Showing 36001 words to 39000 words out of 157081 words

Chapter 13 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

25

iya da shi, sannan da kike jin ba dad'i hmm Zainab ya dace ki kula da kanki da lafiyarki me zaki mishi ban da wahalar da ke da zai yi, babu wani abinda zaki tsinta a jikinshi sai azaba da wahala don Allah kada ki nuna ya dame ki, ta hana ne zamu gyara mishi zama, ni da nake miki kallon Jarumar mata, ina miki kallon babbar mace sai ki kama kuka don kin gan shi wato ya ce Umminsa tana wahalar da ke?" Zare idanun nayi da suka yi ja murmushi nayi nace mata. "A'a Ummi!" "Tow gaya min me ya miki?" Ta janyo kujerar stool ta zauna tana kallon yadda nake ta raba idanu. "Ina jiranki gaya min? Idan ya miki wani abu sai ka mishi bulala yau ba sai gobe ba!" Murmushi nayi ina sosa kaina na ce mata. "Kawai haushi ya bani yazo sai wani sannu yake min, sannan kuma." Riko hannuna tayi tana kallon yadda na sunkuyar da kai. "Kishi ne! Ina son irin kishinki, ba zai cutar da kowa ba sai ke kanki da Mijinki, kada ki bada damar da wani zai fahimci ainihin kishinki! Ya kwana biyu bai shigo ba yayi kiba haka ya nuna min alamar ya zauna lafiya da matanshi." A hankali na fara ƙoƙarin zame hannuna cikin nata. "Kada ki damu ina rike da hannunki, har sai ranar da kika iso Matsayin da nake. Kishi ne kuma Zainab na tambaye ki?" D'ago kai nayi na kalle ta da idanuna da suka cika dab da kwalla.."idan kika ce kada ya kusanci sauran matan ke zaki iya daukar laluransa ne?" Kunya ce ta kama ni na sunkuyar da kai, "look at me, mu yi magana akan gaskiya sannan mu ajiye surukanta da yake tsakanin mu, muyi magana akan auratayya, idan kika ce kada ya zauna da sauran matan zaki iya daukar sabgarshi ne?" Wani irin danasani na ji ya lullube ni. "Good girl, tunda kin san akwai hakkin sauran matan me yasa kike damuwa? Ya kamata ki saba da wannan yanayin tun auren Ijlal fa? Nasan wannan cikin ya hanaki sakat ko? Ki yi hakuri zaku rabu lafiya." Gyada kai nayi sai kuma na ji kunya, na kasa d'ago kaina. Ban san ta yadda mai babbar daki ta karance ni ba amma tabbas daga ita sai Maluma suka karanci yadda nake da kuma yadda nake ji, sannan sun fi ni sanin abinda ya dace da kaina.

Haka muka cigaba da rayuwa ga cikina kullum kara sauka yake duk wanda ya ganni sai ya ji tausayina, wata ranar Litinin da ba zan iya goge shi a cikin rayuwata ba.

Shi da kansa ya sani shiryawa zamu tafi asibiti don ma nace ba zan kara komawa ba, amma haka ya saka ni dole na shirya, ina saka takalmin da ya zo min da shi jiya, na ji kafana yayi dum-dum a cikinsa. Ajiyar zuciya na sauke Mai Babbar daki ta shigo tana rike da kofin madara ta mika min. "Maza sha kafin ki fita!" Haka na amsa na sha sannan na ci dabino da zuman nan. Na saka Hajib dina har kasa da nikkaf domin ba karamin muni nayi ba duk wanda ya sani a baya yar firit ce ni, amma yanzu na zama kamar wata Giwa ga katon ciki kamar randa haka na fito a hankali nake takawa ina hutawa domin cikin yayi kasa, shi a sonshi ma yau ayi min aikin na huta tunda saura kwanaki ne EDD na, haka na fito a hankali ina jin kamar nayi kuka ga Sailuba da take rike da jakata, "Sannu!" Inji wani bafade da yake kofar shiga cikin gida, "yawwa" na faɗa, a hankali ina tafiya har na isa inda motar Sadi yake, fitowa yayi ya bude min, na shiga Sailuba ta mika min jakata. "Allah ya tsare ya dawo dake lafiya. " "Allah yasa!" Na fada ina gyara zamana a cikin motar, Faruq da wani da ban san waye ba suka iso gaban motar ya shiga Faruq ya zo inda nake ya ce min. "Akwai motar yan rakiya da zasu raka ku, shi wannan mutumin kirki ne." Murmushi nayi nace mishi. "A'a ya sauka kawai, iya sauran da sadi sun iso!" Ni kaina na ban san lokacin da na fadi haka ba, shima kuma faruq bai min musu ba, ya ce ya sauka haka muka bar kofar fada da tawagar masu kula da lafiyata. Wani lokaci idan Allah ya ƙaddara baka cikin ƙaddaran mutum sai ka ga wani sanadi kalilan ya fado cikin abin, sai da muka bar fada mun dauki hanyar wajen gari dama a can asibitin yake, kuma ba a ce wajen gari ba domin dai yayi bayan gari kaɗan, kawai muna cikin tafiyar wata kara mai karfi ya tilasata mana tsayawa sakamakon fashewar Tayar motar, haka motar bayanmu suka fada cikin wannan yanayin, dukar kan motar Sadi yayi cikin karaji ya wani juya motar yana faɗin. "Tarko ce aka mana!" Karar harbe-harbe muka ji, haka yasa nacewa sadi a rud'e. "Tsaya ni suke bukata!" Da Mamaki ya juyo yana kallona. "Eh ni suke bukata kada wani ya motsa." A hankali na matsa kaɗan na bude motar sauran masu kula dani suna ta sake wuta, kuma na ga kamar an harbi mutane biyu a cikinsu, ina fitowa wani cikinsu ya ce."Fulani Babba ki koma motar!" Girgiza kai nayi nace musu. "Ku bar harbin ni suke bukata!" Jin yadda nayi maganar yasa can bangaren suka tsayar da harbin, a hankali nake takawa wurinsu, na tsaya domin na rasa tsorona bakiɗaya, rayuwar mutanen da suka yarda da Mijina yana da muhimmanci, ashe kuwa don na kare rayuwarsu ba wani abu bane. "Fulani Babba!" Na ji muryan Sadi, juyawa nayi na ce mishi. "A'a ka zauna ni suke bukata!" Aikuwa yadda na juya na gansu sun fi su dari rike da manyan makamai. Sai a lokacin na fahimci abin da nayi ba karamin kasada ba ce. Wani dan karamin mutum na gani kamar yaro saboda rashin jiki da kuma fitina sai wani katon mutum, da yake tsaye kamar bishiyar kuka. Yana zuwa ya tako gabana yana faɗin. "Tabbas sun yi gaskiya Awatif ba zata tab'a yarda a salwanta da rayuwar kowa ba, ashe da gaske ne! Amma taya kika samu karfin zuciyar dakatar da su." "Surutu kake so ko ni kake so?" A hankali aka fito da wata mota kirar benz daga cikin dajin. "Ance mu dauke ki a mace ko a raye, sai kika bada kanki a raye. Da alamu jinin Shago ya shiga naki fiye da yadda ake zato tunda gashi ban ga tsoro a tare da ke ba! Ku buɗe musu wuta muje ke kuma!" "Sai dai kuma ba isa ba, zaka zab'a ka tafi dani ko kuma ka hada mu ka kashe bakiɗaya!" Na fada ina kallonshi. Cizon bakinshi yayi ya ce min. "Idan naki fa!" "Ban san me zai faru ba, amma na hango wani abu yana jan ka cikin wancan duhuwar! Ina iya hango idanunsa a buɗe!" Juyawa yayi yana faɗin. "Kina nufin akwai wani abin tsoro bayan mu anan!" "Gaskiya akwai shi kana tab'a wani anan zaa a samu matsala!" Ban san me yasa nake ganin wata irin fusatacciyar dabba tana gurnani ba. Amma tabbas ana yin wani abu zata yi abinda zai bada tsoro, a da can ma ana yawan fadar wannan titin ana yawan samun hatsarin miyagun dabobbi suna fitowa tsakiyar hanya su yi b'arna daga lokacin da dare yayi zuwa karfe goma tow kada ka taso wannan hanyar. "Shi kenan ki shiga." A hankali na tsaya ina kallon Dabbar, durkusawa nayi na shafi ƙasar wurin sai na ji tana wani irin kuka tare da ja da baya ta koma ta kwanta kamar zata yi barci. Ashe shi talala suka yi idan aka fara tafiya dani a budewa su sadi wuta. "Kada ka sake ka basu umarnin kashe kowa, domin har inda kuke zata farmake ka." Na fada mishi ina kallon abin. Dayawan mutane idan ka gaya musu magana, basu cika yarda ba sai idan wani abu ya faru da sun nan zaka ga sun firgita, bamu dauki minti ɗaya da fara barin wurin ba suka bude wuta, ni dai naji wani irin ƙarar abu, wanda karfinsa ya bangaji motar da muke tayi wani irin girgiza sannan ta tsaya cak, kaina da ya bugu na fara jin wani irin ciwon kai, dafewa nayi na ji wani irin kamshi kamar an hura min iska a hancina, daga nan ba nace nasan kome ya kara faruwa ba.

Bangaren masu kula da Lafiyar Ikhlas kuwa, yan bindigar na sake wuta duk suka durkusa a bayan motarsu, domin maganar gaskiya Ikhlas ake bukata a raye ba a ma fatan a kawo ta a mace. Domin wannan shirin ba yau ake yinta ba, sannan wata irin guguwa ce ta turnike dajin da kan hanyar da wanda ya haifar da wani irin duhu duk da safiya ne, ko tafin hannunsu babu iya gani ihu suka fara yayinda masu kula da lafiyar Ikhlas suke kwance a kasa , sai dai su ji karar faduwar abu. Mutane biyu da suka dauki Ikhlas ba da azabar gudu suka nausa cikin dajin da ita. Cikin wani irin azabar tsoro domin akwai inda matukar suka isa wurin babu abinda zai same su. A takaice sai da wannan dabbar ta kashe su tas. Sannan ta tsaya tana mutanen Ikhlas da suke tsaye, dabbar gata kamar zaki, mage ce gata nan dai wata irin suffa mai kamar da maguna. Haka ta juya bayan ta gama kallonsu sannan ta nausa cikin dajin kamar wata walkiya, ta b'ata cikin dajin wani wani irin ƙara mara daɗin ji.

Sai dai duk gudun dabbar bata sake su ba, wani irin ihu da kara tayi tare da tunkarar inda take tsammanin sun bi, amma ina ji tayi kamar an saka mata shinge mai karfin tsiya. A hankali tayi ihu mai karfi da ya haddasa guguwa a cikin dajin wasu dangin magen irinta suka yi ta fitowa suna taruwa a bayanta, juyawa tayi tana kallonsu, ta kwanta hawaye na zuba a idanunta. A hankali jikinta ya fara dawowa daidai Ismaha ce take kuka, sauran magunan suka nufi hanyar haka suka dawo suna kallon ismah tare da isa wurinta suna lashe fuskantar.

**

Fada.

Daren jiya yana zaune da it, ya ce mata.."My Lady gobe zaki je awo ina ga zasu miki aiki a rabu da cikin nan!" Girgiza kai tayi tana faɗin. "My Namamajo babu wani aikin da za ayi min da kaina zan haihu in sha Allah." Ta fada tana lumshe idanunta domin bata son dalilin da zai mata maganar aikin nan. "Zamu je da ni ne fa?" "Yaya zan tafi awo amma ba zaka bi ni ba!" "Me yasa?" Kawai bana son ka bani ne!"

Kura mata idanu yayi kafin ya ce mata."Kiyi hakuri amma zan bi ki!" Dariya yayi ta ce mishi.."matuƙar gobe zanje awo ba zaka bi ni ba, domin daga ni sai Sadi da yan rakiya kai kuma gobe zaka zauna a fada har da Faruq ka yarda da batuna!" Ta fada mishi tana dariya. Rike hannunta yayi yana faɗin.."Am always strong because of you, idan babu ke a rayuwata im not, nothing please ki bari a raka ki!" Murmushi tayi tana shafa kansa. "But you're King!" Ta fada tana shafa kanshi. "King without Queen it's nothing! Don't change my topic, kada mu yi haka da ke!" Murmushi tayi tana faɗin. "This is not necessary, abin da nake son ka sani baka cikin ƙaddarata domin jikina da idanuna sun nuna min haka, wata shafi na ƙaddarata zata buɗe ruwanka ne ka nime ni a kodayaushe ka tsaya min, ni kuma xan tabbatar zan haihuwa a hannunka!" "Kin san me kike fada kuwa? Wannan wacce irin magana ce? Kin ga gobe zamu fita tare haka yana jefa min shakku!" Ya fada bayan ya tashi zaune domin yaji ranshi ya fara b'aci. Sauka yayi a gadon ya zura kafarshi a kasa. "Kayi hakuri Yaya idan na rayu ka kasance da ni, idan ban rayu ba don Allah kada ka yi nisa da ni! Koda kuwa ace mutuwa na yi!"

Abinda ya hango a cikin idanunta ba karamin tsoro ya hango ba, yau ta fara ganin tsoro a cikin idanunta, yau ta fara ganin karaya a cikin idanunta. "Gaya min me yake faruwa?" "Yaya tsoro nake ji, yau kusan sati kenan ina wani irin mafarki!" Juyawa yayi ya rungume ta yana shafa bayanta, tana kuka sosai. "Yaya ina ji kamar zan mutu ne, Yaya kada ka wulakanta koda gawana ne."

"Kada ki damu babu abinda zai faru da ke."

Wannan shine dalilin da yasa ya haɗa masu kula da lafiyarta, da shi da Faruq duk suna cikin tafiyar amma wani ikon Allah sai ga wani sako daga fadar gwamnatin Zanzabiran, wai a kawo mishi daurin auren kanwar Gwamna Musharraf, wanda shi gwamnan ya zabi Salmanu Faris din ya daura mata auren, haka yasa Faruq ya haɗa ta da Goga shi kuma Ikhlas tana ganinsa ta ce a'a ya je kawai bata bukatar kowa ya shiga tafiyar matukar ba Salmanu Faris ba ne kawai kowa ya hakura. A lokacin da suka bar fadar hawaye ne ya cika mata idanu, wani irin tsoro yana kara tabbatarwa a cikin ranta. A yanzu ta kara fahimtar shine kwarin gwiwarta. Shine kome nata, a kullum tana zuwa awo amma a yau tsoro ne a cike a ranta.

........

Wurin minti talatin da barin zuwa minti arba'in aka kira Faruq tare da gaya mishi an dauke Fulani Babba. Wani irin zufa ce ta shiga karyo mishi ta ko ina. Ya kalli Ubangidansa, ana mishi bayani yana sauraron mutane. A hankali ya saka kai zai fita sai kuma ya dawo, ya tsaya a inda yake ya tura sako akan a koma wurin a bincika hanyar da suka bi. Cikin ikon Allah suka turo mishi sakon to, a wannan lokacin ba karamin damuwa ya shiga ba, har bayan awa guda babu labarin a hankali ya taka har inda Mai gidansa yake ya ɗan yi kasa da kanshi sai ya rasa mai zai gaya mishi domin wani irin tsoro da tashin hankali haka ya tattara bugun da zuciyarsa take ya sauke wata ajiyar zuciya mai matuƙar nauyi da zafi ya ce mishi. "Allah ya baka nasara, yan bindiga sun dauke Fulani Babba!" Cak aka nime annurin da yake kan kan fuskarshi aka rasa, yanayinsa ya wani irin sauya, tashin hankali da tsoro suka cika mishi rai, ya kalli Faruq da kyau ya ce mishi. "Kasan me ka fada?" Gyada mishi kai yayi tare da cewa "Eh Yallabai!" Lumshe idanun yayi ya bude a hankali ya ce mishi. "Shi kenan ko akwai wani magana?" Girgixa kai yayi, ya koma inda yake. A hankali aka cigaba da zaman fada. Har zuwa azhar kafin Faruq ya kara sanar da mutanen fada, an sace Fulani Babba. A wannan takin tsoron da ake son ganin a idanunshi yayi ƙoƙarin dannewa hankalin kowa ya tashi amma ban da shi da ya shiga aka yi sallah da shi ya koma cikin gidan, Faruq ya bada labarin abinda ya faru kafin wani lokaci Malam Junaid Gobir da yan gidanshi.

5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint 500₦

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 14

Kafin wani lokaci labarin b'atar Fulani Babba ya watsu. Har zuwa lokacin babu wani alama ta fargaba ko tsoro da aka gani a kan fuskarshi, duk da a razane yake a cikin ranshi amma yayi amfani da shirunsa yaki magana, sannan daga fadar gwamnatin Zanzabiran an turo jami'an tsaro amma ina, karewa bayan sallah la'asar aka kai shi inda abin ya faru. Da yadda jami'an tsaro suka mai da wurin wata karamar officen bincike na musamman. An saka drup domin niman hanyar da suka bi amma babu wani labari, buɗe ido yayi ya kalli dajin da gawarwakin da aka samu a wurin.

Harde hannu yayi a kirjinshi, yana kallon kome kamar mafarki. "Allah ya huci zuciyarka, in sha Allah zata dawo." Inji Alhaji Mamman Abba yayari, murmushi yayi ya juya yana faɗin.."kawai nayi mamakin yadda aka yi waɗanda suka zo ɗaukarta har suka iya mutuwa bayan nasan haka kawai ruwa bata tsami banza, duk inda take Allah yana tare da ita." "Wannan haka yake domin kuwa kowa yaga abinda ya faru yasan akwai kudirar Allah a cikinsa, don haka duk inda take zata bayyana in sha Allah." A hankali ya juyo tare da barin wurin ya dawo cikin motarsa ya zauna yana murmushi bakin ciki.

Ganin Magariba tayi yasa Faruq ya dawo da shi, koda ya dawo sallah suka yi ya wuce fada, karon farko a rayuwarsa da ya ji tsoron da bai tab'a ji ba, lokacin da ya shiga kujeran da yake zama yayi ta shafawa yana zagaye shi. Duk wanda ya dauki Zainab da tsohon cikinta abinda yake bukata wannan kujeran ne, sannan ba zai tab'a bayyana kanshi domin kada ayi ram da shi, zai yi ƙoƙarin ya isar da sako ta ko halin k'ak'a ne, amma ba zai yarda ya fito da abin da ya ke ranshi ba idan ba'a yi sa'a ba ya gwada wasa da hankalinsu.

Yasan a wannan lokacin kawazucinsa kawai zai danne idan ba haka yayi ba daga Zainab har abin cikinta, irin wannan abin ya faru lokacin da aka sace shi, da ace mai Martaba a lokacin ya amshi bukatarsu, da sun sake shi amma kin ansar bukatarshi koda yake ai shi na shi sace shi da aka yi a rubuce yake domin tun can a shirye al'amarin yake, wannan kuma an shirya ne akan wata manufa tasu.

A hankali ya juya zai fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login