Showing 1 words to 3000 words out of 185502 words

Chapter 1 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

477

03/04/2021 脿 15:04 - Les messages et les appels sont chiffr茅s de bout en bout. Aucun tiers, pas m锚me WhatsApp, ne peut les lire ou les 茅couter. Appuyez pour en savoir plus.
06/08/2021 脿 11:49 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*1*

A nutse suke taka k'asar kowace da jakarta a hannu da dogayen hijab d'insu har k'asa, yanayin kamalarsu da fuskokinsu zai nuna maka sun samu tarbiya a zahirance dai, girgiza kai d'ayar tayi tace "Gaskiya yau ba zan je ba, dama ina shiga kallo ne a gidan idan ans s茅rie d'in da nake so, yau kuma ba'a yi dan haka ina gida."

Wacce tafi tsayi da haske sosai ga kuma 'yar k'ibarta tace "Ni kam zan je, dan jiya mbc Bollywood sun yi tallar khabi kushi khabi gham, dan haka zan je nayi kallo."

Tab'e baki tayi tace "Amma *Mimi* da dare ne fa, kinsan Abbanki ba zai barki fita ba."

Kallonta tayi ita ma tace "Kinsan yau asabar yana tafiya babban masallaci wajen sauraren karatu, yana tafiya ni ma zan tafi, awa d'aya suke yi kafin su gama na dawo."

Sake tab'e baki tayi tace "To yau *Mas'ud* ba zai zo bane?"

Wani dogon tsaki tayi tace "Ina farin ciki zaki lalata min shi ta hanyar kiran sunanshi."

Da mamaki ta kalleta tace "Mimi, Mas'ud fa shi ne iyayensa suka kawo kud'in gaisuwarki gidanku kuma iyayenki suka karb'a, sannan sun tsayar da magana cewa ana fara azumi zai kawo lefenki da sadaki, amma shi ne ba ki son maganarshi."

Yatsina fuska tayi tare da cunno leb'enta na k'asa mai kalar pink sosai tace "Wa ya fad'a miki zan yarda ya kawo? Wallahi bana son shi."

Da mamaki sosai tace "Ba kya son shi kuma kika bari manya suka shiga maganar?"

Cikin rashin bawa abun mahianci tace "Eh, saboda kawai ya takura min ba yanda zanyi, sannan bani da wani tsayayye har yanzu da zai dinga d'aukar d'awainiyata, sannan kuma yana da wani abu da nake son namiji ya kasance da shi."

Girgiza kai ta shiga yi da mamaki kafin tace "Mimi me yake damunki? Me yake da shi da kike so? Dama ba dan Allah kike kulashi ba?"

Wani murmushi tayi da yasa kumatunta masu tudun gaske sake fitowa tace "Sam bai min ba ne *Asma'u*, sa'arshi d'aya ya iya d'aukar wanka."

Jinjina kai tayi tace "Kenan kamar bankinki kike mayar dashi?"

Dariya tayi da tasa hak'oranta fitowa farare tas tace "Kusan haka?"

Cikin jimami tace "Allah ya shiryaki." Da dariyar mugunta tace "Ameen."

Suna k'arasowa gidajen na su Mimi tace "To nasan dai saida safe, dan ke ko 'yar wayar nan baki da za'a dinga yin jira ta WhatsAp."

Murmushi Asma'u tayi tace "Ke ma da kike da babbar wayar karki manta ba da sanin mahaifinki kike yi ba, kuma duk ranar daya sani zaki kad'e."

Dariya tayi tace "Ba ma zai sani ba, kafin lokacin na yi aurena na tafi na barsu."

Dariya Asma'u tayi tana girgiza kai tace "Mimi haka kika zama yanzu?"

Fari ta mata da ido tace "Ah to! Zamu zauna rayuwa babu ci gaba ne, ke ma kina son kiyi auren ai rashin matsayi ne."

Girgiza kai tayi tare da shigewa gidansu, ita ma shiga tayi tare da yakice hijabinta ta cire tana siririyar sallama, babu kowa a tsakar gidan sai mahaifiyarta dake zaune bakin murhu tana kad'a miya, yatsina fuska tayi tace "Mama yau ma dai na gadon ne?"

Juyowa tayi ta kalleta, girgiza kai tayi ta yi banza da ita ta ci gaba d脿 abinda take, da sauri ta shige d'akinsu bayan ta duk'a kafin ta iya shigewa ciki, aje kayan makarantar tayi sai siket d'in data ja sama tayi d'aurin k'irji da shi ta fito, bokiti ta d'auka ta je gaban randa zata d'ibi ruwa uwar ta kalleta cikin muryarta kamar ta yara tace "Karki fara *uwa*, kar ki d'ibar min ruwa kinji na fad'a miki."

D'agowa tayi ta kalleta da mamaki tace "Mama wanka zanyi fa."

Cikin fad'a tace "Ruwan alwala kawai zaki iya d'iba, shi ma idan za kiyi sallah."

Da mamaki tace "To me yasa? Babu ruwan ne?"

Kai tsaye tace "Babu, kuma kinsan ai ke kinfi k'arfin d'ebo ruwan, k'annanki ne ke d'ebowa da k'yar suna kawo mana, amma ke kika fi kowa anfani dasu."

Turo baki tayi tace "To yanzu dai bari na yi wankan, zan d'ebo miki gidansu madame *Maimuna*."

Hararanta tayi tace "Ke d'in? Ke ce zaki d'auko bokitin ruwa?"

Da sauri tace "Wallahi zan d'ebo."

D'ibar ruwan tayi rabin bokiti ta shiga d'aki ta d'auko kwandon wankanta mai d'auke da rantsatsen sabulu mai tsadar gaske da samarinta suka siya mata tare da maclean da brush ta shiga ban d'akin. Ta jima a ciki tana gyara jikinta kafin ta fito rik'e da kwandon, bokitin kuma ta baroshi a can,da kallo uwar ta bita dan ita har ta gaji da mata maganar d'auko bokiti ma, idan ta tashi ta d'auko kawai.

Buta ta d'auka tana sake zubawa k'afafunta ruwa tana fad'in "Gaskiya Abba ya daure a shafe mana ban d'akin nan da simitin, haba ban d'aki kamar wani filin dambe."

Tana saurarenta ita dai har tayi alwala ta shige d'akin, mai ta fara shafawa tare da d'auko k'atuwar jakar kayan kwalliyanta, sanyayya kwalliya ta yi wa kanta mai birgewa kafin ta mik'e ta nufi wajen kayanta. Tabbas kayan dake cikin akwatinta kana kallonsu zaka san sun fi k'arfin 'yar wannan gida, k'arya da d'aukarwa kai ne kawai zai bata wannan suturu, dan duk girman akwatin nan na k'arfe shak'e yake da kaya, daga kallonsu a ido kawai zai tabbatar maka sababbi sun fi yawa kuma duk d'inkunan zamani ne masu tsada.

Wani mahaukacin leshe ta d'auka ta saka riga da siket wanda aka cika gaban rigar da duwatsu masu k'yalli, dake tana da kumari sosai sai suka zauna mata d'ass a jiki musamman siket d'in daya fito da mazaunanta sosai, hijab ta saka ta fara gabatar da sallah magrib kafin ta gama ta d'aura d'an kwalin kayan, wani mayafi ta d'auka shara shara ta feshe da turare ta fito tsakar gidan.

Kallon mahaifiyarta tayi dake tsaye tana sallah, hallitar Allah kenan, domin kuwa duk kyan *Maryam* da tsayinta da wannan baiwa da Allah ya mata, mahaifiyarta 'yar wada ce, ma'ana irin gajerun nan k'anana, dan da zata tsaya kusa da ita ba zata kawo mata a k'ugunta ba. Matsawa tayi kusan kwanukan data gani ta shiga bud'ewa, d'an tsaki tayi tace "Yunwa nake ji amma wallahi ba zan iya cin tuwo ba."

Mik'ewa tayi ta koma d'akin ta d'auko 'yan canji a jakarta ta fito daidai da gama sallarta, kallonta tayi tace "Ina zaki je kika yi shiri haka?"

Cikin turo baki tace "Babu inda zan je Mama, nan gidansu madame ne zan shiga."

Girgiza kai tayi tace "Uwa bana son kowane lokaci kina zuwa musu gida, me yasa ba zakiyi hak'uri da kallon ba wai? Tunda Allah bai hore mana ba."

Kamar za tayi kuka tace "Mama zan daina, yanzu ma wani film ne za'a saka mai kyau da ban tausayi, yanzu na dawo fa."

Jinjina kai tayi ta d'auke kanta daga gareta tace "Idan ma baki dawo ba ke da mahaifinki ne babu ruwana."

Cikin rad'a tace "Mama har sun tafi karatun ne?"

D'aga mata kai tayi tace "Sun tafi tun kafin ki shigo."

Murmushi tayi ta nufi hanyar fita tace "Yanzu zan dawo Mama."

Da kallo ta bi k'ugunta dake bala'in juyawa sosai, tafiyar kuma a nutse take yinta amma dake Allah ya horesu, girgiza kai tayi tana fad'in "Allah ya shiryaki Mimi."

Gidan yana kallon nasu ne babban gida ne mai d'auke da babbar k'ofa, kai tsaye ta shiga bayan sun gaisa da mai gadin, saida ta tsaya a farfajiyar ta ciro wayarta daga k'ark'ashin siket d'inta kusa da cibiya kafin ta shiga d'aukar kanta selfie, saida ta d'auki masu kyau kafin ta shiga WhatsAp ta d'ora wanda suka mata a statu tana wa jama'a barka da da dare, da sallama ta shiga babban falon yaran da matar gidan suna amsa ma ta, gaisawa sukayi a mutumce kafin ta nemi kujera ta zauna tana fad'in "Tanti mbc basu saka film d'in nan ba?"

Lalaba kujerar da take kai tayi ta d'auki remonte ta mik'o mata tana fad'in "Gashi duba ki gani."

Karb'a tayi inda Maimuna ke fad'in "Ni fa kallon ba damuwata yayi ba, idan ta ni ne ma saina wuni ban kunna tvn ba."

Dariya kawai tayi sanda take nemo tashar, ganin ana tsaka da film d'in yasa ta gyara zama tace "Yawwa an fara."

Tattara hankalinta tayi gaba d'aya ta mayar kan tvn, kallonta Maimuna tayi, yarinyar na birgeta sosai saboda iya d'aukar wankanta da saka kaya, kamar ba 'yar talakawa ba, dan ko ita dake auren mai kud'i bata kai ta saka kaya masu tsada da kyau ba, uwa uba jikinta dake d'aukar ido kamar na wata babbar yarinya. Mik'ewa tayi ta bar ta nan ta shiga k'arasa kimtsa gidan, tana kammalawa ta saka turaren tsintsiya kafin ta d'ebo abinci a plate, k'asa ta aje ta kalleta tace "Mimi sauko mu ci abinci."

Kallonta tayi ta kalli plate d'in, kai har ga Allah ba zata ce a'a ba, macca ce fa da jar miya da naman kazi, ai duk rashin had'amarta tafi k'arfin cewa a'a tunda dama yunwa take ji, tasowa tayi a hankali ta zauna cike da kunya, ita kan ta Maimuna tayi mamaki dan gaske duk sakewar Mimi a gidan nan bata cika cin abinci ba, yanzu ma dan taga akwai yaran makwabta ne yasa ta zubo mai yawa idan ita bata ci ba su sun ci.

Cikin nutsuwa suke ci suna kallon tvn saidai babu mai magana, basu ji tsayawar motarshi a k'ofar gidan ba sallamarshi kawai suka ji a tsakiyar falon tare da amsa gaisuwar da yaran mak'wabtan ke mi shi.

Bayanta yake kallo dan tana fuskantar tv ne, saidai daga yanayin shigar yasan ita ce, ga k'amshin turarenta *pure love* daya gauraue d'akin duk da turaren wutar da aka yi, musamman data aje gyalenta a kan kujera saiya samu kan shi da k'urawa bayanta ido, d'inki ne kamar na yanzu bayan ya sauka sosai fiye da kafad'unta, rigar kuma a kan k'ugun take zaune har yana ganin zip d'inta da kuma zariyar da akayi a baya na salon d'inki. D'an lashe leb'enshi yayi tare da kallon gashinta data dunk'ule ta rufeshi da ribom, dan yanayin d'aurin d'an kwalin yasa tsakiyar data tara gashinta a bud'e yake. Murmushi ya saki yana k'arasowa yana fad'in "Sannunku, abinci ake ci?"

Tunda ta ji sallamarshi ta tsaya cak saboda kunya, sunkuyar da kan ta tayi saida taji ya baro bayansu kafin tace "Ina wuni."

Da sakin fuska ya amsa da "Lafiya lau Mimi, an wuni lafiya?"

Sunkuyar da kan ta kawai tayi ba tace komai ba, mik'ewa Maimuna tayi tana fad'in "Sannu da zuwa? Yau ka shigo da wuri."

Murmushi ya mata yace "Hakane, zan d'an fita ne shiyasa."

Tsaye tayi gabanshi tace "Muje kayi wanka ko?"

Jinjina kai yayi tare da mik'ewa, hakan yasa ita ma mik'ewa tana kallon Maimuna tace "Aunty ni zan tafi, saida safe."

A tare suka kalleta da sauri yace "A'a Mimi zauna, ba jimawa zan yi ba kinji, zauna ki ci abincinki."

Murmushi tayi sai lokacin ta kalleshi, a k'alla ba zai gaza shekara arba'in da bakwai zuwa da shida ba, yana da kwalliya saidai matsalar mutum ne mai k'iba. Girgiza kai tayi tace "A'a zan tafi, saida safe."

D'aukar mayafinta tayi da wayarta duk da hannu d'aya hannu d'aya kuma a sagale saboda abincin daya tab'a ta juya, duk da yana gaban matarshi saida ya sake bin bayanta da kallo, lumshe ido yayi ya sake lashe leb'e yana ayyana a ran shi "Insha'Allah zaki zama matata ke ma, ina son ki Mimi, wannan surar taki zata zama tawa ni kad'ai, gidan hutu ne ya dace dake."

Saida ya ga fitarta kafin ya kalli Maimuna data wuce gaba ya bi ta baya. Tana fita a farfajiyar ta wanke hannu ta sha ruwa a bakin panpon, yafa gyalenta tayi ta shiga latsa wayarta, tana kaiwa k'ofar gida kira na shigowa wayar, dubawa tayi ta ga an ruba *d'an wahala*.

Tsaki tayi tare da d'auka dan bata tsallake kiranshi kasancewar mutum ne mai sakin hannu, a yanda ta wuni ba wadataccin kud'i zata so samun na kashewa.

Cikin sanyayyar murya tace "...




*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:49 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*2*


Cikin sanyayyar murya tace "Hello."

Amsawa yayi da "Gimbiyata, ya kike?"

A dak'ile ta amsa d'脿 "Lafiya lau."

D'orawa yayi da cewa "Na ga statu d'inki na yi magana na ga ba kya en ligne (online)."

Cikin yatsina fuska tace "Hakane."

Cikin murmushi yace "To ki hau za muyi magana."

A k'asan mak'oshi tace "Um um!" Da sauri yace "Me yasa?"

Shiru tayi hakan yasa shi cewa "Ko babu mega (data) ne?"

Yanzu ma a mak'oshin tace "Um." Wani murmushi yayi yace "Haba gimbiya Mimi, kuma shine baki kira kin fad'a min ba? To kinga bari na turo miki da kati yanzu saiki hau zamuyi magana."

A dak'ile tace "Uhm! Nagode." Da fara'a yace "Haba ba komai, matar da zan aura ace babu kati a wayarta, ai abun kunyata ne."

Yana kashe kiran taja tsaki tace "Aikin banza, ko me zanyi da shi? Wani k'azami dashi ko turare bai iya sakawa ba."

Mayar da wayar tayi ta soke a siket d'inta kafin ta fita a gidan, canjin hannunta ta nufi bakin titi dan samun wani abu da za ta ci, dan da tana da kud'i isashi kayan shayi zata siyo, dan a rayuwarta tana son shayi sosai musamman da bred da soyayyen k'wai, a hankali ta taka har ta k'arasa bakin titin, babban birni kenan ba'a cika samun irin kayan soye soyen nan ba, a hakan ma wai dan suna unguwar marasa k'arfi, wani shago ta k'arasa kawai ta siyo sardine da bred ta juyo dan komawa gida.

Tana ganin motar ta sunkuyar da kai dan ta gane shi ne, duk da haka saida ya tsayar da ita ya fito daga motar yana fad'in "Mimi daga ina kuma? Na d'auka ai gida kika shiga."

Da ladabi tace "Na je nan ne bakin titi siyo abu."

Murmushi yayi yace "Mama ce ta aikeki?" Da sauri ta kalleshi jin yace wai mama, bayan kuma tana da tabbacin ya girmema mahaifiyarta ma, d'an tab'e baki kawai tayi ba tace komai ba, hannu yasa aljihu ya ciro yan jaka biyar biyar gida biyu ya bata yace "Ga wannan kya siyawa su *Amir* abun kari da safe."

D'an d'aga idonta tayi, a gaskiya ita kallon uba take masa da kuma mai taimakaonsu, ba kuma su kad'ai ba duka unguwar yana tallafawa gajiyayyu, haka yasa ta karb'a ba tare da tunanin komai ba tana fad'in "Angode, Allah saka da alkairi."

Murmushi ya mata yace "Ki shiga gida kinji, bana son ganinki a haka ana kallonki."

Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi amma kuma saita sunkuyar dan idonshi a kanta suke, jinjina kai tayi alamar to tare da takawa tana maimaita kalamanshi, saida tayi nisa kafin ta ji ya tayar da motar yayi gaba, da sauri ta sake kallon kud'in tana murmushin jin dad'i su ma ta sokasu a poshet d'in wayarta kafin ta saka wayar ta b'oye ta k'arasa gida.

Daf da shiga gida wayarta tayi vibrations, tana dubawa tsabar kati ne ya turo mata har na jaka biyar, ko a jikinta dan ya turo mata fiye da na haka ma, shigewa tayi gidan da sallama tare da nufa wajen kwanuka dake cikin kwando a killace, k'aramin faranti ta d'auka na silba ta dawo ta aje kan tabarmar tare da ledar hannunta, d'aki ta shiga ta b'oye wayarta da kud'in kafin ta dawo ta zauna kan tabarmar ta mik'e k'afafu, uwar na kallonta ita dai har ta bud'e kifin ta juyeshi a ciki ta d'auki bredin, turawa uwar tayi tace "Mama ci."

Girgiza kai tayi tace "Um um, a ci lafiya."

Jawowa tayi ta ci gaba da cin abin ta tana fad'in "Mama har yanzu su Abba basu dawowa ba?"

A sanyaye tace "Basu dawo ba, kinsan tafiya tare da su *Yaseen*."

Cikin had'e fuska tace "To mama shi ma Abba ya dinga zaman shi a masallacin nan unguwar mana, yana wahala doguwar tafiyar nan fa."

Da mamaki ta kalleta tace "Mimi d'aukar karatun da yake zuwa? Kuma kin fi kowa sanin shi d'in yana matuk'ar k'aunar karatun *Sheik Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif*, ba zai daina ba tunda yana so."

Shiru tayi ba tace komai ba hakan yasa mahaifiyar ta sak茅 kallonta da kyau tace "Mimi, ni ko ki mayarwa da Mas'ud wayar daya baki?"

Turo baki tayi tace "Na mayar Mama."

Nunata da yatsa tace "Tsakaninki da Allah kin mayar?"

Shiru tayi sai kuma ta kalleta kamar zatayi kuka tace "Wallahi mama gobe da ya zo zan mayar masa, ni dama wayar bata min ba."

Jinjina kai tayi tace "Idan baki maida masa ba wallahi mahaifinki zan fad'a ma, ya fad'a miki baya son ki da waya yanzu Mimi, shiyasa ko da Mas'ud ya baki wayar nan nace ki mayar masa."

Cikin turo baki tace "To naji zan mayar." Tuttura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login