Showing 87001 words to 90000 words out of 157081 words

Chapter 30 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

24

jikinka suna kara nanike maka kamar kaska ba."

Na bude murya na gaya mishi magana, ganin yadda na hauro da Bala'i sai yai shiru ya kama zare idanun ai ya zata ba zan d'aga murya ba ne, ina gama cire kayana, na nufi hanyar part dina ya fisgo ni ya dauke ni, ya haura da ni sama ina faɗin. "Sauke ni nayi wanka na wuce gidan Ubana!" Marin duwai yayi yana faɗin. "Ai kaf duniya babu me kara barin wannan kayan daɗin yayi nisa da katon bunsuru irina!" A hankali yake faɗa min wasu dirty words, wanda ban san lokacin da na biye mishi muka fara gayawa juna kalaman batsa ba,shi kenan fa magana ya ƙare nima kuma yau nayi amfani da karfin yadda ake juya mishi lissafi a daki a gado, nayi poise din mind dinsa da zaman Aneesah a gidan na rashin dalili, bai ce kome ba, amma kuma na ga yayi accepting din maganar da idanun basira, daga baya na ce mishi. "Kada ka dauki maganata fa, kawai na faɗa ne " daga haka muka shirya, washi gari da wuri ya kai ni gidan, nima kuma ina zuwa na saka aka hada kayan Yaran idan zan koma zan tafi da su, haka aka yi wunin bikin yan uwansa da mai babbar daki sun zo, suka ta mita bana kai musu Yaran, nayi dariya na ce musu.."idan muka dawo zan kawo muku su, amma basu jin gari!" Sai a lokacin Mai babbar daki ta ce min.."Nifa?" Murmushi nayi na ce mata."Haba ai zan kawo miku su Ummina!" Daga haka muka shirya fa. Ba kome ake daukar mataki a kai ba, haka ba kome ake zubawa idanu ba mutanen yanzu basu san kansu ba. Yana da kyau ka so kanka atow.

Bayan bikin nan koma kowa na kai mishi tsarabar bikin,himm wannan hidimar na ga ƙoƙarin Ikram da tazo ranar wuni har Mamanta, don haka na kai mata sabon Umma da Maluma, na san Ta yarda da ni amma ni ban yarda da ita ba, tun akan idanuna take cikin kayan bikin. Har na barta, na shi da na kawo mishi nan ma da ya shigo ta ce ya kara mata ta cinye na ta, Ikram na son shiga jikina amma nakasa yarda kawai kowa yayi rayuwarshi.

Sannan na kaiwa Bilkis Yaran suka kwana biyar a wurinta, suka gida na.kara shirya su zuwa wurin Kubrah, da suka dawo na tura su wurin Daulah, sai da suka yi wata guda kai sai da Mai Babbar daki ta tura aka dauko mata su tayi ta fada akan me zata rike su har haka? Ita bata son haka fa, Yaran nan nata ne taya za ayi ta rike su a wani wurin haka kawai.

Ana haka Salim ya zo shima ya dauki Ayaaz da yake makale mishi, ai kawai Mai Babbar daki hakuri tayi amma a cikin zuciyarta taji haushin abinda yayi mata sai da yaron yayi wata uku a wurinshi ya dawo da shi dakyar suka rabu, ban san wani irin so Yakewa Ayaaz ba domin yana yawan fada musu wai yana kama dani, ni nafi ganin kamar su da Yaran.

Ina kwance Ayaan suna can, na ji ihu Nana A'isha na.gyara kwanciyata ashe Aneesah take saka su fadar nan, Princess ta saka wani abin feke pencil ta yaga kumatun Yarinyar nan, innalillahi wainnalihir rajoun, na ga tashin hankali a ranar domin Uwar Yarinyar tana kwance ba lafiya tana fama da Laulayi, haka ta fito ta ga yadda Jinin Yar ke zuba itama yankar jiki tayi ta fadi, da gudu na fito har ina hada step biyu na dauki dankwalin zanin jikina na daure fuskar yarinyar yadda jini yake tsirta. Na sako Hijab muka dauki Uwar muka saka A mota itama yar Ikram ta zo ta ɗauke ta aka saka a mota, Nadiyyah da ta ga haka guduwa tayi da yarta suka bar zanzabira. Ni da ikram muka tsaya akan Ijlal da tayi barin cikinta, haka aka mata wankin ciki a lokacin da ya iso shi da Mai Babbar daki suka same mu akan Yarinyar. "Me ya faru?" Ya tambaye ni, "ban sani ba wallahi kawai na fito na ga jini a jikin Nana A'ishah, ashe fuskarta ta ne!" "Me kake tambaya? Ina ranar da Ikhlas ta mari Aneesah kowa juya mata baya yayi saboda naku san gaskiya ba? Wannan rashin binciken shi zai illta rayuwar gidanka ka saka idanu wannan lamarin ba zai tafi haka ba;" inji Ikram tana fada ta bar ɗakin. Da mamaki nake kallonta har ta bar ɗakin, can waje ta nufa ta zauna tana kuka. "Ki fita a jikina ki fito!" Hayakin ce ta fito tana dariya, "Kina sonshi amma ai na gaya miki ban shiga jikinki don na zauna haka ba."

"Me yasa kika aikata haka? Me yasa?" "Ba zaki tab'a tsira sai na saka kin biya abinda kika aikata a baya. Kazama dake ni yanzu ba zan kara zama a jikinki ba tunda kika fara sallah na ji bakin cikin fara sallah da kika yi kuma ki sani sai na rama abin da kika min!"

Daga haka ta b'ace, kuka ta saka tana faɗin.."Na shiga uku!" Zama nayi a gefenta ina tab'a bayanta a hankali ina sauke ajiyar zuciya, a yanzu da na ga abinda ya faru ba zan tab'a yarda da Ikram ba, d'ago kai tayi ta ce min. "Ikhlas, akwai aiki a gabanki ki dakatar da abinda zai faru, domin ni dai na san kowani lokaci labarina zai iya zama tarihi."

"Ban gane ba?" Cikin shashekar kuka ta ce min.." na na sayar da rayuwata domin na auri Salmanu Faris gashi ban san samu yadda zan kubutar da rayuwata ba domin ba zasu kyale ni ba, wannan hayakin da nake magana da ita ita ce Aojanah." Rike hannunta nayi muka nufi wurin motar da ya kawo mu, ban tsaya ba sai fada na kira sadi, muka nufi can wurin Bana titi. Muna shiga garin , a bakin gona muka same shi, da sauri na janyo ta muka nufi wurinsa. "Baba titi akwai abinda zaka iya? " Juya min baya yayi yana faɗin.. "A hankali zaki ta gani sako fari da baki, ita tayi kyau domin ta gano kuskurenta da wuri, tun lokacin bai kure ba., Allah ya baku hakuri itama ta koma ta cigaba da ibada ta iya dacewa!" Kuka nake ina jin kamar yau mutuwar Ibrahim Tauhid. "Allah yasa idan zan mutu na ya kasance kina kusa da ni, ki yafe min kin ji!" Girgiza kai nayi na ce Mata.."A'a Ikram ba zan amshi ban kwananki ba." "Ai sun kashe kurwana!" Ta fada tana murmushi." Haka na cigaba da kuka a durkushe, a hankali na bude idanun na ganmu a cikin gidanmu tana tsaye tana murmushi. "Ikhlas kina da kirki, in sha Allah babu me yin nasara akanki sai wani ikon Allah, domin Allah ya haɗa ki da mutanen kirki." Ta juya ta koma bangarenta, ranar haka na wuni lokaci zuwa lokaci ina zuwa bangarenta na duba ta, kai karshe sai ta bar min kofar a buɗe, tana dariya. "Idan zan mutu in sha Allah, Ubangiji zai ilmantar da ku, in sha Allah a kusa dake zan koma gare shi, ki min fatar na tafi a sa'a." Daga nan na dawo. Kwanakin Ijlal biyar a lokacin Ikram ta fara wani irin ciwon kai idan ta fara haka zata yi ta zubar jini ta hanci da baki, a ranar nayi kuka na tausaya mata. A daren na rike hannunsa ina faɗin. "Yaya ka min wani alfarma daya daga shi bana bukatar wani Alfarman don Allah!" Yadda nake kuka ina rokon shi ya sa shi rungume ni. "Me kike so?" "So nake ka zauna a tare da Ikram ka mata kome kamar yadda kake yiwa Matanka."

Girgiza min kai yayi yana faɗin. "A'a wallahi kyamarta nake ji!" Don Allah. Kayi min wannan alfarman mana!" "Daga baya ki zo ki ci na juya miki baya?" "A'a wallahi ka min wannan alfarman." A cikin kwanakin da muke tare da ita sai ta kalle ni sai tayi murmushi ta ce min. "Gashi don baki son na mutu kina ta bibiyata, tow ki sammin Mijinki mana!" "Shi kike so?" "Iya kwana daya." Yau da na ga, bakiɗaya sai naji zan iya mata kome,.abinda take fada min ya bani tsoro da mamaki yadda take ta tona asirin abinda ake aikatawa a cikin Masarautar nan, ta ce min. "Mijinki ba haka kawai yake wani abu kamar sakarai ba, wani lokaci idan abin yayi mishi yawa, shine zai ta wasu abubuwan kamar mara hankali, wallahi baya barci idan kuwa zai yi barci sai idan yana tare dake, Zainaba kada ki rabu da shi, domin ke da Ayaan kune garkuwansa, dukkan mu matansa ba na ce miki waye mai gaskiya ba amma kowace ta samu dama zata kashe shi, abincin da yake ciki ana saka masa gub.....

*Kuyi hakuri zan dawo yi update biyu kawai a rana, amma pages din zasu kasance masu tsawo, yanzu nayi wannan karfe sha biyu sai karfe goma na dare in Sha Allah, saboda wallahi ina shan wuyan typing ga hidimar Yara da ake hutun ga hidimar Mai gidan bakiɗaya idan dare yayi dakyar nake typing wani lokaci ina gyangyadi ina typing ku fahimci uzurina 😔😔don Allah biyu is ok enough*

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 32

Wannan maganar ya gigita ni ya hana ni cikin tashin hankali, amma yau da nake gaban Yaya. Kiri-kiri na hango kyama da tsangwama tare da kyakyanmi kamar yaga wani kayan amai. Cak ya ɗauke ni zuwa dakinsa. "Yau zaki gaya min me yasa bakya kishina!" "A'a Yaya ba haka ba ne" na fada ina kuka. "Wato ko wani kare da doki ya kawo miki uzuri zaki amsa ko?" "A'a Yaya na haka bane!" Ban tab'a sanin yaya mugu ne ba sai da ya saka ni a daki tun yana yi a dadin rai sai da ya ga ina kuka da rokon shi Allah da Annabi, amma yayi banza da ni kai ko ranar da muka fara zama inuwa daya bai min wannan tozarcin ba, sai da yayi min abinda da kyar nake nishi, kasana kuwa kamar an watsa min barkono mudu guda, marana da cikina wani irin ciwo suke min, na gagara tsayawa da kafana ina tashi zan zube a kasa, Yaya mugu ne yana fitowa ya kama murmushi yana share kasumbarshi, irin yaji dad'i babu abinda ya dame shi. Bakin ciki ya sani fashe da kuka..cikin ko in kula ya ce mishi. "Ai ke daya nakewa tauranci sauran kowa bana musu bunsurancin da nake miki, ke yar iya gaki nan shafaffiya da mai uwar masu imani da jin kai ta Zanzabira yarinyar da tun fil azal na sake ta, ke nan zaki min kinibibi, ke nan kika kafa min sharadi!" Ban san lokacin da na ce mishi. "Sake ta kayi Yaya?" Wani kallon banza yayi min yana shafa mai da ya mika min robar yana faɗin. "Oya shafa min a bayana!" "Amma Yaya!" "Tun ranar da aka daura na sake ta, don Allah ki kyale ni!" Daga haka ya ajiye min robar man ya juya min baya, a hankali na lakuta na shafa mishi a bayansa, kafin na daura kaina a bayanshi kamar zan yi kuka. Janyo ni jikinshi yayi inda ya d'ago kaina. "Kin san yadda nake tsoron ki juya min baya? Bani da raunin da ya wuce ke amma ki yi nazari da kyau taya zata sauya tare da fake sick? Ranar da kika saka ni kuka a gaban jama'a baki san mutuncina kika tab'a ba? Ke daya ce kika tab'a min kimata har yau nake zaune da ke da wata ce tuni na turata gidansu, akwai abubuwan da nake yi amma bana son wannan ya zama kamar na rusa ginin da nake yi ne. As queen ya kamata ki san yadda zaki yi control din emotiona ɗinki, na farko ki yi kamar baki gani ba, zai gaimaka miki wurin nazari akan magana ko wani abu. Na biyu ki yi kamar ba ki ji ba, zai taimaka miki wurin fahimtar kome, na uku kuka ko ihun wasa kasa yasa ki zama sakarya. Kina bin kome da ki-da ki, haka zai saka kome ya zo miki da sauki sannan duk wani magana da wani zai yi ba zai taba shigarki ba, fuskarki ta kasance bata amsar sakon kuka ko farin ciki haka zai sa kowa yana jin kamar baki da imani da tausayi after ba haka ba ne, kishiyoyinki ne amma yana da kyau ki koya daga kuskurenki na baya, Nadiyyah bata miki da dad'i ba akan me zaki zake dayawa!"

"Yaya hakkin Aure!" Murmushi yayi yana faɗin. "Hakkin Aure? Zainab tun ranar da aka daura auren na sake ta, zan miki karya ne? Idan har akwai kuskuren da xan yi shine wata ƙaddara ta haɗa ni da ita." Zaunar da ni yayi ya riko hannuna. Sannan ta durkusa a gabana. "Ba zan sake ta haka kawai ta fita waje ba, ina da wani abu a kanta ne ke kuma kece raunina kowa yasan kece raunina, Please kada ki kara wani motsi ki saka idanu akan kowa da idanun basira. Allah ya kyauta!" Ya fada min yana mikewa, bin shi da idanu nayi.

Tabbas rayuwar Ikram akwai wani abu da ta boye, tana asibitin na tafi wurin Baba titi. "Baki kyauta min ba " zubewa a ƙasa nayi hawaye na zuba min. "Ya kamata ki bawa Mijinki dama ya samu nutsuwa ba ki kara mishi matsala akan matsala ba, ita kanta yanzu ba zata iya amfanar d kanta da kome ba, amma a yanzu da suka kashe kurwanta zasu cigaba da amfani da Aojanah a jikinta. Sai dai ki sani kamar kamar a kashe maciji ne ba a sare kansa ba, ita kan ta kare mata amma bai zama dole ya biya alkhairin da zaki iya mata ba, sannan kada ki kara saka Mijinki ya kyautatawa wata yafi ki sanin abinda ya dace da kowaccenku!" Shiru nayi ya ce min. "Ibrahim ya kyauta sosai, Allah zai tsare miki shi gaba da bayansa!" Gyada kai nayi ya cigaba da cewa. "Ki kula da kanki, sannan ki cire abinda kika saka a jikinki na hana daukar ciki, abubuwa masu yawa suna gab da ke amma katangar da kika saka yana kara nisanta wasu abubuwan masu yawan gaske. A yanzu kuma ba ruwanki idanun ne naki na gaya miki, ku bil adam kuna da shegen taurin kai!" Daga haka ya bani ruwan addu'a, sannan ya ce min. "Isma ta koma wurin mai ita ko?" "Ai taki ni sam, kamar bani ce na hadata da Ayaan din ba!" Murmushi yayi ya ce min. "Dan baiwa ne shi soyayyarsu daga Allah ce."

Da wannan nayi mishi sallama, na dawo na cigaba da kula da wasu abubuwan, kwanakin bana ganin Ijlal. Sannan mai da hankalina akan kitchen, abincin da ake yi da sauransu. Idan aka gama da kaina ake dubawa sannan idan suka gama sai na saka su, cin abincin. Wannan tsarin da na dauko sai ya razana su. Har Mr Brandy ya gayawa Faruq. Sai da ta kai a karan kaina idan aka daura abincin zan san me zasu yi sannan nayi bincike a kai.

Ashe shirun da Ijlal tayi da wata a kasa, domin kuwa Nadiyyah da Yarta suna dawowa, bata wani damu ba haka itama Aneesah ba karamin fada ta sha da mai babbar daki ba, bata taɓa nuna alamar zata rama abinda aka yiwa Yarta ba, sannan bata dauki wani mataki a daidai lokacin da abin ya faru ba, kamar yadda ta rasa cikinta sai abin ya mata zafi biyu, gidan ya cigaba da tafiya. Kwana biyu da dawowar Nadiyyah aka kawo min Ayaan da yake zazzaɓi, mun je asibiti aka ce ana ganin kamar fika ce sai lokacin na tuna basu yi fika ba, yayi laushi bakiɗaya kamar ba shi ba.

Magani da allurai suka bashi muka dawo gida, "Ummi kada ki damu kada ki kalle su." Ganin masu aikin gidan a tsaye a bakin kofar shiga suna tsatsaye yasa nayi gyaran murya, tuni suka watse. Shiga parlourn na yi da sallama ina dauke da Ayaan. Ijlal tana bin Aneesah da gudu zata rama, ga Nadiyyah da ita kwance cikin jini. Jin wani irin abu nayi ya tsaya min xan yi magana naji Yaron nan ya saka min hannu a baki. Sannan ya ce min. "Muje, kada ki damu sharri dan aike ne ya koma musu ne!" Haka ina ji ina gani na wuce duk da yadda naso nayi magana Ayaan ya hana ni, daga cikin dakin ya tab'a bangon kujeran da yake zaune. "Ta tsira!" Sannan ya dawo ya kwanta. Muryan Uban naji a hankali ya dawo jikina ya kwanta.."Zai shigo zai miki magana, kada ki ce kome kin ji!" Ya fada yana kwantar da kanshi a kirjina, ai kuwa sai gashi nan ya shigo ya fara faɗa, ji nayi kamar an rufe min bakina. Kafin kuma ya yi shiru ya ce min. "Na manta ashe kina asibiti da Ibrahim dina!" Sai kuma ya fita waje, murmushi yayi yanzu da kin biye mishi fadar su ce zata dawo kanki, Abban Ayaan akwai lafiya , kaf duniya ke ce zaki iya saka Abba ya zauna ya zauna ko yayi wani abu da bai yi niyya ba, bayan nan sai mai babbar daki. Idan ya kwaso zafi sai yi share shi bai dA wuyar sauka kamar haka, ni zan tafi Allah ya bashi lafiya!" A hankali ya kwanta ya cigaba da barci. Kwantar da shi nayi na sauko kitchen din ƙasa na fara hada mishi abincin da zai ci, lokacin da na dawo dakin na samu abinci ne da wasu kwanuka sun kai kala goma, an jera su kamar wani na babba, kome na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login