Showing 102001 words to 105000 words out of 157081 words
bayan sai kin ga karshen binciken nan naki!"
"Na gode sosai!" Na fada ina sauke ajiyar zuciya lokacin da muka iso gidan, na bude na fito Yaranma suka fito, nayi mishi godiya sannan na wuce cikin gidan.
Sai da na duba Yaya sannan na wuce dakina nayi sallah shafa'i da wutir, sannan na kwanta, ina sauke ajiyar zuciya. A daren nayiwa Faruq text ya zo da wuri please zai min wani aiki ne, kuma cikin ikon Allah karfe shida na safe da gashi dakin Yaya muka nufa na kunna mishi maganar da Abba, na nuna mishi hoton Malam Barau, gyada kai yayi yana faɗin.."za a nimo shi." "Ba nimo shi bane matsalar, a san yadda zamu yi approaching dinsa ne, akwai wani rubutu da nake son na sake nace na fara sanar da kai, amma Abbana yasan da ga zancen."
A hankali na warware mishi bayanin, shiru yayi kafin ya ce min.."Abinda nake tunanin zamu yi shine mu fara samo waɗannan mutane biyu ai sun boya ne don rayuwarsu, idan kika sake wannan rubutun zasu kara boye kansu, saboda baki san gaskiya ba, yanzu mu fara nimo su sai ki sake bayanin, kin san dalilin haka? Na farko sun gaya miki gaskiya amma kin gaskiya na biyu, zasu iya yin amfani da wannan damar su sake bayanin da kika fitar nawa hasashen fa nake gaya miki."
Gyada kai nayi ina faɗin, "yanzu ya zamu yi wurin nimo su kenan?" "Ina da wani yaro a kaduna, bani hoton na tura mishi ya iya kome kamar yadda ba ki zato baki tsammani." "Na gode sosai!" Daga haka muka yi sallama, ya tafi a cikin yan kwanakin ba karamin aiki muka yi ba domin sati daya muka dauka muna aiki, kafin muka samu malam Barau, ban bar garin ba domin nasan an saka min masu bibiyata, Yaron Faruq shi ya kawo mana Malam Barau har gida.
Zama yayi cikin girmamawa na gaishe shi, kafin na ce mishi. "Baba Barau, Kuma sai ka tafi ka bar inda ka saba na tsawon shekaru aru-aru?" Sunkuyar da kai yayi kafin ya ce min. "Kiyi hakuri, yau kome ya faru ne saboda son zuciyar wasu, sannan wasu sun rufe wasu abubuwan kamar bai faru ba. Ba gudu nayi don kada gaskiya ta rayu ba, na gudu ne domin zuciyata da ta Yarana ta rayu duk wnada yake cikin da'irar ƙaddara shi kaɗai zai bada labarin yadda yake kokarin fitar da kanshi. Fulani Babba Allah yasa mu dace kawai."
Shiru yayi kafin ya cigaba da cewa. "Wato a daren ranar da abokai uku suka hadu ba tare da aboki na hudu ba, sai nayi mamaki domin kaf duniya abokan nan hudu suna haduwa su tattauna matsalarsu da kome nasu, amma kafin yau anan samu matsala tsakanin Alhaji Saddam da Nafi'u, domin shi Alhaji Nafi'u akan dukiyarshi bai da hakuri abin da ya lalata auren Yaransu, duk wannan abin da yake faruwa abokai biyu a gefe suna ta fadi tashi ganin an daidaita yadda ba sai duniya tasan da barakarsu ba, amma ina Allah ya nufa duk wata zama matukar akwai azzalumai a cikinta sai Allah ya lalatata, haka ne ya faru ina jin ban taba jin ko tashin hankali da na shiga Malam Junaid da Mai Martaba Attahiru Yayari, sun yi kokarin da ni kaina ban san me zance ba, sai dai yadda Nafi'u ya sha alwashin ganin bayansu yasa kome ya kara kwab'ewa, ranar wata juma'a na fito daga gidan da nake haya domin iyalina sun koma gida dama mata biyu gare ni, daya ta rasu daya kuma ta koma wurin gyatumana,ranar dai kamar Alhaji ba zai fita ba ya kira ni muka fita ai ko da muka fita abu daya na iya tunawa shine mun je Fada mun kuma tsaya min dauki Mahaifinki daga nan kowa ya kama gabanshi, wurin karfe goma abokai hudu suka hadu a fada abinda na sani Alhaji Nafi'u ya fito a fusace,haka Alhaji Saddam da Malam Junaid kowa rai ba dad'i,a wannan daren da Alhaji Saddam bai kwana a cikinsa wurin sha biyu aka kira shi aka ce ya fito za a kashe Malam Junaid, wannan fitar da muka yi naga yadda yake ta waya yana magana mai muhimmanci amma ban bada hankalina ba, sai dai mun hadu da Alhaji Nafi'u inda Alhaji Saddam ya je gare shi suka yi magana fitarwa da yayi na ga yadda yake ta kokuwa da numfashi, ban san me suka shaka mishi ba amma yana zuwa abinda ya ce na kai shi gida, na ce mishi Alhaji asibiti dai ya ce a'a gida kawai kada na bari wani abu ya same Junaid shine shaidarsu.". Daga nan yayi shiru kafin ya sauke ajiyar zuciya yana share kwalla. "Sanin cewa na zauna a Zanzabira nima tawa ta ƙare yasa na gudu dangina, ina da baya ina da Uwa wacce nake kula da ita, a yanzu ma nasan zasu fahimci nazo nan domin bayan rasuwar Alhaji Nafi'u ya min kashedi ba ruwana, sai dai har yau ina jin kamar ni nayi laifin domin kuwa na gudu ba tare da na fadi gaskiya, sannan na boye abinda Alhaji Nafi'u ya aikatawa Alhaji Saddam, amma ko yanzu na mutu na san na sauke hakkin kaina"
Gyada kai nayi na ce mishi, "Baba iyalanka suna Kaduna har da Babarka suna Kaduna cikin kulawarmu, babu abinda zai same su in sha Allah!" Na ce Faruq ya tafi da shi masauki ya zauna a can muga abinda hali yayi, kafin muka fara bibiyar Sallama, wanda aka wayi gari kwatsam ba labarinsa.
Alhamdulillahi a wannan bangaren Aryan ya mana wani abin kai, domin shi da Faruq suka tafi faran kasa suka dauko Sallama wnada jinya ta saka shi gaban, a asibiti suka kwantar da shi, na tsawon kwanaki goma, kafin ya dawo dai-dai. Dauko shi aka yi zuwa gidan , a keken mara sa lafiya, aka kai shi dakin da Yaya yake kwance, rufe fuskarsa yayi ya fashe da kuka. "Na zalinci kaina, na ci amanar yarda da aka yi min. Wallahi na cutar da bayin Allah nan kuma na daurawa wnada bai ji ba bai gani ba, Fulani Babba, ko kin san ni ne nan na sace Salmanu Faris yana Yaro?" Gyara tsayuwa nayi na zuba mishi idanu, domin maganar tafi kamar da mafarki waye zai ce haka zai faru? "Fulani Babba, ni nan na sace Salmanu Faris, saboda kawai an bani abin duniya da yasa na ci amanar yardan da Attahiru ya min.
A ranar da aka je daukar Yaran da gayyana nace kada a koma a dauke shi ni zan je na dauke shi ba don kome ba, sai don kawai na cimma burina, wato akwai wani mutum a cikin masarautar nan wanda ya kasance Babba da wasu mata a cikinsu har da Jakadiya Iyaami." Kallon juna muka yi ni da faruq da Aryan, muka jinjina kai. "Ranki shi dade nayi ƙoƙarin kasa danne abinda yake raina, domin Jakadiya Iyaami ta kawo min aikin da tsabar kuɗin aikin da aka bani, a tunanina ai duk zaman da muka yi da Attahiru Shehu Yayari bai tab'a bani irin wannan kuɗin ba, sannan na farko basu ce batar da shi zasu yi ba, haka yasa na sace shi ta hanyar zuwa na ce yazo mu tafi gida, Yaron ya yarda da ni, domin bai kawo a ranshi ni sace shi nazo yi ba, sai da muka bar makarantar muka nausa cikin dajin, anan ya ce min.. me muke yi anan Baba sallama, ban bashi amsa ba na cigaba da tafiya karshe zai min gadama na hura mishi yar hodar da aka bani, ni dai na san na kai musu shi, daga nan na dawo aka buge ni a motar yadda babu me cewa ai Yaron na dauka kawai kagaggen hatsari muka yi, wannan abin ya bala'in tab'a ran Attahiru Shehu Yayari ga sace mishi d'a da aka yi ga ƙoƙarin kashe ni da aka yi. Domin a lokacin na sha wahala gashi nan shiri aka yi amma kuma na sha azaba kafin na warke.
Yau zasu sake Salmanu Faris,.karshe dai na fahimci ba zasu sake shi ba, sai na samu Jakadiya Iyaami, da ta yi wani abu ko na tona mana asiri, domin nayi abin amma ni yake damu, matar nan ta ce min. Matukar tana raye sai ta ga bayan kowa." Shiru yayi kafin ya fashe da kuka, yana shashekar kuka yana kallon Yaya a kwance, ya cigaba da cewa. "Abinda ta ce min ya girgiza ni domin ta gaya min na tuna ina da baya kuma suna nan kada nayi tunanin ina da goyan baya domin babu me yarda da ni, ba ita ba sun razana ni kuma na ji na hakura da kudirina, sai dai bayan tsawon lokaci na fahimci ana shayar da Attahiru guba wanda tayi karfin da ba zai ina daina shanta ba, don a lokacin yayi fama da matsanancin ciwon basir sai ya kasance sai da aka mishi aikin daga nan akai yi ta kawo mishi magani , yana sha musamman wata shayin da ake dafa mishi yana sha sau uku a rana ko yana fada sai ya sha, a ranar da na fahimci guda ce tariga da tayi mishi illa, domin Jakadiya Iyaami da wata cikin matanshi suke da hakkin dafa mishi ko Mai Babbar daki bata dafa mishi, domin ta tab'a dafawa aka ce taji tiririn ta suma, daga lokacin ta ce ita ba zata kara sakawa a dafa a bangarenta, shi kuma ya dauka ya bawa daya daga cikin matansa. Tun bayan b'acewar Salamanu sai aka rufe maganar kamar bai wanzu ba, bayan wasu shekaru sai aka samu labarin ana jin an ganshi. A lokacin Mai Martaba da Malam Junaid da Mamman Abba yayari suka yi ta yawon nimanshi kafin Walid Mamman yayari ya ce ya same shi, sanin cewa likita ne kuma idan yazo zai fahimci ainihin abinda ya kashe mahaifinsa yasa aka yi maza aka nime shawarar shi aka fitar shi zuwa London, amma wallahi kome a shirye yake.
Abu daya aka rasa ganewa shine shirin aurenki domin babu wanda ya san da shi, sannan da an san cewa zaki hanko irin wadannan abinda aka rufe babu me yarda ki shigo cikin gidan, nima kome ya kare Yarana da nayi domin su sun mutu, yanzu d'a daya gare ni shima ya gudu ya bar ni. Saboda zunubina da sanin an aikata wani abu nayi shiru dangina ma babu me tare da ni, nayi asara kaicona."
Abu biyu ya fito min a wannan binciken, Yadda aka sace shi da yadda wasu abubuwan suka faru, kenan ba iya wannan ba akwai wasu abubuwan da yake rufe a cikin zanzabira da idan na tona su zai zama rushewar daraja da mutuncin Magabatar Zanzabira? "Ka kai shi masauki, zuwa yanzu ka tattara bayanan ka turo min a rubuce ta email dina. Sauran dan duba lamarin!"
"In sha Allah zan yi haka!" A hankali nayi ta zaga gidan, yanzu kan ya dace yaya ya tashi ya ji da sauran idan na cigaba da wannan aikin ni mace ce, wasu abubuwan zasu fito ta yadda ban zata ba, shiru nayi Aryan ya ce min. "Ko ya tashi wannan shashashan ba zai iya kome ba wallahi, gashi nan kin rage aikin da tafiyar da kika fara shi shekara bawa yana kujeran ya iya yin kome ne? Ke ko ya farka Allah sai na kwantar da shi bai da wani amfani a yanzu ko ya tashi shiririta zai kama yi miki ya cigaba da kwanciya. Allah yana tare da ke." Ajiyar zuciya na sauke kafin na watsa mishi harara na ce mishi. "Wai yaushe zaka bar min Yarona ne? Kasan Allah sai ka kyale min Yarona na gaya maka!"
"Idan kin isa ki fitar da ni " ya fada tana wani murgud'a min baki, aljanin nan ya buwaye ni. Yadda na zuba mishi idanun haka ya zuba min yana murmushi takaici ya cika ni na ce mishi. "B'ace min da gani!"
A hankali na dafe kaina, na zuba idanun ina kallon Yaya. Jakadiya ba zan mata shigar sauri ba domin nasan tana ankare da ni, kuma bana son haka ya faru. Idan har ta san cewa ina tafe zata iya yin wani abu da zai kara sakawa nayi motsi, kiran Abba nayi muka yi magana, kafin na kira gidan Jaridar da muka gama kome na kasancewar a Scotland ne, haka suka buga labarin da na basu tare da daura ayar tambaya, sannan yadda na basu labarin abin ya girgiza mutane domin daga karshe an zargi Malam Junaid Gobir.......
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 37
Ban san cewa wannan aikin da nayi ya kara jefa Abba cikin tashin hankali ba, sai da aka fara tuhumar Abba da wasu abubuwan da ni kaina na rud'e, anan wurin sai ya zama nayi amai na lashe ne. Domin kuwa kafin Allah ya fitar da Abba sai da na cire rai, ba don kome nayi haka ba sai don masu laifi zasu motsa sai kuka ayi dace wanda ya fara motsawa Alhaji Nafi'u, haka yasa kafin yayi wani yunkuri Malam Barau yayi hira da wata gidan Jarida, wanda ya fada musu asalin abinda ya faru. Ban tab'a wanin haka zai faru ba, sannan Alhaji Nafi'u ya motsa ne yayi wasu magaganu a gidan tv, na Zanzabira inda ya ce ai ya fada shi ba zai iya kashe abokinsa na Yarinta ba, duk da banbanci na ra'ayin da suke da shi da wasu abubuwan da suka samu a rayuwa shi bai nufin kowa da sharri, wannan abin ya min ciwo, haka yasa Malam Barau ya fito yayi magana inda ya cewa Al'umma ya kamata su daina zaunar maganar kowa domin lokaci yakure da za a yaudare su da maganar kisan Alhaji Saddam da Mai Martaba, ya san cewa next victim yana nan very close, don haka mutane su daina yanke hukunci da abinda basu da sani a kai, sannan ya ce idan ana maganar mutuwar Alhaji Saddam ne a jikin motar Alhaji Saddam akwai ajiyar camera ya ajiye shi tun daga lokacin da abin ya faru ya ajiye, a hankali ya fitar da Camera aka shiga duba abubuwan da ya faruwa wannan abin yasa ko minti goma ba ayi ba aka tafi gidan Alhaji Nafi'u aka saka nishi ta kunkumi sannan Malam Barau ya kara da cewa. Ba asalin dalilin fadar ba kenan, Alhaji Nafi'u na sadaukar da Yarshi Iman ga dodon tsafi wanda haka ya tsorata Alhaji Saddam.
Take aka dakatar da labaran sannan bar zancen Yayinda Malam Junaid ya ji ciwo domin abinda suke ta boyewa kenan, a lokacin da suka rabu bawai don abinda Khalifa yayi ba ne, a'a Iman ta tafi wurin Alhaji Saddam ta gaya mishi yayi wani abu akan lamarinta tana jin babanta yana wani abu da bai dace ba, a cikin kuwa har da shigowa ɗakinta cikin cikin dare yana wasu abubuwan ba kaya, a lokacin hankalinsa ya tashi sannan shima ya samu Malam Junaid da maganar, shi kuma ya samu Mai Martaba da al'amarin sai mutumin nan ya kafe da cewa sharri yarinyar tayi mishi, dama kuma abubuwan da suke faruwa lokaci zuwa lokaci yasa an fara zarginsa. Haka yasa bayan sun gama magana ya tashi ya zazzage su da cin mutuncinsu, kasancewar su abokai na amana ne, haka yasa bakiɗaya suka boye abinda ya faru musamman Malam Junaid da Mai Martaba, amma ga Alhaji Saddam yayi hiran da makusantar shi, kafin rasuwar Alhaji Saddam aka nime Iman aka rasa sai cewa tayi kada a nime ta, abokansa sun san cewa akwai abinda ya faru, duk da wannan abin basu tab'a cire rai zai dawo hanya. Saboda suna da kyakyawar zato akan shi, amma har yau Malam Junaid bai cire rai da Alhaji Nafi'u zai dawo hanya ba, bai tab'a munanna masa zato ba.
**
Tunda Allah ya kawo mafita, gida na je na gaida Abba. Na zauna a gefenshi yana shafa kaina yana gwiwarshi. Ina shashekar kuka. A hankali yake shafa kaina yana faɗin. "Ki yi kuka yanzu, ki yi hakuri gaba, Zainaba tunda kika samu hujjoji masu kyau, ina ga lokaci yayi da sallama miki kome, Zainaba ko yanzu na koma ga Allah na cika alƙawarin da na daukawa Attahiru. Alhamdulillahi na sauke kaso saba'in cikin dari, yau ina ji a jikina kodayaushe mutuwa zata riske ni, Alhamdulillahi Alhamdulillahi Alhamdulillahii, Alhamdulillahi." Murmushi ya sake yana mai d'ago kaina ya ce min."kukan na mene ne? Ba gani ba! Ai babu abinda zai kara faruwa in sha Allah."
"Abba tsoro nake ji." Shafa kaina yayi yana faɗin. "Ba abinda zai faru sai ikon Allah. Tsoro makiyinki ne daga lokacin da kika fara jin tsoron tow daga nan kowa zai tsaya kuma kowa zai ta razana ki, da dan kwaikwayo da dan akuya da dan tinkiya da al'adu zasu ta razana ki, daga nan zaki fara gudu kina noman hanyar gudu, zasu ta min nimanki ruwa ajalo sannan zasu ta binki kina gudu, ban san yadda zaki fahimta ba, amma tabbas rayuwarki zata zama abin boyawa da gudu, Fada kika shiga kuma duk abinda yake faruwa ana sanar dake, saboda Mijinki da zai yi aikin tun kafin ya kwanta ya gaza. Gaya min zaki tsaya ne su razana ki saboda kina tsoro ko zaki bari a cigaba da zalinci ne? Idanun duniya take kanki kowa yana kanki nauyin al'umma yana kanki, kowa yana kallonki ya zaki ji idan yau wayi gari bana raye ba zaki yi? Zaki cigaba da kuka ne ko zaki zauna kina Jiran wani ya gaya miki yadda zaki