Showing 135001 words to 138000 words out of 157081 words
na koma ina kawo na karshe kamar an ce na juya Nadiyyah na gani tana kallon cikina da ya fito a gown dina, kallon cikin tayi ita ta rasa nata na wata biyu yau ta ganni da ciki har yayi kwari, ganin Mijinta ya tsaya mata kawai kamar wata mahaukaciya tayo kaina, ai kuwa aka yi sama da ita aka buga da kasa, tashi tayi da kyar ko ihu bata iya ba, ta wuce da gudu. Dariya abin ya bani mangareta Aryaan yayi, yana faɗin. "Kafiran banza!!" Na ce mishi. "Sai ka kashe musu yar mutane!" "Wancan sakaran Mijinki na ga bai da wani amfani bude mishi idanun da nayi, Zainaba, kwana biyu ina jin wani abu a raina."
"Me ya faru?" Shiru yayi yana bina na ce mishi. "Ina da baki kada ka mai da ni mahaukaciya!" "Mafarki nayi kina cin danyen nama, kuma ana ta kuka a gefenki!" Sai na kalle shi cike da mamaki. Domin nima kwana biyu da suka wuce nayi mafarkin kamar yadda ya faɗa amma ba bari a raina. "Nima haka nayi mafarkin!" "Zainaba ban da ilmin mafarki amma akwai wani abu da zai faru ki cigaba da sadaka. Allah ya kare na gaba." Daga haka na fito na zauna ina nazarin me ya ce aka yi ta hira.
****
Iram
Kuka take tana rike da hannun Mommy Turai, da take ƙoƙarin cutar da kanta. Alhaji Nafi'u ya shigo dakin ya ce mata. "Kin shirya?"
"Me fa?" Ta tambaye shi, "cikar burina yau zai kai inda ban zata ba, kuma ana bukatar jinin mace budurwa irinki Uwarki ta sani!" A tsorace take kallon Mommy Turai cikin wani irin kuka ta ce mishi. "A'a wallahi!" Gyaran murya yayi wasu kartin maza suka zo suka fitar da ita tana ihu tana kome, aka fitar da ita zuwa inda zai yi aikin. "Allah na tuba, Ya Allah tunda na tuba ban kara hada kaina da wani sabonka ba, Ya Allah ka kare min rayuwata da mutuncina." Ya fada tana rufe idanunta, wani abu da ta gani ya bata mamaki Yar shi Iman ce a tsaye, yana kiran sunanta sai ga kudi yana fita ta bakinta asalin dollars, Murmushi yayi yana faɗin. "Ke kuma nasara zan yi da ke!" Haka tana ji tana gani suka zuba mata garin magani, sun kara kenan sai wuta ya kama dakin, ganin yana matsowa kusa da ita tayi kokarin fita a cikin inda suka sakata. Ita kuwa ta samu ta fita a dakin da gudu, bata san inda take shiga ba, haka ta samu ta bar gidan ta isso bakin titi daga ita sai rigar barci, gudu ta cigaba da yi, har zuwa wani wurin kasancewar dare yayi ihun mutanen Alhaji Nafi'u ta ji ta shiga wani lungu ta boya, Allah sarki Abba. Abinda ya zo mata kenan, tana zaune a wurin har kamar ta cire rai, kukan Isma ta ji, ta waiga a hankali, ganin ita ce ta fashe da kuka tana faɗin. "Ki kai ni wurin Ikhlas!" Ya fada tana kuka kamar ranta zai fita, jin takunsu, ta rufe idanunta da karfi, ji tayi kamar ta fado a wani wurin, bude idanun tayi da tunanin sun kamata, sai gata a gaban Gidan Ikhlas, kuka taji yazo mata, da sauri ta mike ta nufi gate din tayi ta bugawa aka bude mata bata jira tambayarsu ba, ta shiga cikin gidan da gudu tana kiran Ikhlas.ina dakin sama na ji muryan Iram, bayan nasan Maluma ta gaya min ta koma wurin Mamanta, fitowa nayi na ganta tsaye tana niman yadda zata zo wurina, na ce mata.."Shafa'atu!" Kallona tayi hawaye ya zubo mata, da sauri na sauko kasa na nufo ta, kuka take tana faɗin. "Ki boye ni zasu sake daukana!" Rungume ta nayi ina faɗin. "In sha Allah babu me zuwa nan da sunan cutarwa!"
Haka muka shiga cikin wurina ta zauna tana kuka, take gaya min abinda ya faru. Na kadu sosai da naji Iman tana can an tsafeta. Wurin karfe tara ya shigo ta ganmu da ita, yayi kamar bai gane ta ba, ta gaishe shi ya amsa.
**
Salim
Kallon Aneesah yayi da aka mata wulakancin da ko gobe ne ba zaka kara motsi ba, ya tsuguna a gabanta yana faɗin. " Ban so ki kawo ni wannan wurin ba, ban san me yasa nake kasa hakuri da duk abinda muke yi ba, amma ko shi lusarin can, kyale shi nake idan kika sake wani ya ji abinda na miki har zuwan Fulani Babba ya fito ban san me xan kara aikatawa ba, amma zan rufe idanuna su keta alfarmarki, ba tare da na ji ciwon jini da muka hada ba, ita din rayuwa take da Dan uwnaki amma rayuwata nata ne, tana ce min na mutu wallahi zan mutu, nasan cewa ba zan taba zama Sarki a zanzibara ba, amma wani ya saka ta kuka sai na azabtar da shi." Ya fada yana kai naushi jikin bango tsoro da tashin hankali yasa ta ji kamar zuciyarta zata buga ita fa bata taɓa jin tsoro irin na yau ba, yanzu ta san waye ya ke tare da Zainab idan tace zata kara wani haukar tabbas mutuwa zata yi, haka ya sakota a gaba ya dawo da ita, wani irin tsoro yana cin ta amma son ta ga bayan Ikhlas yana kara azazzalar zuciyarta. Haka yasa ta rike ranta bata yarda ta yi wani abinda zata yi har ya sani ba.
Kwana biyu tana daki tsoro fal ranta, ta dauki wayarta kira Ikhlas, wacce ta ɗauka muryanta a sanyayye. "Ki fito ki gayawa Duniya alakarki da dan uwan Mijinki idan ba haka ba zan gayawa Dan uwana yadda kike cin amanar shi, na ji labarin za'a naɗa shi a matsayin Galadiman Zanzabira meye shirinki ki kashe min dan uwa ki bawa Salim mulki ko...............
[8/26, 11:31 AM] Ramlat Manga41: 51
Dariya Aneesah ta ji Zainab take tana faɗin, "Idan baki gaya mishi ba, ke ba yar halak bane waye ya gaya miki dan uwanki namiji, raunanne da bai san gobensa ba, wai ai dan uwanki ba Uba bane kuma ba miji ba ne, look Aneesah da zaki yi sanadin da zai sake ni da na taya ki da har karshen rayuwarki. Ki yi fatan ki hadu da Allah lafiya Maluma ko yau na rabu da Salmanu Faris na gama muku kome domin na haifa muku Hassan da Hussaini da Gambo da kanwar Gambo ga wani cikin ma ban san me xan haifa ba, sannan ki tambayi Yayanki da ba abinda ya sani sai mace ya ci mace duk inda ya ga mace bai da hakuri. Ya ci na kazamai balle nawa mai tsafta, ke kuma zan iya cewa asarar haihuwarki aka yi dalla kashe min waya."
Shiru Aneesah tayi tana mamakin yadda aka yi Ikhlas ta samu kwarin gwiwa haka, taya zata kulla mata sharrin da sai ta bar gidan hankalinta zai kwanta yadda babu wanda zai yarda ita din ce tayi haka. Dole ta nimo mafita.
***
Aryaan yana tare da Yaran ya ji yadda nake waya raina a b'ace, ina gamawa na wurga da wayar ina tsaki. "Maryam Aneesah ko?" Dauke kai nayi na cigaba da tsaki." "Zan yi maganinta" "kyale ta!" Na fada mishi. Ina murmushi ya girgiza kai. "A'a Zainaba ba zaki kashe aurenki ta sanadinta ba, akan me?" Murmushi nayi na ce mishi. "Bata sona duk abinda zaka mata ba zata tab'a sona ba, sannan zata cigaba da tsanata ne domin a ranta yake, amma idan na kyale ta, tayi sanadin auren dangin bakiɗaya ne zasu tsaneta, daga lokacin da ka fahimci tasiri ka a cikin al'umma yana da kyau ka bawa masu ganin ka tare musu wani wurin iska."
Shiru yayi tare da zuba min idanu, ya zata zan yi magana ne sai ya ga nayi shiru. "Shi matsalar Mijinku son kanshi, bayan nan bai da matsalar kome sai yadda ya kasa tsayawa akan kafarshi." Tsaki yayi ya share muka bar zancen.
A lokacin da abubuwa suka mana tsamari Allah muke kira a cikin lamarinmu, sai ban wani d'aga hankalina ba, haka na cigaba da kula da kaina da kuma cikina idan na samu lokaci ina kwashe Yaran muje gidanmu na gaidasu Maluma da Umma, har yau suka gaya min Salmanu Faris bai yanke musu hidima, abin ya bani mamaki domin daga kayan abinci har zuwa kudin cefane ya dauke musu, Sannan a duk zuwansa zai zo musu da Ayaanah ta yi musu hira sai dare ya zo ya dauko ta, a hankali na fahimci a cikin Yaran yafi ji da Ayaanah domin sunan Babarshi ce, wata irin kauna yake mata, wanda kwanaki da tayi ciwon bakon dauro, haka ya dawo da ita bangarenshi yayi ta kwana da ita yana kula da ita, wannan abin ya yiwa Nadiyyah zafi. Tunda ya kula da Ayaanah take mita da faɗa, a ranar na san ashe yasan abinda yake gundarin iskanci ne da renin wayo. Ya ce mata, "Me kike so nayi miki? Ita din sunan Uwata ce, me yasa ba zan kula da ita ba?"
"Amma yadda kake kula da Ayaanah da Amiratul Zaitunah sauran Ba Yaranka ba ne? Ko ita Saadiyyah ba yarka ba ce!" Tabbas duk abinda zai yi Zaka ga Yan watan nan kusa da shi, ko aiki yake hankalinsa yana kansu, murmushi yayi ya ce mata. "Bayan kin lalata min tarbiyyar Yarinya ne xan zauna ina kusan takaici da abinda take yi? Sauran Ya'yana ba haka suke ba, duk da lalacewar Ijlal tana kula da goben Yaranta, da ta zauna a ɗakinta ta gwammace ta biyo ni nayi abinda zan yi ta koma ɗakinta, ita kuwa Zainab kamar yadda dakuna biyu suke Bangarenta haka ta raba Yaranta da ɗakinta, sau nawa ina ce miki, ki rufe kofar dakin? Sau nawa Princess tana zuwa kanmu muna Rayuwar aure? Ko Yahudawa suna boye kwanciyar aurensu soyayya suka bayyanawa amma ke, kin ci mutuncina da zarafina kin lalata min tarbiyyar Yarinya sannan ki yi tunanin zan kyale ta, ta zauna da ni abinda kika b'ata sai ko gyara," wannan lamarin ya mata ciwo, sai da tayi kuka kamar ranta zai fita shi kuwa ya ce ba zai ja ta a jiki ba, duk yadda ya ja ta zata lalata sauran Yaran ne, wani abin da ya saka ya shiga hankalinsa, ya kuma janyo Yara matan jikinshi bakiɗaya, malamar makarantansu ne ta sami Faruq ta gaya masa, shi kuma ya mata gargadi da kada ya ji labarin nan a waje, shine ya gayawa mishi. Sai a nan ya ji tsoron kada dai Zainab da Ijlal sun fi shi gaskiya, ya saka yar a gaba yana kallonta tambayar da yake mata tana bashi amsa babu tsoro yasa shi jin wani tashin hankali a cikin rayuwarsa. Yana bala'in son Yaranshi Mata, baya kaunar abinda zai wargaza musu tarbiyyarsu, amma yau shi da kanshi ya wargaza tarbiyyar yarshi, domin baya mantawa tun Yarinyar bata mai haka ba. Tasha zuwa kansu suna kwanciyar aure idan ya ga haka sai yayi maza ya bar uwar ita kuwa tayi ta kwakumar shi ko tana kwakule kanta, wannan abin ya haifar da wagegen rami a zuciyar yar tana kallon haka a matsayin abu me kyau sosai, shi kuma yanzu gashi yana son Yaranshi sama da kome shi yasa ya gayawa Nadiyyah ta ji haushi.
Wannan abin da zaman Iram a gidan ya kara bata haushi ni bai dame ni ba, don ko zuwana gida ban gayawa su Maluma Iram tana tare da bi ba, ita ce ta damu tare da rokon a mai da ta gidan Ya Abid, haka kuwa na saka Faruq ya mai da ta, ya zauna a can, nima na samu saukin fitinar Nadiyyah.
Zan iya cewa daga ni har Ijlal hankalinmu ya koma kan Yaranmu, domin babu da sama da su, ita ta fara maganar a kawo masu lession, sannan aka kawo bayan nan ta kara saka idanun akansu. Duk wani abinda zamu yi muna saka idanun kama daga maganarmu zuwa abinda zamu aikata saboda Yaranmu.
Ban san me ya faru ba, sai dai da yamma ina zaune sai ga dattawan fadar zanzabira, a lokacin da suka zo na ji wani irin abu a raina, sun girmama ni sun kuma kara nuna min ni din Fulani Babba ce, a hankali Alhaji Mamman Abba yayari ya ce min. "Lokaci guda kika b'ace abinki Y'ata, yau gamu a gabanki muna son a kawo karshen wasu abubuwan da ake yi a fada domin Mijinki yana gani kuma yana ji, amma ya kasa daukar mataki a kai. Rayuwar al'ummar masarautar nan tana wuyarshi amma ya kasa kome a kai." Nutsuwa nayi na kalli Aryaan a gefena kafin na ce mishi. "Babana meke faruwa?" Gyara zama yayi sannan ya ce min. "Masarautar nan tana da bayi kimanin mutane dari uku, ban da waɗanda suke gidajenmu." Shiru yayi kafin ya cigaba da cewa.."Fulani Babba, nayi ƙoƙarin na dauke kaina akan kome amma na kasa, an shigo da wasu abubuwan da bamu san da shi ba, na farko aka sayar da miyagun kwayoyi a cikin masarautar, na biyu ana satan Yaran bayi na masarautar musamman mata da yara ƙanana, idan an yi dace a dawo da matan Yaran kuwa kashe su ake yi, ta hanyar zubar da jininsu. Fulani Babba abin nan ya fara wuce gona da iri, ki yi wani abu kamar yadda kika bankado wasu abubuwan, zuwa yanzu Nurun da Kabiru sun amshi sakamakon abinda suka aikata." Shiru nayi kafin na sauke ajiyar zuciya, na ce musu. "Shi mai martaba bai san me yake faruwa bane?" "Ya sani domin ko jiya satar da aka yi ta shafe shi tunda motar Mai Babbar daki aka bude dauki kayan cikinta. Mun zo nan ne a matsayinki na uwar magada, ba wai a matsayin matar sarki ba, sannan kina da ikon a dakatar da sarki da mu yan fada." Shiru nayi kafin na ce mishi. "Babana ka je ku bani awa ashirin da hudu, zan muku magana!" Daga haka suka yi ta min godiya, sannan suka bar gidan, kallon Aryaan nayi nace mishi. "Ka bincika min ka bazama fadar zanzabira." "An gama ranki shi dade." Ya fada yana mai b'acewa.
Lokacin da Faruq ya rako Ubangidansa na saka Madinah ta kira min shi, yana shigowa ya zube a gabana. "Faruq meke faruwa a cikin masarautar nan ne?" Wani irin hucin takaici ya fesar ya ce min."Don Allah ki taimaka ki sumar mana da Babansu Ayaanah, wallahi bai da wani amfani a fada, ana barna a cikin masarautar nan!" Zuba mishi idanun nayi kafin na ce mishi. "Ban gane ba?" Kamar yadda suka gaya min haka ya gaya min, "kuma bai ce kome ba?" "Fulani kamar baki san halinsa ba!" Shiru nayi kafin na ce mishi. "Ka yi min binciken kai da kai!" "An gama Fulani Babba! Amma ina son amsar nan da kwana ɗaya ne!" "In sha Allah za a yi kamar yadda kika ce."
Fita yayi bayan na zauna tsam meke damun Yaya ne? Me yasa ya kasa kome a ciki masarautar? Akwai wani babban al'amari a tare da shi. Dakinsa na nufa na same shi ya dafe kanshi, zama nayi ina kallonshi. "Yaya!" Kallona yayi kafin ya ce min. "Zainab!" "Na'am!" "Zainaba ba zan iya samun damar barin Zanzabira ba ne?" "Me yasa?"
"Zainaba na gaji! Matsaloli sun sha kaina zanzibara ba nawa ba ne!" "Me yasa ka ce haka?" "Na gaji!" "Waye kake ganin ya dace bayan kai ne Babba?" "Zainaba ina ji kamar ina konewa ta cikina! Zainaba ni kaɗai nasan yadda nake ji, don Allah ki warware min wannan tashin hankalin da nake ciki." Idanuna ne ya cika da kwalla. Tashi nayi na rungume shi, ina shafa bayanshi a hankali. Ya daura kanshi a kan cikina. "Zainaba abubuwa suna faruwa, ina son na dauki mataki amma zuciyata da bakina sun kasa aikata kome!" "Yaya kana sakaci da addu'a." "Ba zaki gane ba ne hatta sallah idan nayi ji nake kamar ana korata. Nayi nayi na tashi, Zainaba idan ka tsannanta addu'a zuciyata nake ji kamar zata buga, na gaji."
Shafa kanshi nayi ina ta nazarin, me ya faru. Baba titi ne ya zo min rai,taya zan ganshi tunda ya sha fada wata rana xan zo gare shi, haka nayi ta shafa bayanshi har ya shiga sauke ajiyar zuciya, kwantar da shi nayi kafin na samu damar zama a gabanshi, na ja mishi bargo na lullube shi. Shigowar Nadiyyah da wata tire ta ajiye tana wani yatsina fuska, kallonta nayi na ce mata. "Me kika kawo mishi?" "Ruwan tea ne!" Tsintar kaina nayi da cewa. "Zuba mana har da ke mu sha!" "Ni na koshi!" "Ni zuba min kuma dole ki sha!" Na fada ina mikewa, ganin haka ta dauki kayanta ta fita, ni lissafina guba ta kawo mishi ashe ita maganin lafiyar gado ta kawo mishi, haka ta bar dakin da takaici.
Haka yasa na saka idanu akan abincinsa, kusan kwana biyu bai je fada ba. Sannan lokacin da aka kawo min bincike, na kira Alhaji Mamman Abba yayari na ce su dakatar da Salmanu Faris, ma tsawo wata shida domin bai da lafiyar da zai yi facing matsalar masarautar, na biyu su nad'a Mai Bauchi a matsayin sarkin rikon kwarya, domin haka ne kawai zai magance matsalolin dan uwansa, sai bawa Salim Galadiman, ayi kome cikin satin. Sai maganar zabe yake ciki.
Ya gaya min mutumin