Showing 69001 words to 72000 words out of 185502 words

Chapter 24 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

504

*Sheikh*


Dake a jirgi suka shigo hakan yasa suka zo bayan magriba, tunda yasan yau asabar yasan a lokacin Hafsat tana cikin gidan a b'angaren karatu tare da matan da suke karatun dare, kai tsaye b'angarenshi ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya ya nufi masallaci, saida sukayi sallah isha'i sukayi karatunsu kafin duk da gajiya kam kafin suka tashi k'arfe tara. Yana shigowa gidan a falo ya sameta tare da Aisha da wata budurwa mai d'inkinsu, gaisheshi tayi da ladabi ya amsa haka ma Aisha kafin ya wuce ciki, mik'ewa tayi a sanyaye ta kalli Aisha tace "Ki duba kayan kiga idan sunyi sai ki bata kud'in, idan akwai wanda bai yi ba saiki bata ta koma dashi a gyara."

Kallon budurwar tayi tace "Dan na sanki da shiririta wani lokacin."

Dariya tayi tace "Insha'Allahu ma anti daidai wannan Mamar Aisha."

"Allah yasa." Ta fad'a tana murmushi ta shige falon yallab'ai, a tausashe a sanyaye ta furta "Assalama alaika sheikh na wa."

Tsura mata ido yayi har ta k'araso sannan yace "Wa'alaiki salam *Manga* ta wa."

Murmushi tayi tare da zama kusanshi tace "Sannu da zuwa uban gidana, an zo lafiya?"

Saida ya d'ora hannu a cikinta yana shafawa yace "Yawwa sannu abokiyata, na sameku lafiya?"

Da fara'a ta amsa da "Lafiya lau muke, ya k'ok'ari?"

Murmushi yayi yace "K'ok'ari muna ta fama da taimakawarku."

Murmushi tayi tace "To yanzu me ye abunyi? Nasan dai mijina sarkin tsafta ne bare nayi tunanin baiyi wanka ba, yanzu abinci zaka ci ko kuma karatu zamu shiga?"

Gyara zama yayi yana kallonta yace "Sanin matata sarauniyar tsafta ce yasa na fara wanka kafin ta sakani dole, abinci kawai za'a taimaka min dashi yanzu dan yunwa nake ji, amma kafin nan a amsa min tambayoyi na."

D'an bud'a idonta tayi sosai tace "To fa! Wane tambayoyi kuma?"

Hannunta ya kamo ya rik'e yace "Hafsy na, yanzu kina ji kina gani da had'in bakinki da yardarki da kuma tallafawarki su Asas zasuyi wani abu wai kamu? Miye ma kamun nan ne? Shin bidi'a ce ko sunna? Me ake yi a wurin? Maza da mata ake tarawa ayi rawa a ci a sha a fita tsirara? Mi ye ma anfanin yin shi kamun?"

Wata ajiyar zuciya ta sauke tace "Da fari dai ba sunna bace zamu iya cewa bidi'a ce tunda al'ada ce aka rik'e gam, na biyu kuma ana tara maza da mata amma wannan iya zallar mata ne insha'Allah, abu na gaba kuma ba zamu saka kid'a ba bare har ta kai ga rawar ma, dan mu ba iyata mukayi ba."

Ta k'arashe tana k'yalk'yalewa da dariya, shi ma yar dariyar yayi yace "Yanzu kenan a matsayinki na ustaza kin bada goyon baya d'ari bisa d'ari akan al'ada marar tushe?"

Marairaicewa tayi tace "Dan Allah ayi hak'uri a barmu, kaga fa har na kai wa amarya kayanta da zata saka a ranar, insha'Allah babu abinda zamuyi da ya sab'a k'aida."

Zura mata ido yayi sakamakon fad'uwar da gabanshi yayi sanda ta ambaci amarya, Ryam! Lallai yarinyar ta koya mishi darasi na rayuwa akan karatun mata, hakan ya cire mishi sha'awar k'ara aure gaba d'aya, ita ce ma dai yake ta koyon yanda zai yakiceta a zuciyarshi, ma wani ikon Allah sai ma k'ara samun muhalli take tana zama, babban tashin hankalin shi ne ko waje ya fita aka kirashi da sunan sheikh ko wani suna na ladabi da girmamawa saiya tuna wacce ta iya kallonshi ta ce Abdul, wasu lokuta sai ya ji kamar ya biya kud'i ayi zaune gabanshi ayi ta kiranshi da Abdul, saidai tasirin ba d'aya bane ko kad'an, gashi lokaci na sake kusantata da d'an uwanshi da zasu zama abokan rayuwa mata da miji, shi kuma zuciyarshi na sake daffaruwa da tunaninta.

Jinjina kai kawai yayi bai ce mata komai ba, hakan ya sata mik'ewa tace "Godiya muke sheikh, bari na kawo maka abinci a nan."

Yana kallo har ta fita a d'akin kafin ya gyara zamanshi yana sauke numfashi, cire babbar rigarshi yayi ya aje tare da hula ya shiga shafa kanshi yana lumshe ido yana tuna abinda ya faru a waccen ranar, abunda yafi tsaya mishi a rai shi ne da likitar tace zata je ta samu mahaifinta suyi magana, da sauri ya bud'a idonshi yaja wani dogon tsaki a zuciyarshi yake fad'in "Me yasa Ryam? Me yasa kika ballagazar da kanki haka? Baki san cewa mutumcinki shi ne darajarki ba? Me yasa kika zama mai arha haka? Kika wofantar da abu mafi daraja?"

Wani tsakin ya kuma ja tare da sake muskutawa ya gyara zamanshi, yana haka Hafsat ta shigo da sallama da babban tire a hannunta d'auke da kwanuka masu kyau na alfarma sa茂 d'aukar ido suke.


*Safiyar lahadi*

Su hud'u suka gama shirinsu har da Asma'u da sukayi fad'a jiya amma an shirya da safe, suna zaune tsakar gidan k'aramar wayar Asma'u tayi kuka, d'auka tayi tana fad'in "Abokin ango barka."

Daga b'angarenshi ya amsa da "Barka k'awar amarya, kun shirya ne?"

"Mun shirya ai ku muke jira." Ta fad'a tana kallon Mimi, daga can ya amsa da "Da gaske? Ko kuma dai maganar yan matan amarya za'a mana."

Cike da tabbaci tace "Da gaske mana, idan baka amince b芒 gwada cewa mu fito ka gani, sai mu tabbatar su waye yan matan amarya da abokan ango tsakaninmu."

Dariya yayi yace "Da gaske? To ku fito mu gamu a k'ofar gida."

Saida ta mik'e tsaye suma suka mik'e tace "Kuma ka yarda idan baku k'ofar gida ku zama yan amatan amarya?"

Dariya yayi sosai yace "Anya Asma'u kina son gaskiya? Yanzu so kike ki rabu da abokin namu?"

Ita ma murmushi tayi tace "Ina so ne dai na nuna muku mu ma jarumai ne zamu iya d'aukan duk wani caji da yan matan amarya zasu mana."

Cikin d'aga sauti yace "Iyeeh! Lallai Naanah Asma'u kin iya azanci, amma dai kina da sha'awar siyasa ko? Ko kuma dai a gidanku akwai d'an siyasa."

Dariya tayi sanda suka fito k'ofar gidan tace "Ko kad'an, wayo ne dana fara koya a wajenka."

A lokacin shi ma ya karyo kwanar gidan yana fad'in "To gashi mun iso tare, yanzu kowa sai ya zauna a matsayinshi ko?"

Shiru tayi ba tace komai ba har ya tsayar da motar, sauke glas yayi yana aje wayarshi yace "Sannunku."

Duk amsa mishi sukayi banda Mimi dake lab'e bayan Asma'u tana sunkuyar da kai, murmushi yayi yace "Ina amaryar ta mu? Asma'u ya zaki b'oye mana ita haka?"

Kama hannun Mimi tayi ta bud'e motar ta shiga haka ma su Rauda, har zata shiga Sadeeq yace "A'a ya haka? Ki dawo gaba mana, ko ba kya son hira dani ne?"

Murmushi tayi tace "Ni dai ban fad'a ba."

"Amma ai aikinki ya nuna haka." Ya fad'a yana kallonta tana zagayawa, bud'ewa tayi ta shiga ta zauna kafin ya tayar da motar, a hankali suke tafiya yana jansu da hira irinta yan matan amarya da abokin ango wacce duk rigima ce a cikinta su ja ya ja, da haka har suka isa salon d'in da Asas ya umarceshi ya kai su. Duk ajin Mimi da son k'aryarta saida ta ji ta raina kaita da suka shiga ciki, babban wuri ne katafare daya tsaru ya had'u, ga ma'aikata suna ta aikonsu ga manyan mata na shiga da fice.

Mai saloon d'in ba musulma bace amma tana ganinsu dake tasan su Sadeeq da fara'a ta mik'e ta tarbesu, fita yayi ya barsu bayan ta tabbatar masa ya dawo bayan awa uku. Nan fa ta shiga yi wa Mimi aiki da kan ta su Asma'u kuma yaranta suka kama musu, gyaran kai aka fara musu da wankin k'afa da hannaye, Mimi kuma saida ta shafa mata wani had'i na gyaran fuska tare da rufe mata idonta da kokonbre, minti k'alilan suka rage Sadeeq ya dawo aka kammala musu, dan haka yana zuwa ya damk'a mata kud'i suka tafi suna godiya inda suka ji Sadeeq na fad'in sai jibi idan ya maido su kuma.

Suna dawowa gida ta samu Iya Delu da mama suna hira ta 'ya da uwa, gaisheta duk sukayi sai Mimi da tace "Ni dai ba zan gaisheta ba dan ina daf da shiga gidanki a matsayin kishiyarki."

Duka Iya ta kai mata tana fad'in "Ke kauce can ja'ira, naga inda zaki je d'in ai."

Dariya sukayi suka shiga d'aki sai su Iya da suka ci gaba da hirarsu akan dangin malam da har yanzu babu wanda ya tako k'afarshi, malam da kan shi ya basu goro ya kuma fad'a musu, sannan jiya ma da kan shi ya sake komawa k'auye ya tunashesu lokacin, amma babu wata gamsassen amsa daga garesu kowa yayi gum da baki saboda su aurenshi da Iya ne basu so ba, abu kuma an ja shekaru gasu da 'ya'ya da jikoki amma a ce sun kasa fahimtar hakane Allah ya nufa. Dan haka jiya d'in yace ma Iya suyi hidimarsu kawai, tsirarun danginshi ba zasu hana yiwuwar wani abu ba, auren 'ya'yanshi ma aka yi shi ba dasu ba bare kuma jikanyarshi, dan haka za'ayi bikin Mimi kuma dama ba wata tsiya suke buk'ata daga garesu ba.


*Yammacin litinin*


Daga farfajiyar gidan take jin shewarsu suna shigowa, kallon Asma'u tayi tace "Su Salma ne fa da Ruky, nasan sun samo muku d'inkin."

Da zumud'i Asma'u tace "Allah yasa." Suna shigo d'akin ya gauraye da hayaniyar yan matan suna murnar samun d'inkinsu na anko wanda zasu saka ranar kamu dana kan amarya, zaune Salma tayi kusan Mimi tana nuna mata hotunan wasu amare da fad'a mata sunan wanda suka musu kwalliya, a haka ta kawo wata amaryar da kwalliyarta tayi kyau sosai kamar inji (ingine) ya mata, da zumud'i Mimi tace "Wannan tayi kyau, wa ya mata?"

Salma ce tace "Sara ce."

Da sauri Zeinaba tace "Baa ita ce jiya Sadeeq ya kaimu salon d'inta ba?"

Asma'u ce tace "Ita ce."

Mimi ce tace "Gaskiya aikinta na kyau, dubi kiga hannayena data wanke min jiya sun k'ara wani d'an banzan laushi wallahi, kinji k'afafuna."

Asma'u ma dariya tayi tace "Ai ni k'afata a hannuna ta kwana wallahi, dan sai nake jin kamar b'era zai iya gwaguye min k'afa."

Dariya suka kwashe da ita inda Salma tace "To kinga tunda ma kun tab'a zuwa dan Allah ki ma Sadeeq magana ya sama mana rendez-vous a wurinta ranar alhamis ta mana kwalliya, akwai tsada fa amma nasan zata mana sauk'i ai."

Asma'u ce tace "Yace fa sun san ta sosai tare sukayi karatu da ita a universit茅, kuma jiya daya kaimu yace Asas yace gobe ma a koma saboda gyaran amaryarshi."

Dariya sukayi inda Salma ta bawa Ruky hannu suka kashe tana fad'in "Shegiya Mimi, ta fa d'auko mai zafi wallahi, gayenta ya had'u k'arshe, komai na kece raini ya ke mata."

Yatsina fuska Mimi tayi tace "Ba kamar ke ba da zaki auri sa'an babanmu ba."

Dariya akayi sa茂 Salma data had'e fuska tace "Mimi bana son wulak'anci wallahi, wai me yasa kike min hakane? Kinga fa sati uku ya rage aurena amma saboda kece na zo ina ta zirga zirgan aurenki."

Murmushi tayi tace "To yi hak'uri na daina." Da haka yan matan suka ci gaba da shirye shiryen bikinsu inda kowace ta gwada doguwar rigarta da aka musu iri d'aya mai kyau da dogayen hannaye, saidai babu wacce rigarta ke da d'an kwali hakan na nufin dole su nemi wanda zasu d'aura.

Sun jima a gidan suna hirarsu kala kala ta nishad'i da k'aruwarsu dan Mama ta fita tare da Sahura da Shapi'a, har bayan azahar kafin suka ci abinci da Rauda ta musu mai sauk'i kafin suka bar gidansu suka barta tare da yan uwanta suka ci gaba da farin cikinsu.



*Indai da comment to da aiki tuk'uru insha'Allah.*



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*24*



*Asubar talata* tana cikin bacci bata riga ta farka ba Mamar Asma'u data shigo gidan yanzu ta shafa mata lalle a kan ta da hannaye da tafin k'afa, zunbur ta tashi zaune tana kallonta tana mata dariya, ganin ta fita a d'akin sai kawai ta cire lallen na hannayenta ta shafawa fuskar Zeinaba dake baccinta, a firgice ta tashi tana fad'in "Waye? Mimi."

Dariya ta kwashe da ita tare da mik'ewa ta fita a d'akin ta shiga ban d'aki da d'an kwalinta a kai.

Safiya na yi Mama ta dinga aikinsu Yaseen suna raba alawa ta wankan amarya da yamma, Mimi kam banda fad'uwa da gabanta keyi duk jikinta ma yayi sanyi sosai, sai taji tana rasa karsashinta da zumud'inta da ma farin cikinta, misalin 08:00 Mimi dasu Rauda suka shirya suka shiga gidan Maimuna, anan k'awayenta suka dinga zuwa suna shan hirarsu da haka har aka samu wuni, dan kuwa saida la'asar tayi kad'ai aka kirasu suka shigo gidan, lokacin gidansu kuma ya cika da mutane yan uwa da yan unguwa an zo wankan amarya. Daga gurin angaye aka turo da motoci guda takwas dan kai su inda za'ayi wanka, kusan mutanen babu wanda bai je ba saboda wadatar motoci da aka samu, gidan yar uwar su mama dan waankan farko ana yin shi ne a dangin uwa.

Gaba d'aya basu d'auki minti arba'in ba tafiyarsu da dawowarsu, Mimi kam ta jik'a tayi laushi sosai dan tasha wankan ruwan lalle masu d'auke da itatuwan da kakaninmu suka yarda cewa yin wanka dasu yana zubar da duk wata shiririta da shirme, yana k'ara maka hankali da nutsuwa, tun a mota take hawaye har suka zo gida bata daina ba, tunda ta shiga d'aki kuma k'awayenta duk suka watse zuwa nasu gidajen aka barta da su Zeinaba kad'ai.

Alhamdulillah kam aure rahama ne kuma alkairi ne, a dalilin auren Mimi Abba da Mama sun samu gudumuwa sosai daga dangi da kuma abokan arziki, hatta da Alhaji Saminu ya aiko da gudummuwar buhun shinkafa da kuma kud'i har jaka hamsin, duk da dai baya bayar bane cikin dad'in rai, kawai yayi ne dan kar ace bai yi ba amma sosai ya ji zafin yanda Mimi ta banzatar da shi ko wayarshi bata tab'a d'agawa ba. Wasa wasa sai gashi lokaci na ta tahowa kamar almara.


*Ranar kamu*


Ko da k'arfe 08:00 ta buga suna salon ana ma su Asma'u kitso da k'unshi Mimi kuma saida aka fara mata gyaran jiki, ana idawa aka shiga zana mata k'unshi da jan lalle, mai salon d'in ce ta tsaya kan ta zata fara mata kitso k'anana, da sauri ta janye kanta tace "A'a, a'a bana so."

Da mamaki tace "Ban gane ba kya so ba? Kina amarya?"

Kamar zatayi kuka tace "Bana so ni dai, zafi ke akwai wallahi, bana son kitso."

Kamar da wasa Mimi ta ko dage ba za'a mata kitso ba ita kuka zatayi, dole k'arshe ta k'yaleta amma suna ta mata nasiha ta gyara a matsayinta na mace, ita dai saurarensu take bata kula kowa ba. Da azahar su Salma suka zo suma sunyi lalle da kitson su tsaf, dan haka ko da 03:00 tayi na rana suka fara shiri dan dukansu da kayansu suka zo, mimi ma ana ida lallen aka mata siraci ta shiga wanka, tana fito a sauk'ak'e kuma a nutse aka fara mata gyaran kakkauran gashin girarta, kad'an aka rage mata shi hakan yasa yayi kyau sosai tuni fuskarta ta fito shar da ita dake gashin nata bak'i ne wulik, kayan da Hafsat ta kawo mata ranar ta fara sakawa.

Doguwar riga ce abaya kalar ja mai duwatsu da kwalliya, tun ranar da aka kawo kayan Mimi bata duba su ba har Asma'u ta so bud'ewa ta hana, yanzu kam data saka sai suka saki baki suna kallonta, yanda rigarta ta zauna mata d'as a jiki ta mata kyau, ga tsarin rigar na ban mamaki wanda ya birgesu, wato idan sun fahimta komai a mutumce ne ya mata shi dan kar a sab'a k'aida, rigar zubin babbar riga aka mata na maza saidai a rufe take kirip har k'asa tana jan k'asa, gashi hula ce a bayanta irin na rigar sarauta alkyabba, sannan tana da kallabi ware daban wanda ake fara d'aurawa.

Kwalliya aka mata mai kyau da sauk'i wacce zaka rantse abonda aka shafa mata a fuska dama a fuskar ta ta yake, ana gama salllah la'asar dukansu yan matan sun fito sun haska a cikin rigunansu kalar pink na kakkauran yadi mai taushi, inda dukansu aka d'aura musu d'an kwali kala d'aya wanda suka siya.

Dogayen takalma k'afa ciki aka saka mata da jakarsu k'arama mai kyau da walk'iya, ga agogo data kama tsintsiyar hannunta dam ta zauna, kallabin abayar yanda aka d'aurashi daga ciki da kuma hular da aka d'ora mata sai ta fito sak gimbiyarta yar sarki jikar sarki.

Yamma sosai motoci guda uku dukansu k'irar benz suka paka a k'ofar salon d'in, a hankalce kuma a tsare yan matan duka suka kewayeta suka shiga takawa har waje, suna fita Asas ya hangesu daga cikin motar, wani murmushi ya sub'uce masa tare da jin yana sha'awar ya tsokaneta kamar ita d'in *matar yayanshi ce*, a sanyaye ya bud'e motar ya fito tare da bud'e mazaunin da zata shiga ta zauna, duk tsaye sukayi a bayanta saida ta shiga ta zauna ya rufe ya kallesu yace "Nagode k'awaye da gyara min amaryata."

Murmushi sukayi Salma tace "Mu ba k'awayenka bane, ga k'awarmu nan kana shirin rabamu da ita."

Murmushi yayi yana tsaye yana kalli duk suka shiga motar, sai Asma'u data zagaya d'aya b'angaren da Mimi take ta shiga, a hankali suka bar wurin suka d'auki hanyar gidan saukar bak'i na sheikh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login