Showing 9001 words to 12000 words out of 157081 words

Chapter 4 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

6

ne ba damuwarsa ba ne ta shiga fada, amma ita mai Babbar daki ta fahimci dalilin fushin Zainaba din, bayan sallah la'asar kuwa sai gashi, na fito daki ina waya da Yeemar. "Allah idan zaki tawo ki duba ko zaki ga mai rake, ko gyada mai gishiri, yawwa ki hada min da garrin kwaki." Dariya nayi da naji ta ce min. "ina zaki zuba su?" "A cikina mana, kawai ki hado min ina jiranki fa." Na fada ina zama a daya daga cikin kujeran parlourn. "Ummi Yeemar tana zuwa." "Allah ya kawo ta lafiya!" "Amin Ya Allah!" Murmushi nayi na juya idanuna akan Hajjah da na ga bakinta yana motsi. "Mariama haka kike kallonta tana gaba da Mijinta? Ke Zainabu abu ki raba kan ki da zuwa jahima, ina kallonki kika fito idan ni ban samu arzikin gaisuwa, shi ba Mijinki ba ne?" Kallon Hajjah nayi cike da takaici, na kwantar da kaina akan kujera, "ke bana son munafunci da shiru shiru, Ni jikar mai kalwa. Zaki gaishe shi ko sai na rufe ki da duka. Ke kaniyarki." "Hajjah don Allah kyale ta, bata jin dad'i baki ga ta kwantar da kai ba ne?" Ya fada yadda ya ga ina lumshe idanun yasa shi mikewa ya zo inda nake tsaye, wani irin juyi cikina yake, kafin yayi aune na sheka mishi amai bakiɗaya, sakayau naji cikina yayi dama ina ta jin haka tun dazun da na shiga na kwanta abincin ya tsaya min a ciki gabakidaya daurewa nake. "Sannu Are you okay?" Ya tambaye ni, gyada kai nayi ya mike zuwa dakin da nake ya cire kayan ya wanke sannan ya fito daga shi sai farin wando da singlet, kiran Faruq yayi a waya ya ce mishi. "Ka dauko min wasu kayan wannan ya b'aci." Ya fada sannan ya kashe wayar, ina ƙoƙarin mikewa ya dauke ni cak zuwa dakinki. "Lallai Salamanun faransa ya yarda zuciyarsa kare ya cinye. Ni jikar mutum huɗu." Inji ta fada tana kallon Mai Babbar daki da ita haka a wurinta ba kome ba ne, can kuwa sai ga Faruq, ya shigo bayan sun gaisa ta ce mishi. " Kai yanzu haka kullum zaka na yawo a tsakaninsu? Ba zaka yi aure ba ne?" Murmushi yayi yana faɗin. "Hajja kina nan ina zan kalli wata mace!" "Bana son gulma ina nan nace zan tafi fada wurin Salmanun Faransa, yarinyar nan ta nuna min kada na je yanzu don lukutar masifa daga zuwa ta kwara mishi amai, ina ita uwarsu bata gani sai ni ce mai bakin lusa nake shiga abinda bai dame ni ba, ai na gama gajiya da halin Takwara idan duniya da gaskiya ai bai dace ayi haka ba, tunda ba wurinta ya zo ba, wurina ya zo sai ta barshi ya gama gaishe ni ba wai ta kama tayi mishi amai ba. Maganar Allah wannan abin ya min ciwo." Yanzu mai babbar daki ta fahimci lallai da gaske iyayen Zainaba suka ce kada tazo, zasu ta raba hali ne! "Hajjah ki yi hakuri bata kyauta ba!" Ya fada, dai-dai fitowar Faris ya mika mishi kayan cikin girmamawa, shi kuma ya mika mishi takardar ya ce mishi. " Ka amso min drip ne yanzu!" "Ok Sir!" Ya juya ya fita, shi kuma ya shiga ciki ya sauya kayanshi, ya fito yana faɗin. "Dama tana zazzaɓi ne?" "A'a kawai dai yanzu jikin ya mata haka!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Akwai abinda ta ci kafin ta fito ne?" Yadda yayi tambayar mai babbar daki ta ce mishi. "Wani abu kake zargi?" "No!" Yayi shiru kafin can ya ce mata. "I'm think, ko food poise ne!" "Ok eh ta sha fura kafin ta shiga cikin dakin, ina ga kwanciya tayi daga shigarta. " Inji Mai Babbar daki, "Mariama me kuke ta fada ne? Na ji sai Yaren nasara kuke, kune kuke ji bamu ba." "Abincin da ta ci ne ya lalata mata ciki!" "Innalillahi wainnalihir rajoun Innalillahi wainnalihir rajoun Innalillahi wainnalihir rajoun. Cikin ya lalace?" "A'a Hajjah ba irin wannan lalacewar ba, cikinta ne ya kumbura shine bai sakata kashi na ya sakata amai!" Yadda Mai Babbar daki ta warware bayanin ya saka hajjah cewa. "Kai haba na zata irin wannan ake kashe dan tayi ne! Allah ya bata lafiya!" Ta fada tana leka dakin, shiru ne ya wanzu a parlourn har faruq ya shigo ya amshi tarkacen ya shiga dakin, ni ina samun kaina da nayi aman barci ya dauke ni. Saka min ruwa yayi da allurai barci ya dauke ni. Ya fito parlourn ya cewa Ummi. "Don Allah kada a tashe ta, ko hayaniya a barta tayi barci, Munirah zata zo in sha Allah!" "A'a bar Munirah nan, zamu kai ta ina take ganin likita!" Kallon Mai Babbar daki yayi kafin ya ce mata."ba matsala !" Bai san dalilinta ba, amma zai iya cewa yana da nasaba da sauran matan wurin Munirah suke wasu abubuwansu. Fita suka yi can kuwa sai ga Amina Zurmi, ita da kanta ta duba ni, domin ina barci har yadda take tab'a cikin na bude idanuna. "Sleeping beauty kin farka?" Ta fada bayan ta gama abinda zata yi. "Hajiya Maryam yarinyar nan jininta yana hawa, ji ga barci take amma jinin bai sauka yadda ya dace ba." Shiru tayi kafin ta ce mata. "Tow yanzu Mai zance? Ko zaa kaita asibiti ne?" "A'a nasan abinda kike gudu Allah na tuba wannan gidan naki ai bai da banbanci da sansanin mayyu. " Tana fadar haka ta min allura sannan ta juya suka fita, barci ne ya dauke ni, ban farka ba sai can cikin dare na bude idanuna. Allah sarki Hajjah da Isma ne a gefena ita hajjah tana sallah, isma tana kwance jikin cikina, sai gurnani take yi.

****

Rayuwar Ijlal kamar hell ta ke jin shi, abubuwa goma da ashirin, na farko Salamunu faransa dai ya hana a shiga bangarenta, na biyu ya hana ta fita idan ma awo ne a cikin gidan ake zuwa ayi mata, na uku ba ita ba Amiratul Zaitunah tsakaninta da ita sai gani sai hange. Kome ya jibga mata amma bata isa ganin shi ba. Sannan wani abin da yayi shine kwace wayarta, bata fita, kuma na a shiga mata. Haka yasa rayuwarta ya zama wani irin tashin hankalin, mijin da take ta makircin a bar mata shi gashi nan amma sai dai ta ji fitarshi da shigarsa, asalin nurse ya dauko ya sakata a BQ dinsa, sannan ya bar bayi biyu wanda suke lura da yarinyar, sai nurse da take zuwa ta wuni sai dare ta koma. Yana biyanta kudi kawai don ta kula da Amiratul Zaitunah kusan dubu dari biyar, sannan ba iya jinyar ba hatta bata yadda za ayi na koya mata wasu abubuwan da tausar kashin jikinta..sai dai a yadda yarinyar take har yau bata zama sai a kan keken yara, kanta naya tsayuwa, rayuwar yarinyar abar tausayi ne idan ya dawo da dare zai je ya dauko ta ya mata wanka ya bata abinci sannan yana mai saka mata abubuwan da zasu taimaka mata wurin motsa jikinta da kafarta. Wannan abin yayi matuqar taimakawa, sannan ya sani wani Machine da ake sakawa a wuyarta, yana taimaka mata wurin juya kanta. Idan ba don ciwo ba yarinyar nan wani irin kyau take da shi tabarkallah, haka yarinyar take kamar ka sace ta ka boye.

Tun ranar da Zainab ta gaya mishi magana, yake ganin kamar laifinsa ne na samar da Amiratul Zaitunah ta wannan hanyar duk yadda yaso ya cire ganin laifinsa baya iyawa. Wannan abin sa shi yake jin wani zafi da ciwo. Yana tsoron rabuwa da matan kada ace yakasa zama da mata, sannan gefen Nadiyyah bai tab'a kawowa Iyayenta zasu sauko da wuri duba da yadda Zainaba ta karya mata hannu, amma Ubanta har kiransa yake yana bashi hakuri, shi kuwa yaki amsawa.

- A irin wannan lokacin aka fara azumin watan Ramadan, kamar yadda nayi rabo wancan karon haka wannan ina gida nayi, zuwan Iyayen Nadiyyah uku amma mai babbar daki ta ce ita babu ruwanta su samu mijinta, Baban Nadiyyah yayi ta bada hakuri amma Mai Babbar daki tace ita ba ruwanta, ko Zainab da yace ta zauna har yau bai waiwaiyeta ba, haka suka koma Jos, ranar da aka kai azumi goma, ba sai ga Nadiyyah ba, abinda yayi mata sai da ya bani tsoro na kuma yarda idan yayi fushi yana da wuyar sauka. Domin sakawa yayi aka hanata shiga cikin masarautar, da ta matsa kuwa ya tura Faruq ya amso mishi princess, ya ce ta tafi dama ita ɗaya ya aura. Yarinyar kuwa ganinsa ta kwanta a jikinshi har tana ajiyar zuciya, saboda Salamanun Faris Yana son Yaranshi. Har aka sha ruwa Nadiyyah tana zanzabira, ganin fa wankin hula zai kaita ga dare ta wuce wurin Alhaji Mamman Abba yayari, tana kuka har yanzu hannun bai warke ba, tana rokon ya saka baki Salmanu Faris ya bata yarta. Sanin kwanan ana wani rikici wnada yasa shi dole ya koma gefe domin abin ya shafi dattawan fadar, a matuƙar fusace Mai Martaba yake da kowa haka yasa duk suka shiga hankalinsu. Kasa yayi da kai kafin ya ce mata. "Maganar gaskiya kwana biyu nan muna fama da Mijinku, wallahi rikici yake ji yanzu dai bari na kira Uwarsa sai ta barki, ki kwana fada gobe ki koma sai mun yi da gaske ya hakura , sannan kema kin yi laifi akan me zaki tafi matarsa da ciki ki mare ta, yanzu gashi ita bata saka an daure ki ba, sanadin haukarki da kishi kin saka ya sake ki, sannan yadda ya gayawa mahaifinki ba yau kika fara ba don Allah ki daina wannan shirmen ita kun ji ya tab'a yunkurin rabuwa da ita ne?"

"Alhaji ka bar wannan zancen amma maganar gaskiya malam Junaid bai bar shi haka ba!" Kallon matarsa yayi ya ce mata. "Zaki iya tsayawa a gaban Ubangiji ki bada shaidar haka? Idan da Junaid yaso haka da har abada bawa Faris zai zama a wurin yar Junaid, ki gane Junaidu bai daga cikin mutanen da suka kauce hanya, baiwar da Allah ya mishi ba don ya kafa Yaranshi ba ne, yarinyar idan kika ce min bata da kunya a baya zan yarda amma koda wasa bata taɓa irin wannan haukar ba. Duk gidan da tarbiyar ya samu gindin zama zai matuƙar wahala mace ta ɓata lokacinta kanshi, ita zata yi ta gudunsa shi kuma yana nanike mata abinda yake faruwa kenan a cikin gidanshi, sun kasa zaman lafiya ta miji hankalinsa ba zai karkata kan wacce take bashi nutsuwa ba, ki jira na kira Maryama!" Wato mai babbar daki, haka kuwa ya kirata, kasancewar akwai mutuntatta juna haka ya roketa alfarmar ya turo mata Nadiyyah ta kwana wurinta kafin a san nayi gobe, ita tunanin Nadiyya ai ya kawo min yarta ce, haka yasa koda aka shigo da ita abinda ta fara kiran Yarta, sai ta ji shiru cikin damuwa ta zauna gaban mai babbar daki da take kokarin yin Allah Magariba, ni kuwa ina daki don tunda aka fara azumi ban iya ba, ban kuma ki yi don lalace ba, condition dina nace zan yi azumi daga ni har babyn zamu jigata domin bana iya rike cikina yanzu, haka yasa duk abinda aka yi na buɗe baki an kawo min dakin. "Kin zata ya kawo yarki ce nan? Hmm bai kawo mana ita ba, balle mu rike miki ita. Har yanzu wannan haukar yana cikin kanki, tow wallahi zaki saka ya nisanta ki da yarki matukar kina son zaman lafiya ki cire yar nan a ranki domin ba zai baki ita dukka ba."

Daga haka ta wuce daki ta tashi sallah, ita kuma Sailuba ta kawo mata kayan shan ruwa, a hankali take ci tana kuka. Sai wurin karfe tara saura ya kawo Yarinyar domin babu wnada ya gaya mishi uwar tana nan, itama mai babbar daki bata mishi magana ba, yana ganin Nadiyyah ya haɗe rai kamar bai tab'a dariya ba, shigowa yayi ya zauna yana gaida Ummi da shan ruwa ni kuma na fito, zan yiwa Ummin korafi na gansu, kunsan sai da gabana ya fadi sai na tuna ashe fa ya sake ta. A hankali na wuce wurin zaman mai babbar daki na ce mata. "Ummi a cikin maganin nan anya babu na cin abinci? Wallahi cin da nake ya isa ace mutum uku suke ci!" Murmushi tayi ta ce min. "Alhamdulillahi tunda lafiya ce! Ni dai yau tunda Hajjah ta tafi unguwar Malamai bata dawo ba!" "Yau baki ji ni da Isma mun wuni cikin salama ba,ai Hajjah ruwane kawai bata daura min ba." Na fada ina kallon kayan abincin gabanta. "Ummi na karasa sauran?" "A'a bari a zuba miki wani mana?" "A'a wallahi!" Na dauke kwanon na fara cin dan waken ina gyada kai, har lokacin Nadiyyah kanta na sunkuye Yarta tana jikin Ubanta. Ko da wasa yarinyar bata yarda da kowa kamar Uban a raina nace. "Mugu yasan yadda yake saka yaransa su kaunace shi, sama da kowa." Bayan na gama cinye dan wake na wuce kitchen na wanke hannu, na samu Sailuba tana fama da aikinta na ce mata. "Sannu ina gurasan nan?" "Maman yan biyu abincin aka zo ci!" "Ke dai bari bakina ya gaji amma cikina bai koshi ba!" "Ya isa cin abincin nan, ki kula da lafiyarki mana!" Ya fada yana ɗaukar Madara. "Ni fa Yaya ka saka idanu!" Daga haka ya fita bai ce uffan ba, haka na gama kwadayina na koma daki na zauna, ina kwance ba sai ga Nadiyyah ba ta shigo dakin. "Wato ke baki da zuciya ne?" Kallonta nayi ta bani dariya na ce mata. "Na yar kare ya cinye!" Kallona take a hankali tana gyada kai. "Ranar tare ta kore mu, me yasa baki tafi ba?" Shigowa yayi ya ce min. "Idan kin gama ki shirya zan tafi da ke!" "Tow!" Haka muka shirya muka fita ya ja kofar dole ta fita daga dakin, can dakin da Hajjah take nan ta zauna ya bar mata yarta a wurinta, baya ya ce Faruq ya kula da gidan, lokacin da muka isa gidanmu, tarba sosai aka yi min musamman ni din, abinci babu wanda ba a kawo min ba, na ci sosai har ina nishi. "Abba a bar namar nan xan tafi da su gida, Maluma yaushe zaki min panke!" "Allah sarki ki ji da kanki ma tukun dole ne sai kin ci ya fi karfin ki?" "Gaya mata dai ai Mariama tana ƙoƙari, yi wannan ai riketa dai gwamnatin tarayya, wuni take ci bakinta baya zama lami, tayi ta saka saloba tayi ita kanta Mariama jiya tana fama da azumi wai ta shiga jefa mata dan wake, ni ina zan iya wannan danyen aikin, shekaran jiya haka ta saka ni kunun tsamiya amma na madara, kada ka ga yadda na gaji yar banza karshe ta ce wai yana karnin madara ai ga Salamanun faransa idan karya nake mata." "Abba don Allah ka rike Mamarka kada nauyi yiwa Ummi yawa." "Ungo naki yar banza mai mugun hali, Salamanun faransa kada ka ce min hade kai kuka yi ku ci amanata kai da Matarka!" Tura baki nayi na ce mata......

[8/26, 5:41 PM] Ramlat Manga41: 04

"Hajjah nawa ke na zo dauka dama." Murmushi tayi tana faɗin. "A'a ai ni dawo kenan, mai zan yi wanda mairamu bata mata ba? Hatta ruwan sha idan ta ce ba zata sha da kanta ba, zata bata ne! Ina ganin abubuwa rayuwata amma soyayyar Mairamu da Zainabu abu daga indallah ce ban isa ba shi yasa da Tauhidi ya zo na bashi fantigwarwata ya kawo min ba zan iya zama cikinku ba, iya wannan kuka mun ma ya ishe ni na gode sosai. Sannan ina ta son na baka wani abu amma ban san yadda zaka amsa ba." Ta mike tana faɗin.."taso muje!" Haka ya bi bayanta har zuwa dakinta. Yana zuwa ta d'ago bankaden gadonta, ta ciro wasu ciyawa a takarda da wani tsinke ta mika mishi. "Wannan kakanina Buzaye suke amfani da shi, sai wannan ciyarwar shayinsa zaka na dagawa da kanka, da Zainabu abu tana tare da kai da zata iya dafa mata, in sha Allah ka sha wannan sannan ka rike wannan ka wanke bakinka da shi, Salamunu faransa sai kace mace ta tsalleke maganarka, na lura matanka sun renaka baka isa kayi gyaran murya ba babu wacce take ji, Mahaifiyarka tana cikin damuwa da rashin zaman lafiyar gidanka. Wannan kwalli ce dan gidan Tarasulu ya haɗa min, cikin gidanka matuƙar akwai ajiya ta mugun nufi zaka ganshi. In sha Allah domin ba karamin hadi aka yi ba, sannan wannan kuma a sayi gaban sa da gwaiwar sa jijjiyar raƙumi Mairamu ta dafa maka ka ci sau daya ka tashi. Wallahi matuqar kasan ciwon kanka tow mata zasu ta bin ka ba zaka kara bin mace ba, kada kara bin mace ko da yake wancan yar mai kama da sauron tana baka wahala, kana mamakin yadda ita bata damuwa da kai karya ne tana sonka, ita haka Allah ya yi ta idan ka cire fada tow zata iya boye maka kome ba tare da ta fito da shi wani ya sani ba, ta iya danne ciwon da yake ranta don kada mata dariya kuma mahaifiyar ta gada. Kayi hakuri daukarta da aka yi saboda lafiyar cikin ne, Salamunu faransa gidan nan naku, na ji abu na ga abu. Kaga wannan yar magen da kake kora, Allah ne ya hada ta da ku." Murmushi tayi ta kara murmushi ta ce mishi. "Gidanku cike yake da fitina asalin na kafuwar masarautar nan, sannan akwai wnada aka gayyato. Ban san yadda zan gaya maka ba, amma sai kayi da gaske." Ta mika mishi wani garin magani a jikin fatar kura. "Garin nan ban san iya fatar namun dajin da aka hada ba, amma da kake ganinshi. Idan zaka fita fada kayi hayakinsa, in sha Allah duk wnada ya so da mugun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login