Showing 51001 words to 54000 words out of 157081 words

Chapter 18 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

18

cikina uku ne, cikin wani irin kad'awar iska mai sanyi da shiga jiki , na gan shi a gabana. "Yaya!" "Lu'ulu'a!" Ya tako da sauri, cikin karewar karfin da nake da shi, jikina ya sake wani irin gajiya da barci nake ji, na ji an kaiwa cinyata mari tass. "Bude idanun!" "Ka riketa ka rike bayanta da kyau! Haihuwa ce ta gaji sosai!" Inji dattijuwar da ta mare ni. "In sha Allah!" Wasu mata ne suka rufe wurin da mayafi. Na sake mai da kaina baya zan fara barci, matar ta wanke ni da mari. Bude idanun nayi ta ce min. "Zaki iya Zainab daure daure da kyau zaki iya!" Ta fada tana kara kai hannunta kasana, ta kai hannunta. "Baaba ba zan iya ba!" "Malam ta gaza ina ga sai an kaita ga asibiti!" "Zata iya mana Ma'idah! Shago yayi wani abu mana zata iya!" "Ka taimaka mana da naka hikimar, ka tuna akwai alƙawarin da aka tab'a yiwa wata mace mai ciki! Ita kanta ka yi mata alƙawarin zaka kasance da ita taimaka mana !" "Zainaba! Nayi miki alkawarin haka, ranar irinta yau zamu kasance tare. Ki bude idanunki, mu karasa aikinmu tare!" Sama sama nake jin shi saboda barcin da nake ji, "tashi maza!" Ya matse min hannu wanda yayi sanadin bude idanuna da ƙarfi wani irin nishi da ji kamar numfashina zai bar jikina, na ji kamar wani abu ya fita daga jikina, ajiyar zuciya na sauke na koma zan kwanta ta ce mana. "Allah sarki bai zo da rai ba," ta aka mika mata zani ta nad'e shi ta ajiye a gefe, fadar bai zo da rai ba yasa ni jin kai wata nishin, take wani Yaron ya biyo bayan ya fasa ihu kuwa kowa, irin kukan jarirai. Ban gama dawowa daga wannan ciwon ba sai ga wani babyn, yana faɗowa ta ce mana. "An samu Gambo;" bata rufe baki ba sai ga wani nishi da mabiyar bakiɗaya suka yo waje, komawa jikin Yaya nayi, matar ta fasa wata irin gud'a mai karfin gaske. Faruq da yake can ya ce musu. "Me aka samu?" Yara hudu daya ya kom.." bata karasa ba, ta ga yadda Isma take tsalle akan Yaro daidai kirjinsa ta daka wani tsalle sai da yaron ya fasa ihu, sauka tayi akanshi tana wani goge fuskarta a gefenshi, tana kuka ciki da kauna da kulawa, kuka na fashe da shi ina kallon Yaron da Isma, na kai hannu aka mika mishi. "Sannu ka ji, ka ɗauke duk wahalar kowa!" Ya fada ina kallon Babyn. "Yaya baka ganshi ba ne?" "Na ganshi, na ga Ibrahim, mutumin kirki. Allah ya raya shi tafarkin addinin Muslunci." Ya fada yana mai da hawayen da yake shirin zubo mishi.

"Mun samu Ayaan Ibrahim Salmanu Faris!" Na fada ina kallonshi. Mika min daya, ya kalle shi ya ce min. "Attahiru Salmanu Faris Ayaaz." Ya fada a karo na biyu mika min ta ukun tayi. "Mariama Salmanu Faris,



Ayyanah" ya fada a hankali. Sumbtar goshinta nayi ina jin wani dad'i. Na uku da aka miki min ya ce mata.." Ayaat Zainab Salmanu Faris, amma sunan Hajjah ce!" Jingina kaina nayi a bayanshi, na gaji ni dai ban san me ya sake faruwa ba.

A daren suka bar dajin domin daga nan zuwa cikin gari tafiyar minti minti talatin ne, don haka Faruq ya kira wayar Team dinsa, kafin wani lokaci sai gasu nan, daga nesa su dai sun hango rugar Fulani har suka isa wurin, suna isa Faruq ya haske wayarshi, suka yi parking. "Sir ina Mai Martaba da Fulanin?" Inji Goga, hango mutanen suka yi da fitilar kwai irin na da can, Salmani Faris dauke da ita ikhlas, sai shi mutane hudu dauke da Yaran, bude mishi motar aka yi ya kwantar da ita, sannan aka aka yaran a jikinta, yadda zasu na jin duminta,gaban motar ya shiga yayi ta yiwa Mutanen nan godiya, isma kuma ta wuce wurin Faruq ya buɗe mata motar ta shiga itama, kai tsaye suka wuce asibiti da ita motar masu kula da lafiyar Salmanu ban da wasu motar yan sanda da wasu yan tauri ga motar Dogarai da wasu daga cikin mutanen gari domin Faruq yana kiran wayar aka sanar an same ta, kafin wani lokaci an cika asibitin na gaba a cikin mutanen Salim Attahiru Shehu Yayari ne...

08130269641

5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint 500₦

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 19

Wani irin yanayi yake ji, yana kallon Yaran kamar ya kwace su, haka aka shiga da su wards tare da Doctor Munirah da sauran staffs ganin har shi Mai Martaba yana tsaye akan Matarshi, yasa suka shiga bata taimakon gaggawa, cikin ikon Allah suka samu numfashinta ya dawo, suka saka mata ruwa sannan suka saka mata bututun zukar iska, sannan ta koma barci. Wurin gadon Yaran Munirah ta koma, a lokacin aka shigo da kayan Yaran a cikin wata ƙatuwar trolley Bag. Aka shiga cire kayan, sannan suka shiga goge yaran a hankali cikin nutsuwa da kulawa har suka gama sannan suka sakawa kowa kayanshi. Sai dai kayan da za a sakawa Ayaat ne babu dole aka saka mata na Ayaan domin shi da ita iri daya ne, na Ayaaz da Ayyanah iri ɗaya.

A can waje duk yadda Faruq ya so tafiya da Isma ki tayi, karshe sai da suka fara tafiya ya nime ta sama da kasa, babu dakin da aka kai Zainab da Yara ta shiga tsakiyar su, daidai inda Ayaan yake kwance ta je ta kwanta a gefenshi. Bayan an gama shirya uwar da take kwance Nurse Nabilah ta koma wurin Yaran, ihu da tayi ya saka Salmanu Faris shigowa dakin kafin Salim ya rufa mishi baya, koda ya shiga Isma ya gani a gefen Ayaan har da wani matsawa da shi can gefe ta kwanta sosai kusa da shi. Murmushi yayi ya isa wurinta, yana shafa kanta. "Dan uwnaki ko? Tow ai ki bari a koma da ke gida zaki takura musu ne!" Gyara kwanciyarta tayi, "isma!" "Yaya kyaleta don Allah!" Jin haka ya juya ya taba barci kamar ba ita tayi maganar ba. Sai ya d'aga hannunshi akan Ismaha ya cewa Nabilah. "Kyale ta!" Kallon shi Salim yayi kafin ya fito ya tsaya har zuwa lokacin da ya fito. "Allah ya baka nasara zan koma gida, tunda Fulani Babba tana barci." A hankali yake tafiya ba zai iya fadar yadda yake ji ba. Amma har yanzu soyayyar Zainab Junaid Gobir sabo ne a ranshi, murmushi yayi a hankali ya ji wayarshi tayi ya duba Hisham ne, murmushi yayi ya dauka. "An same ta!" "Na gode sosai, ban tab'a ganinta ba a zahiri amma ina matuƙar son ganinta!" Murmushin kan fuskarsa ce ta dauke bakiɗaya ya haɗa rai yana faɗin.."kana karatu kuwa? Ko har yanzu shashanci kake yi?" A hankali ya ce mishi. "Ya Salim ina karatu fa, ina son zuwa gida ne nima na ga yan uwana!" "Shi kenan ka karasa in sha Allah zaka dawo gida lafiya!" Ya nufi wurin motarshi, yana tafiya a hankali har ya bar cikin asibitin ya dauki babban titi, ya samu labarin rasuwar Tauhid da yadda aka samu gawarsa, a hankali yake tafiya har ya isso traffic jam, yana tsaye ya ga wani mutum akan machine, kallon titin yayi. Ana sake shi ya nufi hanyar wajen gari, mai machine din yana binsa,, har suka dauki wani hanya mutumin yana binsa, sai da ya isa wani wurin da ya kasance da duhuwa ya tsaya yana mai ciro wasu bakaken safar hannu ya saka. Sannan ya dauko wata wukar da yake ajiye ta mai da ita yayi ya dauko wata gatari, sabuwa dal yana cirowa mutumin yana kwaankwasa mishi kofar, bai bude glass din ba domin ya ji labarin kome in details no need ya bude glass, a hankali ya buɗe motar, ai kuwa mutumin ya bude motar da karfi da wani irin fusata ya sari wuyar mutumin da gatarin, ya kwala ihu. A hankali ya fito daga motar mutumin yana baya. Zai gudu ya kuma jifarsa da gatarin a gadon bayansa sai da ya fadi, ya isa wurin mutumin da yake ja da ciki. "Layla ta aiko ka ko?" Murmushi yayi yana faɗin." Zata aikata ta zata ni karamin Dan iska ne? Kai ka manta da ni waye ne?" Haka yayi ta sarar mutumin har ya ga yadda zai yi, kafin kyale shi. Ya wuce motarshi ya shiga ya bar wurin sai da ya bar wurin da minti goma sannan ya kira Yaranshi suka gyara wurin aka dauke gawar. Gidan Layla ya nufa tana ganinsa ta ɗan razana. "Yarima Salim!" "Na kashe yaron da kika tura, ai nasan ba shi kika tura ya kashe yaron tauhid ba, and Layla meye matsalarki da Ni?"

"Ba ni ba ne wallahi, jagora ne ya ce tunda ka kashe wanda ya tura ya kashe Zainab ka saka aka kashe shi, sannan ka kara da kubutar da ita kungiya take jin haushinka." Rike bakin shi yayi yana faɗin.."yanzu lamarin har ya kai ku aikata min haka? Lallai kuwa!"

Zama yayi a kujeran parlourn sakata kiran Jagora. "Ni zaka ciwa dunduniya, matsalar ni mahaukaci ne da ban cika gane kaina ba, yanzu zan baka kyautar da zai baka mamaki!"

"Ka ga idan don abinda na aikata ne kayi hakuri,.ba zan kara ba shi kenan." "Haka bai isa ba haka bai wadatar ba sai ka shiga ka fita an bani zanzabira."

"Ka haukace ne? Ko baka da hankali ne?" "Daga turu nake, n a gaya maka idan a haka ba zaka ga wulakanci irin wnada baka tab'a gani ba!"

Daga nan ya bar gidan yana mata kashedin matuqar ta kuma irin wannan ga gangancin ita ce zata kwana ciki.. haka ya barta da tarin tsoro da fargaba, abin ya tashi hankalina. Tasan Salim sosai ta kuma san abinda zai aikata da wanda ba zai aikata ba.

***

Kafin karfe shida na Asuba bakiɗaya yan uwan Zainab sun cika asibitin tare da yan uwan Faris kowa burinsa ya ganta. Amma tana barci sai wurin karfe sha daya na safe ta farka.

A lokacin da na farka Abba, Yaya, Maluma, Mai Babbar daki, Umma da Iram. Ya Abid da Ya Nuraim sai Ya Nawwas sai Ya Yunus, yan gidanmu da yan uwansa. Kallonsu nayi ina lumshe idanuna, na mikawa Yeemar da take can baya hannu. Takowa tayi, na mika mata hannuna ta rike tana kuka. "Ba gani ba?" Na fada a hankali, sannan na juya ina kallonsu kamar a mafarki na ce musu. "Ina Tauhid?" Don har su Aunty Sajidah da Nu'aymah tare da Aunty Shukrah. Shine babu a wurin sai Hajjah da take can, bata iso ba. Lumshe idanuna nayi kafin na kara budewa na ce musu. "Ina Ina Tauhid?" Na kara tambayaar a karon na biyu, shi kadai nake son gani, kallon kofar nayi na kara cewa. "Yaya yunwa nake ji, ina Tauhid?" Sai a lokacin suka sunkuyar da kansu. "Me ya faru?" Na tambaye su zuciyata tana wata irin bugawa. Rike hannuna Yeemar tayi tana faɗin. "Tashi ki yi wanka sai ki ci abinci, Tauhid yana nan lafiya!" Yadda suka yi ta fita daya bayan daya, yasa na fara jin wani irin bugun zuciya. Kallon Yeemar nayi na ce mata. "Ina Tauhid din ya tafi?" Umma da ta haɗa min ruwan zafi ta fito tana faɗin.."yayi tafiya ne zai dawo nan kusa!" Hadiye yawun nayi ina jin tsinkewar zuciya, na kasa taka kafana a kasa saboda azabar ciwo. "Umma ba zan iya tafiya ba!" Fitowa tayi ta kalle shi. "Ko zaka taimaka mana tayi wanka ba zata iya tafiya ba!" "Tow!" Ya shigo dakin ya cire kome na shi, ya cewa Umma. "Ku je bari na mata!" Duk da nauyin shi da Umma take ji haka bai hana shi daukata ya rufe ban dakin, ya haɗa min ruwan ya shiga cire min kayan jikina. Kwantar da kaina nayi a jikinshi ina sauke ajiyar zuciya. Hawaye na zuba min at least ina tare da shi all my dreams be coming true. "I miss you Yaya!" A hankali ya saka ni cikin ruwan zafin, naji wani irin dumi ya na ratsani, rike hannunshi nayi shima haka ya sarkefe hannunmu, yana sumbatan hannun nace mishi. "Yaya yunwa nake ji!" Haka yayi ta zuba min ruwan zafin ina jin ruwan har cikin raina. Sai da yayi sanyi sannan ya dibi wani ya shiga gasa ni, musamman kafata da take alamar zata tsage, haka ya cigaba da gasa min sai da na sha ruwan zafi har ina zufa a cikin ruwan sannan ya ce min.."ki kula da ruwan dumin bari na saka a haɗa miki abincin sai n akawo miki kayanki!" Ya rike hannun kofar zai fita nace mishi. "Yaya dawo ka fita da ni, ina jin tsoron kada su dauke ni!" D'aga kanshi yayi yana jan iska, ya dawo ya rungume ni, na fashe da kuka. "Yaya yunwa nake ji ka bani abinci, yaya kwana uku ban ci ba ban sha ba, Yaya Allah ne ya raya ni Yaya ban san zan dawo gare ka, Yaya babu abinda yafi rayuwa muhimmanci, Yaya idan ban yi kukan farin ciki ba me zan yi? Alhamdulillahi Alhamdulillahi Alhamdulillahii Alhamdulillahii at least na rayu!" Na cigaba da kuka yana buga bayana. Kafin ya mike ya isa bakin kofar yayi magana akan haɗa kayan aka kawo mishi, ya shigo ban dakin ya zo ya taimaka min na saka kayan, sannan ya dauko ni a hankali, kwantar da kaina nayi a kirjinshi, ina shashekar kuka na kai hannuna, na sakale wuyarshi ina jin wani irin kuka yana zuwa min kawai ji nake kamar kada ya tafi ya bar ni. "Kina son mu tsaya a haka ne?" D'ago kaina nayi ina kallonshi, kafin na gyada mishi kai ina kwantar da kaina a kirjinshi, kwankwasa kofar aka yi na kalle shi, "kada ka tafi ka bar ni, ka ji!" Na fada ina kuka. Ajiye ni yayi sannan ya gyara muryanshi, suka shigo tare da abinci. "Abba yaushe Tauhid zai dawo?" Mika mishi kofin tea din yayi yana faɗin. "Ki nutsu sai mu yi magana!" Gyada kai nayi ina cikin shan tea din a hankali ina kallon Yaya da ya rasa sukuni. Mika mishi hannu nayi, ya tako inda nake ya zauna a bakin gadon, na daura kaina a kafad'arshi, ina kuka. "Yaya Allah ya isa min! Yaya ban yafe ba, Yaya ba gaji ko ina na ciwo yake! Yaya kasan wahalar da na sha kuwa? Yaya daga inda suka sauya min inda zan fito Yaya tafiyar kafa nayi yaya kamar wata dabba haka suke kora ni." Haka na mika mishi tea din na koma na kwanta a jikinshi ina kuka. "Yaya ina son nayi kuka kada ka ce min nayi shiru, Yaya a haka wani ya ganni da wannan halin da nake ciki ya ce wai yana sona yaya ji nayi kamar alfarmata ya keta!" Na fada ina wani irin hakki rungume ni yayi yana buga bayana, ina kuka ina faɗin. "Yaya ina jin ciwo a zuciyata, ina jin kamar xan mutu." Haka nayi ta kuka kowa yana kallon yadda nake kuka, a hankali ya d'aga ni daga jikinshi, ya shiga bani tea din ina sha ina lumshe idanuna, har na gama sha sannan na koma jikinshi na kwanta, a hankali yayi ta buga bayana, har barci yayi gaba dani. Bude idanun nayi ina kallonsu, na fara barcin ko minti goma ban yi ba na bude idanuna, ina kallonshi. "Yaya ba zan iya barcin ba!" Na fada ina rike shi.." ihun da yaran nan suke wnada ban san me ake musu ba, yasa na rike kunnena da hannu bibbiyu, na fasa ihu na ce musu. "Ku kyale ni nace!" Na fada hawaye na zuba min ina jin wani irin abu yana yawo a kaina, a hankali na fashe da kuka ina kallon gefe, ina jin kukan Yaran a lokacin da za a fitar da ni daga cikin gidan, sai da aka kai ni inda yaran suke ihu, da ransu da lafiyarsu tare da ransu, tare da hankalinsu aka saka abu mai kaifi ana yankasu, a cikinsu har daya yana mika min hannu, rintsa idanuna nayi da karfi na fashe da kuka, ina rike shi nace mishi. "Yaya ban san ta yadda zan taimaka musu ba, Yaya yanka su ake da ransu Yaya ya zan yi kukansu nake ji." Rungume ni yake, idan na bude idanuna. Yaran nake gani, ji nayi kaina kamar zai kunce, na cigaba zunduma ihu da karfi na ina cewa su tafi bani da hanyar da xan taimaka musu, sai da ya saka kawo mishi alluran da ya min, ina kwance a jikinshi.

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 20

*Assalamualaikum Barka da safiya! And ina son nayi wata Magana Allah yasa kada na bata muku rai!😔 Don Allah duk wanda yake ganin 50₦ is expensive please ya dawo telegram! Duk iya ƙoƙarina a 40₦ gaskiya abin sai a hankali Please ku dawo telegram, Arewabooks VIP ne shi yasa na bar Royal politics 500₦ domin na yi amfani da rashin tsadar book 1,2,3, a 500₦ kun ga gaskiya sauƙin yayi da yawa fa! So da ace littafin bakiɗaya 1k ne dole na barshi 40₦ amma yanzu sauƙin yayi masifar yawa ga rubutu akai akai gaskiya ku yi hakuri da soyayya da Kauna nake rokonku ku dawo telegram yadda ba zaku ga tsadar labarin ba, My loyalty fans Bismillah nasan kuna tare da ni dare da rana safe da yamma ina kaunarku har gaban abada Nagode sosai Ubangiji ya bude muku kofar samu dare da rana, Ya Allah ya kare min ku ta rufa muku asiri ya saka albarka a rayuwarku! Sharrin mutum sharrin Aljan sharrin karfe sharrin duk wani abin halitta Allah ya muku tsari da shi ya ƙare ku da kariyansa ina matuƙar kaunarku saboda yadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login