Showing 72001 words to 75000 words out of 157081 words
wanke kaina!" Wai me zai saka na kasa yarda da shi ne? Ai tuni na yarda da shi tare bude mishi rigar jikina ya shiga shagali da kayan alatun da yake kara mishi lissafi.
A hankali zaman sai ya daure, yana waya da gida haka nima, sannan yana yin koma daga nan, satin mu biyu ranar wata juma'a, muna parlourn da Yaran Mira tana wasa da Yaran sai dariya suke ba sai ga akwati ana shigo da shigo da shi ba gidan, Nadiyyah ce, kallon juna tai ganin yadda nake bawa Ayaan abincinsu cak ta tsaya Princess da take kallonta, da gudu ta je ta rungume ta. "Mommy welcome!" Murmushi na sakar mata, ita kuwa ta hade rai. Tare da ɗaukar Yarta suka hura sama. Ban kuma jin motsinsu ba, sai kukan Princess, har cikin raina nake jin zafi da kukan tana kiran Ayaan ita zata zo wurin Ayaan ne, shima Yaron da yake jin kukan yar uwar sai dube-dube yake ina nimanta, can ya kalli sama inda yake jin kukanta. Karar bude kofar da aka yi tare da fitowarta da gudu ta sauko kasa yayi daidai da shigowan uban, ta nufi wurinsa tana faɗin. "Daddy Mommy ta mare ni!" Kallon sama yayi ya dire yarinyar kasa yayi sannan ya nufi sama, ban san yadda aka yi yasan tana gidan ba, koda yake zai sani tunda gidansa ne kuma yana sane da duk wani abinda yake faruwa. Daga nan ƙasa muna jiran sautin muryansa. Lokacin da ya shiga cikin dakin, Yarana basu saba da jin yana fasa ba, sai suka fashe da kuka. Idan na cire muku Ayaan, da yake kallon sama yana saka hannu yana damar Isma, yana fada Nadiyyah na faɗa, sai na rasa me yake min dad'i, domin ƙarshen sa'in'san mari na ji ya dauke da shi tare da kiranta da ita ma Kashiya ce idan ta samu dama kashe shi zata yi, aikuwa haka ce ta faru ta ce mishi. "Na rantse sai dai mu rasaka dukkanmu idan kace Zainab ka zab'a." Anan na fahimci fadar nawa ne dama ashe, shi kuwa ya kifa mata mari tare da janyo ta waje ya watsar da kayanta.
Abun sai ya bani mamaki da dariya, na zuba mishi idanu, ban kara cewa akan me yake rayuwarsa da matansa ba, wai ka fa duk wannan bala'in da ake bai sake ta ba, taya zan shiga maganar da bayan na san aure rai ne da shi, bayan isha wurin tara yara sun kwanta ba sai ga yan sanda ba, ta shigar da shi kara yayi kidnapping din Yarta. Wannan shine mafi girman abinda Nadiyyah tayi har ni sai da ya min ciwo, daga nan suka wuce police station, har da yar da visarta, wasa wasa sai ga su har kotu washi gari, ni dai kwana nayi ban rintsa ba, da safe ya dawo ya zuba min idanu yana sauke ajiyar zuciya. Ruwan wanka na hada mishi yayi na shimfida mishi abin sallah, nan ma yayi sannan ya kwanta a gadon yana fada min. "Karfe daya ki tashe ni zan tafi kotu." "Allah ya kai mu!" Na fada ina fita daga dakin. Har zan fita na ce mishi.."na kawo maka break fast?" "Ina azumi!" Yana fadar haka na juya na fita, duk sai na ji zaman garin ya ishe shi. Tun karfe sha biyu da arba'in na tashe shi, ya shirya sai da yayi Sallah sannan ya fita wurin Yaransa, ya ɗauke su daya bayan daya, sannan ya bar gidan bayan na rako shi, ganin yana azumi da kaina na shirya mishi kayan bude baki, karfe biyar da rabi sai gashi da princess, hawayen farin ciki ne ya zubo min itama yarinyar ta sha duka kasancewar kalar fatar uwar ta sauko fuskartar da jikinta yayi ja, amsarta nayi ta fashe da kuka tana faɗin. "Mammy she beat me! She kick me!" Rungume ta nayi very tight ina faɗin. "Sorry my princess, hkaa ba zai ƙara faruwa ba."
"Na gode sosai Zainaba, kin koya mata abinda ni ban fahimta ba, yarinyar nan yau a gaban jama'a da alkali ta wanke ni, tunda suka tafi da ita masaukinta, yarinyar take kiranki da ke da yan uwanta, shine tayi ta marinta, ko da muka zo kotun aka ga yarinyar tana kuka bayan ta mata barazana da cewa matuƙar ta ce wurinki zata zauna zaki kashe ta, haka bai isa ba sai da ta mata duka, Zainaba wannan wani irin son zuciya ne? Yarinyar nan haka ta zo tana ajiyar zuciya, abu ne farko da aka fara tambayarta me ya same ta, abun da ta ce ya bani tsoro ta ce musu ai Mommynta ta ce idan ta fada musu zata yankata, sai kallo ya koma kanta, me yasa ta mata dukar ta ce tana son zuwa wurin yan uwanta ne ta mata duka ta ce mata stepmom dinta muguwa ce! Zainaba yarinyar nan take fada cewa tunda na kaita wurinki baki tab'a, mata ko tsawa ba. Amma yau Mommynta ta dake ta, tayi kicking dinta, ita a kaita wurinki dasu Ayaan!" Ajiyar zuciya na sauke. Na ce mishi. "Kasan Allah? Addu'ata ba zai tafi a banza ba, Saadiyyah ita ce rokona ce. Tawassali na ce, sujadar godiya da nayi da azumin da nayi dominta Allah sai ya kintsa mata so da kaunata wanda babu dalili babu iyaka, ban rabata da mahaifiyarta ba amma soyayyar da zata min na musamman ne , ina sonta ina kaunarta ko an raba ni da ita zata dawo gare ni domin nasan tun kafin wanzuwarta Allah ya cusa min soyayyarta, da ta bayyana Allah ya daura min jarabawa a kanta, y'ace no reason na ce ba nawa ba ce. Burina da fatana yana kanta, na san Nadiyyah zata dawo amma Saadiyyah tawa ce." Na fada ina kuka, saboda kishi ka cutar danka, haka na wuce da ita daki na mata wanka na bata magani, shima ya zo yake gaya min na hada mishi ruwan dumi yayi wanka, ina gamawa na wuce kitchen na hada abin buɗe baki na kawo mishi, ana shan ruwa yayi bude baki da addu'a sosai, n a shiga dakin na samu princess na basu chips, sai mamula Ayaan yake Ayaaz kuwa ya amayar, Ayyanah tana da shi. Ayaat kuwa kallonshi take kamar zata yi kuka ita fa zuciyarta bai cika aminta da kome ba, don rashin wayonta ya gaya mata kada ta yarda da kome. Wuce su nayi na gabatar da sallah, ina idarwa na saka princess itama tayi, kallona tayi ta ce min.."Mammy ki yi musu alola su zo mu yi sallah!" Aiki ga mai kai, haka na musu alola ta kuwa shiga gabansu, ita nan limamamiya, wannan ai sai ace ina niman rigima, yadda suka hadu har da isma aka yi sallah, bayan an idar aka yi ta addu'a. Kafin aka idar aka fito parlournshi, aka shiga bashi labarin yadda aka yi sallah, da zasu yi isha nan ma shi ya ja mu, wurin tara nayi musu wanka yaran na kwantar da su, ita dama da wankarta. Bayan sun yi barci na tafi dakinsa, duk yadda yaso mu tattauna naki domin cewa nake. "Aure rai ne da shi. Anyi irin abin da yafi haka sai a dawo a zauna lafiya kamar bai tab'a faruwa ba." Wai akan me zan fadi haka, share shi nayi ai ba zai kara min gorin na janyo uwar yarsa sun rabu kamar wancan lokacin.
Haka ya gama iyayinsa ya murza ni son ranshi, the next day sai ga Nadiyyah ita yarta zai bata ba, yarinyar da ta ga Uwar dakina ta shiga ta boye kanta cikin abin wasansu. Murmushi nayi da na shiga na ganta tana kuka ita ba zata na. "Kwantar da hankalinki babu inda zaki!" Da wannan yarinyar tai barci.
Ban yarda nayi wani abun da zai saka ta fahimci ina cike da ita ba, shima da ya dame ni kamar ma tsoranta yake ko shakkarta ya ce min. "Ya zanyi da ita?" "Ni kake tambaya? Bayan baka sake ta ba zaka tambaye ni ya zaka yi da ita?" Cikin gatse na ce mishi.."sai ka dawo da ita tunda dukkanku kuna bukatar juna!" Hmm namiji dan babansa, ba sai ya dauki shawarar ba, cikin kwanaki goma sha biyar, ya dawo da ita bayan sun yi yarjejeniyar sulhu da idan ta kara cutar da shi ko iyalinsa sai ya sake ta, sannan ya rabata da Princess, ya bar min kai abubuwa dai gasu nan, tun daga ranar na watsar da lamarin.Yaya domin na fahimci yadda yake da mugun son kai da son zuciya, batun idan kanshi ne tow magana ya ƙare, ya dawo da Nadiyyah domin muradinsa na ya haɗa mata biyu gefe da gefenshi ne, ni kuwa nayi alƙawarin duk abinda zasu yi nawa idanu.
Zan iya cewa rabo yana daga cikin dalilin da yasa ya dawo da ita, domin a cikin kwanakin da ya biyo baya an yi shagali anyi ta iskanci daga shi har ita, kwashe Yaran nayi na mai da su zaman dakina. Abin yana min ciwo, amma haka na share kamar bai dame ni, kishi halal ne amma irin kishina ni daya ke ci, domin kuwa sai na fara lalacewa, ga ciwon kai da ciwon kirji, haka nake kwana. Kusan wata guda ina fama da shi ranar da ya zo dakina ya ga yadda nake kwanciya cikin damuwa, sai ya ce mu shirya mu je asibiti, gwajin da aka yi ta yi aka gano ciwon kirjin yana da nasaba da ciwon zuciyar da nake fama da shi, ganin yadda har lokacin ban yi magana ba, bayan bayanin da nayiwa likitan, sai tsoro ya kama shi, bayan na amshi duk wani kulawa da ya dace, mutumin nan ya tattaro ni da Yarana, ya ce mu dawo gida na kula da kaina, tun daga nan ma fahimci ya sake kuskuren da dole na barshi, domin kiri-kiri ya karbe yarsa, ni kuwa da na fishi hauka kafin ya gama nima min dawowa, na yi fix din nigar da Addis Ababa, lokacin da na gama shi kuma ya samu min adidis Ababa da Nigeria, haka muka bar gidan, ban bin ta kanshi ba. Ranar tafiyar da na shi tsira kwana biyu ne, haka yasa na hakura har aka gama kome na tafiyata. Dole na yi sabon booking, ranar da na bar Scotland. Muka sauka a Ethiopia, ina shiga na jira jirgin nigar, na kuma yi cancel din Nigeria. Ban gaywa kowa ba, kai tsaya Niayam muka sauka, anan mijin Ihsan yake aiki da ita ma, tunda na sauka nake fama da jinya, haka muka yi ta fama, sati biyu ina fama domin abin yana min ciwo, ko tunawa nayi sai nayi kuka, haka nayi ta jinyata har na samu sauki, sannan na cigaba da zama a cikin Nijar. Domin ban boye mata abinda ya kawo ni ba, na hakura da shi kawai. Murmushi tayi ta ce min. "Ki zauna anan sai duk lokacin da kika bukaci komawa don kanki, amma ni babu me sanin kina nan in sha Allah.!"
Haka nayi ta fama da jinyar zuciya, kafin na samu sauki. Kawai sai na dauke duk wani social media na, domin na samu nutsuwa ina bukatar na nisanta kaina da abinda zai hada ni da Salmanu Faris.
Haka na bude sabon shafin rayuwa, a kasar Nijar ya je can ya zauna da Matarshi.
***
Tunda muka bar kasar, yake kiran wayata bai same ni ba, sannan ya kira Mai Babbar daki ya gaya mata mun tawo fa, Ni da Yarana amma yau kwana uku bai ji daga gare ni ba, wannan abin ya d'aga mata hankali, haka aka tambaya gidanmu babu labarina, da farko sun zata wasa ne sai da aka tabbatar mishi da cewa da gaske ban zo ba, sam sai Allah ya mantar da shi zuwa addis Ababa, sannan koda ya bincika an tabbatar mishi jirgin Nigeria na bi sai bai wani saka kanshi bincike ba, haka ya dawo, Nigeria aka shiga bincike akan ko ina cikin garin da sauran wuraren da zai. Hankalin kowa ya tashi.
Lokacin da ya sami Abba da maganar ko za ayi wani abu, murmushi Abba yayi ya ce mishi. "Tunda Zainab ta dauki wannan tsarin na nisanta kanta da kai. Ina gaya maka tabbas ka yi mata abinda gara ta hakura da kai ta samu zaman lafiya. Gaka da hankali amma baka aiki da shi, saboda ka renawa hankali ka dawo da yarinyar da nan ka kira ka shigar da kai ƙara akan Yarku. Haka kuka gama zubar da darajar juna a titi, sannan yau ka dawo da ita. Ai ba laifi ba ne dama can haduwar bariki ce, kuma dole ayi irin wannan zaman, madalla da halin Zainab ta shi ka bani wuri." Cikin sanyi jiki ya ce mishi. "Abba ita ta ce na dawo da ita!" Kallonshi Malam Junaid yayi ya ce mishi. "Kana rawan jiki kamar akan aka fara tarayya da y'a mace me yasa zata ce kada ka dawo da ita? Kaf ba alfahari ba ni nadan ko Ubanka yana raye gatar da zai maka kenan ya nima maka mace irin Zainab, dalla b'ace min a gaba Allah yasa taba bayyana ta ce saki take bukata na ga yadda za ayi ka ce ba zaka sake ta ba. Wallahi sai na baka mamaki, tunda baka san ciwon kanka ba ga ka babba amma ba na hankali ba!"
Wayyo haka ya fita da damuwa, ya nufi Fada wurin Mai Babbar daki. Yana gaya mata yadda suka yi da Malam Junaid. Wani irin kallo ta mishi ta ce. "Da ya bi bayanka da na tsine maka albarka ka lalace ka daidaice mara hankali wawa katon banza da bai da hankali. Anya kai kasan halicci? Baka sani ba amma kasan bin mata kamar bunsuru ka fita min kafin na maka Allah ya isa saka zuciyata da kayi cikin kunci da damuwa sakarai mara wayo ka je can ga su can ka cigaba da musu abinda ka saba musu..
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 27
Haka na cigaba da kula da kaina, zama hakan ya dame ni sai na biya kudi na shiga wata makarantar kwarewa na harkar jarida na tsawon wata shida. Haka na mai da hankali na kuma saka kaina a gaba da karatu, duk da ina jin kewar gida da kowa na saba da can amma haka sai yasa na samu wani irin nutsuwa, na farko gani ga Isma, na biyu bani da matsalar kome da kowa. Sai karatu kudi ina da shi, ba zaune nake haka kawai ba.
Yarana kuwa ina da Nanny wata yar garin damagaram, ita ke kula min da su ina biyanta, don daga baya da kaina na bukaci barin gidan Ihsan na kama apartment, Mai kyau na zuba kome domin Yarana da kuma kaina. Idan na samu lokaci ina duba email dina, anan na ga sakon Abba yana tambayar ko ina laifi na kuma gaya mishi lafiyata lau, Yaran ma na tura mishi hotonsu ya gansu har yadda suke rararfe. Ya tambaye ni ko akwai abinda nake bukata na tura da international account dina ya tura min kuɗi, dariya nayi na tura mishi kudin da yake account dina, hoton murmushi ya tura min ya ce min shi zai yi haka ne a matsayinsa na mahaifi, ban yi kasa a gwiwa ba na tura mishi, yadda muke yawan hira da shi lokaci zuwa lokaci, na gaya mishi ina Nijar amma idan ya gayawa Salmanu Faris zan bata ba za a kara ganina ba, dariya yayi min yana faɗin. Tow shi Yaro ne da zan mishi kashedi? Zai zo ya ganni ya ga halin da muke ciki.
Ban ki ba na bashi address, sati biyu a tsakanin Abba suka zo da Nuraim, ganin ina cikin kwanciyar hankali yasa shi jin dadi ya kuma tambaye ni ya na lalace, na ce mishi goyon da kuma karatu sai rashin lafiya da nayi fama da shi, har na nuna mishi maganin da nake sha, ya ga duk na ciwon zuciya ne. Tausayina da wani irin kauna yake min ya ce min." Zainab idan kina ganin zaki cutu ko zaa raba auren ne? Tunda na san ba halinki ba ne fushi haka amma da alamu kin yi haka ne don lafiyarki da rayuwarki!" Idanuna ne ya cika da kwalla, na ce mishi. "Abba duk abinda kayi dai-dai ne, ni kawai ina son zuciyata ta huta da damuwa ne, don Allah kada ka kara hada ni da shi, na gaji!" Gyada kai yayi sannan ya ce min. "Shi kenan zan saka ya sawwake miki!" Gabana ne ya fadi ban iya magana ba, haka suka kwana biyu suka koma, ni kaina na ji kamar nayi wani kuskure ne, amma da na tuna ban mishi kome ba sai na bar zancen na cigaba da kula da kaina.
Haka na samu wata uku mai kyau, anan ne da muka samu hutu na ji zaman garin ya ishe ni na dawo Maradi nayi hutuna, muna cikin hutun Ya Abid ya zo, yayi mamakin ganinmu, domin babu wanda ya gaya mishi ina maradi. Shiru yayi yana kallon yadda Yaran suke ta wasa a gidan Kawu Hamidu cousin brother din Maluma, daukar wayarshi yayi ya kira Maluma yana gaya mata gani a gabanshi. Cikin nuna mishi ai ta sani ya sake baki, murmushi nayi ina gyara wandon Ayaan da yake son lallai ya cire Tente Amarya sai dariya taƙe mishi tana mishi waya, yaron sai haɗe rai yake yana kokarin cire wandon Ya Abid ya ce min. "Dama kowa ya san kina nan?" Gyada mishi kai nayi ina faɗin. "Eh sun sani kawai na zabi na zauna a nan!" "Wani irin kin zabi zama a nan e kawai? Kin san abinda kika