Showing 33001 words to 36000 words out of 157081 words
ya hadu da parlourn, Nadiyyah ma ganin yadda Fasalin gefena yake sai da tayi magana, duk wannan bidirin Ijlal tana nan bata ko leko ba, domin ta rigasu dawowa. Sannan taba da lokacinsu, babban abinda ya kuma hana ta fitowa shine tasan suka haduwarta da Nadiyyah bazai mata kyau ba, haka yasa taki yarda ta fito yanzu cigaba da aka samu daga dakinki zaki kira kitchen ki fadi abinda kike so kuma a kawo miki har kofar dakinki, sai kin bude kofa a shiga a jire miki, yanzu daga ita sai Yaranta da masu kula da Yaran.
Daga gidanmu basu fara shirin dawowa na ba, amma ana kan shirin haihuwa ta. Amarya ta shigo a tunaninta mijinta ta aura zata same shi ne, sai aka yi rashin dace ranar da aka yi daurin auren yayi tafiya baya kasar ma, abun ya d'aga mata hankali domin ta gama shaye-shayen kayan mata. Karshe kamar tayi hauka.
Satinsa biyu a wurinmu ya sauka, duk sai ya bani tausayi. Haka nayi ta hidima da shi duk da bana iya tashi yanzu saboda girman cikina bana iya kazar-kazar kamar da, haka nayi abin da zan iya mishi na koma na zauna ina numfashi, sauran Sailuba da Jakadiya suka karasa sai sannu suke min. Ina murmushi kafin ya shigo ya same ni kishimgid'e ina nishi. Zama yayi yana kallonsu ya ce musu sannu, suka amsa suna masu barin dakin. Ni dai ban ce musu kome ba, har shi kwanciya nayi. Saura kwanaki na shiga takwas, bayan fitarsu.
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: Ba karamin dadin abincin ya ji ba, yana ci yana kallona. "Ko za ayi miki cs ne?" Girgixa kai nayi na ce masa. "Cikina lafiyarshi lau,babu abinda zai faru ai na kusan sauka sun ce ba lallai na cinye wata tara ba! Zan ina haihuwa a wata takwas!". "Amma har yanzu tafiyar ya fara gagaranki ko?" Murmushi nayi domin na lura ko murmushi nayi ba kyau nake ba, na ce mishi."hmm!" Haka ya gama cin abincin ya shiga wanka ya zo ya zauna a gefena yana ja min kafana, tare da min tausa sai na ji dadi, jin yadda yake min tausa ba sai barci yayi gaba da ni ba, ban tab'a tsammanin zan farka na ganshi zaune yana aiki ba, a hankali na fara ƙoƙarin tashi amma ina sai da ya ga ina motsi sannan ya riko hannuna ya taimaka min na tashi, ya tattaro kafana ya zubo min kasa sannan ya tashi ya riko ni muka nufi ban daki nayi fitsari da kanshi ya min tsarki sannan ya riko hannuna muka dawo dakin ya ce min. "Kina son wani abu ne?" "Yunwa nake ji!" Da kanshi ya riko hannuna muka dawo parlourn ya kunna min Tv inda ya kunna min Saudi inda ake karatun Alkur'ani, shi kuma ya shiga kitchen ya fara aiki, bayan ya gama ya fito tare da ajiye min ya cigaba da aikinsa kafaffuna suna kan cinyarsa. Har na gama ya kwashe ya kai kitchen, ya zo ya rike hannuna muka tafi dakin, fitsari ya kai ni nayi ya min tsarki sannan ya riko hannuna muka dawo dakin yana kallona. "Waye yake miki wannan aikin?" "Ummi da Sailuba!" "Allah ka ginawa Ummina gida a cikin gidan aljanna mafi girma da daraja!" "Amin Ya Allah!" Na zauna sannan shima ya zauna kusan raba dare muka yi muna hira. "Gobe zaki tafi awo ko?" "Yaya ina ji a raina bana son zuwa!" "Me yasa?" Ya tambaye ni, "kawai ina ji wani irin yanayi ne.mara dad'i!" "Allah ya kai mu gobe sai mu kai ki da Faruq!" "Allah ya kai mu goben!" Na fada ina gyara kwanciyata.
Haka na kwanta wurin karfe biyu da wani abu na farka shima ya tashi ya riko hannuna muka shiga ban daki yana min sannu, ban yi wani fitsari mai yawa ba haka ya wanke min jikin muka dawo dakin, dabi'a irinta ciki ya tsufa dai.
Haka muka kwana barci rabi da rabi, da nayi sallah asuba barci me dad'i yayi gaba da ni, haka ya bar ni na cigaba da barcina.
Karfe sha daya na tashi da yunwa da fitsari na je nayi na kuma ci abinci, a lokacin na kira wayarshi.
"Baby a hakura da zuwa asibiti wata sati sai na kai ki!" "Allah ya kai mu!" Nima Kuma bana son fita da rana tayi zafin nan, kuma aka y.
Na hakura kai karshe ma na ce na gaji ba zan kara zuwa asibitin ba, domin kuwa ba karamin gajiya nake da fitar safiyar nan ba, wai ma don asibitin kudi ne sai dai. akwai wani sauyin da Yaya yayi, bakiɗaya yadda yake shigo min ya daina, ko ya shigo ma wuta wuta zai tafi, sai na fuskanci ai tun da ya dawo ya sauka a wurina ya koma can gidan na fahimci fuskanci akwai wata a kasa domin Amaryan a ranar da tazo Ismaha, ta hanata zama a parlourn gurnani da wani irin kai mata cafka kamar zata cinye ta. Sai da Yaya yayi kwallo da magen madadin ta fadi can ta dirko kan cinyata tana wani kare. Cikina tare da mikar da gashin jikinta da bindinta kamar zata kai farmaki. "Isma, ya isa haka Abba ne ba a fada da shi kin ji!" Kwantar da kanta tayi a jikina tare da wani irin dungure cikin sai da ya juya. Bakiɗaya naji kamar numfashina zai dauke. Jingina kanta tayi da cikin sai na ji ya tsaya cak. "Wallahi kika sake wani abu ya same abin cikinki, ta sanadin magen nan sai na konata!" "Lallai fa, ba mai tab'a min Magena wallahi oya Isma muje dakinmu ki min tausaa.." dakin na shiga na zauna Isma sai tsalle take da cikin jikina wanda yayi kasa sosai, duk da wasa take amma sai naji zafin shigar da Ikram tayi abin ya fara min ciwo, Yaya mayyen mata har ta d'aga mishi kafa ya ci kenan, shi yasa zai fara min bare, ina cikin wannan tunanin aka kira mai Babbar ake gaya mata jikin Baffanta ya motsa, haka yayi ta jajjantawa, har washi gari ina kwance aka kara gaya mata an sallame ta, kwanansu Yaya kusan takwas aka kira jikin yayi tsanani, kwana biyu a tsakani Allah ya mishi rasuwa, itama sai da tayi zazzaɓi, maganar Baba titi ya dawo wato Wannan shine rashin da zata yi, ranar basu tafi ba sai washe gari suka tafi, wanda ya bada kwana goma da zuwansu, bayan la'asar Mai Babbar daki sun tafi faran kasa ita da Mai Martaba gaisuwar mutuwar Baffanta, da aka yi musu, ina zaune da su Jakadiya Iyaami muna hira, ba sai ga Ikram ta shigo kamar mahaukaciya. "Gaya min me kika yi mishi ya kasa mancewa da ke? Me yasa sai ke? Me yasa sai ke?" Shafa Ismaha nayi ina mai daura daya kan daya, nayi murmushi nace mata. "Mai xan yiwa shago kuwa soyayyar Awatif lallai gaskiya ce, takowa tayi da wani irin fusata wani haske ya fito daga jikin Ismaha ya dakatar da ita wanda yayi sama da ita sannan ya buga can. "Aojanah, Barka da zuwa gidan shagona a karo na biyu ki tsammanci zuwa na, bayan na sauke nauyin da yake kaina kishi da yaki akan shi yanzu zamu fara, kin zata ban san ke bace? Ai tun ranar da kika kashe Matasan nan a mota na san da zuwanki, ki koma inda kika fito ki bar Ikram ta zauna lafiya, idan kika kuwa tarihi ba iya maimaita kansa zai yi ba, omo kome zai faru domin akanshi zan kashe kuma zan binne inda kowa ba zai ji ko labari ba, na baki aronsa shine zaki min shirme? Gaya min ya shiga tsakiyar ko a'a?" Na fada ina wani irin murmushi, "yadda kika hana shi tarayya da ni da sauran matan sai ka cire miki nutswa da kwanciyar hankali da ni kike zancen!" Ta juya fuuuuu ta bar parlourn, dariya Jakadiya Iyaami tayi tana faɗin. "Kina nan Allahnki yana can, ga miji nan ta samu amma ya mai da ita hoto, hmmm jiya laminde Mai wanke-wanke take gaya min wai ai kullum gidan sai anyi dambe a tsakaninsu, su uku." Zare idanun nayi na ce mata. "Jakadiya a cikin tsohuwar ganuwa ake dambe?" "Wallahi na rantse miki da Ubangijina, dambe ake domin kuwa kowacce taki yadda ta dauki alhakin laifinta akan abu kaɗan sai ki ji ana doke doke, ko shekaranjiya da ya shigo yana fushi ba dake yake ba, wallahi matansa suka hada mishi ruwan dumi akai, sai da ya kore su bakiɗaya Malam Junaid ya shiga lamarin da Waziri suka mai dasu." Duk ina gidan nan ake wannan aikin dole ya shiga damuwa.
A can kuwa ranar da ya dawo daga fada, ya wuce bangarenshi, Faruq da Brandy suka kai mishi abinci bangaren shi Faruq yana tsaye aka jera abincin suka fita, mr Brandy ya mika mishi wata takarda. Amsa yayi ya buɗe. *Akwai wani abu da ya faru kwana biyu har Princess Haliey ta suma bamu san me ya faru ba, amma a duba lamarin*
Gyada mishi kai yayi sannan ta fita, kafin daga bisani Dan mai babbar daki ya fito sanye da kananan kaya, ya zauna sai da Faruq ya gama zuba mishi abincin sannan ya koma gefe yana jiran ya gama, daukar flat yayi ya zubawa Faruq. Sannan ya ce mishi. "Zo ka ci!" Zama yayi ya fara cin abincin, har suka gama a hankali ya kira kitchen aka zo aka dauke kayan, Faruq ya bashi labarin abinda ya faru, suna cikin haka sai ga Nadiyyah ta shigo, ba sallama ta tsaya daya can. "Ka dawo lafiya?" Kallo daya yayi mata ya ce mata. "Lau!" Ya cigaba da aikin da yake yana shafa kanshi. "Wai mai ka ɗauke mu ne?" D'ago kai yayi yana kallon yadda take tsaye kamar wata doki, kasa yayi da kai "get out!" Yadda ya daka mata tsawa, kamar wacce aka turata haka taji kai ko bude baki tayi magana ta kasa haka ta bar parlourn, murmushi Faruq yayi yana jin wani irin dad'i a ransa, yanzu yasan Ubangidansa namiji ne, tsawar da yayi har parlourn tsakiya haka yasa kowacce ta kama kanta basu yi gigin shiga ba, domin wani irin tsoro da shakkarsa ya darsu a ran Ijlal da Ikram, idan zai iya yiwa Nadiyyah tsawa haka ai idan suka shiga sai ya mare su.
Fitowar Nadiyya suka kwashe mata da dariya, ai kuwa da yake mahaukaciya ce ta wuce bata kula su ba, tana shiga kitchen dinta kawai ta dauki muciya tayo waje da shi ta rufe Ikram da duka kafin Ijlal ta samu damar tserewa ta buga mata a gadon bayanta, ai kuwa ta kidima musu lissafi kamar mahaukaciya dama tana cike da Ijlal sai da ta karya mata hannu ihunsu ne yasa shi fitowa ya same su ta haɗa su awurin guda tana cin Ubansu tuni Aojanah ta fita jikin Ikram don ta lura Nadiyyah mahaukaciyar gaske ce. Yana fitowa ya kifa mata mari sai da ta zube can, kamar ya yi ihu, ya ce musu."kowacce ta koma bangarenta na kara ganinku a nan sai na sabb'a muku!" Da gudu suka wuce domin yadda yake maganar zai iya kara musu dukar, sai Nadiyyah suka bari a parlourn tana kuka, bayan taci Ubansu. Share ta yayi ya bar ta nan zaune, tana kuka ya ce mata. "Wallahi kada na fito na same ki!" Bai rufe baki ba, ta bar parlourn.
.....
"Kayi hakuri Sadauki!" "Matan nan zasu kashe ni!" "Ayi hakuri!" Bai kara bin takansu ba, sai ranar wata Alhamis yayi azumi. Domin tunda suka dawo babu wacce ya gayyata a dakinsa, balle su mishi hakika. Kusan faruq ne yake mishi kome, gajiya da zaman haka Nadiyyah ta kira Babanta tana kuka tare da gaya mishi, ga abinda yake faruwa, shi kuma ya kira Abban Ikhlas. Suka yi magana, Malam Junaid da kanshi ya same shi bayan sallah juma'a ya mishi magana da nasiha, tare da tuna mishi ya ji tsoron Allah kada ya cutar da su, har su fada wata rayuwa. Shine yayi set din kwana biyu biyu tsakanin Nadiyyah da Ijlal su ma kuwa abinda ya ce musu duk wacce take buƙatar ya kwanta da ita sai ta je tayi tsarin Iyali tunda bai ga tarbiyyar da suke da shi da har zasu bawa wasu generation din ba.
Son mace sama da daya dabi'ar da namiji ne, haka Allah ya halicce su sai cikin ikon Allah wannan dawowar da aka yi bai wani damu da su ba, abu ba farko da ya karanta a cikin zamansu, Zainab duk da ciki da dawainiyya hankalinta kwance yake, ko yaya ya kusance ta akwai wani abu da yake ji daga dangin nutsuwa, na biyu yafi kwadayinta sama da sauran matan su din a gare shi kamar ruwan kashe gobara ne, sannan yasan idan da Zainab tana cikin gidan ba zata tab'a kyale shi ya ci abincin masu aiki kullum ba, zata na hada mishi da nata baiwar da Allah ya mata, sannan ita Zainab bata yarda fada ya hada ta da wata mace ba tare da ta tsayar mata ba, sannan tana da wani irin aji da ita bata bin shi kamar yunwa take ji akansa hatta dukiyarshi Zainab tana kiyayewa, sannan bata da Kwadayi da hango abinda bana ta ba, ko abu zai mata sai ta nuna mishi tausayi da kada ya wahalar da kanshi, tana da kudi a tare da ita, da wannan ya saka ranshi zai fi son ta cika mishi gida da Yara yadda zai taya ta tarbiyyar su ban da waɗannan dirka-dirka masu zubin shanu ba..
Ikram kuwa a yadda ta ga mata na rawan jiki a kan Mijinsu, kawai ta same shi akan me zai yi rabon kwana amma ban da ita, kallo daya ya mata. "Dukkansu mata na ne, Nadiyyah ta aure ni saboda tana sona ne, Zainaba ina sonta sai aka yi dace Mahaifina ya haɗa auren tun ban ganta ba, Ijlal kuwa mahaifiyata ce ya sani a aure ta, Uwar Yar da nafi so da kauna, ke kuma duniya kika fito kina min barazanan na aure ki ko ki kashe kanki, makaryaciyar banza me yasa baki kashe kanki ba, kazama datti irinki zan hada alaka da ke, fita min a daki idan kin gaji da zama ki tafi wurin wanda suka shiga maganar su saka na sake ki, yar iska mara kunya out.........
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 13
Kamar wacce ruwa yayiwa duka haka Ikram ta fita daga parlourn, a bakin kofar ya hadu da Ijlal dariya ta saka mata, tana faɗin. "Waye ya gaya miki shi din irin kawai ne? Welcome to the hell amma sai kin yi dansanin auren mijinmu!" Tana gama fadar haka ta barta a wurin, tana dariya.
Zaman gidan babu dadi, don haka ba tare da wani ba. Ta daina zama a gidan yana sane kullum sai ta fita. Idan ta kuwa sai ta kashe wani idan ka shiga gonarta domin zuwa yanzu ita kanta Aojanah abinda take hari a kanshi ba zama dole ya zama gaskiya ba. Sosai abin yake mata ciwo!"
***
Ina kwance ya shigo da sallama, kallonshi nayi na ga kwana biyu sai wani murna yake, duk yadda aka yi hankalinsa yana kwance. Zama yayi kusa da ni na dauke kai ina rintsa idanuna domin jikina yana bani ya samu nutsuwa ce ta wurin matansa, musamman Amaryanshi wani abu ne mai nauyi da zafi ya tawo min kirji ya tsaya, idanuna suka cika da kwalla na ji wani abu ya tsaya min a kaina bakiɗaya, yadda yake min magana ya ga naki amsa mishi sai jikinsa yayi sanyi. "Sannu?" Ya ce min, amma a harzuke amsa mishi. "Yawwa!" Na fada a dakile domin haushi yake bani, ganin haka shima sai ya yi kokarin kin min magana, haka ma bai dana bani haushi ba, ina kwance jikina ya bani yana kallona. Ai kamar an ce na buɗe idona mu kayi ido hudu da shi, wani abu ne ya daki zuciyata ban san lokacin da na tashi zaune na dauko hulana da ya zame a kaina, na fashe da kuka sosai kamar an yi min wani abu kuka nake tsakanina da Allah ina ji ina jan zuciya kukan tun iya ni da shi ne har Mai Babbar daki ta shigo ganin yadda daga ni har shi muka zaune a wuri guda abin ya bata mamaki shi yana zaune a bakin gadon ni kuma ina tsakiyar gadon. Sai kuka nake ina karan kuka. "Me kayi mata?" "Wallahi daga nace mata sannu shi kenan kawai ta kama fushi kamar na mata wani abu." "Akan me zaka ce mata sannu? Ka ga tayi kama da wacce take buƙatar sannu ne? Don Allah idan ba zaka zo ka kyautata mata ba kada ka zo ka sakata cikin tashin hankali, ina cewa rabonka da kazo nan ka raba dare kwana nawa?" Ai kuwa kamar mai babbar daki ta fahimci inda yake min ciwo na kara rushewa da kuka har ina jin cikina yana amsawa. "Ya isa haka, tunda kallon Allah sarki yake miki, kema kina Haihwa sai ki bar mishi Yaransa ki kama gabanki. Tunda lamarinsa yar haka ne, bana son na ga kina shiga damuwa!" "Shi kenan Ummi tayi hakuri!" Ya fada yana mai barin dakin, yana fita ta juyo kaina ta ce min. "Ya ina gini kina rushe min? Akan me zaki na kuka yana ganin ki? Nasan kishi da zafi amma akan me ba zaki iya mancewa da shi ba? Kishi halal ne ban hanaki ba amma don Allah ki rufa min asiri ki daina barin ana gano lagonki, ta haka kawai zai iya tab'a ki kuma ba yadda na