Showing 108001 words to 111000 words out of 157081 words

Chapter 37 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

37

ba su nima su sha, sai suka ga idan suka ki basu ruwan zasu hallaka sai suka bud'a kasar jirgin karshe suka sha ruwan kuma ruwan ta hallaka su, bakiɗaya da na sama da na kasan, Allah bai tab'a buga misali ba tare da ya fito da hikimar sakon ba, idan kika ce da dambe ko kuka zaki kwaci kanki, kiyi duba da wahalar da Abba ya sha akanki? Na farko ya sadaukar da kome na shi domin ya cikawa abokinsa muradinsa, na biyu ya samar miki abinda ake bukata a cikin fada,na uku ya barki da sauran mutanen kirki a gefenki domin ki rayu kuma ki tsaya a inda kike, wannan hikimar ta Allah da ya fitar na masu jirgin ruwa yana nufi duk inda aka zauna kada na sama su kasance masu son kansu, kada ki yi tsammanin babu wnada ya san kome hatta motsinki yana yawo a gari, ki yi ƙoƙarin ganin kin dauke kanki!" Ta fada min, wani irin abu na ji ya tsaya min. "Me yasa kika faɗa min hakan?" Hawaye na zuba min, da na kasa rike shi. "Saboda kishiyoyinki suna ƙoƙarin kai ƙararki."

"Bari na gyara miki wani abu, ita ya sake ta tun aurensu, sannan bata tare da shi tun da."

Mika min takardar tayi tana faɗin. "Wannan shine dalilin zuwana, a office dinmu aka turo, ba wai ina nufi ki sarara musu ba ne, amma ki yi aiki da hankali yafi aiki agogo." Sunkuyar da kai nayi tare da d'ago kai nayi sama da kaina ina jin wani irin yanayi, ban san yadda xan fada ba. Murmushi nayi na ce mata. "Me suke so?" "Suna son a fitar da Sarki Salmanu Faris zuwa asibiti ne!" "Ba zan bada shi ba, ba zai fita ba duk sati ana zuwa ana duba shi, idan na basu shi ban san me.." dafa hannuna yayi yana gyada min kai, yana kallon yadda nake razane. "Ki basu shi!" "Aryan!" "Gasu ga shi mana, ce miki Shago baya tare da shi ne? Ke kanki wani lokaci idan kika yi wani abu an gaya miki baya tare da ne?" Murmushi yayi yana faɗin, "Tun daga lokacin da ya kwanta yake tare da ke. Ba zai tab'a a cutar dake ba, shi yasa ya bari yake kwance domin zaki iya abinda yake yi! Amma maganar fita da shi daga Zanzabira shine asalin kuskuren da zasu yi, domin zasu kashe shi." Damke hannunsa nayi. "Ka taimaka min kada su yi nasara!" "In sha Allah ba zasu yi ba!" Kallona Ya Nuraim yake. "Zainaba da wa kike magana?" Juyawa nayi na kalle shi, ashe Aryan ba a jikin Ayaan yazo ba, na juya ina kallonsu. "Aryaan ne!" "Waye shi?" Hadiye yawu nayi domin nasan shi bai tab'a sanin wannan al'amarin ba, ba iya shi ba har su Maluma Abba ne ya sani. Cizon lips dina nayi a matuƙar gajiye yana min magana a karo na biyu na dafe goshina kafin na ce mishi. "Hey!" Kallona yayi cikin mamaki. "Aljani na ne, akwia matsala ne bayan wannan?" Yadda nayi maganar ina kure shi da idanu. Murmushi yayi tare da riko hannuna yana faɗin. "Ina fatan bai saka ki kuka?" Kura mishi idanu nayi, tare da gyada mishi kai. "Bai tab'a ba!" Na fada ina cizon lips dina, "when kuke tare?" "Tun haihuwarsu Ayyanah!" Murmushi yayi ya ce min. "Shi kenan, kina yawan azkar kada ya saka ki sauka akan hanya." "Daga babban gida yake shima zuri'ar Malamai ne!" Na fada tare da juya kaina cikin takaici na ce mishi. "Kada ka damu ba zai tab'a cutar da ni ba, yana da kirki sannan danginsa suna da kyakyawar nasaba da ahalin family Abubakar Mustapha Modibbo Estate! Mahaifiyarshi Umma Zulja Mahaifinsa Sarkin Mallamai Kisra, Sheikh Imran." Kallona Aryan yake yana mamaki kafin yayi samu zarafin magana na cigaba da cewa. "Shi din renon Ummu Aiman ce, ba zai iya cutar da kowa duk da basu da tabbas amma idan har jinin Umma Zuljah ce ba zai iya cutar da bil adam ba." Ganin yadda nake bayani sai Aryaan yayi ta murmushi, yana faɗin. "Ashe kin san ni kike min wani rashin mutunci." Ya tashi da wani uban tsalle har cikin kaina nake jin ihun da tsallen, na dafe kaina da yake min wani irin ciwo. Saboda karfin abinda yake yi. Jini ne ya zubo min daga hancina da kunnena. Cak ya tsaya tare da isowa kama kunnena da kaina ya damke da wani irin ƙarfi, a hankali na zube a kujeran na fara barci.

Hankalin Nuraim ya tashi ganin halin da take ciki, murmushi Abidah tayi tana faɗin. A ranta. *Kome yayi yanzu zaki fahimci yadda kowa yake cutuwa da abinda kike aikata* "Abidah maza mu kaita asibiti!" Ayaan da ya fito daga dakin wasan su ya ce mishi. "Babu inda zaku da ita, zata watsa ke ka karanta mata Fatiha da suratul Yasin yana magani!" "Kai Yaro!" Da wani irin murya ya ce mata. "Ki min shiru Bakar munafuka! Me kika bata a takardan nan......

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 37

Ban san cewa wannan aikin da nayi ya kara jefa Abba cikin tashin hankali ba, sai da aka fara tuhumar Abba da wasu abubuwan da ni kaina na rud'e, anan wurin sai ya zama nayi amai na lashe ne. Domin kuwa kafin Allah ya fitar da Abba sai da na cire rai, ba don kome nayi haka ba sai don masu laifi zasu motsa sai kuka ayi dace wanda ya fara motsawa Alhaji Nafi'u, haka yasa kafin yayi wani yunkuri Malam Barau yayi hira da wata gidan Jarida, wanda ya fada musu asalin abinda ya faru. Ban tab'a wanin haka zai faru ba, sannan Alhaji Nafi'u ya motsa ne yayi wasu magaganu a gidan tv, na Zanzabira inda ya ce ai ya fada shi ba zai iya kashe abokinsa na Yarinta ba, duk da banbanci na ra'ayin da suke da shi da wasu abubuwan da suka samu a rayuwa shi bai nufin kowa da sharri, wannan abin ya min ciwo, haka yasa Malam Barau ya fito yayi magana inda ya cewa Al'umma ya kamata su daina zaunar maganar kowa domin lokaci yakure da za a yaudare su da maganar kisan Alhaji Saddam da Mai Martaba, ya san cewa next victim yana nan very close, don haka mutane su daina yanke hukunci da abinda basu da sani a kai, sannan ya ce idan ana maganar mutuwar Alhaji Saddam ne a jikin motar Alhaji Saddam akwai ajiyar camera ya ajiye shi tun daga lokacin da abin ya faru ya ajiye, a hankali ya fitar da Camera aka shiga duba abubuwan da ya faruwa wannan abin yasa ko minti goma ba ayi ba aka tafi gidan Alhaji Nafi'u aka saka nishi ta kunkumi sannan Malam Barau ya kara da cewa. Ba asalin dalilin fadar ba kenan, Alhaji Nafi'u na sadaukar da Yarshi Iman ga dodon tsafi wanda haka ya tsorata Alhaji Saddam.

Take aka dakatar da labaran sannan bar zancen Yayinda Malam Junaid ya ji ciwo domin abinda suke ta boyewa kenan, a lokacin da suka rabu bawai don abinda Khalifa yayi ba ne, a'a Iman ta tafi wurin Alhaji Saddam ta gaya mishi yayi wani abu akan lamarinta tana jin babanta yana wani abu da bai dace ba, a cikin kuwa har da shigowa ɗakinta cikin cikin dare yana wasu abubuwan ba kaya, a lokacin hankalinsa ya tashi sannan shima ya samu Malam Junaid da maganar, shi kuma ya samu Mai Martaba da al'amarin sai mutumin nan ya kafe da cewa sharri yarinyar tayi mishi, dama kuma abubuwan da suke faruwa lokaci zuwa lokaci yasa an fara zarginsa. Haka yasa bayan sun gama magana ya tashi ya zazzage su da cin mutuncinsu, kasancewar su abokai na amana ne, haka yasa bakiɗaya suka boye abinda ya faru musamman Malam Junaid da Mai Martaba, amma ga Alhaji Saddam yayi hiran da makusantar shi, kafin rasuwar Alhaji Saddam aka nime Iman aka rasa sai cewa tayi kada a nime ta, abokansa sun san cewa akwai abinda ya faru, duk da wannan abin basu tab'a cire rai zai dawo hanya. Saboda suna da kyakyawar zato akan shi, amma har yau Malam Junaid bai cire rai da Alhaji Nafi'u zai dawo hanya ba, bai tab'a munanna masa zato ba.

**

Tunda Allah ya kawo mafita, gida na je na gaida Abba. Na zauna a gefenshi yana shafa kaina yana gwiwarshi. Ina shashekar kuka. A hankali yake shafa kaina yana faɗin. "Ki yi kuka yanzu, ki yi hakuri gaba, Zainaba tunda kika samu hujjoji masu kyau, ina ga lokaci yayi da sallama miki kome, Zainaba ko yanzu na koma ga Allah na cika alƙawarin da na daukawa Attahiru. Alhamdulillahi na sauke kaso saba'in cikin dari, yau ina ji a jikina kodayaushe mutuwa zata riske ni, Alhamdulillahi Alhamdulillahi Alhamdulillahii, Alhamdulillahi." Murmushi ya sake yana mai d'ago kaina ya ce min."kukan na mene ne? Ba gani ba! Ai babu abinda zai kara faruwa in sha Allah."

"Abba tsoro nake ji." Shafa kaina yayi yana faɗin. "Ba abinda zai faru sai ikon Allah. Tsoro makiyinki ne daga lokacin da kika fara jin tsoron tow daga nan kowa zai tsaya kuma kowa zai ta razana ki, da dan kwaikwayo da dan akuya da dan tinkiya da al'adu zasu ta razana ki, daga nan zaki fara gudu kina noman hanyar gudu, zasu ta min nimanki ruwa ajalo sannan zasu ta binki kina gudu, ban san yadda zaki fahimta ba, amma tabbas rayuwarki zata zama abin boyawa da gudu, Fada kika shiga kuma duk abinda yake faruwa ana sanar dake, saboda Mijinki da zai yi aikin tun kafin ya kwanta ya gaza. Gaya min zaki tsaya ne su razana ki saboda kina tsoro ko zaki bari a cigaba da zalinci ne? Idanun duniya take kanki kowa yana kanki nauyin al'umma yana kanki, kowa yana kallonki ya zaki ji idan yau wayi gari bana raye ba zaki yi? Zaki cigaba da kuka ne ko zaki zauna kina Jiran wani ya gaya miki yadda zaki yi? Ina miki nasiha da ki tsaya da kafarki, domin nimawa kanki mafita da Yaranki tare da mijinki, idan kika gaza zasu zo har gida sun kashe Mijinki, idan kika tsaya da kafarki zasu ji tsoron zuwa inda kike, zaki wayi gari ke daya ce gayya. A sauran wuraren mata basu da karfinki why not ki hada karfin wadancan da naki domin zama mace da zata tsaya da kafarta, idan har kika tsaya da kafarki zai matuƙar wahala wani yayi ihu a gabanki sai dai yayi a bayanki, Zainaba ko bana raye na saya miki jama'ar fada ga shi nan." Ya dauko min wasu takardu na musamman. Ya mika min, ya sauke ajiyar zuciya kafin ya cigaba da cewa. "Na sallame ki. Ki sani bayan ni akwai Abid zai iya tsaya miki amma kada ku rayu baki da namiji da zai baki kariya, ko ana hamaza hamata kada ki sake baki tsaya da kafarki ba, domin cikin duniyar da kike a yanzu daga ni sai Umar muke tare da ke, idan bana raye Maryamu tana tare da Umar suna tare ke, shi yasa nake son kada kiyi kuka kada a kawo labarin mutuwata ki yi kuka domin ta haka ne zasu fahimci gundarin nasarar da suka yi akanki, idan kika ji kuka ki shiga daki ko rufe ko ina ki kunna ruwa a ban daki , ki zauna ki yi kuka sosai zaki samu sassauci. Ni ina ji a jikina lokacina ya kusa ina ji kamar xan tafi nan da ba da jimawa ba.

Wato ban tab'a jimawa a gida irin na yau ba, domin mun dauki lokaci muna hira da Abba kuma na shiga damuwa amma daga baya da kanshi yayi ta bani dariya, har na manta na nuna mishi nasarar da na samu, da zan tafi har waje ya rako ni. Yana tsaye nima haka hira muke, har Ya Abid ya shigo budar bakinsa ya ce mishi. "Tauhid ka shigo, shiga ka jirani ai nima zan rike hannunka mu tafi." Zuba mishi idanun muka yi na ce mishi. "Abba Tauhid kuwa?" "Au Abid zance, don tauhid ne a raina." "To Abba xan tafi!" "To Allah ya tashe mu lafiya!" Ya fada yana kallona, "Amin Ya Allah!" Na wuce zan shiga mota ya ce min. "Jiya kin ga sakona ta E-mail?" "Eh na gani Abba, sannan na tura shi zuwa ga Faruq zai san yadda za ayi da kome."

"Shi kenan Allah ya miki albarka, ya albarkaci rayuwarki!" Ya fada yana kallona, shiga cikin motan nayi ya ce min. "Kin san yadda kome ya faru ki rike Allah kada yi wasa da Sallah, domin kiyayye sallah yana kare ka daga aikata kaba'irai manya da kanana. Kada ayi wasa da azkar safe da maraici, Allah yana tare dake fa kada ki yi wasa da sadaka ko ta ruwa ce ana rabawa sadaka."

"In sha Allah! Na gode sosai Abba!" Na shiga motar takowa yayi ya zuwa wurin motar ya ce min. "Allah ka so Zainab, Ya Allah ka so baiwarka, Ya Allah kasa bayinka na gari su so Zainab, Ya Allah ka bawa Zainab sa'a da nasara, Ya Allah ka kare Zainab daga miyagu mutane da miyagun shaidanu, Ya Allah ga Zainab ka bata nasara da sa'a!" "Amin Ya Allah, Abba dare yana yi je ka kwanta ka huta."

Dakyar muka rabu da shi, nima da na fita sai na tsaya na dawo cikin gidan yana tafiya na ce mishi. "Abbana!" Juyowa nayi na isa wurinshi da gudu na fada jikinshi ina jin wani irin kuka na zuwa min. "Abba na gode sosai!" "Allah ya miki albarka!" Da kanshi ya kai ni wurin motana, na shiga ya ce min, "je ki Allah ya tsaya a gabanki da bayanki ya baki kariya gabar da yamma. Idan har ban zalunci kowa in sha Allah babu me cutar dake, sai Abinda Allah ya ƙaddara miki!" Haka na bar gidan ina kuka, ban bar unguwar ba na kira shi. Yana ɗauka nace mishi.."Abba ina kewarka!" "To ba gashi kin kira ni!" Har na bar unguwar na kusan wuce g.r.a, muna waya kusan har na isa gida, na kifa kaina akan motar ina jin wani irin kuka yana zuwa min. A lokacin na samu Mai Bauchi da Salim, Yaran suka zo da gudu suka rungume ni. "Ina kika je haka? Tun tuni kin bar Yara a gidan nan bayan kin san gidan ba wani safe!" Inji Salim, ya fada yana wani haɗe rai. Kaina a sunkuye na ce mishi, "na je wurin Abbana ne!" Sai kuma yayi shiru, haka na shiga gidan suna bin bayana. Har dakin da Yaya yake na bude musu, suka shiga cikin suna mishi fatan samun lafiya. Ina tsaye ina jin yadda Mai Bauchi yake mishi, fitowa nayi na koma dakina. Can ciki na shiga ina kuka, haka na zauna nayi kuka sosai, kiran sallah Magariba, domin kiran sallah, ban daki na shiga nayi alola sannan na fito, ina shimfida abin sallah, sai da nayi idar kafin na fito waje, na samu sun tafi sallah, sai Ayaan da suke cin abincin na ga Princess tana bakin kofarsu itama Nana Aisha, yadda na fahimci Yaran Babansu suke son gani. Kiran Yaran nayi da hannuna, suka sauko da sauri na saka su a gaba har da su Ayaanah, muka shiga dakin. "Daddy!" Princess ta kira sunanshi, a hankali Ayaan ya bar dakin ina ga ba shi bane, suna tsaye sai kallon Uban suke Nana Aisha ta rike hannuna ta ce min. "Mammy daddy yana barci ne?" Sai na ji hawaye ya cika min idanu. "Eh My Princess!" Na fada ina mai durkusawa a gabanta, Saadiyyah ta ce min. "Mammy I miss daddy alot!" Mai da hawayen da yake zuba min nayi nace musu. "Me too I miss him!" Ina kallon shi, bakiɗaya zuciya tana gaya min wannan shine kallon ƙarshen da xan mishi domin ina ji kamar xan rasa shi a kowani lokaci. "Nana!" Muryan Ijlal da ya ratso dakin na juya ina kallonta. Shigowa tayi tana ƙoƙarin riko hannun Yarinyar ta koma bayana. Sake fusata tayi zata riko hannun yar na rike hannunta. "Ki je zan kawo miki ita!" Yadda na rike hannunta. A hankali nake jin wani abu me karfi kura mata idanu nayi da jini a hannunta. Da fuskartar. "Zan kawo ta ki kawo Amiratul Zaitunah ta zo ta ganshi." Gyada kai tayi sannan ta fita daga dakin can sai gata da yarinyar, ta kawo ta tana ganin Uban ta fara buga kirjinta. "Da....da....da....da ....da..daa.dah" ta daki kirjinta ta juya kanta, ta rasa inda zata cusa kanta don murna tana hawaye, Yarinyar tana kewarshi. Idan Ummi first love dinsa ce, Amirah ita ce second love dinsa ce. Son Yarinyar rubutacciyar kauna ce a zuciyarshi, ɗaukarta nayi na nufe shi na hada hannunsa da nata, wani irin zillo take tana faɗin. "Daaada!" Mikawa Uwarta nayi ita, naki yarda mu hada idanun da kowa a dakin na fito nasa Rebecca ta rufe kofar idan suka fito domin dukkanmu muna dakin ne, ita kanta da take security hawaye take sharewa tana faɗin. "Allah ya tashi kafad'arshi Queen!" Suna gama ganinsa suka fito, tare da rufe kofar dakin. A daki na samu Aryan yana ganina ya juya min baya. Zama nayi a bakin gado, yadda muka gan shi ya kara karya mana zuciya. Haka nayi sallah isha, na dauki Alqur'ani ina karantawa ya zo ya zauna a gefena. "Kiyi hakuri! Kiyi kuka ki yi kuka ki yi kuka yanzu, gobe sai ki shanye kukan ya zame miki makamin yakar kowa zan koma wurin Ummina, amma ina tare da ku Kamar yadda Inuwarku take haɗe da ku. " Gyada kai nayi. "Na gode sosai Aryan ka gaida Ummarka!"

"Zata ji!" Daga haka ya kwanta barci ya dauke shi, haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login