Showing 84001 words to 87000 words out of 157081 words
wacce ta kara magana..
Bayan sallah azhar ina kwance na ji ana ihu ina fitowa Nadiyyah ce suka fada da Ikram,ana ta rabon fada abu ya gagara. Yaran suna kwance. Kawai Yaron nan ya fita ya leka ya ce min. "Koma ki kwanta yanzu kangaye ajo!" Yanzu kadangare zai zo! A matukar tsorace na ce mishi. "Haba Ayaan me yasa zaka haukata ni!" Wayyo dariya yayi ya wuce dakin ya kwanta.
A can kuwa kasa dambe suke kamar zasu kashe kansu, an rasa mai raba su kuma duk akan shanyar kaya Nadiyyah tasa an zubar da kayan Ikram kuma suka bi kai tayi mata magana ta ce tayi din idan gidan Ubanta ta dauki mataki, ita da ma bata san matsayinta a gidan ba tunda bata da d'a ko ciki. Abinda yayiwa Ikram ciwo kenan ta tare ta suka fara fada kamar me, abinda na fahimta ga matan Yaya shine akan wani abu sai su maka gorin d'a ko haihuwa. Ita kuwa Ikram ta ce mata. "Na yarda shi yasa da danki ya mutu kika kasa hakuri kika kama hauka da sharri wa Ikhlas, kamar yadda kike ciki da Faris nima haka xan yi waye ya sani ko Saadiya ba jininsa ba ce shegiya aka ɗauko a waje waye bai sani cewa dashen ta aka yi. Hala yar wani arne ne" shi kenan dambe ya kaure, dambe mai sunan dambe suka yi suna cikin yi. A hankali kadangaru suka yi ta cika parlourn kasa. Can suka ji wani yana faɗin. "Kai namakoro matsa kada a a take ka!" "Ni dai ko an take ni zan tashi kawai sai nake a buga wata da kasa na samu mafakar siyasa. Tunda abin ai haka ne yau shekaru dari hudu ina niman mafaka a zanzabira sai ga mai gida ya gayyato ni, inji wani katon damo.
"Kai kuwa aminin birbiri baka ga yadda wancan take juyi ba ai tana tare da bakar Inuwa." Inji wani biri a wurin, wata kaza a wurin ta ce musu.."maza su cigaba da dambe ai yau zamu sha kallo!" Cak suka tsaya tare da juyawa suka kalli yan kananun halittun da suka cika parlourn. Wani bakin akuya ya fashe da dariya yana faɗin. "Na rantse sun gano mu yi huhuhu.......(Duk wanda yaji tsoron ba ruwana)
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 31
Ihunsu da guje-gujen su ya cika gidan, Yaron nan kwanciya yayi son ranshi ya daura kafa daya akan ɗaya, yana wani shegen murmushi irin ya haɗa boom ya koma gefe yana jin ƙarar tashinsa, daukar shi nayi tare da rungume shi. "Don Allah ka bari!" Na fada da karfi ina jijjiga shi, kallon kwayar idanunsa nayi na ga ya koma tankar ta isma. "Nace ka bari!" Na daka mishi tsaya tare da d'aga hannuna kamar xan mare shi, lumshe idanun yayi ya kwantar da kai a kirjina. "A bayi!" Ya faɗa yana me tura min baki gaba. Sai na ji dadi ko babu kome na fada kuma ya ji.
Tunda na ga abin ya koma haka sai na daina yarda ina bari rigima tana hada ni da yan gidan, kowa yana wurinsa da Yaranshi. Ni fa tun dawowana ban ga Aneesah ba, ko da na tambayi Sailuba sai ce min tayi ai tana Farin ƙasa, kuma tana hanyar dawowa can ma sun haɗu da Amrah suka yi rigima akan ita take saka Ijlal aikata wasu abubuwan, Ni dai nawa idanu ban kara bin wani batu akanta ba. Sai yau juma'a da muka shiga cikin gidan, anan na ga kowa hankalinsa a tashe, wai ashe yan fashi sun tare motar da ya je ɗaukarta ne,
Muna zaune a gidan har wurin karfe tara na dare suka dawo, anyi mata mugun duka. Tare da zana mata sunanta a a bayanta, abinda ya faru bai saka ta shiga hankalinta ba, amma kuma bata nutsu ba, wannan abin da yake damunta bai dame ta ba, kamar yadda ta ganni a cikin gidan dan uwanta. Ban san me yasa ta tsane ni ba, sai dare muka koma gida, da yake na bar Ayaan a wurin mai babbar daki. Domin an wuce da Aneesah asibiti. Tunda muka dawo gidan na wuce bangarena ya wuce wurin Nadiyyah. Wacce har yanzu take fama da depression har yau na mutuwar danta amma bai hanata fada ba. Wanka nayi na kwanta bayan nayiwa Yaran wanka suma. Ina kwance dai gashi ya shigo, zama yayi yana kallon yadda na kwanta. "Zainab?" Tashi nayi zaune ina kallonshi. "Ina son mu yi magana ne!" "Ina jinka!" Murmushi yayi na zauna da kyau. Shiru yayi kafin ya ce min. "Kin san dukar da aka yiwa Aneesah yana da alaka da ke?" Sosai na zauna ina kallonshi. "Yes ta ce yana da alaka dake, wnada suka mata dukka sun ce matuƙar bata fita harkanki ba, sai sun kashe ta Please Zainaba gaya min gaskiya meke faruwa ne?"
Wani irin bugawa zuciyata tayi na dafe kirjina, da sauri ya mika min goran ruwa bayan ya bude min na sha, ajiyar zuciya na sauke ina kallon shi. "Yes maganar da nake haka ne, Zainaba tun ranar da aka sace ki, nake ji akwai wani abu da yake faruwa a cikin gidan nan, a tattare da ke akwai wani daga cikin gidan Yayari da yake bibiyarki!"
"Tunda ka gano haka me yasa zaka tambaye ni? Tunda ka fahimci wani abu yana faruwa me yasa ba ka magance shi ba?" Na tambaye shi idanuna jajjur, ban bashi damar kara min wata tambaya ba na ce mishi. "Kana nufin ina cikin masu son ganin bayanka kenan? Ko me kake son faɗa? Idan wannan shine lissafinka wallahi baka min adalci ba, amma na gode!" Na juya na kwanta, ban kara tanka mishi ba. " Dole nayi magana, daga cikin gidan nan aka turo min sakon kina nijar, daga cikin gidan nan aka tabbatar min da cewa kafin ki dawo gare ni sai na zube a gabanki ina kuka. Kin zata nayi kukan ne don ina son ki dawo? Muradin kare Yarana ne idan na barki kika tafi haka rayuwar Yarana nake tunani, shi wnada yake aikata kome yana cikin gidan nan, sannan." "Tashi ja bar min dakina, tashi ka fita nayi dansanin dawowa gare ka domin kai ba mutum ba ne da zuciyata zata aminta da shi!"
Sai naji raina ya b'aci sosai, haka ba bar mishi dakin, zan nufi kitchen. Wato ina fitowa waje ji nayi an ingizo ni daga bakin kofar dakina zuwa stair na fado sosai, ji nayi jina da ganina ya dauko, amma kafin lokacin na ga kamar an fita daga ɓangarena ban kuma sanin me ya faru ba.
Shima jin shirunta yasa ya fito waje, sai dai kunna hasken wayarshi ya hango ta kwance. "Zainaba!" Ya kwala mata kira da karfi. Amma ina shi passing out. Haka ya dauke ta ya hauro sama da ita, ya shiga bata duk wani taimakon gaggawa. Har ta farfaɗo, kafin ya zauna a dakin ta kara komawa barci. Sai da ya rufe ta sannan ya nufi bangaren Nadiyyah da take barci abinta ya kwanta a bayanta, kai kasa hakuri yayi ya bar dakin ya nufi bangarenshi, haka ya shiga dakin sirrinsa anan ya shiga bincike sai yau ya ga abubuwan da yake faruwa a gidansa idan baya nan, sai ya manta da abinda ya kawo shi ya shiga wani abin, yadda Ayaan yake bawa Nadiyyah mamaki kafin ya sauka kan abinda yake faruwa, ya ga an fita amma abin mamakin wasu abubuwan baya ganinsu domin kamar ana dauke wurin wurin ne, a abin da ya kara bashi mamaki kamar yadda aka turo Zainab daga sama aka gudu haka ya ga wani video ranar da Yaron Nadiyyah ya rasu,.abin sai ya kara bashi mamaki mutumin da ya turo Zainab da irin gudun ya gani amma ya rasa waye take ya kira Faruq ya gaya mishi, Faruq da yake fama da kanshi da kuma Yeemar da take laulayi. Haka ya taso shi a gaba a daren suka yi ta bincike amma basu wani samu wani abu haka Faruq ya bar gidan.
Washi gari haka na tashi jikina da wuyana yana masifar ciwo, wani abu da na kasa ganewa waye ya tunkud'o ni daga sama? Meye ribarsa? Haka dai na cigaba da jinya har na ji sauki ana haka sai da Aneesah ta dawo gidanmu. Ayaan yana wurin mai babbar daki, Ayaat da Ayaanah da Ayaaz suna wurina, haka idan muka gama karyawa nake kai su parlourn kasa su zauna su yi ta wasa, ina aiki sama da kasa. Tunda Aneesah ta dawo sai ta tsiro da wani abu daya shine zata kira Yaran su zo parlourn wurinta, ko ta dauko su bakiɗaya. Idan ta haɗa su wuri guda, sai ta saka yar Nadiyyah a gaba tayi ta musu wasan banza ana dukar su, Ayaaz sam yaron son damuwa ko wahala shi bai da juriyar hayaniya kamar yan matan. Haka yarinyar nan ta dauki wayar charge tayi ta tsulla tsiyarta da shi tana zane su, kukansu ya ki karewa na fito magana. Amma yana dawowa ta ce mishi ya ja min kunne don ta kwashe Yara tana wasa da su, na saka mata idanu. Shi kanshi yasan tunda nayi magana akan Yaran ba karamin al'amari ba ne, haka yasa bai fara min magana ba, sai ranar girkina ya min magana ina rungume a kirjinshi ya ga bance kome ba, har ya gama magana kaina a kwance, haka har ya gama kwanakinsa. Ya bar dakin sai ta cigaba da abinda take, ai kuwa Ranar da ta ishe ni, domin bakiɗaya Yaran kuka suke wai sai take cewa. "Ai da yake kunne ƙanana dole manya su gyara muku zama;" "inji wani dan kutumar buran uban?" Yadda na fito a fusace, ta zuba min idanu. Dariya ta kama tana faɗin. "Na zata baki damu da yaran ba ne ai naga da kike tsula tsiyarki ai dawo mana da Yaran kika yi?" "Kamar yadda kike rokon a turo miki Yaranki dangin Mijinki da shi mijin ya ji shine aka ce miki ni sakarya ce irinki mai kan dusa? An gaya miki ni akan yaran nan zan iya haukar da wasu matan suke yi ne? A gabana babu yar bura uban da zata tab'a min su na kyaleta amma kin ci karya kin kwana da yunwa ki dakar min Yara ki dauka zan kyale ki, daga yau ba zasu kara fitowa ba."
"Ke karamar yar iska dama ina jin haushinki, shegiya munafuka yar matsafa." "Ni dake ban san waye yake tsafi ba." Na juya zan fita ta janyo min rigana, ai kuwa na juya na kifa mata marin da sai da parlourn ya amsa dai-dai shigowarshi cikin parlourn, a zahiri ni kaina na ɗan razana amma yadda ya wani dauke kai kamar bai ji ba, yasa na hada kan Yarana muka koma parlourn, kuka ta fashe da shi tana fada mishi abinda ya faru, ban ga wani tashin hankali a lokacin ba. Sai dai wani abu da yake yi ya daina shigo min dakina. Yaran ma ya dauke kai akan su. Amma naji yana damuwa da Ayaan nace ayi a banza. Tun daga lokacin Aneesah take takalata da fitina. Kai da na gaji na wuce wurin mai babbar daki, a lokacin na san nayi wani kuskure ɗaya, shine idan har ni Uwa zan dauki doka a hannuna ita da ta haifi Aneesah da Faris fa, yadda take karbana da nuna datajata a gaban jama'a, yau sai na ga kamar bata wani yi appreciate da zuwana ba, sannan ga Princess da Amirah da Nana A'ishah a wurinta, abinda na yi niyyar fada sai na fasa, aka ce idan shege ya b'ace shege ake turawa ya nimo su, don haka na ga zasu tara min ciwon kai, ranar talata na kwashe Yaran har ayaan na tura gidan Faruq na ce ya rike su,Allah ya sakawa Faruq da Alkhairi da shi da Yeemar sun min kome sun kaunace ni, sun fahimci kukan da nake yi silently or loudly, sun fadi yadda nake survive domin na tsaya a kan kafana. Sai gashi ko wata shida ban yi da dawowa ba Aneesah zata sako ni gaba, sai na tattara kowa na watsar, haka da nayi ita mai babbar daki sai da ta kasa hakuri tayi ta min magana ina Yaran, domin dai.daga Ijlal har Nadiyyah babu wacce zata bata aron Yaran kamar yadda nake yi, ai kuwa na yi tsalle na bar zancen karatu da zuwa shigo ya ishe ni, satinsu daya na tura su gidan Ya Abid, domin a satin muka fara bikinsu Nuraim da Ya Yunus, kome ya kacame min. Tsakanina da shi ina kwana shima sai mun haɗu idan ba mu hadu ba, lafiya lau kowa ya kama ganshi. Nifa ba fada da ni ba ne kwana mita, bai tashi ganin Yaran ba sai ranar daurin aure ya gansu, tsakaninsa da Allah yayi kewar Yaransa, haka yayi ta daukar su yana ajiye su. Kamar ya dawo da su gida ba. Lokacin da ya shigo ya samu ana ɗaukar hoto, gashi na saka wani lacce da ya min kyau domin fittergown aka yi min, ya bi jikina ya kwanta sosai. Karin bayani kuwa an yi min Makeup kamar wata aljanar yar kwalliya haka na koma, duk wanda ya ganni ya ga Yarana sai ya rantse da Allah bani ce na haife su ba, domin jikina bai yi irin budewar nan ba, na samu kulawa sai na koma kamar wata yar budurwa mai ji da yan matanci, haka muka yi ta hidima idanunsa yana kaina, shi ya ma rasa me ta shiga kansa da ya jingine Zainaba, tsaki tayi yana jin haushin kansa.
Bayan an gama ɗaukar hoto na zata ya tafi ne fa,sai ga Amir din Aunty Nu'aymah Wai na je parlourn Abba idan da bako, ko mayafi ban dauka ba na nufi bangaren Abba, ina shiga naji Yaran suna bashi labarin abinda suka ci, sai saurarensu yake daga bakin kofar na juya na hado masa kayan bikin da aka yi. Sannan na dawo parlourn, ina jin wani cikin abokan Ya Yunus yana faɗin. "Don Allah tsaya ki bani number wayarki mana kanwarmu!" "Ya Yunus bai gaya maka cewa, ni Matar aure ba ce?" "Oh sorry ba sani ba, ba kome,;" na shigo parlourn, cikin idanunshi na kalla na hango kishi fal, ajiye mishi nayi na riko hannun Yaran na ce musu.."oya Ayaan ga shi ka raba muku kowa a bashi kudin karinsa ko!" Na ciro Naira hamsin na basu na yan biyar biyar, kallona yayi shi ya rena hamsin. Ya ki amsar kudin hannu Uban ya saka a cikin aljuhunsa ya cire dubu daya daya ya raba musu su hudu, bakiɗaya a wannan watan zasu cika shekara biyu, amma wayon Ayaan yayi yawa. Kamar na saka kuka na dauke kai. "Ni dai kada a lalata min tarbiyyar yara da kuɗi!" "Ai naga tarbiyyar da kike da shi kike yawo a cikin kartin maza da suke taya ko a kasuwa kike?" Murmushi nayi na ce mishi na kai hannuna kirji cikin yanga da yauki na ce mishi. "Ni ba tashin hankali nake bukata ba, muna shagali da hidima ka bari idan kana da wani magana sai ka jira na dawo gidanka." Na faɗa ina kokarin tashi. Ya ce min. "Karfi da yaji kin shiga tsakanina da Yarana, haka bai miki ba kin raba su da Kakarsu tana can tana damuwa da Yaran yaushe zasu zo gare ta. Sannan kin zo kina yawo cikin maza tsirara don Allah dubi nonuwarki da suka tsaya a cikin rigar wani shege ne ba zai ji yana kaunar ya kebe da ke ba? Gaskiya zan fara Allah ya isa akan wannan abin da kike min na gaji mai na miki kike min horo ne?" Dariya abin ya bani na mike ina faɗin. "Da girman soyayyarka ranka ya dade abin ba na Allah ya isa ba ne, yara zan duba lamarin!" Daga haka na yi shiru bai ko sha ruwa ya ce min. "Ban yarda ki fita dinner ba yawwa!" Ya saka kai zai fita na ce mishi. "Kayi hakuri amma zan tafi." Cak ya tsaya kafin ya juya yana kallon yadda na dauke kai. "Zainaba!" "Faris!" Na kira sunansa, dawowa yayi ya tsaya a kaina.."Fito ki gaya min me nayi miki?" "Ka addana tambayarka zan dawo gidan jibi!" "Yau zaki dawo ki gaya min me kike nufi da ni." "Allah ya kai mu!" Yana fita nima na fito rai a b'ace, Yaran kuwa ba zan mai da su ba.
Bayan isha ya turo faruq ya dauke ni, yana ganina ni daya ya fara Bala'i kamar zai dake ni tsayawa nayi da kyau don na ga matansa sun leko, sai na wuce abina ban kula shi ba har da Kanwarsa, parlourn kada na shiga na zauna ya biyo ni. "Ina Yarana?" "Oh yanzu dai na bar su gidan Malam Junaid." Na fada ina cire gwagwaron kaina."kika ce me?" "Da Hausa na fada ai!" Na cigaba da rage kayan jikina. "Yaran da kika watsar kika ce baki bukatarsu, shine kika hauka akansu?" Ya fada da ihu. "Daga ni har kai a wannan lokacin ban san waye yake haukar ba, matankau suna jinka, kasan ni ba zan d'aga murya ba!" Wayyo ashe bala'i na tono da ranta. "Kika ce me?" Ya fara masifa ina mai da mishi kasa yadda shi ɗaya yake jin amsata, yadda suke jin ihunsa sun zata nayi yi shiru ne yake masifa sai da suka ji.na kwashe da dariya na ce mishi da ƙarfi. "An gaya maka ina tsoron saki ne? To ka sake ni wallahi wata uku na cikawa zan buga aure mai tsada ka ji na.gaya maka ni ba irin kucakan matan nan da kana pushing ɗinsu daga