Showing 141001 words to 144000 words out of 157081 words
min cikin har mabiyan ta fado, sannan ta ce mishi. "Bari na toshe ta. Sai ka ɗauke ta kafin ayi jana'izar Mariama an shirya su!" Haka ya ce mata tow. Mai Babbar daki da take can gefe ta amsa wayarta. "Ok Alhamdulillahi, ku rufeta ku mata azabar da ba zata tab'a mantawa." Juyawa nayi ina kallon Mai Babbar daki na ce mata.."sun kamata?" Marin cinyata Maluma tayi tana faɗin.."kina hauka ne ba zaki ji da kanki ba!" Kukan da ban yi ba shi na fasa mata, kuka nake har ta gama gyara min jiki ya dauke ni cak zuwa cikin gidan aka gyara wurin, kasancewar kazantar bata wani zuba a wurin ba. Aka saka kayan kashe karni aka kashe, kafin a gama mata sutura an kawo kasa da duwatsu an rufe swimming pool din. Ana gama sutura aka kawo min ita daki, saboda ina kwance ina hutawa. Amma kuka nake an kira Munirah.
Ana fita da gawar ta tsaya tana faɗin. "Sir meye na gaggawa? Wani lokaci sai ka manta da matsayin aikinka, sai abin cika sanadin mutuwar da kuma me ya dace amma a kai gawar kamar an kashe maciji ne ba a sare kai ba." "Gaskiya kan" inji Mai Martaba Sarkin rikon kwarya, haka aka ɗauki gawar aka wuce da ita asibitin, aka fara bincike kamar akan gidan Salmanu Faris aka fara mutuwa, sannan ta shigo ta min allura har lokacin kuka nake, wanka nayi na gyara jikina ta duba ni tace min. "Fulani babu karuwa, sannan xan saka akawo abin saka bakwaini, ki ci abinci a cikin alluran da na miki akwai na barci." Gyada mata kai nayi, Mai Babbar daki ta bani tea na sha, na kwanta bayan na sha wasu magungunan. Yaran bakiɗaya suka koma daki suka taru, babu me kuka amma kuma zuwa wani lokaci ina barci naji ihun Ayaan yana birgima da ihu, ina son na farka amma na kasa, haka na cigaba da barcin ina jin ihunsa.
Ban farka ba sai karfe goma na dare a lokacin na farka, ina kallon dakin babu kowa sai dumi da yayi ga abin kwantar da babyn an saka shi, sai ya zama bani da wani kuzari, shigowa Umma tayi ta ce min.. "jikina ya bani kin farka!" Hawaye ne ya zubo min, "ki yi hakuri!" "Umma wata goma kenan da na tasa Abba, tauhid kuwa shekara uku da rabi ake nima, Umma shekaran Ayaanah uku da rabi Umma me ta musu? Yarinyar da ko zagi bata iya ba me yasa sai ni? Me yasa Umma?" Na kara fashewa da kuka, "Allah ya kara miki hakuri shi xan ce, ki yi hakuri kowa ya mutu Lokacinsa ne yayi kada ki ce ko ke daya ce kowa ma idan a cikin masarautar nan yake idan kika tab'a shi, ki yi hakuri!"
Asibiti.
Sakamakon binciken gawar, da gawar Marigayi Attahiru, da gawar Alhaji Saddam, duk abu daya ne, daga haka ya fara nufar inda aka rufe Jakadiya da ta gama razana,. "Tuba nake, xan gaya maka gaskiya." Zama yayi yana kallonta, cikin wani irin tsoro da irin kallon da yake mata ta ce mishi. "Wallahi abinda take yi ne aka ce a tab'a itama ta ji yadda kowa yake ji tunda bata ji zafin mutuwar Mahaifinta ba." "Inji waye?"
Kamar zata yi kuka ta ce mishi. "Alhaji Nafi'u!" Ta fada tana zare idanu. "Idan ka samu karya kike fa?" "Kayi min kome ma!" "Ya aka yi kika dauke Mariama?" "Wato ranka shi dade, da na ta ganni kasancewar tasan ni shine ta zo, ni kuma ban yi niyyar kashe ta ba wallahi!" Murmushi yayi irin wanda ake cewa yafi kuka ciwo ya ce mata. "Jakadiya Alhaji Nafi'u baya gari tun kafin zaɓi ya gudu, Kawu Rilwani baya gari kuma babu wani hanyar da zaki same su, Jakadiya gaya min waye ya baki izinin kashe min Yarinya?" Shiru tayi tana zare idanu."dame kika kashe Mariama?" "Wallahi ban san zata musu ba, ihu zata yi shine." "Kuka mata alluran ko? Bayan kun shake mata wuya ta daina motsi don rashin imani sai da kuka karya mata wuya! Jakadiya ni tun ranar da kika hada kai da Alhaji Kabiru da Sallama kuka sace ni,.duk abinda zai faru nasan da hannunki, Jakadiya ina sane ke kika kashe kakana Shehu Yayari da Abbana, me halina suka miki? Alhaji Ahmad Yayari shi ya lalata miki yarki da kike bin jinin Shehu me ahalin Shehu suka miki?" Wani irin kuka take tana marin kanta tana faɗin. "Na sani amma son zuciya ce ka yafe min!"
"Ni ba zan yafe miki ba, kuma ba zan kyale ki ba, ki gaya min wanda ya saka ki aikin ba nasan kin fahimci dukkaninsu abokan gaban masarautar ne shi yasa kike faɗin su suka aiko ki."
"Wallahi ranka ya dade, Salim ne iya gaskiyar kenan! Saboda yana son Matarka Fulani Babba, shi yasa ya bani umarnin na kashe Yaranta bakiɗaya." Kallonta yayi yana murmushi ya ce mata. "Ban yarda ba, ko jikina kunuwa ne kuwa, ki gaya min waye ya saka ki? Sannan me zaku da jinin da kuka diba?" "Wallahi babu abinda za mu yi da shi. Sharrin shaidan ne " Ya sani tana boye wanda ya saka ta ne, mikewa yayi zai fita ya ce mata. "Shi dai shaidan ya shiga uku da mutane kowa yayi abinda yake so sai ya ce shaidan ne. Nan wurin babu wnada ya isa ya shigo amma tabbas idan baki fada ba, zan saka ayi ta gana miki azaba." "Tuba nake amma gaskiya na faɗa!"
"Gwaska dakare!" Da wani irin razana tayi baya tana girgiza kai, yayi murmushi ya ce mata. "Shi ɗaya zai saka ki wannan aikin, baki san ina kallonki ba ne? Har kina cewa sakaran Sarki bai da wani abu sai bin mata, kin yi kuskure zan nuna miki abinda baki sani ba." Ya fita. "Kada ku mata kome ki kyale ta!" Yana fita bai tsaya ko ina ba sai gida, ana yayi sallah Magariba da isha, kafin nan ya saka aka rufe fadar tabbas akwai wani abu a cikin masarautar da yake da alaka da Jakadiya wanda ba iya mutanen waje suka saka ta aiki ba, har da na cikin gidan, wannan abin ya taba shi yasa aka bi bangaren bayi aka fara fitar da abubuwansu, ba a samu kome ba, kasancewar fadar tana da girma sosai. A daren ya saka aka cigaba da shiga cikin tsohuwar fada inda aka taba zama wurin babu kowa sai tsofin kufayi, anan aka cigaba da bincikawa, anan ya ga abin mamaki wani gida da yake can tsakiyar tsohuwar masarautar, bai lalace ba a hankali suka isa. Abin da ya bashi mamaki da al'ajabi, hotunan Yaran da taurarin Yaran, uwa Uba Uwa Uwar Yaran. Da kamancecciniyar taurarin yaran da na Uwar, ita na Ayaanah yafi na sauran na Ayaan yafi na fita, Na Uwarsu yafi nasu. Shi nashi tauraron bai kai nasu ba, jinin Ayaanah da aka diba, ba iya jininta ba, har da wasu abubuwan kamar sassan jikin Yara kanana, tun kwanaki aka gaya mishi amma bai dauki mataki ba. Sai yau da aka tab'a shi yake jin kamar kaf duniya shi ɗaya aka yiwa irin wannan kisan. Ya sauran iyayen suke ji? Ya sauran iyayen suka fuskanci rayuwar Ƴaƴansu da aka kashe? Wato baka tab'a gane kukan wani sai ranar da kukan yazo kanka, wannan ita ce asalin rayuwar da ke yi a kasar nan, babu me jin kukan kowa tunda baa tab'a shi, kowa ma oho!......
[8/27, 5:14 PM] Ramlat Manga41: 54
An fitar da kome na cikin gidan aka kona shi, sannan aka rufe wurin. Suka fita daga fadar gwamnatin Zanzabiran aka kawo maka bincike ya hana ya ce case din cikin gidan, idan na ce muku a lokacin ƙwaƙwalwar Yaya bai tabu ba nayi karya, domin fushi da aikata kome, a lokacin na nime nawa b'acin ran na rasa sai na samu natsuwa da dangana, sati daya aka share makoki yaro ya ci sunan Abdullahi, muna kiranshi da Annur, amma mutuwa Ayaanah ya shige Ni domin sai da na kwanta jinyar wata uku cib, karshe Yaron ma madara aka ci gaba da bashi, domin mutuwar ta dake. Yaya yasa aka dauke Jakadiya daga inda aka ajiye ta. Bamu san inda ya kaita ba, amma tabbas Faruq ya gaya min an dauke ta. A hankali kome ya cigaba da tafiya kamar bai tab'a faruwa ba, a bangaren shi kuwa mulki da aka mishi magana ya ce a rantsar da Mai Bauchi , wato Yakubu Attahiru Shehu Yayari, baya bukatar mulki ai shi babu abinda zai ce da mulki sai godiyar Allah, a hankali ya koma bakin aikinsa na ƙwaƙwalwa, akwai wani abu da ake fada wasu mutanen baka sanin me yake faruwa a rayuwarsu sai ka matsa kusa da su. Yaya ya wani irin sanyi baya ko kazar kazar, haka yasa Nadiyyah ta sauya takunta, tare da nunawa ita fa yanzu ita ce da shi, ni dama damuwata na samu lafiya na rabu da shi.
Watan Abdullahi shida na tafi Maradi, kamar ba zan dawo ba haka yayi ta damuna da waya, kira a kai a kai. Ya bar musu mulkin ya bar musu kome amma har yau basu barshi ba, ya bar musu kome. Amma fa basu kyale shi ba, na fi yarda da cewa mulkin ce take buƙatar shi ba shi yake bukatarta ba, ina can na ji labarin rasuwar Jakadiya, sati biyu da dawowa na ji labarin Kamal Yaron da ya soke Abba, yana asibitin Yaya, Mahfouz Nuru Yayari, ma bai da lafiya. Wani abin da ya bani mamaki shine kusan aka bincika me ya faru zaka samu labarin hauka suke babu ji babu gani.
A wannan lokacin Nadiyyah ta haihu, ta samu d'a namiji. Wayyo murna kamar zata kyautar da kome nata, sai dai fa wani ikon Allah, an wayi gari yaron ya rasu babu kome, kawai aka tashi da mutuwar Yaron. Na tausaya mata domin tun kafin ya cika kwana uku take kiranshi little King, sai gashi ba a je ko ina ba. Yaron ya rasu. Sannan Babu wani alamar da zai nuna maka kashe shi aka yi, Ijlal da hankalinta yake kan karatu bata wani damu can ba. Amma ta shigo ta ce min mu shiga mu mata ta'aziyar rasuwar da aka mata domin ni har mutuwar Ayaanah matar nan bata ce min ashe haka ya faru ba. Na haihu bata ce min ashe kin samu karuwa ba, sai na fahimci yanzu kishinta shine akan me yasa nake haihuwa, wani sabon labari.
Haka da tayi bai bani mamaki ba, domin kafin tayi dubunta sun yi, haka muka shiga madadin mu samu tarban arziki sai muka tsinci zagi da cin mutuncin, Ijlal da bata da hakuri ta ce mata. "Ai da kika ganmu bamu shigo don ke ba sai don Yaya muka shigo, amma tunda mugun nufinki yasa kina kallon kowa kamar yadda kike abu yayi kyau Allah ya kyauta." Dama na rigata fitowa. Ai kuwa mai gidan yana dawowa ta kawo kara da zumar ai zai tsaya kamar da. Sai dai kuma tayi mamaki da ya gaya mata. "Ki saka idanun ki ga yadda Allah zai mai dake, ba kina ganin kamar kowacce a cikinsu zata cutar dake ba, in sha Allah sai kin ga iyakarki kuma abun da suka yi ya b'ata min rai waye ya aiko su ganin jahila irinki har a miki ta'aziya, mahaukaciya jaka dabba wacce bata san ciwon kanta ba. Akwai lokaci ki jira naki sakamakon idan na sake ki, zaki fita ki ce don matana na sake ki, amma na barki da halinki ga mu ga zanzabirawa zaki ji a jikinki."
Yana gama fadar haka ya barta nan cike da mamaki da tsoro ba dai ya fara samun lafiya ba ne.
Kwana uku da rasuwar ta koma Abuja, ita tayi yaji shi kuwa da yake yafita iskanci ya tura mata da sakon saki ɗaya, ta wurin Ubanta, kamar zata yi hauka an yi biyu saura ɗaya, Nadiyyah na barin gidan zaman lafiya da kwanciyar hankali ya wanzu yarta kuwa Ijlal ta kama ta rike, da yake yanzu kowa da kanshi yake babu wnada ya saka a ransa zai cutar da ita, da wannan aka dawo min da Khairat na muka hada su bakiɗaya muka rike, baya fada baya shiga harkan Fada amma har yau idan abu ya faru ina zaune da a kawo lamarin mu tattauna ya sha zuwa ya samu ana tattaunawar kuma ya wuce abinsa, me ya dame shi, mulkin ne baya so. Wani abin da na kara hangowa a lokacin da yake mulkin ya sakarwa kowa a fadar damar yayi yadda yake so, bai takurawa kowa ba kuma ana sake kudi, ko sati biyu da suka wuce sai.da aka kawo korafin Mai Martaba, suka samu Mai Babbar daki ita kuma ta kira ni, aka fara magana anan na fahimci shi fa ya fisu gaskiya ba zai yi ana wasa da dukiya kowa yana azurta kanshi ba. Kuma yadda yayi maganar yasa ni dauko Yaya washi gari na sako shi cikin lamarin, sai yayi shiru na ce mishi. "Ka kyale kowa yayi yadda yake so, sannan ka koma gefe kayi shiru kamar ba kai ka lalata kome ba, maganar gaskiya kayi wani abu domin ka lalata tsarin mulkin nan bakiɗaya." "Ni me zan yi yanzu?" "Ana kwashe kudi kuma yayi magana sun ga laifinsa. Ka san yadda zaka yi." Murmushi yayi ya ce min. "Fulani Babba kudin da yake fita, ana biyan mutanen da aka cutar da su a cikin masarautar nan ne, daga ɓangarorin bayi zuwa sauransu, ban san na fadi haka ba, amma a tsarin da nayi shine duk wani bawa da yake cikin masarautar ana biyanshi daga cikin Baitul Malin masarautar, sannan zai kasance zasu samu ilimi da harkan kula da lafiyarsu, shine dalilin fitar kudaden da yake gani amma babu wani wanda yake cikin kudin masarautar nan ai idanuna yana kan shi ba zan kara barin ayi wani abinda zai wargaza Zanzabira ba kuma in sha Allah."
Sai kuma muka ji kunya ya kama mu. Haka yasa muka mai da hankali akan abinda yake gabanmu. Watan Nadiyyah hudu tayi ta kama kafa tare da rokon a dawo da ita, shi kuwa ya rantse da Allah bai san zancen ba, Mahaifinta yayi zuwa ya kai goma amma bai sami ganin ko mai babbar daki ba, sannan a wani bangare na rayuwarmu yaya ya rage fitinar mace ko Ijlal da bata da goyo Yaya baya damunta, dama ashe abin iskanci ne, sannan yanzu ya damu da ra'ayin kowa da son sanin me ke damunki me kike so, me zaki yi babban shagona kuwa haka ya kara habbaka, lokaci zuwa lokaci ina zuwa wurin Yeemar koda yake itama Mijinta bai cika zama ba, tafiye-tafiye yake yi baya zama sosai.
A gefe guda xan iya cewa Aneesah ta rasa yadda zata raba ni da Ijlal da kowa ita a sonta na zama ni daya ba ni da kowa na zauna kamar mayya, sai Allah yayi ta kunyatatta, domin ranar ina zaune Daulah take gaya min an zo maganar aurenta, sai da aka gama maganar sai magana ya lalace, aka rasa me ya faru. A hankali ta fara fuskantar wani irin masifa a rayuwarta, domin ko yaya ta tsaya da namiji, gobe danginsa zasu zo su roketa ta barshi domin kiri-kiri ranar da ya zo wurinta yana komawa zai fara wani irin fusga da ihu. Za a kashe shi wannan yasa ana zuwa aka yi mata magana ta ce ta fada Aurensa shi kenan, maza uku suka suna fuskarta haka, a cikinsu har da mijin da ta aura na farko uban Yaranta, shi kan sai da suka dangana da asibiti, da farko abin da ya faru bai dami Mai Babbar daki ba, sai da ya fada kan tsohon mijinta anan hankalinta ya tashi, aka fara zargin ko ta fara maita, lamarin Babban gida ai kuwa maganar yayi ta yawo har ta kai bata fita. Ina kwance Yaya ya shigo ya zauna gefena yayi shiru kafin ya ce min.."Zainaba!" Tashi zaune nayi ina kallonshi, murmushi yayi wanda na hango damuwa da karfin hali ya ce min. "Magana zamu yi da ke na fahimtar juna!" Zama nayi da kyau kafin na kalle shi. Rike hannuna yayi da kyau sannan ya ce min. "Lokacin rasuwar Ayaanah nake jin wani al'amarin." Shiru nayi ina kallonshi, a hankali yake warware min maganar, ya kara da cewa. "Yanzu Aneesah take kara gaya min." Murmushi nayi na ce mishi.."Yanzu wani mataki zaka ɗauka? Zaka zauna da ni ne ko zaka rabu da ni!" Murmushi yayi yana kallona, ya ce min. "Bana jin haka zai faru, domin kuwa nasan abinda yake faruwa zuwa yanzu bana jin zan iya rabuwa da mace irinki, sannan uwar Yarana, macen da ba kowani namiji ba zai samu ba."
Murmushi nayi na ce mishi , "lokacin da aka sace ni, Salim ya kubutar da ni, nayi shiru ne domin na nuna mishi ban san yana yi ba, daga lokacin da na san yana yi zan cutar da rayuwarshi. Salim yayi abinda ba zaka iya ba, har a kwanan gobe yana kare ni da Yarana."
A hankali na dauko table pad dina na kunna, na mika mishi. Sako ne ta email da aka turo min, daga cikin har tsarin da ake shirin yi na tsige Mai Martaba, tare da wasu abubuwan da ake shirin yi da goyan bayan gwamnatin Zanzabira, na ce mishi. "Salim ya turo