawa da kanta tayiwa danta addu'a, domin yadda mai babbar daki ta tsaya kai da fata, na kara yarda duk abinda ka ce Allah zai amsa maka, kowacce harshe kowa yayi amfani da shi Allah zai amsa mishi. Na yarda kaf duniya babu kamar Uwar, bayan ita sai Yarka da zaka kula da ita, daga nan sai Matarka da zaka sadaukar mata da kome idan tasan girma da alfanun soyayya ta baka kyautar alkhairin da ka yi mata. A lokacin hankalina a kanshi yake, yayinda Ijlal hankalinta ya koma kan Yaranmu, sai ya zamana kome ya zo da sauki kuma kome yana tafiya yadda ya dace, karfi da Yaji na janyo Ya Abid tsamo-tsamo cikin siyasa, sai dai duk abinda nake da shi yayi rauni, shi kanshi Mai Martaba da yake ya ga uwar Bari tare muka shiga wannan fafatawar, babu hanyar da zamu bi ba a toshe ba, a haka Aryaan ya saka aka yi yanka da sadaka. Kwatsam sai ga wani hatsari da aka yi a garin Abuja, Yaron shugaban kasa ya bugu a kai har da fitar da shi zuwa America, ba sai suka nime Yaya ba, good opportunity ya same shi lokacin Nadiyyah ta kusan haihuwa wai ya tafi da ita Ya ce mata a'a aiki zai ya dawo.. haka ya fita yayi wata guda har ya dawo a cikin private Jet na shugaban kasa. Dad'i kan dad'i kunama ya harbi gyambo, ba sai ga Jami'ayyar da take mulki ta hannun shugaban kasa sun bawa Ya Abid damar zama memba kuma wanda zasu tsayar a matsayin gwamnan Zanzabira, sai dai kash ba kudi.

Lokacin da aka dauka, wanda yayi daidai da Haihuwar Nadiyyah. A lokacin Allah da ikonsa ta sake samun da namiji, bana gari ta haihu. Sai dai zargi ya darsu a ranta ko ni ce nake taba mata Yara, kwanaki biyu da haihuwar na dawo, na ji labarin ta haihu amma bata yarda kowa ya shiga mata ba. Don haka ma shafawa kaina ruwan sanyi ban shiga ba balle ace kai ne, ina hutawa domin na gaji Sosai ba kawai dai ga Nadiyyah cikin kuka da tashin hankali ba.

Zubewa tayi a gabana rungume da jaririnta, hankalina yana kan hisnulmuslim. Rarrafawa tayi gabana. Daya cikin bayanin ta ce mata.."ranki shi dade koma baya!" Kuka ta fashe da shi cikin shashekar take mika min jaririn. "Zunubi na ne yake ƙara ƙarfi a kansu, Zainaba shima mutuwa zai yi" ban amshe shi ba na ban kuma bata amsa ba, kaina a sunkuye tun mutuwar Ayyanah nake kara jin wani irin ciwo a duk lokacin da ka ayi wani mutuwa a cikin gidan tabbas akwai wani abu da yake bayan inuwar Yaranmu haka yasa Ayaan da Ayaad, tare da Ayat suka kasance basu shiga harkan kowa musamman Ayaan wanda ni kaina tsoro yake bani idan yayi wani abun. Tun rasuwar Ayyanah yaron ya koma kamar wanda wani abu yake tattare da shi, idan ka gan shi yana mai wasa shi da Ismaha ne. "Zainaba na tuba taimake ni kada ya narasa shi a karo na biyu!" Sai lokacin na amshi Yaron wannan shine karo na biyu da Nadiyyah take rasa jarirranta duk lokacin da ta haife su basu amsar suna ma suke mutuwa. Fitowar Ayaan da Ismaha a kafad'arshi ya ce min. "Mammy bata danta sun kashe shi, sai dai gaba idan ta kuma samun wani amma wannan shima kamar su Ayyanah sun sadaukar da shi." Sannan ya wuce tare da magen a kafad'arshi. Da gudu ta bishi tare da zubewa a gabanshi. "Ayaan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login