Showing 66001 words to 69000 words out of 157081 words
gyara dakin na saka turaren wuta ba hadawa Yaran ruwan dumi na musu wanka sannan na dawo kitchen na dauki abinda zan dauka, ina komawa na samu Rabi a daya dakin tana ta gyarawa tana tattara kome zata kwanta. Murmushi nayi na ce mata. "Rabi jira zan kawo miki abinci!" Na fita sanye da doguwar rigar da na sauya. Da ikram muka haɗu tana kallon na nufi dinning room, ta sake murmushi kawai sai naji zuciyata bata yarda da abincin ba, haka na dauki ruwa kawai na dawo dakina, samunshi nayi ya kawo kayan abincin, ajiyar zuciya na sauke ina tunanin ko ba zai zo bane, sai gashi nan ya zo kuwa murmushi nayi mishi, haka ya kawo abincin, ya zuba mana ni kuma na kaiwa Rabi,na dawo daki na zauna muka abincin, sai da muka gama na sha sirki da garin hulba sanan na bi Yaran da suke gadonsu na bawa kowa ya sha kafin na wuce wurin Rabi na mata sai da safe. Sannan na dawo dakina, na same shi yana yana mai shiga ban dakin, yayi wanka ni kuma na kwashe kayan zuwa kitchena na kasa na rufe ko ina na tofe gidan sannan na zuba ruwan addu'a, na dawo na rufe kofar Parlourna da yake da nashi, gam don zasu iya biyo mu su mana labe, wannan karon Yaya bai taɓa burge ni irin wannan lokacin ba, haka na koma dakin na samu Ayyanah tana ta rikici kamar zata shide na karbeta haka muka yi ta fama da ita wai ashe ruwa take so, shi ne yayi tunanin bata ruwan har tana kwarewa. Bayan na bata na kuma bata nono ta sha sannan nayi ta mata yar dabara har barci ya dauke ta, Maluma ta koya min yadda ba sai da nono yaro zai yi barci ba, na kwantar da ita na gyara jikina, kallona yayi yana faɗin. "Ke yanzu ba zaki iya kwanciya da su?" "A'a akwai takura sun saba da kwanciyarsuna gefe ba lallai sai da ni ba, gidan har ta saba da sai da ni nice zan wahala, gara su saba kafin su hana ni barci gara su saba da haka!"
Jan hancina yayi yana faɗin. "Allah ya shirya ki dai kin yi haka ne don kada a hana mu barci ne ai na gano ki!" Rungume ni yayi muka kwanta yana kallona. "Final gani ga ke ba zancen ciki ko wani abu!" Murmushi nayi ina kallonshi. "Yaya kenan!" "Me nene?" "Ka tuna lokacin da kake cewa nayi musu girki, saboda ni ban haihu ba!" Haka ya rufe min bakina yayi yana faɗin. "Kome ya wuce fa!" "Akwai ciwon da idan aka ji maka, har ka mutu kana jin zafin shi, yau gani nima gani da Yarana,.maganib gori ya kare ko fada akan Yaran nan, wani lokaci idan na farka sai na ga kamar ba nawa bane amma tabbas wannan lamarin Allah ya dace na godewa!" Shiru yayi don bada ta cewa. Ina jin shi ya ja igiyar da yake gaban rigar jikina, lumshe idanuna nayi ina jin shi kamar na hana shi, rike hannunsa nayi ina jin abinda yake ni Yarana nake tsoro, ganin yadda yake niman wuce iyakar shi na ce mishi. "Yaya ni dai ban shirya ba, Yarana gaskiya ban shirya musu wani abu ba, ayi hakuri kada mu dauki wani cikin." Shiru yayi yana kallon yadda na damu sosai, kafin ya ce min. "Shi kenan zan yi kome a hankali!" Ya fada yana lallabani, idan nace ban ji tsoron wannan lamarin nan nayi karya, sai da ya zo kofar, nan ne na ji dadin kamar xan shide, ni kaina ban san yadda aka yi nake jin wani irin kewarshi da son ya yi kawai domin na haukace na rikice kamar xan yi hauka haka ya shiga sarrafa ni cikin nutsuwa da kwarewa hade da wani irin zazzafar kaunarshi, ban san lokacin da na yanka mishi cizo ba. Domin ban tab'a jin dad'i da gamsuwa irin na yau ba..
Duk yadda munafukai zasu shigo Part dina, domin Kofar a rufe.
***
Mahfouz Nuru Yayari....
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 24
Mahfouz Nuru Yayari.
Shi ɗaya ya nufi gidan Alhaji Mamman Abba yayari, ya sami Salim da Walid. Suna zaune a kofar gidan. Kallon gayen kawai Salim yayi amma zuciyarsa kamar tayi waje. Lakace hancinsa yayi yana kallon yadda Yaron yake tafiya tun da aka sauke Alhaji Nuru Yayari a matsayinsa yake wani fisga yana wani jijji da kai, murmushi Salim yayi yana shafa kasumbarshi da ta kwanta lufu-lufu. "Yaron nan ya zata sarauta da yaki da ita wasa ne. Amma bari mu ji yadda aka kwana a ragaya!" Inji Walid suka rufa mishi baya har harabar gidan inda Alhaji Mamman Abba yayari yake, haka suka isa wurin suka zauna bayan akwai wasu da daga cikin manyan Yayari. Zama yayi yana kallon Alhaji Mamman Abba yayari, cikin idanu ya ce mishi. "Akwai wata matsala ne, dattijo naji an ce kana bukatar gani na." Murmushi Alhaji Mamman Abba yayari yayi yana faɗin. "Ko Nuru bai isa na kira shi ya ce min dattijo ba." Wani dariyar shakiyanci ya saka yana kallon Walid. "Naji ance yarinyar nan da aka gyarawa zama ta hannunka ce? Gashi Yarana basu kai ga." Ruwan zafin da aka zubawa Salim ya dauka don ya kurba yana kallonshi zuciyarshi na ci da wuta, Mahfouz ya cigaba da cewa. "Ai na ga yadda Yar uwarta take kuka kamar zata mutu, ni fa na ga ana kuka tare da rokon a ray...." Watsa masa ruwan zafin Salim yayi a fuskarshi. A wani rikice ya kalli Salim saboda yadda zafin yake ratsa fuskarshi. "Kasa da idanunka, ko ka sauyawa audigar jikinka lauyi ruwa mai karni da hawa kai. " Wani iska ya ja tare da lumshe idanunshil ya cigaba da cewa. "Kowa da ka gani anan yana da nufi akan Salmanu Faris, amma ka sake ka kalli Yarinyar da take tsaye akan kafarta da sunan ka ga rauni a tare da ita." A hankali ya mike yana mai isa gaban Mahfouz ya wani haɗa kanshi da pillar da take jikin pillar, yana jan wani irin iska, ya ce mishi. "Kowa da ka gani thug ne, dabanci da aikata miyagun abu yana yi sai dai ya boye don kada darajarshi ta zube, ba laifi ba ne. Idan kaso ka kashe Salmanu Faris, duk wannan tsakaninku ne, kuskure ne babba saka yarinya irin Zainabu Junaid Gobir kuka yin haka tankar gayyatar mala'ikan mutuwa ce lokacin da baka shirya zuwa ga mutuwar ba." Ya fada yana wani shake mishi wuya. "Please Salim kyale shi." Sake shi yayi yana faɗin.. "Salmanu Faris ya sauke Ubanka a matsayinsa, shi zaka tunkara ido da ido, ba wai ka zauna kana bin mace ba, wannan kashedina da kai ke nan na ƙarshe!" Daga haka ya bar gidan yana yarfe hannunsa da yasan ya ji ciwo, ya nufi bangaren Mahaifinsa Fulani Balkisu. Zama yayi yana kwafa, domin kuwa yasan me yake mishi ciwo shi ya ga Zainab tana kuka gara ya ga mutuwar Salmanu Faris a gaban idanunsa da ace Zainab tana kuka.
Har kusan sha biyu na dare yana nan, yasan zuwa wannan lokacin tana tare da lusarin Mijinta nan, da ba zai iya kome ba sai lalata mata tsarin halittar da Allah ya mata.
***
Washi gari.
Muna tare abinci ma Faruq ya kawo mana, ina ga tun jiya suka yi magana zai kawo mishi, ina wankar Yarana ya shigo ya zuba min idanu. Zama yayi yana kallon yadda nake wanke Ayaan sai wani nishi yake a cikin ruwan, Rabi ta mike zata fita na mata alamar ta tsaya ta kawo min wani bokitin, nuna mata kofa yayi tare da mata alama da ta tafi da yarensu na sign language, tana fita kuwa ya ce min. "Me kike so?" "Bokiti nake so domin bawan Allah yana shirin zuba jari a wurin wankar!" Murmushi yayi ya nufi ban dakin ya dauko bokitin. Yana ajiye kuwa sai gashi nan yana zuba kashi har da wani irin nishi a hankalinsa a kwance yana bude idanu yana rufewa. "Wato shi kuma tashi mulkin kenan a cikin ruwa?" Murmushi nayi nace mishi. "Ai ko a gida haka suke yiwa Umma musamman shi!" Haka na kara dauraye shi na mika mishi ya nad'e shi sannan ya haura gadon yana faɗin. "My best friend! Kana samun dama kayi yadda kake so, idan ka samu mace irin Mammynka kayi wuf da ita!" Girgiza kai nayi ina faɗin. "Aiki ya same ku!" Na tashi na zubar da ruwan, na dawo na haɗawa Ayaaz na shi ruwan, ina fara mishi wanka yayi barci. "Yaya ka ga ajebo!" Kallon shi yayi yana jingina kai ya ce."wannan ko fada na kai shi sai dai na saka Faruq, aikin safa da marwa. Don haka ya sha zamansa a wurin Mai Babbar daki su ta juyi daga parlour zuwa turakarta."
Dariya abin ya bani na gama mishi, na dauko Ayyanah, na fara wanke ta kenan ta fara kuka da saka hannu a baki, na juya ina kallon Yaya da ya saka musu pampers da hoda sun yi buzu-buzu, a raina na ce. "Aiki ya samu manyan mutane!" Haka na gama mata, sannan na dauko Autana na sakata tayi mika kafin na tsomata cikin ruwa ta callara kuka kuwa, murmushi na ce mata.."haba Hajjah na ai baki isa ba wanka da kin yi kin gama!" Daga haka na wuce wurin Kayansu na ciro musu kayansu, sannan na zo na amshe su. Wato a yadda su Umma da Maluma suka koya min ba karamin rana yayi min ba, domin har na gama musu wanka babu wnada ya sha nono, ina gama shirya su tsaf na shirya su, sannan na shiga wanka ban fito ba sai can da naji Yaya yana buga min kofar ban dakin. "Yan mata na shigo ne?" Da sauri na gama wankar na ce mishi. "Gani nan fitowa!" Na saka rigar wanka na samu sun yi barci, yana rab'e da Ayaat. "Taki kwanciya ko?" "A'a yanzu tayi barci!" Daga haka na wuce na cigaba da gyara jikina yana tsaye a bayana, har na gama shirina sannan ya shiga wanka anan, ina nan ina gyara jikina, har ya fito ban gama shafa wanan goge wancan ba, don ya san cewa yarinyar nan dai ta dawo, haka ya fita zuwa bangarenshi ya shirya sannan ya dawo muka karya muna hira. "Amma Mr Brandy ya dawo?" Jinjina min kai yayi yana cin soyayyen nama da aka saya shi cikin kwai. Nima ci nayi naji yayi min dad'i, haka na cigaba da ci ina kallon Yaya mikewa nayi cikin sauri na nufi dakin da Rabi take da abincin na cika mata bowl da abincin itama. Ina shiga na samu tana ci har kamar zata yi amai. "Au an kawo miki?" Na tambaye ta, gyada min kayi tayi tana gaya min wai mai martaba ne ya kawo mata. Murmushi nayi har ta gama min bayani sannan na fito bayan na bata umarce ta tayi wanka ya sauya kaya. A hankali na fito yana ganina ya fara murmushi na ce mishi. "Dama kasa a kai mata abincin ne?"
Murmushi yayi ya riko hannuna muka ci gaba da cin abincin. Har muka koshi, wunin ranar ko waje bai fita ba, sai wurin karfe huɗu ya shirya suna fita har da Yaran shi da Faruq da Rabi suka bar ni don ya ce min yana son girkin gargajiya, haka na shiga yin tuwon dawa. Wanda ya ji qanwa yayi kyau yayi danko, na sha shi sosai. Sannan na hada mishi miyar kuka sabuwa amma danyen kuka, wanda ya ji daddawa da wake. A hankali na gama kome, ina rufe miyar ana kiran sallah Magariba, shima na ji muryanshi. Ajiyar zuciya na sauke sannan suka shiga da Yaran shi da Rabi da Faruq, Suka wuce masallaci, nima na yi alola sannan na gabatar da sallah ina cikin addu'a suka fara nishi, kafin su yi nisa na shafa addu'a. Sannan na zo na fara kula da su, ina azkar. Ina cire masu kaya, ina basu nono na umarci Rabi ta haɗa musu ruwan wanka, na wanke musu jiki na saka musu kaya na kara basu nono, sai da suka koshi sannan na haɗa musu madara shima da kyar suka sha, bayan sun sha na gyara musu jiki suka yi barci, ana kiran sallah isha. Nima na shiga wanka karo na biyu. Isma sai wani kad'a bindi take ita gata nan tana farin ciki..
Yadda ake ta buga min kofar kasa yasa ni lekowa ta window ban ga kowa ba, haka yasa na fito zan bude kofar koridon sama Isma ta tsayaa a gaba na, tana wani irin juyi. Murmushi nayi na shafa bayanta xan wuce ta kara min wani irin ihu dole na hakura, tana wani girgiza jikinta. Ji nayi kamar takun mutum ba a buɗe kofar ba, amma nake jin takun sahun mutum wani irin gurnani itama tayi cike da wani irin kuka mai matukar ban tsaro, yadda ta koma kamar wata damisa yasa ni jin tsoro ya kama na juya da gudu, juyawa tayi tana kallon kofar ta shiga juyi kamar wata mai shirin yin wani abu, haka na ga ikon Allah kukan Ayaan yasaka, ban gama fita daga matsala naji an kwalla min kira. Ni ban yi mamaki da abin da ya faru ba, ji nayi kamar an rufe min baki haka na koma ina kallon Ismah da take kallona. Ihu na uku na mike jikina kamar ana wani abu. Na ji kamar kirana ake. "Nutsu da kyau ba kiranki ake tsakani da Allah ba, nutsu ki ambaci sunan Allah da girmamawa ki yarda ba mai yi sai shi, wannan kiran ba kome ba ne sai kaɗan daga cikin shaidanun da suke bin ki, don haka ki kwantar da hankalinki, ai na gaya miki wasan da muke a gidan ba na kome ba ne domin lokacin da za ayi na gaske hala wasu basu nan!" Daga haka aka yi shiru, nima na ji a raina kamar ba a tab'a min kira ba.
Banɗaki na shiga nayi alola sannan na fito na gabatar da sallah isha na idar, ina zaune sai ga Yaya. Kallonshi nayi hawaye ya zubo min, haka nayi ta kuka har Yaya ya dawo massalaci ya ce ya kuwa daga wurina ya duba shi da ko akwai wani abu an saka a wani kayan ne,.ina ganinsa na fashe da kuka na ce mishi. "Mai yasa ka tsaya a waje ne? Sau biyu ana firgita ni! Wallahi na razana kamar na hadiye zuciyata ta buga."
Rike hannuna yayi yana bani hakuri domin ba karamin razana nayi ba, mun jima kafin muku shiga cikin dakin muka kwanta sai rarrashina dakyar nayi barci. An so hana Ni barci domin sai da dare ya raba sannan aka shiga kirana da "Ikhlas ki zo mana ki fito mu memika ki ga shugabanmu, k'amk'ame yaya nayi. Shi fa yana ta barci tashi nayi na shiga wayata na saka karatun Alqur'ani, daga haka barci mai karfi ya dauke ni, daga wannan ranar da ya gama kwanakinsa ya koma wurin matansa wani abu da na fahimta shi dai ba'a taɓa a kwana lafiya....
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 25
A cikin gidan ba, imma ka ji Nadiyyah da Ijlal suna fada ko kuma ka ji yana fada a cikin gidan, sannu sannu sai na kara gano yana yawan fushi da fada ko da abin bai kai ma faɗa ba, Nadiyyah kuwa ban san wani irin yanayi suke tare da shi ba, bakiɗaya Salamunu Faransa ya sauya sama da yadda na sanshi a watanni baya, sannan wani abin da na kara jin a jikina ana yi domin ni ce, shine waka ko sauti a kure shi a cikin gidan, musamman idan na samu na kwantar da Yarana, Nadiyyah da Ijlal suke wannan abin, haka nake ji kamar nayi kuka domin kuwa Ayaaz da Ayaat basu barci sai su ta kuka basu ba, ni kaina da nake Mahaifiyarsu abin yana damuna balle su. Idanuna a lumshe haka nake zama, nayi ta rarrsshinsu ko rabi ta taya ni da goyan daya ni na goyi daya. Wannan abin yana min ciwo haka nake hakuri da duk wani abinda suke yi domin ba ni da yadda na iya.
Ban tab'a bude baki nayi musu magana ba, tow ba fita wurin kowa nake ba. Kwanan mu shida da dawowa yana fada domin ranar ta fita amma bai da niyyar zama a can, ina kwance sun kura sauti, kamar an wurgo shi ya dawo ya ji gidan ya cika da sauti, shigowa dakina yayi ya samu ina jijjiga Ayaat Ayaaz yana bayan Rabi itama na gaji sosai domin ina kokarin kammala abincin rana ne,.juyawa yayi ya fita ban san me ya faru ba,.sai gashi ya dawo gefen kanshi yana zubar da jini. Wayarshi da take ƙara ya ɗauka ya ce. "Kayi hakuri Alhaji Jamil ko Nadiyyah ce autar mata na yafe ta, na gaji zata kashe wata uku zuwa hudu niman soka min wuka tayi, idan na kyale Nadiyyah zata kashe min wani a cikin gidan nan, yau kuma abu ta dauka ta buga min. Sai dai ka yi hakuri domin na koya mata yadda ake zama da miji! Sannan ta dawo na gaji!"
Dauko first aid box nayi na shiga mishi gyaran wurin, idanuna cike da kwalla da Mamaki na ce mishi. "Yaya me yasa take haka ne?" "Daga waje ake shirya mata gadar zare take hawa, don yanzu bata shiri da kowa! Idan ta dauki abu sai dai ta ce zata min illa da shi," ina gamawa gyara mishi wurin ya tashi ya bar parlourn, ya wuce wurinta, ba sai