Showing 90001 words to 93000 words out of 157081 words
bude a wurin kamar yanzu aka sauke akan wuta yana wani irin turiri ga kamshi mai dadi,hannu na saka zan diba na ji an ce min. "Abincin mara lafiya ne fa."
Da sauri na ajiye na wuce daki nayi alola da sallah, na jima ina addu'a kafin na fito na samu ya tashi yana dariya, ga wani dan itacce, yana ci yana wani wurin yana faɗin. "Aryan!" Kallonshi nayi na ce mishi."Tauhid dina kai da waye?" Cikin jin dadi ya gutsira dan itaccen ya ce min.."Mammy ga Aryan, Aryan ga Mammyna!" Kallona yayi ya ce min. "Wai yana gaishe ki"
Tsoron abinda ban gani ba ya kama ni. Rike hannuna yayi ya ce min.."ba ruwanki da abinda yake faruwa!" Gyad'a mishi kai nayi tare da saukowa kasa. Anan na samu ana ta drama da case ashe har da mai babbar daki, itama ta shigo case din Nadiyyah sai kuka take Ijlal kuwa ta rantse ba zata yarda ba, domin kukan karya ce ita cutar da mata da y'a da aka yi ba wanda ya bata hakuri. Wani abu ne yayi Crossing mind dina,dama haka uwa ya dace ta tsaya danta? Sai dai me? Take ba sai reshe ya juya da mujiya ba. Inda aka bawa Ijlal laifi, ita aka zalinta amma ita aka tattara laifin aka bawa,ina jin yadda take kuka tana faɗin. "Yanzu ni ce ma nayi laifi? Su da suka aikata abinda ya faru har guduwa da Yar aka yi fa amma ni yanzu da na dauki mataki za a ce ba a yarda ba? Wato ni da Yarana ba mutane ba ne? Hatta ciki aka zubar min fa." Yadda take maganar da tab'a zuciya sai naji kamar na fita, amma haka na cigaba da aikina. Bayan na gama na fito muka kara gaisawa da mai babbar daki, ta ke tambayata jikin Ayaan, ai kuwa sai gashi nan yana saukowa. "Gashi nan yana saukowa!" Murmushi tayi, ta ce min. "Kin ga haukar da suka yi ko?" Murmushin nayi na ce mata. "Allah ya kyauta!" "Jaddar Ayaan wannan hukuncin bai yi ba sam. Ku bawa Ijlal hakuri domin gaskiya kun zalunce ta, sannan daga yau kada Aneesah ta kara dawowa gidan nan, idan ba haka ba zan mata hukuncin da zaku damu!" Rufe mishi baki nayi ina kallon Mai Babbar daki da ta zuba mishi idanu. "Aryan kazo ne?" Yadda tayi maganar na fahimci tasan waye a tare da Yaron. "Shine mai Isma, asalin magunan nashi ne, isma ta haɗa su da shi. malamin jami'an Muslunci da yake birnin Kisra ne kuma shima da na Shida a wurin Zulja da Sheikh Imran, Sarkin malamai." Tsigar jikina ne ya mike kamar xan yi kuka na ce mata.." Ummi dama kin san yana mu'amala da aljanu ne har haka?" "Aryan ne kawai. Baban magana!" Sannan ta kalle shi tana faɗin. "Kana ganin ba a kyauta mata bane?" "Eh baku kyauta ba, kamata yayi ki hukunta Maryam amma kika barta, shima Mai Martaba ya kyale Nadiyyah, sannan babu wnada ya ja ta a jiki duk da itama laifinta ne domin ita ce sanadin zubar wancan cikin Nadiyyah,kuma ta gaya mata ita ce sila,kin ga ba laifin Nadiyyah ba ne zubar Ijlale!"
"Ni kam na gaji ya sake su kowacce ta kama gabanta." "Zai sake su amma ba yanzu ba. Ai Mammy bata fahimci yadda Allah yake da girma ba, shima kuma bai fahimci kome ba har yau a mulkin da yake yi, duk da yankar bayan da ake mishi. Kai bawan Allah an yana tsallake rijiya da baya, yana matuƙar sha a hannun makiyansa gashi sun mishi kawanya ta ko ina sara suke kai mishi da suka."
Razana nayi na damke hannuna. "Bai fa same shi ba? Kawai dai Allah yana kare shi ne, saboda Yaronku idan ba haka ba da tuni anyi sallah gawarshi." Daga haka ya koma ya kwanta yana faɗin. "Ku mata adalci domin yarinyar tasan ita da Uwarta mutane ne!" Daga haka ya kwanta a jikina, barci yayi gaba da shi, tunda Mai Babbar daki ta ji haka da kanta ta haura wurin Ijlal,ta same tana tasaka yar a gaba tana kallonta. "Ya isa haka, in sha Allah zan miki adalci! Kuma zan tsaya a miki adalci!" A lokacin hawaye ya zubo mata ta ce mata. "Duk da Yarana mata ne, matsananci adalci daga gare ki, na zata zaki nuna min rashin adalci ne, amma haka da kika nuna ko baki dauki mata ba, sannan kin nuna min duk jikokin naki ne babu bambanci a tsakaninsu."
Murmushi mai babbar daki tayi ta ce mata. "Dukkanku nawa ne, matan Faris Yarana ne don haka kada na kara jin kin cutar da kowa domin ita Nadiyyah ta jima tana niman hanyar da zata rama zubar da ciki da kika yi, sai aka samu wancan shaid'aniyar ta shiga cikin lamarin daga yau ta bar gidan In sha Allah."
Daga haka ta bar dakin, ai kuwa Mai Babbar daki ta dauki mataki, ta hukunta kowa a cikinsu har da Aneesah, ai kuwa Aneesah tayi ta faɗin ita ba zata bar gidan, tunda gidan dan uwanta ne, Nadiyyah kuwa gida ta sake komawa. Da yake baya gari bai san me ya faru ba sai da ita Nadiyyah ta gaya mishi, ba sai ga kiranshi ba dauka nayi na ce mishi. "Barka ranka ya dade!" "Zaki sani wallahi ki rubuta min duk abinda gani gani nan zuwa."
"Allah ya dawo da kai lafiya!" Daga na yi shiru kawai zai fara min mita na ce mishi. "Kayi hakuri Ayaan bai da lafiya!" "Ya Allah, bashi wayar!" Haka na sakawa Ayaan a kunne na ce mishi. "Abba!" "Abbana!" "Ibrahim dina, me kake so?" "Aciyin!" Zaro idanu nayi na ce mishi. "Kai waye ya gaya maka ashirin!" Murmushi yayi yana faɗin.."Abbana!" "Ibrahim dina gaya min meke maka ciwo?" "Abba bakina!" "Ina Ummarka?" Mika min wayar yayi, na saka a kumnena." Meke damunsa?" "Fika yake!" "Allah ya bashi lafiya, kin kai shi asibiti?"
"Eh mun je an bashi magani da allurai!" "Ok Allah ya bashi lafiya, and me yasa baki gaya min abinda ya faru ba hmm? Fisabiilillahi Zainab!" "Ka yi hakuri kasan ban sa ba, kome aka yi na gaya maka ka yi hakuri zan gyara gaba." "Na san baki saba ba, amma kuma abu har da zubar da jini ai bai kyautu ba, kin san fitar da nayi fitar ku ce, Zainaba idan akace na ban fita ba taya xan tsira da kula da ku? Zainab." "Allah ya dawo da kai lafiya ki yi hakuri!" "Na gode sosai!" "Allah ya baka abinda ka fita nima!"
"Amin Ya Allah!" Daga haka ya kashe wayar ina ƙoƙarin danne damuwata, abinda Mai Babbar daki ta gama magana akai kenan wai nice zan tsaya akan kowa tunda baya nan ba wai na barsu haka ba. Ni nasan haka ba zai yiwu ba domin kowacce ta samu dama zata cutar da ni ne, kwanan shi biyar ya dawo sannan ya samu mai Babbar daki ya ce kada Aneesah ta dawo mishi gida, dama tun kafin haka yake son ta bar gidan, ashe haka ya mata ciwo, kawai ta shiga takurawa Ayaaz wanda kowa ya ganshi sai ya sake magana akan kamar mu da yaron, sai ta cusawa Yaran wani irin tsoro da wani kunci kai ko abincin da suke ciki basu koshi, haka cikin dare zasu ta kuka. Ita nan tana rama abinda nayi mata ai tasan ni ce zan saka a haramta mata zaman gidan. Kusan ajere nayi mafarkin Yaran suna kuka, sosai da mika min hannu haka wata mace da gashi a kanta a tsaye tana zane su. Ranar na biyu na farka na shafa babu babu al'amar shi, Innalillahi wainnalihir rajoun a cikin daren na tashi na tafi bangarenshi nayi ta buga kofar dakinshi ya fito yana tambayar lafiya. "Ayaan baya dakin nan?" Karar bude kofar gidan muka ji kasancewar dare ne, da gudu muka fita. Gate din gidan ake budewa shi ɗaya ya bude ta waje, wani irin tsuma jikina yake yana rawa kamar an saka min wuta. A hankali ya yi gaba kannen suka biyo shi a baya, a hankali na sulale na zauna a ƙasa, na saka hannuna dukkan biyu a kaina na fashe da wani irin kuka, yaushe na haifi monster, yaushe na haifi dodo da cikina, ga Isma a kafad'arshi. Mikewa nayi na falla mishi mari, amma ko irin faduwa yaro yayi bai yi ba kamar irin ka mari dutse haka yake tsaye, na nufi Isma zan yi wurgi da ita ya rike hannuna. "Ni ba laifi ba ne ki hukuntashi, amma ita kika tab'a, You can handler abinda zaki aikata ba." Yaya ya rike hannuna yana fadar haka, sannan ya dauke shi daga shi har isma. Na tattaro Yaran da na ga al'amar idanunsu babu barci sai yunwa. Na dauki Ayaat a bayana, sannan na rungume su bakiɗaya har parlourn Babansu na ajiye su, na shiga kitchen ina kuka domin yaran nan sun bani tsoro, haka na hada musu tea mai kauri sosai na saka ruwan sanyi ya ɗan huce, sannan na zuba musu a bottle ɗinsu, haka na dawo parlourn na basu da gudu Ayaanah ta amsa tana kurba kamar wacce ta shekara bata ci abinci, Yaron nan har lokacin yana zaune fuskarshi a a haɗe, kasa magana nayi yadda nake kokarin yadda ya fita Baban ya bashi ruwan sanyi a gora ya bude mishi yadda ya d'aga goron tas ya shanye. Ya juyo yana kallona. "Kin san rabon da a mare ni shekaru nawa? Kin san waye ni?" Hade rai nayi na ce mishi. " Ni Ibrahim na mara, kuma ka kara kwasar min Yara zuwa wani wuri sai ka zane ka!" "Ban da kece kika haifi Ibrahim da yau na miki abinda nayiwa Maryam! Ke baki san na girma kakan Junaid na uku ba?"
"Sai me?" Tasowa yayi ya nufo ni. "Ke kada ki min rashin kunya bayan kin mare ni!" Shiga tsakanin Yaya yayi yana faɗin. "Ya muka yi da kai ba nace ka kyale ni da ita ba, dole na hukuntatta." A masifance ya ce mishi. "Wani hukunta shi zaka yi? Me zaka yi bayan kana ganin ta kwatsam ta yanka min mari, kaiiii!" Ya koma ya zauna tare da daura kanshi a kujeran ya daura hannunsa, a kan gwiwar kafarshi. Kamar zai yi kuka ya ce mishi. "Uwata basarakiya ce fa? Ubana Sarkin Malami ne fa Yayuna Bintu da Sawwama matan sarakuna ne, wannan karamar alhakin ta wanka min mari kaga yadda kyakkyawar fuskana ya kumbura, gaskiya ba zan yarda ba wallahi sai na rama!" Rigima muka yi ta yi ni da Aryan har aka kira asuba, fada muke yi ni da shi kuma naki bashi hakuri aka bar Yaya da zama alkalin sulhu, cikin jin haushi ya ce min. "Wallahi sai ta bani hakuri zan bar wannan maganar!" "Ki bashi hakuri!" "Sai ya gaya min dalilin fitar min da Yarona." "Yaron Isma dai!" Ya fada kamar zai taso min, "Isma ta ci kaniyarta, Yarona na ne ni na dauki cikinsa!" Wato da yayi wani irin ihu sai gashi tsaye akan iska yana faɗin. "Ni nan na wuce tunaninki, da zaki mare ni you mere human being baku da kunya, You punk jerk!" Wayyo aljanin nan zagina yake kamar ya samu sa'arshi ni kuwa nayi banza da shi domin ban san me yake nufi ba. Wurin asuba ya sauko ya kwanta a kujera ya harare ni ya tafi. "Masifarki har da aljanu baki bari ba!" Kwasar Yaran muka yi zuwa sama suka kwanta sannan yayi mana sai da safe, lokacin da ya koma dakin Nadiyyah ta saka shi a gaba da fada da fitina tashin hankali, sai da ya korota waje, ta cigaba da ihu da zaginsa shi da ni. Kwafa Ayaan yayi. Wani irin duhu parlourn yayi wutar parlourn ya dauke bakiɗaya, wani jahilin tsoro ne ya kamata. Tsaye ta ga wata mata da sanda cikin jin haushi matar ta ce mata. "Ban da iskanci da rena rayuwar al'umma zaki zo kina mana ihu bayan Yara suna barci, gaskiya kina zaluntar na gaya miki, ki wuce don idan kika tashe su sai kin saka su barci wallahi!" Matar ta fada, tana hararan Nadiya. "Ke waye ya ce ko fito ki mana ihu? Bayan mun gama shan azabar shugaba!" Wani katon akuya me suffar mutane, zubewa tayi a sume.
"Kai dan Mama ku dauke ta ku cillata dakinta!" Inji tsohuwar tana bin wata kofa ta samu yaran suna barci wasu masu kama da yan doli. Wato gwagwai.
Kamar yadda ta fada haka suka cillata dakinta kuwa sai gata a cikin dakinta har gadonta, suma tayi suka barta haka sannan suka dawo wurin barci su.
Kusan makara nayi na tashi da wuri na hada musu abin karyawa, na gama basu tashi ba sai karfe goma ina gama na kai musu bayan nayi musu wanka, na shirya su tsaf yaran sun fada. Sallamar mai babbar daki yasa na amsa daga sama bayan na leko. "Me nayi miki zaki kwashe Yaran bayan duk kulawar da nake musu." Idan ka haifi Mutum ko aljan tow kawai kayi ta masa addu'a, wato yaron daga shi sai towel ya tashi a isa ya sauko ya same ta. "Me kika ce? Mairamu? Kin san yadda Aneesah take azabtar da su kuwa?" Wani cizon bakinshi yayi ya juya yana wani galla min harara. "Saboda baki sani ba ne shi yasa, amma jiya akan Yaran nan wancan yarinyar ta kwatsama min mari!" Wannan marin yana mishi zafi, yadda ya mata bayani sannan ya ce mata, ta koma ta duba Aneesah. Hmm wannan abin ya dame ta haka ya dawo ta samu a Aneesah a daure a ɗakinta, tana tab'a ta kama ihu tana fadar abinda take aikata.
Daga nan Yaran suka dawo wurina, na hakura domin babu Allah a cikin lamarin Aneesah, sai dai duk ranar juma'a ina kai su, daga nan suka wuni na dawo da su. A hankali kome ya dawo da sauki..
Kwana biyu a tsakanin, Nadiyyah ta fara ciwo laulayi fa, da kanshi ya gaya min tana da shigar ciki. Wato wannan lamarin na gidan Yaya akwai wani abu da na kasa fahimta shi ne, daga ni zai Yaya muka san tana da cikin domin Ijlal bata sani ba domin tunda ya gano ita Nadiyyah zasu kashe kansu akan kishi, ranar cikin dare yana ɓangarena muka ji ihun Mai aikin Nadiyya, haka muka fito ashe bari tayi a cikin daren, na musu Allah ya sawwaka na dawo dakina, na kwanta barci ya dauke ni. Wurin karfe tara na safe saboda ina period, buga gadon yayi na bude idanun a hankali. "Tashi mu yi magana" tashi zaune nayi ina hamma ga kirjina da ya cika saboda period din. "Ya jikinta?" "Da sauki sosai!" Shiru yayi kafin ya ce min. "Zo muje!" Tashi nayi na bi bayansa, har zuwa can garden anan na ga wani abu, wani bokitina ne naga an jika wani pant din Nadiyyah, kai abin so fun na ce mishi.
"Lafiya ka janyo ni nan?"
Murmushi na sake tare da cewa. "Ban gane ba?" "Baki gane ba? Wannan bokitin ne, yanzu mai aikin Nadiyyah ta fadi a asibitin tana faɗin." Takowa nayi gabanshi na ce mishi. "Aljanu ne da ita? Tow su dawo gidan nan ayi magana da aljanun." Na juya zan bar wurin ya fisgo ni yayi yana faɗin. "Ki tsaya mu yi magana da ke!"
"Ba zan taba tsaya ba!" Daga haka na wuce na je nayi wanka!" "Mai martaba, bafa haka ake hukunci ba, duk lokacin da aka yi abu bangaren biyu ake tarawa ba wai bangaren daya ba. "
Kallon Ayaan yayi da ya goyi hannunsa a baya. "Kazo bin bayan Mamar abokinka dai amma ai bokitin ta ne?" "Idan kuma aka yi dace ba nata ba ne fa? Ku dai baku son zaman lafiya, yadda ku bil adam kuke cutar da juna ko mu aljanu bamu irin wannan muguntar.....
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 33
Murmushi yayi sannan ya cigaba da tafiya hannunsa a baya yana kallon hanya, zuwa yayi wurin da aka tanadar domin shanya, yana zuwa ya saka kafarshi, ya durkusa kamar wani babba. Ya saka hannunsa a kasa, a hankali ya ciro hannunsa ya lumshe idanunshi kafin ya bude idanunsa. Juyawa yayi ya kalli Faruq da yake bayan Salmanu Faris. " Ka dauko diga ka hako nan!" Murmushi yayi ya koma kan lilo yana cillawa da shi, can Faruq da wasu mutane biyu, da hannu yayi musu alama su juya su bar wurin, kallonshi Salmanu Faris yayi yana mamaki.."ya bar nan ka saka a kama shi a bincike shi bai da gaskiya shi wancan mai kama da mutanen kirki "
A hankali Faruq ya fara tona wurin wani irin hayaki yana tashi daga cikin wurin, tashi yayi ya zo ya amshi digar buga daya na biyu wani irin ihu da kara aka yi sai ga hayaki ya tashi sama, murmushi yayi yana faɗin."Gashi nan na tona ka duba da, wancan mara kunyar da wannan abin ka gaya min waye da gaskiya?"
A hankali aka tono babyn roba mace da an rubuta sunan Faris da Zainab. Yadda ya zauna yana murmushi. "Zainab bata da kirki tunda ta kwatsama min mari, amma ba muguwa ba ce!" Yadda yake fadar maganar zaka san iya gaskiyarshi yake faɗa.
Kallon kayan yayi sai gashi ya kama da wuta. "Ina tausayawa masu mugun nufi domin daga karshe zasu girbi abinda suka aikata! Wancan ku nemi wanda ta mata sihirin amma Zainaba bata da lokacin ku, kowa ya tashi aljanu sai a yarda da maganarshi? Zata dawo gidan