Showing 156001 words to 157081 words out of 157081 words
koma fada aka cigaba da mulki, a gefe guda kuwa Aryaan yana lalata duk wani auren da ya fara nima, Namamajo kawai.
Aneesah kuwa sai da aka dangana ya ga asibitin mahaukata itama, amma lafiyarta lau, ganin ba zata daina ba dan uwanta yayi ya sakawa ana bata magani, kan ya kara kuncewa, Yarta daya ce Uban da danginsa sun rike ta gam,cikin so da kauna. Dama sun fara samun matsala ne lokacin da ta ce ba zata shayar da Yarinyar ba. Haka kuma kannen Marigayi Attahiru Shehu Yayari, Hajiya Malika da Nuratu an hukunta su da laifin kisan kai domin har dasu aka samu da laifin kashe Alhaji Attahiru Shehu Yayari, Allah ya kyauta
Mommy Turai an mai da ita cikinsu Maluma, ta warke. Kamar ba ita ba sai niman yafiyar Allah kudin da take da shi ta haɗa ta saka aka yi ta bibiyar Iyayen Yaran da ta lalata tana biyansu wasu abubuwan.
Iram ta haifi danta namiji aka saka mishi Tauhid, haka rayuwar ya cigaba da haɓaka, Yeemar da Faruq yaransu uku. Ni kuwa nice Garken Yara, domin Yara biyar ne da ni, Ijlal hudu da cikin na biyar. Nadiyyah daya itama, Mai Babbar daki ta saka aka yi ta kawo mata maganin gargajiya, gashi nan dai an dace kaɗan amma idan ciwon ta tashi kamar ba zata rayu ba. A hankali wata rana muka wayi gari Nadiyyah ta rasu, bayan Jinyar da ta sha, zamu iya cewa jinya ya ƙare,
Ya Abid ya bawa Fada da kowa na gefena kariya, sannan sai da ya cika shekaru takwas ya sauka, a lokacin aka bawa Fadil damar mataimakin Gwamnan da aka sake sabuwar gwamnati.
Bakiɗaya mu Yawan abokai hudu muka sake haɗe kanmu, cigaba da kwanciyar hankali, haɓakar tattalin arzikin abokai hudu ya sake shahara, Khalisah ta dawo haka Saimah itama ba lafiya Cancer gaba ya kamata, haka take ta jinya.
Hajiya Lailah kuwa ta je sake sakawa a tab'a Tauhid karami aka kamata, a ta ga hauka domin Yaya Nuraim saka rigarshi ta lauya yayi aka ce ba za a shigar da shi ba, sai Khalisah ce ta tsaya a case din kowa ya amshi laifinsa.
A gidan Yarin Gwaska ya kashe Alhaji Nafi'u, shima kuma Goga ya rufe tarihinsa, irinsu suka rayu masifa ce a bayan kasa sai komai ya koma kamar tarihi.
****
Bayan shekaru goma sha biyar, ranar da muke murnar Anniversary na aurenmu, Yan mata uku Sa'adiyyah wacce muke kira da Princess har yau, sai Nana Aisha wacce ake kira da Nancy, sai Ayaat wato Zainaba Takwaran Hajjah wacce ta dawo girma ya cimmata, kawarta Tarasulu ta rasu itama. Tana nan da yake an gyara kuruciyar tun farko an wanke ta da Ibada da Addini tare da Alkur'ani, sai lamarin yazo mata da sauki babu dogon rikicin tsofa.
Sai yan autana Ummina da Ummana wato Mai sunan Maluma Hajar muna kiranta da Amna sai Yar uwarta muna kiranta da Amani, Asma'u da Hajara. Sultanah tana can gefen Mai Babbar daki, sai yan mazan Ayaan tare da Ayaaz, suna turo Aunty Zaitunah. Sai yan biyun Ijlal Amir da Amar, Sai Yaran Faruq da Yeemar. Biki aka yi fa sosai, na cika shekaru sha biyar dinmu, haka ayi ta zoyalatar mu, wai mun yi asiri mun hana shi aure, na ce eh kuma haka ne, domin kuwa Aryaan muka saka ya shafa mishi bakin jinin yan mata, idan muka bi na Yaya sai ya kwaso mana ciwo bai damu ba, Alhamdulillahi shima gefe daya bai so kanshi ba yana gudun tashin hankali da yadda aka sha gwagwarmayar.
Yaranmu kansu a hade, Aryaan da ya gama secondry, kusan a tare suka gama da su Princess, bana zasu fara jami'a. Dangin Nady suna zuwa ganin princess don ma Uban baya son tana shiga wai kada su lalata mishi Yarshi, Allah sai ya taimaka yaran suna tsaye akan tafarkin addinin Muslunci. Itama Ijlal shekaru biyar da suka wuce ta sauke Alqur'ani tare da ajiye kwalin master din ta a shekara biyu da saukarta idan muka tuna baya sai mu yi ta dariya muna godewa Allah da ya bar mu da imaninmu.
Allah ya rufa mana asiri kuma ya budewa mijinmu kofar samu, Alhamdulillahi. A fada kuwa kowani gida anyi replace da yaron gidan.
Salim shima yana haka aka tura shi kasar Demark da iyalinsa, bai boye min yadda ya so ni, na yi mishi fatan ya dace da wacce ta fini a duk lokacin da na tuna nayi rashi nayi kuka a rayuwata sai na ga kamar mafarki nake, Amma Alhamdulillahi kome ya zama tarihi, kafin yaran su fara jami'a na kai su, suka ga Baba titi. Murmushi yayi ya musu nasiha ya ce su dauki darasi a rayuwata. Kafin muka musu sallama. Ayaan yana da matuƙar zurfin ciki bai cika gaya min kome ba kamar yadda yake gayawa Ijlal karshe sai na fahimci mutumin ta ne gulmarmu ni da Ubansa tare suke yi nima na tattara sauran yaran na rike ta je na barta da aljanin danta.
Dafa kafadata yayi yana faɗin. "Tunanin na meye haka?" Murmushi nayi na ce mishi. "Ba kome Yaya kawai ina mamakin yadda kome ya zama tarihi kamar bai faru ba, shi kanshi Yakubu an bashi jakadar Nigeria a Russia." Sumbatar goshina yayi yana faɗin. "Alhamdulillahi da baki fita a rayuwata ba, da al'amarin yafi haka lalacewa."
Rungume shi nayi ina faɗin. "Kowacce rayuwa matuƙar an gina ta domin Allah yana da happy ending, na gode da samunka a rayuwata........
*Alhamdulillahi Ubangiji ya sakawa kowa da alkhairi ban yi tsammanin zan iya kammala Royal politics a cikin wannan lokacin ba, Amma sai gashi Allah da ikonsa ya bani damar gamawa cikin ikonsa da buwayarsa ayi hakuri labarin ya zo karshe masu ganin bana sauri ko na tsaya a wuri guda, da sauransu ku yi hakuri yau kan an gama da yardan Allah na gode sosai Allah ya bar kauna da zumunci tammat bi hamadillah na gode sosai na gode sosai sai kun ƙara ji na bye*
Taku har kullum.
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambun shagali 😹🤣😏
Na fara
May /5/2025
Na gama
August 31//2025
Alhamdulillahi