Showing 57001 words to 60000 words out of 157081 words

Chapter 20 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

45

iya ko sai mu godewa Allah da ya dauke shi, ya mishi rahama." Gyada kai nayi aka cigaba da lallen, hatta hoton bikina sai da ya rike kome yana min tsiya.

Haka suka daura min lokaci guda, bayan sun gama wurin awa uku na cire, suka saka min muhallabiya, sannan suka tafi bayan sun min baki a saman na kafar. Wato shirin da ɗan mai babbar daki ya mana ba karami bane, bayan sallah isha ya zo ya dauke ni da Yaran, muka nufi fada tun kafin mu isa an gyara mana dakin da zamu zauna har da Hajjah wacce take sawun gaba wurin baza Capacity son ranta. Sai waya takewa Tarasulu tazo ita tayi gaba ba zata iya jiranta ba, kamar yadda na fada an kawo namar saniya daya ta guda biyu yadda Umma da Maluma suka bada umarni, Mutanen Maradi sun zo daren da muka wuce fada, suka kwana ana aiki, don ma an bada wasu aikin ma ba ƙaramin ƙoƙari Yeemar tayi min ba. Domin suna tsaye akan kome. Nima da yake mun shaku da aammy sai na dauke ta zuwa fadan mu tare da ita. Wato kowacce masarauta da irin nata al'adun, muna shiga cikin parlourn Mai Babbar daki, wani wanzami ya fauce Ayaan a hannun Faruq, ya watsa yaron sama, tare da bin shi da aska. Ya wani tab'a kan Yaron, sai ga gashin kan yaron yana zuba kasa. Wani gud'a suka saka a parlourn ana faɗin. "Tabbas jinin Yayari ne!" Allah yaso mutumin nan yana rike da hannuna da na fasa ihu, haka wanzamin ya musu aski domin an rigada anyi radin suna taron ne za ayi, haka muka shiga parlourn sosai zan zauna a kasa mai babbar daki ta ce min."A'a Uwar huɗu zauna a sama abinki!" Haka na zauna aka kawo min lalle da ruwa a bawo aka saka min kafana a ciki, aka shiga shafa min lallen ni da Yan matan, kafin wani lokaci mun yi wanka da lalle tas. Kafin aka wuce da mu daki muka yi wanka na gaske.

Hajjah dai bata rabuwa da abin kunya, wai ita takewa Faruq fada. "Don kaushin zuciya da fason rai wai ni Faruku zai wulakanta? Tow kaji na gaya maka Faruku, baka isa ka nuna min iyakata ba." Fitowa nayi nace mata "Hajjah don Allah ki zo nan kin ji!" "Atow gara na gaya mishi, wai Yaron nan ba zai bar ni na shigo da kawayena ba." "Kyale shi niman fada yake!" Na fada ina wucewa ban daki na kara wanke hannuna, zama Hajjah tayi a gaban abinci tana faɗin. "Ita dai Mairamu bata gaya, ka ga wani garan arziki da aka kawo min!" "Shigowar Aunty Sajidah yasa ni sauke ajiyar zuciya, ina faɗin. "Gara da kika zo Hajjah so take na ji kunya!" "Ayya Hajjah ki daina kunyata mu." "Sata nayi ko karya? Daga na cewa Yaron nan Faruku kawayena za su zo suna a ajiye musu git fas, shine zai fara cewa babu tsofaffi irina a wurin!" Gyaran muryan Uban Yaran na ji, na kalli Aunty Sajidah, mikewa suka yi na dauko katon hijab dina na saka, na fita na samu yana zaune a parlourn tare da su Salim da Walid Mamman yayari, Mahfouz Kabir Hammud Yayari, Abubakar Nuru Yayari, sai Abdulhafiz Yayari, sai Mai Bauchi Sulaiman Attahiru Shehu Yayari, suka shigo, daga bayan kujera na tsaya muka gaisa sannan na koma na fito musu da Yara biyun a Rungume a kirjina, shi ya amsa yana murmushi ya ce min. "Ki cewa Hajjah tayi hakuri!" Ina juyawa na ganta ta rungume yara biyun tana faɗin. "Hmm, Sarki Salamanun faransa, ka shiga tsakani na da Faruku, taya zan gama mishi lissafin Tarasulu da su asabe zasu zo wurin taron nan ya gaya min ban da tsofaffi irina? Ban da Allah ya takaita na kai zuciya nesa ba ban san yadda xan iya kyale Faruku ba." Rike baki yayi yana kallon Faruq da ya hade rai. "Faruku!" Wannan sunan yana bala'in bashi dariya murmushi yayi ya ce mishi. "Na'am!" Yanzu da hankalinka ka ce Hajjah ba zata je wurin taron sunan nan ba?" "Tow ai wurin ba na tsofaffi ba ne Yallabai ita kuma gayyar kawayenta tsofaffi zata mana, shi yasa nace gate pass ya kare!" "Innalillahi wainnalihir rajoun, ina gani a gida ka bawa yarinyar nan kawar takwara yaamar wato don ban iya rasayawa da murgud'awa ba shi yasa baka ba Ni ba, ai ina kallonka.."

"Hajjah zaki koma gida wallahi!" Na fada kamar zan yi kuka. "Ba ruwanki da ita, ta kawo kara inda za a share mata hawaye ne, Hajjah ina jinki kyale ta."

"Ina jin dai na hakura don na lura Zainaba bata kaunar na cigaba da maganar Faruku!" "Hajjah Faruq ake fada fa." "Faruku Umaru Faruku zance sai ki cinye ni danye." Ta fada a hassle. "Ina haka kika yiin a sunan yarinyar kishiyarki kika saka aka hanani kayan bikin waye ya sani ko yanzu ma kece kike zuga faruku kada ya bani git fas!" Abinda yake son ji kenan ya sake murmushin da yasa na zuba mishi idanun ina jin wani irin kaunarshi, yana kara boosting a zuciyata, wani irin pumping yake a zuciyata kamar yadda coins din cryptor yake hawa a lokacin da aka zuba mishi liquidity, ina jin kamar na fada kanshi na rungume shi. "Ki kyale Hajjah Faruq bai mata adalci ba" hmm na fahimci son magana yake na juya na barshi a wurin da su, sai can ya zo da Yaran shi da Hajjah, wacce har lokacin mita take kamar anyi mata wani abu akan git fas, na isa nayi magana ne ya ce na saka musu idanu, fita yayi can kuwa sai gashi da gate pass din yana shigowa ya kira ni, daukar wayar nayi ya ce min. "Please come out!" Fitowa nayi ina gyara zaman hijab dina, ban san da shi ba kawai naji ya wani rungume ni cak. Juya ni yayi na zuba mishi hannuna a wuyarshi. "Baby girl kin yi kyau!" "Ina godiya Yayana!" Jan hannuna yayi ya zaunar da ni a kujera. Yana mai bude wani karamin akwati ya ciro wani set na white gold, ya shiga saka min a hannuna da wuyana da kunnena, har da yar hanci da kafana da zoben yatsar kafa. D'ago kofar yayi ya daura min akan daya, yana murmushi ya ce min.."Kin yi kyau!" Murmushi nayi ina gyad'a mishi kai, wani irin tausayinsa nake ji. "Na gode sosai Yaya!" "Ba kome yau daya ji nake kamar ban tab'a haihuwa ba, ko don Yaran da ke kun fuskanci rayuwa da mutuwa ne, ban sani ba amma ina tausayinki da ke da Yaranki baki daya." Murmushi nayi ina faɗin. "Na gode sosai Yayana!" Hada goshinmu yayi zai fara rigima Mai Babbar daki ta ce mishi. "Yarinya da danyen jego ka wani sakata a gaba da niman fitina baka da mata ne?" Hajjah da ba a kirata ba , ta fito tsugul ta ce mata.."Mairamu yaushe kika fara rayuwar kadangaru? Mutum da iyalinsa zaki makale mishi, gaskiya wannan shine kaushin hali da fason zuciya, gaskiya addini bai yarda da rayuwar kadangaru ba, wannan ba dabi'ar muslman kwarai ba ne, kai bawan Allah ka yi sha'aninka idan baka gaya mata damuwarka ba, ai ba sake ganinta zaka yi ba don haka ko can kazo dole na baka Diyoyinka ka gansu." Kiri-kiri Hajjah ta hana Ummi magana, shima da yake gulmanmme ne, ya nunawa Hajjah da cewa. "Ga abinda na kawo mata jin gan shi!" Gyada kai Ummi tayi domin bata isa magana ba, Hajjah ta ce mata don kaushin hali da fason zuciya, gara ta koma abinta bata san yaushe Hajjah ta manta da al'adar jego ta rungume Salmanu Faris ba, mika mata takardun gate pass yayi yana faɗin. "Aminiyar gashi idan akwai karin kawayenki sai ki gaya min na kira miki faruku ya kawo wasu!" "Ai shi yasa nake sonka, kaf cikin surukan Junaidu kai ne Allah bai maka zubin hannun Jarirai ba" wato shine ba marowaci ba, girgiza kai nayi ina cewa jiya Mijin Aunty Nu'aymah da yazo barka ya bata 5k amma matar nan take musu jam'i na ce mata. "Hajjah me yasa baki da godiyar Allah? Jiya Yaya Ubaidullah ya baki kyautar kudi har Naira dubu biyar!" A wani lalace ta kalle ni, ta wani dauke kai tare da kunco habbar zaninta, ta ajiye min dubu biyar din tana mai b'antar goro ta ce min. "Ni yanzu na fi karfin naira dubu biyat da zaki min gori mijin Yayarki ya bani, ga kayanku ki mai da mata Mijinki, kin san nawa ya bani? Dazun dubu dari ya bani gashi a lalitana, yan uwansa kuwa kowa sai da ya bani goma-goma ko Mai Martaba Salamanun faransa?" Gyada mata kai yayi wato ja fahimci Yaya asalin dan rashawa ne na gidigi, wai don ya samu damar kebewa da ni ya bawa Hajjah kudi ta sayar mishi da lokacin da ya dace muna daki. "Yawwa Salamanun faransa Allah ya maka albarka ka gani sai da safe, Allah ya kara maka budi da nasara, Ya Allah ya raba ka da halinsu oo kada su koya maka mugun hali ka daina alkhairi, ato idan ba hassada aka fara ba ace mutum kamar shi sai yayi yar murya ku bashi matarsa duk wannan sanaben ba dani za ayi ba!" Tana shigewa ya janyo fuskana ya shiga kisss dina, hannuna na kai keyarshi ina taya shi sai da muka gaji don kanmu ya ce min. "Ni fa da kika ganni idan ina son ganinki bani da wani dogon tashin hankali, ina da Hajjah." Kamar nayi kuka na ce mishi.."kada ka mai da ta wata iri don Allah Yaya wallahi bana son tana haka!" Shafa lips dina yayi yana faɗin.."ba zan mai da ta ba, sai dai ina buƙatar Hajjah a gefena a kowacce rayuwa ina bukatar Hajjah ita ɗaya ta fahimce ni ta fahimci yadda nake sonki, zan ta bata kudi ba abinda ya dame ni." Kamar nayi kuka haka nayi ta kallonshi, sumbatar gefen wuyana yayi ya ce min.."Kiyi hakuri ba ina nufin na mai da ta mai son kudi ne, Hajjah tana da kirki da mutunci, asalima Hajjah zuciyarta a rufe yake da kin abin duniya. Hajjah ba irin sauran tsofaffin nan da Allah ya daura musu son abin duniya ba ne, bata da wannan yanayin. Sai dai tuwon girma miyar nama, tun da ta ji labarin na saka mata sunan Ayat take jin wani irin so da kauna, har kuka ta min wai na mata abin da bata b'ata ba, na mata takwara kaf duniya babu wnada ya tab'a mata takwara kamar ni!" "Sunana kuma da aka saka min ba nata ba ne?" Haushi ya cika ni, mikewa nayi xan tafi ya rungume ni ta baya yana faɗin.." Ato waye ya sani, ita dai Hajjah tace kaf Yaranta babu wanda ya mata kara ya saka mata takwara sai ni, ai waliyyin Allah ne ni mai cike da tsoron Allah!" Juyawa nayi na ture shi na dauki sauran kayan abin da ya ajiye min har kofar ya biyo ni ya jingina da bango yana faɗin.."waɗancan tagular na Yara mazan nan ne a saka musu a wuya zaki ga har da zare, wannan kuma akwatin na yan matan ne da na saka aka musu dukkansu biyar, Amiratul Zaitunah, Princess Sadiya, Nana A'ishah, sai Ayyanah da Ayaat. A kula min da su, a basu nono su koshi kafin nima na zo na fara rabon arzikin da ni!" Duka na kai mishi ya kauce yana mai fisgo ni yana mai rad'a min a kunne. "Allah kika dawo tare da su zamu na shan madara da ruwan cikin wannan fatar, atow ba zan sake lagwada ya wuce ni ba!"

"Yaya ka tafi sai da safe!" Hannuna ya kai tare da shafa min kayan aikinsa. "Yana jiranki!" Kwace kaina nayi na koma ciki, na samu Hajjah rike da Ayaat tana jijjigata. A raina nace *ba kin amshi kudin rashawa a wurinsa ba dole ki zauna renon Yaranshi!* Na wuce ban daki nayi alola, suma yaran na musu alola, Aunty Sajidah tana taya ni na nuna mata abin da ya kawo min na fitar suna, a daren ta sakawa yan mazan har da zoben azurfa kowa da harafih sunansa. Hajjah ta ce min. "Ai Mijinki nan dan albarka ne! Mutumin kirki ne!" Takaici ya ishe ni yadda take magana. "Kaf zuriata waye ya min takwara irin Salmanun Faransa? Kai tsaye ya salahe min shiga gidansa da shi kansa, ai mutumin kirki irinsa."

"Yanzu haka don rashin godiyar Allah sunan da aka saka min ba sunanki ba ne?" Wani ware idanu tayi tana dukar kirjinta. "A'a wallahi Junaidu yayi dai niyyar saka sunan da yayi niyya, amma ai ko su Sajida da Nu'aymah bai gani lokacin da aka haife su ? Sai da su murja suka roke shi arzikin ya min takwara! Amma shi wannan fa, faruku yake gaya min kina haihuwarta aka saka mata sunana!" "Hajjah kwanta dare yayi ki daina biyewa Zainaba!" Inji Mai Babbar daki. Tura baki nayi nace mata. "Ummi taya wannan matar zata yi ta zubar min da mutunci a gaban Yaya fisabiilillahi!" Banza da ni Hajjah tayi tana faɗin. "Duk bakin cikin dan tsako ba zai ci dan shirwa ba." Dariya Ummi take son yi amma ganin yadda nake kullace da Hajjah sai ta fasa ta isa gadon Yaran tana faɗin. "Sultanah tana barci ne?" Juyawa nayi ina faɗin."Ummina sultanah kike so?" "Eh sunan da ya dace da ita kenan, amma Ayyanah ma suna ne mai dadi!" Ta dauke ta tana mai zama a kujeran dakin, wani irin kauna ce da na hango daga idanunta, asalin bangos dinta da yake hannunta ta cire guda biyu ta saka mata a hannu, sai wani gold da ta saka mata. "Ikon ni yau Mairamu take nunawa iyakata? Dole gobe na zo da gwal dina da Junaidu ya sayan min tun auren Abid!" "Shi kenan mun shiga uku!" Aunty Sajidah ta faɗa, Hajjah kuma, haka Mai Babbar daki ta bar mu da harabar Hajjah kai matar nan da kyar tayi barci,nima na basu nono a lokacin ina zaune muna Waya da shi, can na ji muryan Nady tana tambayarshi da wata shegiyar yake waya. Ya ce mata. "Da shegiyar da take gabana nake magana!" Wayyo shi dai baya kaunar zaman lafiya, kashe wayar nayi bakiɗaya, ai na ji wayar Hajjah yana kuka, firgit ta farka tana mai sakawa a kunnenta. "Waye?" Ta tambaya da ƙarfi. "Ai ho Salamanun faransa ne ka koma lafiya? Tow gata nan!"

Mika min wayar tayi ta koma barcinta tana faɗin. "Band mugun hali taya kana da wayarka ka kashe mijinka yayi ta gantali akan wayoyin mutane salon a kwashe min yan arzikin waya. Kaushin hali da fason zuciya!" Ta juya ta cigaba da barcinta. A hankali na cigaba da sauraren shi bayan na kwatar da Ayaan, da yake kallona Isma tana gefenshi. "Dan uwana ba zaka yi barci bane?" Daga can ya ce min.."ina xan yi barci bayan baki bani nono na b;" "Yaya bana son haka, taya xan baka abincin Yarana? Baga Ijlal tana goyo ba sannan Nadiyyah ai ba zata rasa ruwan nono ba." "Ni naki nake so." Daga haka na chanza mana topic ba zan iya maganar shi ba. "Yaya ka kwanta barci nake ji;" "me yasa kika kashe min wayata?" "Ya ba zan kashe ba naji zaku fara min barna da barin zance!"

"Ina zuwa! Ke ke!" Can naji ya saka salati tare da ihun Nadiyyah tana faɗin. "Sai na kashe ka itama na je na kashe ta wallahi sai na kashe kowa!" Da gudu na dirka a gadon, na nufi dakin Ummi ina faɗin. "Ummi don Allah a je a duba Yaya Nadiyyah tana can zata kashe min shi don Allah a je a duba shi." Itama a rikice ta fita muka shiga niman Faruq, a daren fa yan mazan gidan suka nufi gidansa, sun samu ita ta yanka kanta shi kuma da ta nufe shi ya kifa mata mari, amma ba abinda ya same shi, sun samu ma yana treating hannunta. Kallonta Salim yayi kafin ya gyada kai yana jin wani irin yanayi, bai san me yasa baya kaunar yaji Zainab tana kuka ba. "Ka kira Zainaba ka gaya mata lafiyarka lau domin taji abinda ya faru." "Ba kome xan kira!" "Please right now!" Ya faɗa yana kallonshi, daukar wayar shi yayi ya saka a kunne. "Yan mata!" "Yayana, kai ne? Baka ji ciwo ba ko? Yaya kana jin zafi ne? Yaya kazo ga Ayaan bai yi barci ba don Allah ka zo na ganka!"

"Silly girl! Lafiya ta lau, ki ce Ayaan yayi barci nima barci nake ji!" Daga haka ya kashe wayarshi, ya wurga ya sallame su. Rufe kofar shi yayi ya kwanta ya gaji da fitinar Nadiyyah, bayan fitarsu ya tashi zuwa gaban madubin dakin ya d'aga rigarshi, yanka ce sosai, haka ya dauki kayan aiki ya fara dinke wurin bayan yayiwa kanshi alluran kashe zafi, sannan ya duba magani ya hadiya, kafin ya dauki bandaji ya daure wurin gam, sannan ya koma ya kwanta. *Na sani bata da ilimin addinin Muslunci, amma wallahi tana sonka, don Allah duk abinda zata yi ka rufa min asiri kada ka sake ta, wannan shine alfarma da nake kara nima daga gare ka. Ka rufa min asiri kada ka sake min ita* wannan sune kalaman mahaifin Nadiyyah. *Idan ka gaza zama da matanka saboda fitinarsu bani da hanyar da zan kafa Zainab a gidanka, idan ka iya jure duk wani Bala'i da fitina, shine adalcin da zaka mun Zainab ta zauna a gidanka! Domin dorewar haka sai ka halatta haram ya zama halal, ka haramta halal ya koma ya dawo Haram, ta haka zan cigaba da kusawa har zuwa nan! Yaki dan zamba ne ba zan iya yaki ni daya na ba, ita kuma mace ce ba zan iya gaya mata shirina ba, kada ka duba girma da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login