Showing 3001 words to 6000 words out of 157081 words
ba? Dalla fita min a gida!" Jiki a sanyayye ya fara tafiya, har ya isa bakin kofar ya ce mata. "Ni dai ta koma ɗakinta ta je can mu yi renon kayanmu yawwa!" "Ta je ku kashe ta kai da matanka? Ai ka ga Zainab a gidanka Tsautsayi ne da ikon Allah, amma ta gama zaman aure da kai, jira nake ta haihu ka sawwake mata gari da yawa mayye baya cin kansa, ka je can na gaji da watsa min kasa da kake a idanuna, na gaji da kunyanta ni da kake. Ban san kuskuren da nayi da nake jin wani irin ciwo akan aurenka da Zainaba ba, zaka iya fita ko na dauke ta a dakin.?" Yadda tayi maganar yasa shi juyawa ya kuma kallona, nima kaina a sunkuye yake na d'ago muka haɗa idanu, watsa min harara yayi ni kuwa na murgud'a mishi baki, haka kawai zai ga laifina.
"Ke kuma da yake baki san ciwon kanki , zaki zauna ya saka ki a gaba ban da Allah yasa wannan magen ba ordinary magen da muka saba da su bane, zuwarta yasa na ji a jikina yana can ya titsiye ki kenan, kada na ji kada na gani kin bashi fuska domin wallahi ban isa ba, gara ki nuna mishi kema Mutum ce idan kika sake kika bani kunya tow wallahi babu ruwana, kuma ba zaki koma dakinki ba domin a yanzu rayuwarki da abin cikinki zasu iya fuskarta hatsari, don Allah ki rufa min asiri ki bani goyan bayan gasa shi yadda ko da wasa ba zai kara cewa ki tafi ba!" Gyada mata kai nayi. Ta saka kai ta fita daga dakin.
Washi gari bayan sallah asuba, ta nufi gidan mu,ni daya na ci wannan darajar yadda mai babbar daki take ajiye kome tayi a kaina shi kaɗai ya isa ya janyo min bakin ciki, kowacce mace iyayenta suna kama kafa ne, amma daga mai babbar daki har marigayi ban san yadda suka ɗauki iyayena da daraja ba, sannan shima yayi matuƙar kokarin wurin wanke Abba da zargin da ake mishi na kisan abokansa, tuwo nake ci, tunda na samu sauqin laulayi na rufawa kaina asiri nake son tuwo,
***
Shiru parlourn ya ɗauka, mai babbar daki ta ce musu. "Na san anyi muku laifi amma fitar da ita daga gidan kamar hatsari ne, asalima bana son ta bar gidan. Don Allah ku min hakuri da abinda ya faru, nima uwa ce amma bana son tashin hankalin da ake yi a cikin gidan, nasan halinsa da a ce Zainab ce kaɗai haka ba zai faru ba!" "Haba babu kome wallahi Allah ya sa haka shi ne abin da ya fi alkhairi. Malam ya zamu yi da Hajja da zo jiya?" Shiru Malam yayi ya ce mata. "Ya kuwa za ayi dama waye ta gaya muku zan bar Hajja zuwa gidan Salmanu Faris? Ai kusan kome ma zai faru Hajja bata da hakuri zasu ta kai ruwa rana da ita, don haka na ji daɗin haka da ya faru, ba sai wani ya je ya zauna ba. Zainab zata iya kula da kanta."
"Amma a kirata a mata bayani yadda zata fahimta ba tare da an samu matsala da ita ba." Inji Maluma, Kiran Nuraim Umma tayi ta ce mishi. "Duba mana Hajja ta zo su gaisa da Mai Babbar daki!" Don haka kaɗai zai saka ba za'a samu matsala. "A'a bari mu, muje mata." Haka Mai Babbar daki ta fada suka fito zuwa dakin Hajja, wanda ya sha gyara kamar ba gobe, da sallama suka shiga, tana lazimi ne, sai da ta kai karshen calbin ta sha addu'a, ta kalle shi da kyau tana faɗin. "Kamar Mariama!" "Ni ce Hajja." Mai Babbar daki ta fada tana murmushi, itama gyara zama tayi tana faɗin. "Ikon Allah sannu da zuwa bakuwar safiya, ina mutanen gidan suke da takwara tare da mijinmu, ya kuma nauyin jikin nata. Ai kin ga wancan fanti garwan can, na dibo saiwowi da sauran magani ne na dauri, (hadin itace ne da mutanen da suke bawa mace mai ciki da kuma yaro har zuwa bayan ta haihu, yana da karfi sosai domin kamar riga-kafi ce a Hausan ce) "kin san abinka da cikin fari tana bukatar kulawa daga ita har cikin shi yasa Junaidu yana gaya min na shuri ta kalmi nabi zawuyar da suke cikin Maradi na biya sadaka ayi sauka akan ita da abin cikin da kuma abinda zata haifa, sannan na gayawa Tarasulu zata hada mana itacce a bata saboda kambun baka da na idanu, kin san duniya ta lalace da mayyu da masu kambun baka."
"Dama abin da ya kawo ni kenan, an samu sab'ani tsakanin takwararki da shi mijin naku, da sauran matan abu babu dad'i har ta kai ga saki!" Wani dafe kirjin da Hajja tayi zaka rantse da Allah ita ce aka saka bafa ita ba. Wata salatin da ta sake yasa duk suka mike tsaye yadda ta mike tsaye ta rikice ta shiga dimuwa da tashin hankali. "laahalilallahu Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama tasilima, yanzu Salamanun faransa ya sake takwarata? Yanzu taya zan ji da wannan lukutar masifar? Bayan nabi yan uwa da dangi na gama gayawa su, zan je zaman jiran Haihuwar takwara? Gaskiya wannan cin amanar bai yi ba, wani dan iskan ne ya raba tsakanin amincin da yake tsakanin kifi da ruwa? Hatta Tarasulu ba gaya mata cewa idan zata zo gidan ta shirya kanta tsaye idan wani ya tambaye ta ina zata ta ce musu Fulani Babba jikarta ne, shi ne zai sake min ita ya janyo min abin kunya da abin fada a dangi. Kaf garin maradi babu inda ba aji labarin cikin nan ba, hatta shi salamunu faransa sai da na saka akayi ta mishi rokon Allah Ubangiji ya ƙare shi, ni zai watsawa kasa a idanun. Lallai dan mutum ka ganshi ka bar shi a inda yake, tunda Salamanun faransa ya saki takawara na tabbatar ba banza ba, kin ga Mai babbar daki, ki kyale ni na ganshi waɗannan guduma-guduman matan nashi ba zasu kyale shi haka. Ai ni ko lokacin da na auri Malam Gobir sai da aka yi ta faffta rigima da wasu matan ni kuwa nayi tsaye bisa gwiwata dole nayi wani abu domin kuwa ba zan kyale wanda ya kashe min auren jika a banza ba, nan nake bawa Tarasulu labarin yadda zan soya namar sunan Yar nan ashe shi Salamanun faransa tona min sikiret zai yi inji Turawa, maza muje Junaidu ba wani abu ba ne idan ka bashi hakuri ai duk sulhu ne shi kuma sulhu alkhairi ce" tana gama fadar haka ta mike zata fita, Malam Junaid ya riko hannunta yayi ya ce mata. "Hajiyata dawo ki zauna, Ita Maryama zata ji da kome, na barta da takwara ta rike min ita amana ta kuma kula da ita, girmanta ne ta kula da takwara da kuma abinda zata haifa." Sannan ya juya ga Mai babbar daki ya ce mata. "Har abada ba zan iya karban Zainab a hannunki ba, Zainab yarki ce, kin kuma yi duk abinda ya dace tunda na sake ta yayi ba zamu iya cewa Alhamdulillahi, Allah ya kade fitina da duk wani tashin hankali. Ubangiji ya baki lafiya da nisan kwana idan kika tuna baya haka ya faru da ke fa. Sai nake ganin kamar tarihi ce take maimaita kansa." Ya fada yana murmushi.fashewa da kuka Hajja tayi ta ce mishi. "Ba sai ka gaya min zainabu yarka ce, ni dama ai ban ce dole sai na zauna da ita ba, ban da kawazuci irin nawa ba taya zan kwaso kafaffuna na zo zama da takwara don an mai da ni uwar Benin zan koma can inda na fito, ai dama Malam Gobir bai bar ni kara zube ba, don haka xan koma inda nafi wayo. " Ta wani juya tana share fake hawayen da take, ta tana shirin mikewa Mai Babbar daki da abin ta dame ta ce mata. "A'a hajja shirya mu tafi wurin Takwaranki!" "A'a ta dai zauna anan!" "Ke Asma'u ki ji tsoron Allah, duk me yanke zumunta Allah yana fushi da shi. Haka ayi mutum babu Annabin Rahama a zuciyarshi. Hmm Mariama me ye laifina idan ban zauna da takwara nayi jegonta ba, ai haka zai saka Salamanun faransa ya shiga hankalinsa har ya yi tunanin dawo da takwara.....
(Anya zaman hajja zai haifar da yaro mai eyes)
Kada a manta royal politics na kudi ne!...
[8/26, 5:39 PM] Ramlat Manga41: Page 2
Har ga Allah babu wnada yayi maraba da tafiyar Hajja fada, domin wallahi ba shigarta fada ba ce ita da hakan kawai kamar mai aljanun tashi muje. Anan zata tattara ta bar gidan. Sannan na biyu Hajja bata ganin abu tayi shiru, na uku zasu ta raba hali da ita Ikhlas din, Maluma ta ce mata. "Hajja ke da kike fama da matsanancin ciwon baya?" Kada ki dad'a kada ki ƙara, Hajja ta sake salati kamar an aiko mata da mutuwar Tarasulu. "Innalillahi wainnalihir rajoun, Hajara ki ce kina bakin cikin da zuwana gidan yarki kawai na hakuri na ga bakin ciki kamar wacce aka yi min asiri da bakar jab'a idan yarku ce autar jikokina na yafe da wannan kallon shishigin da ake yi min. Na ma fasa zuwa gidan zan koma gidan Abidi na zauna a can ku rike Yarku kada Hajja mayya ta cinye muku ita." Mai Babbar daki da abin yake bata dariya ta ce. "Hajjah ni fa nace miki muje, ai ko ba don su Maluma da Malam ba ai gidana kamar naki ne! Don Allah kyale su muje ai da nan da can duk daya ne, tunda Takwarar tana wurina." Wani juya kai tayi ta cigaba da hada kayanta ita fa duk da cewa ta fasa ba ta daina shirya kayan ba. Domin ta saka a ranta dole ma ta nunawa kawayenta jikarta kuma takwararta, tana aure Sarki. Kuma ko ba kome ita zata zauna a cikin gidan domin kula da ita, abin ai ko cikin danginta ita mai sa'a ce. Don haka tana gama hada kayanta bata bi kan mai babbar daki ba,tayi waje abinta ita xa'a yi Hassada ita fa yanzu ta san matsayinta a wurin Junaidu da Matanshi, Allah na tuba ko me zasu mata yanzu ai kallonsu take hoto babu me burge ta tunda kiri -kiri suka nuna basu kaunar zamanta a gidan Takwararta. Daga yau ta daina kula so, kuma ai dama an gaya mata sai ka haifi d'a da cikinka ya nuna maka kai bai damu da kai, wannan shine abinda ya faru tsakaninta da Junaidu da Matanshi. Allah na tuba wannan shine abinci, irinsu har guba zasu saka maka don kawai ka damu da masu, ita yanzu ko kallo sun ishe ta ne. "Mariama tashi muje kafin mahassada su kara zuga ki ai ni yanzu ayi walkiya na ga masoyana da makiyana, don dai kada ki ce kin roki alfarman na zauna da takwara, kuma na bad'a miki kasa a idanu ai da na juya da baya na watsar da zuwa zama da ita, tunda ni mayya ce bani da amfani da ina lashe lashe, tow fa tuni nayi na kafatinin jikokina, tow Allah na tuba har ni za a gayawa jikoki ko Murjanatu bata so na zo nan ba, balle kuma Yarta isaniya." Murmushi Mai Babbar daki tayi, Maluma ta kama akwatin karfen Hajja irin wanda ake haɗa almajirai da shi idan zasu tafi makaranta, ta nufi waje ta ce mata. "A banza tunda an nuna bani da amfani!" Kwashe takalminta tayi ta saka a hammatarta, ba don kome ba sai kada Junaidu ya tofe mata kasar da zata taka, ta gagara zuwa ga Fada. Ita fa Hajjah yau ta gama hakura da Junaidu, kafin mai babbar daki ta fito, ita Allah ya bata sa'a tayi waje, ina zata iya bakin ciki kada ta tsaya su zata ta fasa ne, amma ai Junaidu ya watsa mata kasa, ita kuma Mai Babbar daki ta kankaro mata darajarta.
"Mai Babbar daki, ki yi hakuri don Allah da Hajjah idan tayi wani abu don Allah ki kira Malam zamu zo ɗaukarta wallaho."
"A'a a wannan shekarun nata, kada a ce za a na hanata wani abu ko ba kome zamanta babba a wuri zai taimaka matuka gaya. Ku godewa Allah da har Ubangiji ya ja tsawon rayuwarta ina namu iyayen? Yau da ta ce zata zauna da ni, sai da naji ina ma Innah tana raye? Ta ga zauna da Hajjah su yi hira su yi hira. Don haka babu ruwanku, Hajjah uwata ce ba zan iya ganinta tana son ganin jikarta na ce a'a ba, nisan kwana ce ta kawo haka. Bayan haka babu wanda zai taka sa'ar da Zainaba tayi, yarinyar da duk inda ta shiga sai tayi farin jini, haka ya nuna cewa mutanen.da suke kaunarta sun fi makiyanta yawwa, don Allah kada ku damu da Hajja ai na san Hajja ba yau ba, ba kuma jiya ba Allah yasa mu dace."
"Mariama kada su zuga ki, ki ce a sauke min kayana don ni a yanzu babu abinda za'a yi a kuntatta min kamar ace Hajjah dawo ki zauna tun da an rasa hanyar da za a bi a hana ni zuwa ki dai ga mutane amma barshi a inda yake." Sallama mai babbar daki tai musu sannan suka fito, Hajjah ta kame a motar kamar ita za a mai da gida, haka suka bar gidan. Mai Babbar daki tana murmushi yadda Hajjah take kwafa zaka rantse da Allah wani abu aka mata, sun san Hajjah da iya katobara yanzu sai ta je ta kunyata su ba abinda ya dame ta.
****
Tunda Mai Babbar daki ta fito, na gama azkar aka kawo min dumame na biyu na ci na koshi, duk da garin bai gama wayewa ba. Haka na shiga ban daki na watsa ruwa sannan na fito na kwanta barci yayi gaba da ni. Kamar a cikin barcin ana murza na fulanina, a hankali na bude idanuna na zuba mishi idanu. Zuciyata tana wani irin bugawa yaushe ya shigo gidan? Bakinshi ya kai kan cikin ya sumbata, ganin yadda cikin ya juya ya saka shi murmushi. "Assalamualaikum sweeties kuna lafiya!" Ya fada yana Click din inda aka turo yayi gefe guda, tuni cikin ya ware. Buge hannunsa nayi ina faɗin. "Kada ka kara tab'a ni Please!" Na fada ina jan bargo yayye min duvet din yayi tare da cewa. "Hakkin aurena nazo amsa! Idan kuma kika ce ba zaki ba, ba damuwa amma zan barki da Allah ki je ba zan yafe ba. Tunda hakkina ne kiri-kiri kike guduna a shimfidar aure nayi hakuri nayi kawaici Zainaba zina kike son nayi? Hakkina ne fa kike guduna a kai, rabon da naji duminki, tun kafin samun cikinki ko nace tun lokacin da kika samu cikin, akwai adalci cikin lamarinki to Allah ya gani ba zan yafe ba, ba zan bar hakkina ba, ai kin san ba ni da wata mace mai gamsar da ni sama da ke, shine kike hanani hakkina. Ba kome" ya mike zai fita na ce mishi. "Idan akan hakkinka ne kake min Allah ya isa sai ka yi yadda kake so. Amma ka sani ba zan cigaba da zama da kai ba wallahi ina samun dama zan nisanta kaina da kai na gaji da zaman gidanka!" Daga haka nayi shiru na cigaba da kwanciyata, na rantse da Allah na zata zai ji haushi ya bar dakin amma mutumin nan nayi mamakin yadda bai iya hakuri ba ya shiga hanyar da zai nitsar da kanshi, sai dai abin da ya bashi mamaki yadda har ya gama kidarshi da rawanshi ban ce mishi sannu ko na tab'a shi ba, abin ya mishi ciwo domin naki taya shi ko taimaka masa, wato haka abin yake idan mace ta ce maka A'a ka nace? Bai wuce minti talatin ba ya ji ya kome ya gundure shi, kamar a saka maka gayyar tuwo ce babu miya babu mai da yaji. Haka ya saka kai ya fita, ko wanka bai yi ba ni kuwa tunda na ji cikina ya dunkule gefe guda na mike a hankali na shiga ban daki nayi wanka har lokacin cikin yana dunkule sai hakki nake, haka na gama na fito na gyara gadon na cire zanin gadon. Na sauya wani na kai wnada na cire ban daki na saka a wash Machine, na wanke na fito na gyara gadon da kyau, sannan ba kwanta a hankali na ji cikin yana warewa har ya sake can Isma ta shigo dakin ta kwanta a jikin cikin itama. Haka muka cigaba da barcin mu.
---
Wankar da yake kalamanta kawai yake tunawa, gashi ci abinda yake damunka, ci abinda kake ganin zai kare, for God sake, ka mai da kanka wani irin mutum babu macen da take shakkarka a matsayin namiji, kowacce gani yake alfarma take maka, ban ce ina maka alfarma ba amma ina son ka sani wannan rayuwar da ka ɗauka na nuna kai zalamamme ne akan mace ba zai tab'a janyo maka daraja ba, da nasan haka kake baka da aji akan mace har abada da ban fara jera tafiya ta da kai ba, sarakunan baya su mace ke bi, tana fadi tashi akan namiji ya ce yana buƙatarta amma kai yanzu ko me za ayi maka indai mace ce baka da ja zaka bi kuma zaka yi yadda kake so, Charisma and aura kai dai kawai idan buƙatarka ta tashi kamar wanda aka maka asiri da bin kowacce mace taya mace ba zata rena ka ba, da zarar an zo an same me ka magana ya ƙare, kai ne Sarki mafi rauni cikin Zuriar Yayari, kai ne Sarki mafi abin kunya a Zuriar Yayari, kai ne baka isa kayi tsawa a gidanka ba, kai ne kullum matankau suka mai da mahaifiyarka alkaliya. Gaya min taya zan