Showing 18001 words to 21000 words out of 157081 words

Chapter 7 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

53

ba da bakin ciki da kishi sai ya cika ni, a bangaren mai babbar daki da wani irin tausayi take kallona, murmushi nayi mata nace mata. "Ummi idan kina min kallon tausayi zan karaya sosai zan kasa bawa kaina kwarin gwiwa."

"Zainab!" Murmushi nayi na ce mata. "Na'am Umminmu!" "Ki min alƙawarin ba zaki tab'a yarda matsayinki ba?" "Ummi duk matsayin da aka bani zan rike har karshen numfashina!"

"Daga yau zaki fara!" Kallonta nayi irin like how? " Ke a yanzu matsayin sarauniya kike, dole ki sauya!" "Ummi kamar y'a!" "Kowacce sarauniya tana act akan matsayinta ne!" "Ummi na rud'e!" Na fada!" "Ba a haife ki a cikin gidan sarauta ba, amma sarauta yayi choose dinki! Don haka daga yau daga magana, mu'amala da kowa You need to change your role!" "Akwai abinda yake bukata ne?" "Tabbas akwai, kowacce sarauniya tana iko da zamaninta ne, dole sauran su biyo bayanki as concubines!" "A tsarin mulkin masarautar nan daga watan gobe ba zaki kara barin ya ganki ba, kuma ina son ki dauka daga haka!" "Ummi!" "Jakadiya Iyaami zata dawo nan da kula dake zaki yi hakuri!" "In sha Allah!" "Daga yau maganar shiga kitchen ya ƙare!" Zare idanun nayi ta sake murmushi ta ce min. "Da gaske nake!" "Shima zan hana shi shigowa nan, idan zaki zama kamar haka dole ki dauki hanyar da na ɗauka. Tafiyar da zaki yi kenan haka kaɗai zai saka kowace mace ta tsaya a iya inda take, Ijlal ta kai hannunta jikinki, Nadiyyah ta kai Hannunta jikinki bana fatan wata ta kara kai hannunta jikinki ba tare da kin karya hannun ba, nice na tsaya miki."

A yanzu na kara fahimtar me ake nufi da Uwar miji, sai yanzu na gano wacece Mai Babbar daki, kamar yadda ta fada daga ranar ta hana na fito parlour, sannan abun da ya kara bani mamaki yadda nake karatun litattafai na addinin musulunci, su ta tara min ta ce min. "Daga wata shida Yaron cikinki yana jin ki, kuma yana sauraronki, duk abinda zaka yi yana ji. Kuma daga nan yake ɗauka. Kebe kanki daga shiga harkar kowa zai sama miki lafiya, sannan waɗannan zasu taimaka miki wurin sanin akan mutane ne da yadda rayuwarsu take, ki yi hakuri zamanki anan shine mafi alkhairi idan ya tafi zaki iya fitowa ki sha iska. Kema mutum ce." Rarrashi da nuna min fa'idar zamana a daki, sannan Jakadiya Iyaami yazo kome nake bukata zata kawo min, Jama'a ni fa a cikin Turkish film da Kdrama da Cdrama nake ganin yadda za a koyawa mace yadda zata iya zama wata mai dajara, amma ni a wannan duniyar ni ce ake koyawa magana cin abincin, da sauransu..

Ranar ina cin abinci, danne cokalina Jakadiya Iyaami tayi, tare da ɗaukar ruwa a kofi ta watsa min. "Kina Fulani Babba kina cin abinci da sauri, saurin me kike? Me kike so ki cimma? Ki koyawa abin cikinki ladabi da nutsuwa, duk wannan abincin da suke nan naki ne, wannan shine kuskurenki na farko kada ki sake barin na kamaki da laifin sauri, a cikin cikinki akwai Sarki, akwai mai bawa Sarki shawara, taya zaki koya musu gaggawa!" Hawayen da yake cike idanuna ne suka zubo min. Na ce mata. "Jakadiya Iyaami yunwa nake ji." "Idan kika dauki yunwar wata rana da shi za a kashe abin cikinki, domin baki koya musu hakuri ba! Ki yi tauna a hankali, ki sha ruwa a hankali. Ki koya musu kome da nutsuwa!" Gyada kai nayi, Mai Babbar daki tana jinsu, bata yi mamaki ba. Kuma tasan Jakadiya Iyaami ce zata yi aikin nan tsakaninta da Allah. "Kika koya musu ragwanta shine zasu tashi kome aka musu sai kuka, ki yaki rauni ki koya musu jarumta. Nasan kina da gizago zai matuƙar wahala mutum ya kalle ki ya gaya miki magana ba tare da kin rama ba, wannan ba shi nake bukata ba, kwarjinin da yake cikin idanunki da fuskanki nake so a samu wani ya dauka cikin abin cikinki, yadda Ubansu ke dakawa maza gumba a fada a samu wani ya dauka."

Anya ba zan bar musu tsarin su na gudu ba, haba ko magana ce yanzu karfi da yaji an saka ni daina dariya kamar gonar auduga, an mai dani wata bosiya. Mai Babbar daki ta saka Jakadiya dole ta saka ni na koyi Yaren kurame Fisabiilillahi dama can ni ba mai surutu ba ce. Amma ai is too hard ace sai na koyo irin wannan darasin, wai don ina Fulani Babba i follow Fulani Babba da guda tumbur. Sati Uku da farawa ni kaina nasan na sauya daga yawan mai da hankali, rashin abincin abincin kamar wata mahaukaciya, mai da kaina mai girma Fulani Babba.

Wata safiyar talata aka kawowa Mai Babbar daki, sako daga wurin wata kawarta. Wanda ita kanta bata santa ba, duba abin da aka kawo Sailuba da Jakadiya Iyaami suke, fitowa nayi na gaji. Wani ikon Allah mangoro ne masu kyau da ɗaukar idanu, kai duk wanda ya gani sai ya burge shi, haka kawai naji mangoron bai min ba. "Ko a wanke miki ne?" "A'a Alhamdulillahi!" Kamar an wurgo Isma ai kuwa tayi wani tsalle akan abin sai gashi yayi wani irin baki kirin, ta fada wani irin hauka a kai. Juyawa Jakadiya Iyaami tayi ta kalle ni ta ce min. "Kin ga ikon Allah ko?" "Ni dama bai bani sha'awa na, saboda bamu shiga kakar mangoro ba!" Mika hannu nayi xan dauki Isma tayi wani tsalle ta bar parlourn, "I...." A haukace Hajiya Mardiya ta shigo.."Ina fatan baku sha mangoron ba!" Kallonta muka yi, kafin mu sami damar magana ta fashe da dariya. "Ai ya gaya min ba zaku sha ba. Shi yasa na ce a gwada domin mu cire wannan tsinaniyar, da tazo ta kame a cikin gidan Yayari. Maryamu idan ina raye sai na kashe kowa a cikin gidan Yayari, ni Attahiru ya ce yana so kika kwace min shi." "Jakadiya a dauki Sarkin gida ya fitar da ita!" Yadda nayi maganar na mike a hankali, isma ta shigo tare da wani kukan mage mai karfi ta shiga yakusarta da haukata mata jiki da yakushi da cizo, haka Sarkin gida yaso ya fitar da ita tana ihu tare da fadar sai ta ga bayanmu. Murmushi nayi na koma daki, tun daga ranar mai babbar daki da Jakadiya Iyaami suka kara mai da hankali kaina, ana cikin wannan yanayin na shiga wata bakwai, na shiga da kwanaki kusan biyar, ina barci naji tana mishi fada, abinda naji ta fada yasa gabana faduwa. Na fito tare da kallonshi cikin mamaki da yar guntun jin haushina na ce mishi. Kallonshi nayi lokacin da na fito parlourn da Uban cikina mai suffar randa na ce mishi. "Aure zaka kara? Ina zaka kai mu? Wai meye matsalarka da auren auren nan ne?"

Banza yayi min yana faɗin. "An gama magana Ummi!" Yadda ta dauke kai, ya saka shi yin murmushi "Allah ya huci zuciyarki" ya mata sallama ya bar parlourn, "Ummi aure zai kara fa? Ina Yaya zai kai mata ne?" Na fada da wani irin jin haushi. "Ki ji da cikin jikinki, Zainab lafiyarki ita ce mai muhimmanci, ba Mijinku ba." Tun bayan faruwar lamarin dawowr Nadiyyah Yaya ya sauya kai tsaye yake abinsa ko jiya anan Ijlal ta wuni tana kuka, ga Nana Aisha da take jin jiki. Yanzu watansu biyu kenan, cikina yana wata bakwai, kafin ta haifi Yarta take ganin Ukuba ga miji har miji amma bata ganshi, ya ce ba zai fasa aure ba kuma ba zai fasa dawo da Nadiyyah ba domin akan haka take ta bori Ummi, itama ta daure mishi gindi ta ce ba zai fasa kome ba tunda itama an akan wata aka kawo ta, tayi duk abinda zata yi ni wannan rayuwar da Ijlal take gani ya fara bani mamaki da tsoro bakiɗaya kowa ya tsane ta, ta zama kamar mujiya ace tun kafin ka haihuwa miji yake maka wulakanci , ai tuni gidan Ubana zan wuce haka kawai. Ban san da maganar auren ba sai yanzu. Ban san lokacin da na fara bori ba. "Ina zai kai mata, don shine namamajo Sarkin mata sai yayi ta yi, na ba zan zauna yayi ta aure-aure har ya je ya kwaso min masifa ba, tunda mu uku bamu ishe shi ba sai ya kara wata can ya je can na bar musu shi yayi ta jidalinsa, shi yasa babu wacce take jin tsoronsa duk sun rena shi. Haba don Allah." Ba Mai Babbar daki ba hatta Jakadiya Iyaami murmushi take ta kuma kara tunzira ni da cewa. "Budurwa zai aura wallahi yarinyar kamar ka tab'a jikinta jini ya fito." Cikin fusata nace mata. "Budurwan zuciya ce d ashi, ace ka bawa arba'in baya kullum kai kenan tara mata ko me zai ta yi oh!" "Ranki shi dade kada kishi yasa ki fadi sabo, a tafi daki tai ta mita!" Inji Mai Babbar daki, wucewa dakin nayi na bar su ai kuwa na kira Abba na fashe da kuka, ina bashi labarin, sai da na gama bashi labarin tas sannan ya ce min. "Ni ne Uban Amaryan fa, yar uwarki ce sai ku hada kanku a zauna lafiya, Ikram ce yar wurin Babanki marigayi!" Ni nayi kamar an buga min dodon kunnena. Na rike kirjina ina wani irin hakki, na ce mishi "Abba anya kai ka haife ni? Abba mai ka sani ban maka ba? Abba kasan yadda Ikram take kallona!" "Ni na haife ki amma halin da Ikram take ciki duk mai imani sai ya tausaya mata, idan da Mahaifinta yana raye nasan zai mata kome ko don ta samu abinda take so!" A hankali na sauke wayar na fashe da wani irin kuka na ce mishi. " Abba ka dawo da Nadiyyah baka yi tunanin halin da zaka cilla ni ba, Abba yau da kanka ka tafi dauko min mutuwa ta da hannunka, Abba idan wani abu ya faru da aurena." Na sake wani irin kuka na ce mishi. "Kai abotanka kawai ka sani ni kuma You don't care ko na mutu ko na rayu, duk wani abinda za ayi don na muzanta Abba sai na samu da hannunka a ciki why you heat me? Me yasa Iram da take abinda taso baka nuna mata illar abinta take ba, ni duk lokacin da na fara building kaina sai ka rusa ni, daga kai har shi Salman din na tsane ku!" Na fada ina wurgi da wayar na fasa wata irin ihu ina dukar kirjina, wani irin zafi nake ji. Karfina kamar zata fashe kawai sai na fara ambaton Allah, Isma ta zo ta zauna a gefena tana kuka sharshar, shigowa Mai Babbar daki tayi ganin yadda nake durkushe ina kuka. "Idan bashi ya haife Ni ba, ya gaya min inda mahaifina yake, nasan da Iyayena n a gaskiya ne zasu kauracewa abinda zai d'aga min hankali. Aure bai dame ni ba wacce zai dauko ita ce zata kashe ni, why all me? Me yasa sai ni? Me yasa kome za ayi sai an yi da ni? Me yasa Abba bai damu da ni ba? Kowani irin abu sai na samu Abba behind the scenes? Ok shi kenan of okay indeed I move out, amma iya Haihwa zan yi idan na haihu ya nemi me rike mishi Yaransa na gaji nima!" Na fada ina mikewa na bar dakin zuwa ban daki, anan ma zama nayi na fashe da kuka, ina naushin duk wani abinda yake wurin, glass din ban dakin haka ma Farfasa su, ina jin suna min magana amma naki budewa. Karshe ina zaune a ban dakin naji an jingina kofar a gefe, shine tsaye a bakin kofar ina zaune ina kuka kamar raina zai fita. Shigo ban dakin yayi. Durkusawa yayi a gabana karshe ya zauna kamar yadda nake zaune a ban dakin. Ya riƙo hannuna, "auren ne baki so?" Ban d'ago kai ba, na cigaba da kuka. "Taso muje daki kada sanyi ya kama ki!" Ture hannunshi nayi na shiga dukar kirjinshi. "Why Ikram why ita me yasa sai ita, gara ka auro kowa da Ikram mai kake so? Virgin." Rufe min baki yayi da hannunsa. "Duk wacce zata zo bayanki ce, duk wacce na aura bayan kece. Nadiyyah tayi min halaccin da ba zan manta da ita ba, amma ke kusan rayuwata naki ne, nasan a baya bana tsaye da kafana amma a yanzu nayi alƙawarin tsayawa da kafana." Wani irin ciwo na naji ya daki kirjina n a fashe da wani irin kuka na ce mishi. "Jeka kai da Abba ku je ku shirya min mutuwata!" Na fada ina kuka mai karfin gaske domin ta haka nake jin xan ji sanyi a raina, na ji na tsani kowa. Muryan Hajjah na ji tana faɗin. "Ai wannan cin amana ne. Ban da munafunci taya Junaidu da Salamanun faransa zasu ci amanar takawara Mairamu ai anci amanar kauna, yau ban da shekaru sun ja ai da na rufe Junaidu da duka, sannan Asma'u ta gaya min ba shiri suke da juna ba yaran nan tun suna kanana gaskiya.....

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 07

Murmushi yayi yana kallon yadda nake kuka na dafe hannuna dukkan biyu a kasa, ina shashekar kuka kamar raina zai fita. "Ya isa haka kada ki daurawa akanki ciwo!" Kallonshi nayi cikin wani irin yanayi. "Can you get out of my sign!" Cike da mamaki yake kallona. "Ko ni na bar maka gidan ne?" Yadda na kara maganar a fusace ya sashi mikewa amma sai ya koma gefe ya tsaya. Haka nayi kuka har na fara jin jiri da ciwon kai. A hankali na mike naji cikin ya dunkule, a sannu a sannu na isa bakin gadon na zauna a dan jirkice ina nishi, kafin na koma na kwanta sai na ji cikin kamar gungunmemmen dutse, yadda nayi kukan ban tab'a jin nayi kuka a haka ba, sannu a hankali nayi ta sauke ajiyar zuciya, shigowa dakin Maluma tayi, ganin shi a dakin sai ta sauke ajiyar zuciya, ya ce mishi. "Je ka Allah ya tsaya maka gabanka da bayanka, ya baka ikon kamanta adalci, sannu da ƙoƙari Ubangiji ya daura ka akan makoyanka, Allah ya maka albarka!" Ta zo bakin gadon ta zauna, tana shafa kaina a hankali na ce mata.."Maluma kema kina goyan bayanshi yayi auren ne?" Na tambaye ta da disashen murya." Shafa kaina tayi lokacin da mai babbar daki ta shigo ita da Jakadiya Iyaami da Sailuba a bayansu, Sailuba ta kawo min ruwan a hankali na tashi zaune, Maluma ta amshi ruwan mai sanyi ta kumsa ta furza min, wani irin ajiyar zuciya na sauke hawaye na zuba min ta kara furza min tsigar jikina ya mike, sannan ta min na uku a lokacin na sake wani sabon kukan, tare da matsawa jikinta, ina faɗin "don Allah ki tafi da ni na gaji, zuciyata kamar zata fashe!" Mika min goran tayi na amsa na sha na mika mata, sake nuna min tayi na sha, a hankali nayi ta sake numfashi, ina jin abin cikina yana warwarewa, a hankali na d'aga goran na shanye tas, sannan na yi gatsar kukan da naci, na kwanta a hankali. Barci da kuma yajin da idanuna yake ka mike. A hankali nake sauke ajiyar zuciya, ina ji ina karawa har barci ya yi gaba da ni. Gyara min kwanciya tayi ta fito suka zauna a parlourn.."Ni kan tunda bata so a fasa auren nan kawai, ni bana son abinda zai d'aga mata hankali wallahi." Inji Mai Babbar daki tana fada cikin takaici, don ita bata son abinda zai d'aga hankalin Zainaba..

"A'a ba za a fasa ba, ki karfafa mishi gwiwa akwai wani al'amarin da bamu sani ba, ba mamaki ta hanyar auren mu sani. Sannan suna da shaidar Alhaji Saddam Tanimu Jatau ya ajiye rubutun a bisa niman Alfarman abokansa idan wani yayi nisan kwana, ina ganin wannan hujjar ya isa sannan itama Yarinyar ai kin ga halin da take ciki akansa. Kada ya biyewa Zainaba ku lalata wannan zumuncin yana da muhimmanci a cika mishi burinsa." Lumshe idanun mai babbar daki tayi ta rasa yadda zata yi ko, kanta ya kulle. "Ki kara hakuri don Allah kada ta saka ki kasa jure abinda ya zama ƙaddara a gare mu, tayi hakuri wallahi wata rana sai labari Allah ya kara mata hakuri da juriya, nasan tana da hakuri kuma sonshi ya saka ta wannan borin amma ki watsar da wasu abubuwan saboda tana da kulafuci don Allah kada ta yi amfani da raunin da take da shi a zuciyarki, ke mahaifiyarsa ce yana bukatar addu'arki, ba shi ya bukaci auren ba don Allah kada ki taya har abin ta fito fili." Yadda Maluma take rokon Ummi sai ta ji idan har Mahaifiyar Ikhlas zata yi wannan sadaukarwa a matsayinta na uwar miji zata hakura ta janyo shi da ita Zainab din, tabbas shi bai da hannu akan kome shi kanshi ya ce baya so amma ya za ayi, zancen da ake yi duk wani abinda ake Faruq da Abid suke yi ko tsinke yaki bada kudin a saya karshe Malam Junaid ya haɗa kayan aure, amma da yake shi za a yiwa auren gani ake kamar shi da zuciyarsa yake son auren, bata ce kome ba, amma kuma zuciyarta bata yi na'am da maganar auren ba, idan aka yi dubi da yarinyar a saka ma auren ta zumantar iyaye mazan ne,to amma meye ribar hada auren?

Ita kanta Maluma tsan cewa kawai ana danne Ikhlas ne amma auren akwai lauje cikin nadi, sannan idan ta ce zata yi magana tunda abin ya faru Malam Junaid ya tsaya kai da fata babu me iya rusa mutuntaka da yake tsakaninsa da Aminansa. "Amma kina ganin babu abinda zai faru idan ta farka ban tab'a ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login