Showing 153001 words to 156000 words out of 157081 words
waye ke kashe min su? Ayaan gaya min don Allah!" Wani doro Ismaha tayi a kafad'arshi tana wani irin kuka. Shafa kafadar magen yayi yana murmushi ya ce mata.."gubar a jikinki yake, ko.da zaki haifa dubu ne zasu kashe ki kawo kunnenki?" Matsawa tayi tana kuka. Ya ce mata. "Ita Addah sadiyyar ba kyale miki ita zasu yi ba, ke keka amshi ragamar rayuwarki a hannunki. Mammy Kuma Allah ta barwa nata rayuwar!" Daga haka ya fita waje, shafa magen yayi yana kallon Ijlal da Amaryan Babansu, hankalinsa kwance ya nufi hanyar waje. Yadda gate din kofar gidan ya bude kanshi ya juya yana kallonsu, murmushi yayi ya saka kai ya fita daga cikin gidan..
Kukan Nadiyyah ya dawo da ni duniyar tunani, na zuba mata idanun. "Ya isa ki kira Mai Martaba ayi jana'izarshi." "Zainaba haka xan rayu rayuwata a mace?" Zuwa yanzu da nake da cikin na uku tsoron kowa nake ji, koda yake mijinmu ya kara bani kariya tun bayan haihuwarsu Ayyanah, ya bani dukkan ni wani kariya, kofar gidanmu da Yarana suna cikin tsaro, Ayaan ne kaɗai baya bukatar kome na tsaro domin Baba titi ya gaya min cewa kaf duniya Allah kaɗai zai iya daukar Ayaan ba dai mutum ba, a yanzu haka da ya fita fada zai nufa wurin Babansu. Kuma tazarar da take tsakanin fadar da gidan akwai nisa. A yanzu Ayaan yake da shekaru huɗu zuwa biyar amma yasa kowa a gidan barci cikin salama, tun rasuwar yar uwarsa Ayyanah.
Bayan ayiwa Yaron sutura, na kara jan Nadiyya a jiki wacce rashin lafiya ta fara kamata, idan ta zauna sai kuka. Kamar wacce take dansanin abinda ta aikata. Amma ban takura kaina ba, Ijlal ta ce min.."Mammyn Yara kina fama da Laulayi kina daurawa kanki damuwa, akwai abinda take boye mana, wanda Allah kaɗai yasan me tayi yake bibiyarta, sannan ai kin ji Ayaan ya ce gubar a nononta yake. Gara tayi hakuri ta barwa Allah, ga mijin da muke yaki akanshi shima ba nutswa ne da shi ba yanzu duk da yadda yake kaf-kaf da mu. Haka bai hana shi a farmake shi ba, na gaya miki jiya farkawa nayi.na ga Ayaan a gefenshi rike da hannunsa sai zuba Uban yaƙe, Allah yayiwa Yaron nan Albarka Ubangiji ya ƙare shi da kariyansa amma tabbas Ayaan yana cikin ni'imar da Allah ya mana shi. Kin san me ya ce min, koma ki kwanta babu abinda zai faru, ai yayi nasara saura kaɗan kawai." Yadda ta fada min maganar sai naji na kara shiga damuwa. Ni fa Allah ya gani ba zasu bude min idon Yaro ba, na gaji da abubuwan da yake sak na bokaye, a raina nake Maganar sai ji nayi kamar a bayana an ce min.."Kul ba zamu tab'a saukar miki da d'a akan Hanya ba, kulawarsa a cikin ajalinsa ne bayan nan bama fatan mu cutar da iyayen da suke faffutukar tsayawa akan kafarsu ba, in sha Allah nasara tana gaba kaɗan saura kiris!"
Juyawa nayi na ga ba kowa, ajiyar zuciya na sauke wannan lamarin da ban tsoro yake, ni na ma fara tsoron gidan nan. Ina dalili kullum kara razana na min zuciya ake, idan nayi magana Aryaan ta ce sai na bashi hakuri. "Waye ya ce ki ambace ni ranki, ai gani me zan..." Komawa gefe yayi yana faɗin.."Tuba nake Malam!" Kallon Ijlal da ta bar wurin ta koma wurin Yara, na ce mishi. "Kasan Allah na gaji da wannan abin da ake yi min Yarona ya zama mai gane-gane, kai kuma ka fara wallahi ba zan yarda ba."
"Idan na gaya miki, Mijinku yana niman aure hala sai kin falle min kai ko?" Kura mishi idanun nayi na ce mishi.."Ranar Afra ka ce min ina da ciki, yau kazo kana gaya min Mijina yana niman aure da wannan rayuwar da yake yi?"
"Hehehehe, ki bani hakuri na wargaza auren ni fa ba wani abu bane. Iyayen Yarinyar wasu yan siyasa ne ya hadu da ita a Abuja ta makale mishi, amma xan iya yin kome domin lalata auren domin ke idan kin yi hakuri ijlal ba zata iya ba shi kuma ya shirya tsaf!"
Shiru nayi ina kallon kofar raina ya gama b'aci Yaya bai da kirki a wannan yanayin da nake niman hanyar magance matsalolin masarautar shi ta aure ma yake Allah mun gode maka da ka haɗa mu da asalin original Namamajo..............
[8/31, 8:42 AM] Ramlat Manga41: Ending
Kamar Aryaan ya sani ya ce min. "Ba fa na gaya miki ku yi rigima ba ne. Na dai gaya miki ne domin ki san yadda zaki fuskance shi. "Ni an gaya maka zan biye mishi ne mu yi rigima?" Murmushin takaici nayi ban kara nuna mishi na ji haushi ba. Shima Yaya ban yarda na mishi magana ba, abu daya na ce mishi."a lalata auren zama damu kuwa yanzu ya fara!" "Yanzu naji batu;" a wannan lokacin da kome yake ƙara tsamari shi aure ne a gabanshi, banda rashin mutunci irin na d'a namiji, ban san yadda aka yi ya fadawa Ijlal ba, yarinyar nan yar bala'i ce domin haka tayi ta masifa tazo take gaya min ban yi mamaki ba, sai dai hakuri na bata nace nima haka na ji, ai fa ya ga tashin hankalin da bai tab'a gani ba.
Jinyar Nadiyyah sai da Uwarta ta zo tayi zaman jinya kafin yar ta samu sauki domin mahaifar ma an rufe mata shi, an ce ta hakura da haihuwar. Bayan wasu watanni kome yana zuwa da sauki da kuma kalubale. Haka watan azumi ya kara zuwa, ranar da aka kai azumi na farko a ranar aka bawa Amiratul Zaitunah, guba sai dai wannan karon na fara zargin ko Ijlal ce, domin wani lokaci tana yawan nuna da Mutuwa Yarinayr tayi da ta huta, amma ban tab'ata sakawa a raina zata iya cutar da yarinyar ba, kasancewar mahaifiyarta sai dai akwai sakaci irinta Uwa, an ceto rayuwar Yarinyar, sai na zuba idanuna akan Yarinayr da Uwarta.
Haka muka cigaba azumi har aka yi sallah, a wannan shekarar shima Yaya ya kara biyawa Nadiyyah kudin aikin Hajji suka tafi tare, a can suka ga likita har ta sake dauko ciki, tana dawowa jinya ya sakata a gaba, a lokacin asibiti suka gano tana dauke da Cancer, sannan an saka mata wa'adin da suka rage mata bai wuce shekara biyu, sannan sun ce idan cikin ya girma wa'adin zai kara raguwa haka suka cire cikin da ranta yake so, tayi ta jinya da kullum sai an kara mata jini.
Amma wani lokaci haka zata yi ta masifa da jidali, ba mai kulata domin kowa yana fama da na shi rigimar da yake damunsa. Haka Allah ya sauke ni lafiya na samu Y'ace, wacce muka mai da mata sunan Mai Babbar daki, ana kiranta da Sultanah. A ranar da aka yi sunan sultanah, Nadiyyah ta saka a kirani, ina shiga ta rufe kofar tana tari. Zama tayi tana murmushi. "Na kira ki ko?" Nasan ba mutunci ne da ita ba. Haka yasa na zuba mata idanun. "Wannan naki ne, na ga kina ta fadi tashi akan dan uwanki, gashi nan!" Wasu dukiyarta ne, sannan ta kara tura min wasu tana faɗin. "Wannan na Princess ne, Ikhlas ga shi na Saadiya ce. Ke daya zaki iya min wannan alfarman, sai tarbiyyarta na san zaki iya, ni dai na san nayi wani kuskure ɗaya da na kasa fadawa kowa, shine a lokacin da kuruciya da kuma son na zama tauraruwa, na shiga kungiyar shan jini ta ulimuniter, inda na sadaukar da mahaifar ciki, mun yi dasu ba dan taba haihuwa ba, daga baya sai na fahimci ina son haihuwa ina son na haihu nima, wannan yasa suka yi ta farautar rayuwar duk abinda na haifa, kin san me yasa basu tab'ata ba saboda ita din ce kika roka Allah ya bani, ita din tana zagaye da rahamar Allah da ni'imarsa, Alhamdulillahi Ubangiji ya kara kare ta cikin ikonsa da buwayarsa, ni dai nasan kowani lokaci zan iya mutuwa, sai dai ban tanadi kome ba."
Tausayi ta bani domin Nadiyyah yar gayu tayi baki tayi muni kar ba ita ba, kowa ya ganta sai ta bashi tausayi. Haka na baro dakin na jira Yaya da ya dawo na fada mishi, gyada kai yayi shima duk ƙoƙarinsa akanta sai da ya gaji.
Haka muka cigaba da kula da Nadiyyah har aka samu wata uku, ranar Yaran sun parlourn ni ina daki na kwanta bayan sallah azhar, aka yi sallama ban fito ba kasancewar yaran suna parlour, haka na ci gaba da kwanciyar. Can na ji masifar Ijlal wai an shigo gida an basu sako basu fada ba, ta shigo dakina ta mika min. "Sakonki ne!" Tana ajiyewa ta bar dakin dauka nayi na fara dubawa.
_Ki janye daga siyasa ko kuma ki rasa duk wani Yaron da shi Mijinmu domin na shirya tsaf!_
Ikram Saddam Tanimu Jatau.
Tsaki nayi na ajiye takardan, ai kuwa ban yi wata wata ba, na kira Faruq na gaya mishi, har na tura mishi sai gashi ko awa ba ayi ba aka shiga bin Ya Abid domin bashi kariya nima cikin gidan an kara jami'an tsaro, sannan gefe guda an fara shirin zabe saura watani uku. A cikin watanni da suka rage dole na kara saka idanu, duk wani kamfen da za'ayi an yi sannan an duk abinda ya dace, abinda Nadiyyah ta bani shi ya taimaka mana da wasu kashe kudin, a nan na fahimci siyasa idan baka da kudi kai da mabaraci daya kuke.
Haka kwanakin zaɓen suka zo, har aka yi zaɓen sai dai ranar da aka gama zaɓe aka fara kirga kuri'a, a wannan ranar Yaya ya fito sallah la'asar aka harba shi wanda yayi daidai da shigowan Ikram ta dauke Amiratul Zaitunah, ban san me yasa take harin yarinyar ba, sannan nayi zargin da saka hannun Nadiyyah ko Ijlal, ga halin da Yaya yake ciki, haka aka kira manyan likitoci daga asibitin, wanda suka yi harbin an bisu an kama masu. Sannan a cikin gidan da aka kawo shi raina ya b'aci, bayan tafiyar sauran likitocin ya rage Doctor Andrew.
Dama tun kafin zaben na hada Mai Babbar daki da Yaran sai Amirah Zaitunah ce bata samu passport ba su kuma suka bar kasar zuwa Madina daga can zasu wuce Scotland, haka yasa na sake mai daga hankalina wurin kula da Yarinyar ashe ni da sauran matan mun.fita ta shigo ta idda nufinta.
Bayan tafiyarsu na rubuta sako zuwa zuri'ar Yayari, domin so nake nayi musu godiya da tarin Alkhairinsu a gare su Ni.
Safa da marwa nake a parlourn,
Sake zama nayi da kyau na ce.
"Faruq ka rufe shi, kada ka sake ya fita. Ka tabbatar da an binciko duk inda Ikram Saddam Tanimu Jatau take, bata ci bulus ba."
"An gama Fulani Babba!"
"Ayaan da mai babbar daki sun isa Madina daga can zasu wuce Scotland kamar yadda kika shirya."
"Ka tura sakona ga ahalin Yayari?"
"An tura ranki shi dade!"
"Ya batun zaben waye akan gaba?" "Abid Junaid Gobir!"
"Ijlal fa?"
"Tana rufe a bangarenta."
"Na gode! Ka tabbatar an farauci Ikram, Gwaska dakare."
"Alhaji Nafi'u da Rilwanu ba?"
"Na bar mishi aikin ya ji da su...."
"Alhamdulillahi gubar bata yi tasiri!" Inji Doctor Andrew da ya fito a hankali, yana faɗin. "
"Mun gode!" Na fada ina kallon dakin da ya fito. "Yarinyar bata yi kome ba, wannan shine karo na uku da take kokarin kashe yarinyar dole a farauce su, a nime su a gurfanar da su, shi kuma Khalifa da Ahmad duk wnada ya kare su a gaya min zan ji da shi."
"Faruq a dakatar da haduwata da ahalin Yayari, kawai kowa ya saka idanu akan shi." Sannan Doctor Andrew ya ce min. "Harbin Mai Martaba bai wani shiga ba, sannan ko zuwa gobe ne dai iya fara uzurinsa." Ban ce kome ba, na dai amsa da Allah yasa.
Kwanaki uku aka yi su Ijlal suna rufe domin abinci ma mika musu ake, ranar Monday aka fitar da sakamakon Abid Junaid Gobir ya lashe Zanzabira bakiɗaya, sannan na saka a bude Ijlal, Nadiyyah kan asibiti aka wuce da ita, Ijlal dakina tazo inda Amiratul Zaitunah take tayi ta kuka tana faɗin. "Ba zan tab'a kashe ba Ikhlas wallahi na san yadda kike son Yaranki haka kike son Amirah ba zan tab'a cutar da ita b" ajiyar zuciya na sauke Hawaye na zubo min na ce mata. "Ban shirya rabuwa da abinda nake so ba ne, shi yasa na yi haka amma ki yi hakuri."
Haka Yaya ya shigo ya zauna, ya ce min.."an kama Gwaska dakare, zan fita." Ya saka wata jacket baki da bakin hula, sai da ya rungume ni, sannan ya rungume Ijlal, ya fita. "Sai ka dawo Allah ya tsare."
Haka ya fita a hankali yake takawa yau zai rufe wasu abubuwan da suka sha kanshi, yau zai shafe abinda ake rigima akan shi. Haka ya wuce office din Yan sanda ya ga Gwaska dakare, murmushi yayi sannan ya ce mishi. "Duk gudun da kayi tayi yau gashi ka zo hannu." Murmushi yayi ya cigaba da cewa. "Alhamdulillahi!" Daga haka ya bar office din, gidan Alhaji Rilwani Yayari ya nufa, a lokacin ya same shi yana zaune a parlourn idanunsa na kan Jarida, zama yayi yana murmushi ya ce mishi. "Sannu Kawuna!" Kallon juna suka yi, kafin ya cigaba da cewa. "Naso nayi maka farat daya ne, amma a yanzu bata b'aci ba. Ukasha!" Fitowa wani matashin saurayi yayi, ya gaida Salmanu Faris. Sannan ya koma bayansa. "Yarona ne, tsawon shekarun da ka yi kana tare da shi, ai da hannuna na bashi guba yayi ta ciyar da kai yadda kai kanka ba ka sani ba, sannan Ahmad Rilwani Yayari kuwa, tuni an wuce da shi asibitin mahaukata yadda ba zai kara moruwa ba, kaima na maka da kauna saura abokin cin mushenka!" A hankali ya mike tare da kallon Yaron ya cire kayan aikin ya ajiye yana faɗin.."kafin na tafi xan ce wani abu, ni ne wanda ka saka aka kashe mahaifinsa saboda yana tare dasu Marigayi Attahiru yayari da sauran abokan ciniki, Ukasha Jamal kaho!"
Daga haka suka nufi gidan Alhaji Nafi'u, wanda gidan da yake cike da masu tsaron lafiyarshi, haka suka wuce cikin gidan babu wanda ya dakatar dasu. Mikewa Alhaji Nafi'u yayi yana nuna shi da Yatsa.
Murmushi yayi yana kallon Alhaji Nafi'u da yake gabanshi, wanda a baya can aminin mahaifinsa ne amma a yau da ya koma makiyinsa zalla gani yake kamar idan ya kyale shi Allah zai tsine mishi albarka ya tab'e ya lalace ya zama mara amfani a cikin al'umma. "Da fatan kafin shiga da fice kana fahimtar meke faruwa a wannan duniyar! Bumm!" Bai rufe baki ba daya daga cikin bodyguard din Alhaji Nafi'u ya shigo da gudu. "Yallabai mai gida Khalifa ga shi can yana ihu da hauka!" "Khalifa?" Ya furta da karfi zai mike. "Koma ka zauna!" "Kai Salman?" Ya daka mishi tsawa, hannu ya saka a kunnensa ya sosa kafin ya cire ya hure hannun, sannan ya saka hannu a aljuhun gaban rigarshi ya fito da wani kwalbar allura Gamma-Gamma-Aminobutyric Acid (GABA) "Yallabai yana ihu!" Masu kula da lafiyar Khalifa suka fada da ƙarfi. Murmushi yayi ya ce mishi." Regulates mood, stress, and fear
For our brains to operate effectively, the brain releases neurotransmitters that communicate with the rest of the nervous system. The way this process works is, wanann shine halin da danka yake ciki, ba mamaki idan ya kasance ba dukka kwalbar na juye mishi zai dauki short term kafin ya sake shi, idan kuma aka yi dace nan da sati daya yana hauka." Sannan ya mike ya zuba mishi idanu. Ya kai tsaya biyu idanunsa da hannu ya ce mishi. "Ina kallonka idan kaso kada ka bada kai. Ni kuma sai na tabbatar da, bummm." "Me kake so?"
"Idan ka cigaba da zama khalifa zai mutu, domin shine karfinka, sauran Ya'yanka fa? Ka mika kanka ga hukuma sannan ka tabbatar da ka gaya musu yadda aka kwana a ragaya, domin ba zan kyale kowa a cikinku ya sha ba." Daga haka ya bar gidan.
Kamar yadda yayiwa al'ummar Zanzabira barna, haka kuwa ranar ya kwana da zulumi,.
***
Muna gama girki ya shigo, rungume shi nayi ina faɗin. "Sannu da ƙoƙari, da sannu Allah zai hukunta su." Daga haka na kai shi daki na zaunar da shi. Rungume ni yayi yana faɗin.."kina ganin kome ya zo karshe?" "In sha Allah kome ya zo karshe!" Daga haka na bashi magani ya kwanta.
Washi gari, a labaran BBC muka ji labarin rasuwar Alhaji Rilwani Yayari, Alhaji Nafi'u ya mika kanshi tare da wasu manyan mutane da ya lissafi a saka hannu a mutuwar matashiyar Kiristan Joy Moses, tare da bankad'a wasu abubuwan da suke aikatawa. Na tsafi da zalunci.
Alhamdulillahi Zanzabira ta samu yanci domin ba ayi amfani da son kai ko son kudi ba. Ba ayi amfani da suna ko daukaka ba, sai aka ji adalci aka bawa masu laifi laifinsu. Penthouse suites dinshi aka rusa, tare da mai da wurin makarantar Tahfizul QUR'AN.
Ikram kuwa a Nijar aka kamo ta, wallahi sai na kasa koda kallonta ne aka kaita wurin mahaifiyarta satinta daya ta rasu. Nadiyyah kan jinya take sosai. Bayan wata uku saka rantsa da Ya Abid, ya kama aiki, Yaya ma ya