Showing 96001 words to 99000 words out of 157081 words
wata irin shaka tare da tsayawa a gabanta. "Ance ba zaki shiga ba, sai me? Ke har kin isa Fulani Babba ta saka doka ki karya mata? Don haka yau zaki san lokacin da ya dace kina haukarki!" Ya cigaba da shaketa tana ihu, aljanin nan ya shiga jikin Yaron nan ne don ya jaza min bala'i. Ashe zane ta yake dukarta yake Faruq yana parlourn Nadiyyah ta fito ganin yadda ake cin Uban Ijlal sai ta koma abinta, bata kara yarda ta fito ba. Abin ya d'aga min hankali. "Sake ta nace!" Da karfi ya sake ta ai kuwa ta fada akan hannunta ya karye, ihun da tayi sai da ta suma, daga nan yayi wucewar shi ya bar jikin Yaron, ya kama barci. "Faruq me yasa baka hana shi ba?" Na tambaye shi ina jin haushi kamar na hada su na rufe da duka. "Ranki shi dade, ai na gaya mata kada ta nufi kofar amma taki, mai zance mata?" Ya fada yana sunkuyar da kanshi. Shigowar Jakadiya Iyaami da sako daga wurin Mai Babbar daki yasa na ce mata. "Yawwa Jakadiya kamata ku kaita asibiti!" "Wani asibiti kuma a yayyafa mata ruwa kawai!" Ruwan aka kawo aka watsa mata ta farka tana zunduma ihu. "Don Allah ki yi hakuri!" N fada ina ƙoƙarin mikar da ita tana ganin Ayaan ta mike da gudu har tana faduwa, ta wuce bangarenta. Dafe kaina nayi Jakadiya Iyaami ta ce min. "Ranki shi dade! Gashi inji mai Babbar daki wai ki ci kuma ki kwanta ko huta!" Amsa nayi na ga cikin abin yana wani irin baki ga tsutsa ina gani. "Na gode sosai ki ce mata tow!" Tana fita na dauki abin na haura sama har da Yarana kafin na juyo na cewa Faruq. "Faruq kofar dakin nan ina ga a nima min karfin mata da zasu tsaya a wurin sannan a watsa wasu suna zagaye gidan da rama da dare kuma maza zasu yi." "An gama ranki shi dade, dama muna da irin su zan tawo da su."
Haka na shige dakin na zauna ina kallon abin Yaran kowa ya kama wasan shi ban da Ayaan da ya kurawa abin idanun yana yatsina fuska. "Ka cewa Faruq ya dauko mai dauri ya daura hannun Maamah." Gyada kai yayi ya fita da gudu, na ji fitarshi da gudu sai dai ihun Nadiyyah da naji ya sani fita da sauri gabana yana faduwa, ganin yadda ta rike karfen baranda na, wani irin zafi na ji yana cika min rai. "Me ya kawo ki nan? Ina ga ba ga wurinki can ba? Me yasa duk abinda zai zama tashin hankali kike kawowa ne? Ba shiga rayuwarku ba me yasa ni nawa kuke son shiga? Shi kenan abinda kika zab'a kenan Allah ya baki sa'a!" Daga haka na koma dakina, ina jin Saadiyyah tana ihu tana kiran Uwar, sai na ji zuciyata ta gagara amsar hukuncin da nayi a duk lokacin da nayi hukuncin tow ita nake ji, can sai ga Ayaan ya shigo. "Ka kyale ta ka ji Ayaan dina." "Bata ji yanzu ai shi kenan!" Fita yayi yana kallon yadda take ihu, a hankali ya dafa karfe yana murmushi, sauka aka yi da ita, tun da ta falla da gudu, sai da muka yi kwana uku ban kara saka su a idanuna ba, daga ita har Nadiyyah ban kara ganin mai kama da su ba, wannan yasa na fahimci kowacce ta kama kanta ta zauna a inda take, a cikin kwanaki ukun nan ban shi cikin nutsuwa ba, abu na farko da na fahimta abincin da aka kawo min na Yaya an shirya ne a wurin da abin ya faru an samu wani abu wanda Ikram kaɗai nasan take amfani da shi, wato irin farcen nan na zamani, dauka nayi ina kallonshi kafin na fito na same Faruq na ce mishi. " A lokacin da kuka yi hatsarin baka ga wani alama na mace ba?" Shiru yayi na wani lokaci kafin ya girgiza min kai, "Ka nutsu sosai ka tuna ba ka ga wata mace a scenes din ba?" Lumshe idanunshi yayi yana nazarin abin, kafin ya ce min. "Anya?" "Ka tuna da dai akwai makama daya da zan rike ne, idan ka bani amsar da ya dace!" Dafe goshinsa yayi kafin can ya zuba min idanu. "Eh kamar na ga wata amma ban sani ba ko mafarki nayi!" "Alhamdulillahi abinda nake bukata kenan." Kallona nayi yayi na ce mishi. ",Daga yau bana son wani ya kara shiga dakin idan bani ko kai ba, akwai wani lissafi da nake yi ne, ka shiga ka gani." Shigowa dakin Yaya yayi, wani allo na kafa a gefen Yaya, na saka hotonsa sai sunayen mutanen d ban yarda da su ba. "Amma taya kika yi wannan aikin a cikin kwanaki uku?" "Ina da kasa da wata shida ne idan har ya farka shirina zai rushe idan ya kai wata shida zuwa shekara daya kacal, zan cimma nasarar abinda nake bukata." Dauko min laptop Yaya yayi ya ajiye min yana faɗin. "Watanni takwas da suka wuce zuwa shekara daya mun fara aikin binciken, kamar wanda aka razana shi ya rufe binciken, wannan akan rasuwar Mai Martaba marigayi Alhaji Attahiru Shehu Yayari ne, amma daga baya ya rufe binciken kamar ma ba a tab'a binciken ba. Sannan na san akwai dalilin dakatar da binciken, amma a matsayinki na yar jarida zaki samu abinda kike bukata. Ni kuma xan bada rayuwata domin ke da shi kanshi."
Ajiyar zuciya na sauke na ce mishi. "Zaka iya tattara min bayanan haduwarshi da mutane daga ranar da ya hau mulkin zanzabira har zuwa hatsarinsa?" "In sha Allah zan hada miki!" "Cikin sati daya nake bukata;" na kalke shi, gyada kai yayi yana faɗin. "In sha Allah cikin kwana biyar kacal!" Jinjina kai nayi tare da cewa. "Zan bukaci haka."
Kamar yadda na ce musu a ware kudi a cikin Baitul Mali masarautar a fara gina asibiti, an fara kuma aiki ake ba dare ba rana, abubuwa guda uku yasa na bukaci haka. Na farko akwai bayi a cikin masarautar a cikinsu har da Maman Wildat, na biyu ana bukatar ace akwai malaman asibiti a cikin masarautar yadda zasu na zuwa duba shi, na uku mu kanmu ba sai mun sha wuyar fita wajen masarautar ba idan ba wai jinyar ya gagara ba ne, wannan shi ne lissafina.
Duk da likitocin asibitinsa suna zuwa duba ba shi amma kuma mun fi buƙatar wanda zai na zuwa akai a kai, sai dai akwai wata hanzari ba gudu ba. Idan aka iya amfani da wasu don cimma manufofinsu fa? Wata zuciya kuma ta ce min akwai Allah fa, haka yasa na mai da hankali na cigaba da abinda nake, tare da mai da hankali kan duk wani motsin wasu da nake zargi.
Yau juma'a, yau yayi daidai da kwanakin da muka yi da faruq zai kawo min bayanan kuma ya kawo min muka shiga bincikensu, da kuma dalilan haduwarshi dasu, Alhaji Kabiru Hammud Yayari, shine mutumin da yafi haduwa da shi sai kuma wata number da na samu a cikin binciken ana yawan kiranshi da ita. Account din bankinsa da duk wani abu sai da na duba, sannan na kara fahimtar duk wata yana turawa Nadiyya da Ijlal kimanin dalla dubu dubu ashirin duk bayan wata uku, kallonshi nayi a kwance Yaya ya boye wani abu a ransa akwai abinda yaya ya boye ya kasa gayawa kowa ya kasa bayyanawa kowa yana kuma hurt dinsa kamar yadda rayuwa da numfashi yake. Jinjina kai nake, na kira Faruq a waya. "Kayi hakuri na dame ka ko?" "A'a ranki shi dade!" "Dama ina son tambayarka ne ko ka sani shin me yasa yake turawa Nadiyyah da Ijlal kudi haka dalla dubu ashirin duk wata uku?" Shiru yayi kafin ya ce min. "Maganar gaskiya ban sani ba, sai dai ki duba wayarshi. Hotonsu Ayaan zaki jera kamar yadda aka haife su shi ne password din, sannan idan zaki shiga cikin apps ki yi amfanin Zeeyfaris, daga banki zuwa wasu apps masu muhimmanci duk sunanku ne tare."
"Na gode sosai!" Daga nan na kashe wayar na koma bincike, a cikin wani takarda na sunan Abba, binciken kiran da kome nake kai na kasa hakuri na kira Abba. "Abbana dama wani aiki nake na ce bari na kiraka." Na fada mishi ina kokarin daidaita nutsuwata. "Ina jin ki Zainaba!" "Abba a ranar sha shida da watan Oktoba dubu biyu da ashirin da daya ka kira Mai Martaba sau biyu, kun yi magana a kalla minti goma kacal, a ranar uku ga wata sha daya ka kira shi kun yi maganar minti ashirin, sai shima ya kira ka sau uku a ranar, Abba na ga kiran da kuka yi da musayar kira, Abba akan me kuka yi wayar?" "Zainabu abu mai tagwayen suna, kiran farko akan ki ne sai sauran akan abubuwan da suka shafi rayuwar gidan Yayari ne."
"Ni kuma Abba?" "Tabbas ke Zainabu, kin tuna zuwanku Dubai? Akai ne shine Dracula." Ji nayi kome ya tsaya min cak, na rasa abinda zan yi sai zare idanun. "Shi ya ceto min ke da yanzu ina nan ina saka ran yaushe zaki dawo gare ni? Shi ya tsaya akan kome hatta waɗanda suka miku video sai da ya tabbatar ya rufe tarihin kowa yadda zaki shaki iskar yanci, Ki nutsu da kyau shi din ba iya ke ba hatta rayuwarki ya kare ta yau da kullum " mikewa nayi na fito da gudu na sauko kasa har ina haɗa step bibiyu, na nufi dakin da yake masu kula da dakin suka bude min, ina shiga na same shi kwance, hawaye ne ya zubo min. Na nufi gadon na zauna a gefen shi tare da rike hannunsa na saka a fuskana. Ina jin kuka yana zuwa min ban san lokacin da na sake kuka mai ciwo ba, nayi ta jiran ko zai kira ya ce ya janye ta jiran ko zai ce yana nan, nayi ta jiran sakon barazana daga gare shi ashe yana tare da ni, ya zame min inuwa kamar yadda ya ce, ya zauna da ni ya boye kome a kaina. Ya rufe idanunshi yayi ƙoƙarin taya ni faɗa yayi kokarin boye abubuwa dayawa a kaina domin na samu nutsuwa mai yasa ban sani ba sai yanzu? Me yasa ya boye min kome? Me yasa tuntuni yake ta kare ni? Wani irin kuka ne ya zo min, sai yanzu na hango wasu abubuwan da iya kwayar idanunsa nake ganinsu sai na kara yarda kowani sarki da akwai abinda yake bawa kariya a internal life dinsa, idan na nazarci Salmanu Faris ba gazawa ba ce yasa ya koma gefe guda, kawai kariya ce. Wani irin kuka nake wayata ce ta kara yin kuka na dauka. "Abba!" "Ba laifinsa ba ne, ke yake karewa kece rauninsa shi yasa ko me aka ce kin yi madadin ya musanta yake cewa kece, saboda ta haka ne zai kare ki. Mijinku ban fahimce shi ba sai dab zai yi hatsarin nan, na fahimci haka a gare shi wanda shi ya kasa gaya min amma yayi magana da Ummanku, ban san lokacin da zai dauka yana kwance ba, amma ki yi iya ƙoƙarinki, ki biya shi duk abinda ya miki ta haka ne kawai zaki iya." "Abba waye zai tayani? Waye zai tsaya a bayana? Abba ni daya ce shi kuma yana kwance zuwa yanzu babu me taimaka min da abinda ya da ce nayi, Abba ni mace ce mai rauni!" "Zainab ke Jaruma ce, ke uwa ce? Sannan kema mutum ce, ki cire jinsin mace ki dauki kanki a matsayin Namiji, ki yi aiki da ilminki da baiwarki, nasan akwai abubuwan da na hana ki aiki da shi idan kika hada zai iya taimaka miki, Zainaba lokaci ya zo da zaki yi wanka da datti domin fitar da tsafta, kada ki damu da asarar rai ko dukiya, Salmanun Faris yana kwance a wurin ki nutsu ki yi aiki da ƙwaƙwalwarki da zuciyarki. Sai ki gaya min yadda kike bukatar taimakona, ki yi bincike sosai ki yi bincike ainun workhard zaki yi nasara idan kika samu ina da laifi kada ki ji wata tsoro ko wani ki tuhume ni, idan kika ji labarin na mutu, kada ki razana za a iya yin kome domin dakatar da ke, kada haka ya nuna razana ko tsorata, duk wanda aka tab'a ki yarda dama can yana cikin tsarinki, bari na gaya miki wani abu da duniyar yan shi'a suka tsarawa kansu musamman Iran, sun yarda su yi bincike su ilmantar da al'ummarsu, don haka a cikin wannan tafiyar nasu ta daularsu, rayuwarka da ta danginka fansa ce basu tsoron mutuwa ko wani abu suna farin ciki idan aka kashe su matukar buƙatarsu zata biya ba wani abu ba ne, sannan na gaya miki haka ne domin ki aro akidar kome zai faru You can't stop din, don haka duk abinda baki gane ba don Allah ki gaya min ni nan zan gaya miki gaskiya da kuma faruwan kome."
Wannan maganar da muka ji da Abba yasa ka ni jin kwarin gwiwa, sai na ji a raina ashe ban yi kome ba, kuka ba nawa bane. Dole alatis na maida Yaran wurin mai Babbar daki, na bar Ayaan saboda ko na tafi da shi zai dawo, sai gefe guda Aryan yana bani hit fiye da yadda ban zato amma idan ya tuna yadda na kwashe shi da mari, sai yayi shiru. Idan ina fada kuwa komawa bayan Faruq yake yana leko ni yana cewa. "Ashe haka take da masifa ban sani ba!" "Shi!"
***
"Ai ga irinta nan tuntuni na so kashe ta kafin ta haifi masifa yanzu tun kafin shegen Yaron nan ya kwanta nake gudun shaidanin da suka haifa yanzu ga Uwar ma, Salim me yasa baka kashe shi ba a ranar?" Kallon Alhaji Kabiru Hammud Yayari ya ce mishi. "Ba shirina ba ne hatsarin ai na gaya maka ba zan kashe shi da karfi ba, ina son ya mutu kamar yadda Abbanmu ya mutu ne, ina son kada yayi mutuwar da Zainab ba zata mata da shi ba, ina son yayi mutuwar da zata manta da shi farat daya, amma yayi irin wannan mutuwar ai ni nayi asara domin ba zata taba sona ba, idan yayi mutuwar da ita kanta ta gaji da jinyarshi da kanta zata mantan da shi ko arba'in dinsa ba za ayi ba zata rufe babinsa, saboda ya bata wahala a jinya, haka zai saka ina cewa ina sonta zata amince, wani ya sake ya tab'a sai na aika shi garin da ba yan rakiya. Wannan shine alkawarina."
"Amma akanta ka aikatawa Mahfouz Nuru Yayari wulakancin.nan?" Murmushi yayi yana kallon Alhaji Nuru Yayari da ya harde kafa, shima kuma ya dauki katon mandula ta wiwi ya nad'e sannan ya kunna mata wuta yana zuka a hankali yana fesar da hayakin. Wayarshi ce tayi ƙara ya ɗauka. "Assalamualaikum ranki shi dade!"daga can ta ce mishi. "Dama akan maganar Yaya ko zaka taimaka min da wasu abubuwan ne ko ka haɗa faruq da shugaban kamfanin MTN!" Murmushi yayi ya ce mata. "Fulani Babba ya je yanzu xan mishi magana, a duk lokacin da bukatar haka ya taso ki min magana ina tare da ke dari bisa dari, kuma idan akan matsalar kudi ne daga miliyan daya zuwa dari ki min magana in sha Allah zan yi kome da karfina da dukiyata!" Ya fada yana murmushi yadda ba zata tab'a zarginsa ba.
"Allah ya saka da alkhairi na gode sosai, mun gode sosai Daddy karami!" Murmushi yayi yana faɗin. "Ba kome!" Ya kashe wayarshi, kallonsu yayi yana mai d'aga musu gira ɗaya ya ce musu. "My bride!" Ya fada yana zukar wiwi son ranshi yana fesarwa. Kafin ya kira shugaban kamfanin MTN na zanzabira ya bukaci abinda Zainab ta roka, ba wani dar aka amince shi ya kira Faruq ya gaya mishi.. ya je
***
A duk yadda nake lissafina, bana tunanin kowa ya hau jirgin da nake lissafi a kai domin yadda nake son tafiyar da binciken ina bukatar Salim Attahiru Shehu Yayari, domin something fishly, idan na ce muku wani abu na wari tow ina nufin haka shi yasa har na cimma mafarkina bana son ya san ina harinsa amma kafin nan waye abin zargina na farko a mutuwar Alhaji Attahiru Shehu Yayari?
JUNAIDU ABID GOBIR........
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: JUNAIDU ABID GOBIR........
35
Junaid Abid Gobir.
Mahaifina ne, shi na fara zargi, ba wai na ce shi yayi kisar ba amma wasu abubuwan da na mai da hankali da bayanan da Yaya ya haɗa Abba shine a Centre din lamarin, abin kamar yadda ake buga chese haka Abba ya zama abin bugawa domin ya, a yadda na fahimta shi ne dukkansu Abba ta gansu akan abu mai muhimmanci da ya she su. Mene ne wannan abin?
A can ƙasar binciken na hango maganar auren Ikram da Khalil, Uwais da Iman, Wai ma Ina Iman din? Akwai wani abu da ban sani ba akan Alhaji Nafi'u? Ina iman take? Idan har Iman? Sannan a binciken Yaya shima anan ya tsaya. Abinda na fara shine kiran Khalisah, nan muka sha hira da ita kafin na Tambaye ta ina Iman? Ta ce min. "Tun bayan fasa aurenta ba a san inda take ba." Shiru nayi ina nazarin abinda ta faɗa. "And Aunty Khalisah Kuma ba a nime ta ba?" "Eh da farko an nime ta daga baya aka samu wasikar cewa kada a nime ta." "Na gode sosai!" Daga haka na ajiye. Na shirya ranar laraba zan je gida wurin Abba nayi magana