Showing 147001 words to 150000 words out of 185502 words
ta k'arasa kusa da shi ta kama hannun na shi ta shiga gyara mishi, murmushi ya mata yace "Nagode."
Ita ma murmushin tayi tace "Sheikh."
Zuba mata ido yayi cikin sangarta yace "Ryam."
Kallonshi tayi saboda shagwab'ar da ta ji yayi sai ya bata kunya, d'orawa yayi da fad'in "Na fad'a miki'a fi so naji sunan Abdul daga bakinki, fad'in sheikh baya miki kyay ko kad'an."
Cikin rangaji da rausaya tace "To Ab-dul."
Murmushi yayi saboda yanda ta ja sunan yace "Ina jinki."
Cikin shagwaba da turo baki tace "Ina so na ga Mama na da Abba na da su Yaseen, zaka kaini?"
Girgiza mata kai yayi yace "Um um! Amarya bata fita sai ta kwana biyu."
Da sauri tace "To amma ai ni na kwana uku a gidanka."
Dariya yayi yana girgiza kai yace "Ba irin wannan kwana biyun ba, ina nufin sai kin jima."
Bubbuga k'afafu ta fara yi a k'asa tana kuka tana fad'in "Ni dai wallahi sai na je."
Da mamaki ya kalleta yace "Sa茂 kin je? Ta ya ya?"
Kallonshi tayi tana kumburo baki tace "Kana fita ni ma zan tafi, tunda ai na fad'a maka kai ne baka barni ba."
Kyalkyalewa yayi da dariya ya nufi wajen farantin data aje yace "To ki je ga hanyar nan, ina dawowa aljanuna zasu fad'a min kin fita ba da izini na ba."
Matsawa tayi kusanshi a marairaice tace "Yanzu Kenan ba zaka barni na tafi ba? Gidanmu ne fa? A can ka d'aukoni ko ka manta ne?"
Girgiza kai yayi yana jefa lomar farko bakinshi, lumshe ido yayi yace "Uhummm! Ryam wai a ina kika koyi girki ne?"
D'an hararanshi tayi irin ranta ya b'acen nan tace "Ban sani ba nima."
Hanyar fita ta nufa yayi saurin cewa "Ina zaki je?"
Juyowa tayi tace "To miye na ka a ciki? Ba ka hanani ganin iyayena ba."
Ficewa tayi a d'akin ya bita da kallo yana cin abincin shi, murmushi kawai yake saki a zuciyarshi yana fad'in "Da alama sai na koma makaranta dan na k'ara fahimtar yanda ake zama da yara irinki."
A gaggauce ya gama cin abincin ya mik'e ya fita ya samu Hafsat na jiranshi, basu b'ata lokaci ba suka fita a gidan, a hanya ita ma Hafsat ke fad'in "Sheikh na wa dan Allah me zai hana idan kayi niyya ka aje ni wajen Hajia, ina so zamuyi magana dasu akan auren Aisha ne."
Wani kallo ya watso mata yace "Idan banyi niyya ba fa?"
Murmushi tayi tace "Dan Allah kayi niyya to."
Dariya yayi ya dangware mata kai yace "Ja'ira."
Murmushi ta sake yi tace "Sheikh na wa."
Shi ma murmushin yayi yace "Hafsat ta wa."
Da haka suka isa asibitin suka shiga ciki, saida aka fara killacesu aka basu kayan kariya suka saka har da takalmi da hula duka suka rufe jikinsu kafin aka shiga dasu d'akunan da yaran suke, ba'a barsu sun shiga ciki ba daga k'ofa kawai ta madubin k'ofar suka iya hangen yarinyar dake nad'e a cikin farin bandeji da oxyg猫ne a hancinta a cikin kwalba. Wata ajiyar zuciya Hafsat ta sauke mai k'arfi tare da lumshe ido, hakan yasa hawaye sauko mata a kumatu cike da tausayin yar ta ta, jawota sheikh yayi ya rumguma a jikinshi yana fad'in "Kiyi hak'uri kinji, yar ki zata warke har ma ki ganta tana gudu a gabanki."
Cikin shsheka tace "Allah ya yarda sheikh."
"Ameen." Ya fad'a yana kallon yarinyar shi ma yana jin wani imani da tsoron Allah na k'ara shigarshi, wannan kad'ai idan ka gani zai k'ara maka tsoron Allah a zuciya.
Suna barin asibitin gidansu Hajia ya sauketa ya wuce sabgar gabanshi, saidai Ryam na zuciyarshi da tunanin rabuwarsu ta safiyar yau, hakan yasa shi saka dreban Hajia Kabiru ya je gidansu ya d'auko su Yaseen ya kaisu gidan, yasan hakan ne kawai zai faranta mata rai.
Tana falonta ta dinga jin muryar Yaseen da Amir suna ta sallama, ai da gudu ta taso ta bud'e k'ofar ta fito, tana ganinsu da farin ciki ta k'araso tana fad'in "Yaseen, Amir, Ku ne dama?"
Rumgume Amir tayi ta zauna k'asa tana kallonsu suna ta washe mata baki suna k'ara daga kai suna kallon gidan, gaisawa sukayi sosai kafin su fad'a mata wanda ya kawosu da wanda yasa a kawosu, murmushi kawai tayi tace "Abdul kenan, ni ce ba zai bari na fita ba."
Da mamaki Yaseen ya kalleta yace "Abdul fa kika ce? Mimi sheikh d'in?"
D'an kyaci tayi alamar kai share dallah tare da mik'ewa tace "Me kuke so na dafa muku?"
Da sauri Amir yace "Miyar nama da shinkafa."
Tintsirewa tayi da dariya ta dunguri kan shi tace "Amir kwadayi ko?"
Dariya suma sukayi suna kallo ta wuce madafar, aiki ta shiga gadan gadan na gaba daya gidan, cikin nutsuwa da hankali ta kammala girkinta mai rai da lafiya, saida ta kwashe kamar yanda take yi kwana biyun nan sannan ta zubawa su Yaseen ta kawo musu, tare da ita suka ci a kwano daya a lokacin 12:00 tayi, mik'ewa tayi ta gyara falon sannan tace su wuce falonta, su Aisha na dawowa daga makaranta basu samu Hafsat ba, saida sukayi wanka sukayi sallah sannan suka ci abinci, ban da Munzeer babu wanda ya je inda take, ita ma tana falonta tare da kannanta suna ta kwasar hirarsu.
04:07 Kabiru ya dawo d'aukarsu dan dama Mama ta ce su dawo dan su tafi islamiyya, tare suka fito tana rik'e da ledar kayan makulashen data siyo ranar zata basu, suna fita farfajiyar su Aisha na tsaye jiran drebansu su ma zasu tafi islamiyya, da wani kallon raini ta shiga bin su Yaseen Wanda tsaf a idon Mimi hakan kuma ya mata ciwo. Da mutumtawa su Heezam da Aswan suka gaisa dasu Yaseen har Aswan na d'an tsokanar Yaseen ma dan suna had'uwa da shi a babban masallacin Kaddafi wajen karatun sheikh.
Wucewa sukayi ta bude musu k'ofar motar zasu shiga, taimakawa Yaseen tayi ya shiga ya zauna dan tsayinshi bai kai ma, zata d'auki Amir ta saka kawai Aisha tayi yar dariya tare da fad'in "Sunan wata waina wai ita 'yar k'unbu."
Sake fashewa tayi da dariya, da k'arfin bala'i Mimi tayi kan ta bata ankara ba ta kasheta da mari tare da shak'ar wuyan hijabinta ta had'ata da bango. A kid'ime kuma a tsorace duk suka kalleta suna zaro ido, kallonsu suka tsaya yi cirko cirko kowa cikinshi ya d'uri ruwa, cikin b'acin rai da fitar hayyaci tace "...
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*49*
Cikin b'acin rai da fitar hayyaci tace "Ke Aisha wacece ke da zaki raina min yan uwa? Akan wane dalili ne zaki shammaci halittarsu? Saboda ina auren ubanki ne?"
Turata tayi da k'arfi har saida kanta ya bugi bango ta d'ora da fad'in "Zaki takani yanda kike so a gidan nan na k'yaleki, amma idan kika ce zaki tab'a iyayena ko yan uwana wallahi kutumar ubanki zan ci a gidan nan saidai uban ki ya sakeni."
Juyawa tayi har zata nufi wajensu Yaseen sai kuma ta juyo ta kalleta tace "Ba kiyi kama da yar Abdul ba, sam halayenki basu dace dana wacce ta fito a tsatson Abdul da Hafsat ba, kaiconki wallahi, kuma fa duk wannan abun da kike yi kina yi ne saboda na auri Abdul ko?"
Yatsina fuska tayi tace "Mun riga da mun zama d'aya Aisha, zan fad'a miki wani abu kuma wanda na tabbatar cikin biyu za'ayi d'aya tunda ke ma aure zakiyi, ko dai mu haihu tare da ke, ko kuma na rigaki haihuwa dan tsohonki ya jima da tura sak'onshi kuma na karb'e da hannu bibbiyu, mu zuba ni da ke a gidan nan tunda kin kasa fahimtar a yanzu ni ma d'in uwarki ce tunda na gauraya da ubanki ."
Sama da k'asa ta bi ta da harara ta wuce zuwa wajen su Yaseen da sukayi tsuru suna kallonta, saida suka fita a gidan ta juya ta koma ciki ko kallonsu ba tayi ba, Aisha kam ta cika kamar zata fashe ta kawo wuya, Heezam kam girgiza kai yayi yace "Kin ga irinta ai, gobe ma ki k'ara."
Aswan ma murmushi yayi yace "Gaskiya ta fad'a miki, sam bakiyi kama da yar gidan nan ba."
Odar da sukaji tasa su fita da sauri amma ban da Aisha da take tafiya kamar wacce k'wai ya fashe ma a ciki, kalaman Mimi sun tsaya mata sosai a zuciya, musamman yanda take kiran sunan mahaifinta ba girmamawa Abdul gatsau, saida suka shiga mota sai kawai ta fashe da kuka kamar wacce aka k'wak'ulewa ido. Har suka isa islamiya tana kuka bata daina ba, a aji ma ba abinda take sai shashek'a, shiyasa ma ana tashi daga islamiyar ko da dreba ya d'aukesu bai tsaya ko ina ba gida ya diresu.
*Tun* fitarsu dama sunyi waya ita da sheikh suka sha hirarsu ta soyayya, Hafsat ma a can ta wuni sai yamma lik'is ta dawo daf da lokacin tashinsu, tunda sheikh ya dawo da ita kuma bai fita ba yana gida, hakan yasa suna shigowa falon da sallama sun samesu dukansu a falon.
Sheikh na tsaye zai shuge b'angarenshi ya dakata saboda jin shigowarsu, Mimi ta fito daga madafa rik'e da kofi a hannunta ta kawowa Hafsat shayin da tayi na goruba, Hafsat d'in kuma na zaune kan kujera.
Kusan a tare suka amsa sallamar yaran duk suna kallonsu, da sauri Hafsat ta mik'e gabanta na fad'uwa saboda ganin fuskar Aisha, idonta sun k'ank'ance sun kumbura abu ga jar fata, fuskarta ma duk tayi wata kala tsabar kuka sai shatin yatsun daya zauna a kuncinta, dan marin da Mimi ta mata a bazata ne ya zo kuma da mugun k'arfi, da hanzari ta tarbeta tana fad'in "Aisha lafiya? Me ya sameki?"
Sake sinne kai tayi tana ci gaba da shashek'ar kuka, hankali tashe ta kalli su Heezam tace "Kai me ya sameta? Fad'a tayi ne? Ko wani laifin tayi da aka daketa a makaranta?"
Aswan ne ya turo baki ya girgiza kai alamar a'a, sai Heezam daya d'aga kafad'a shi ma alamar uhum! Muryar sheikh ce ta dakesu a bayansu yace "Munzeer yaro na."
Cikin d'aga sauti Munzeer yace "Na'am Abie." Ya fad'a yana nufa inda yake tsaye, kusanshi ya tsaya ya shafa kanshi yace "Shi ne bayan bana nan tayi fad'a ko?"
Da sauri Munzeer yace "A'a Abie, aunty Aisha ce ta yi wa aunty Mimi rashin kunya, shi ne ta mareta a fuska kuma ta zageta."
Tsuru tsuru duk suka zubawa Mimi ido da ita ma ta kafe Munzeer da ido, amma data ga kallon da suke mata sai kawai ta d'auke kan ta tare da aje kofin shayin hannunta akan k'aramin table d'in ta dafe k'ugu alamar tana jiran a yi duk wacce za'ayi.
Hafsat ma d'auke kanta tayi daga Mimi ta kama hannun Aisha da k'arfi suka nufi d'akinta cikin hushi, ganin haka sai sheikh ma ya bi bayanta dan gaskiya baya son b'acin ran Hafsat musamman ma da ita d'in macece da bata cika saurin nuna b'acin ranta ba, Mimi na kallo suka shige d'akin tana tsaye zuciyarta na tafasa tana jin kamar bak'uwa ce ita a gidan nan, kamar bata da wani galihu ko mutumci.
Had'e hawayenta tayi tare da wani abu daya tsaya mata a wuya ita ma t shige d'akinta, saidai zaune tayi a kujerar falo zama irin na jiranka kawai na ke ka zo a yi ta ta k'are, ka zo ayi duk wacce za'ayi amma ba zan d'auka ba.
*A* d'aki kuma yana shiga Aisha na zaune bakin gado Hafsat na tsaye a kan ta tana d'an tab'a fuskar ta ta, da sauri ta juya ta kalleshi cikin hushi da b'acin rai tace "Akan me zata marar min yarinya? Ni ko kai akwai wanda ya tab'a dukansu ne bare kuma mari a fuska mai daraja, fuskar da ubangijinmu kad'ai muke turmusata a k'asa dan bauta masa, me ta mata da zata mareta haka har hannunta ya kwanta a fuskar yarinya?"
D'auke idonshi yayi a fuskar Hafsat d'in ya kalli Aisha yace "Me kika mata?"
A tsorace ta kalleshi cikin shakakkiyar murya tace "Abie ban mata komai ba, kawai daga zata raki k'annanta da suka zo, daga sun wuce nayi murmushi shi ne kawai ta mareni, har zagina ta dinga yi tana ambatar sunanka da sunan Amie tana fad'in wai ita ma matarka ce kuma zata..."
A tsawace yace "Shiru!"
Shiru tayi tana kallonshi tana sauke ajiyar zuciya, da mamaki Hafsat ta kalleshi tace "Tsawa ma kake mata? To wallahi ba zan d'auki wannan wulak'ancin ba, nayi hak'uri akan abubuwa da dama sannan na shanye b'acin rai bila-adadin, amma ba zan tab'a d'aukar cin zarafin 'ya'yana ba."
Kusa da shi ta matsa tana kallon idonshi tace "Ka fad'awa matarka karta sake sauke gigin haukarta akan yarana, inba haka ba wallahi da kaina zan d'auki mataki."
Tana fad'a ita ma ta shige ban d'akinta dan samo ruwan d'umin da zata gasa mata fuskarta data kumbura.
Kallon Aisha yayi ya girgiza kai yace "Allah ya kyauta."
Fita yayi a d'akin shi ma ya nufi d'akin Mimi, tana ganin ta mik'e dan cike take da bala'i ita ma, saida ya tsaya gabanta cikin halin ko in kula yace "Me ya had'aki da Aisha? Shin baki san 'yarki bace ita da zaki zauna d'aukarwa kanki raini a wurinta."
A gadarance ta yatsina fuska tace "Sanin haka yasa ni gaggauwar d'aukar matakin dakatar da rainin da take son d'ora min saboda na tuna mata ni ma uwarta ce."
K'ank'ance idonshi yayi yana kallonta da mamaki yace "Shiyasa kika d'aga hannu kika mareta?"
Rumgume hannaye tayi a k'irji tace "E, saboda ta raina min yan uwa, ni kuma ba kowane raini nake d'auka ba."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Na ji to kiyi hak'uri, Aisha ba zata sake miki rashin kunya ba na miki wannan alk'awarin."
Shiru tayi tana wani kumbura baki ba tace komai ba, matsawa yayi kusanta ya rumgumota jikinshi yace "To saki fuskar mana, ko sai na had'aki da aljanuna?"
Da sauri ta saki hannayenta daga rumgumesu da tayi a k'irjinta tana dariya tace "A'a Abdul karka kirasu."
Dariya yayi shi ma ya rad'a mata a kunne "Ko ke fa, bana so irin wannan hatsaniyar na d'aga min hankali a gidan nan, kamata yayi ki nuna musu ke ma fa gyatumarsu ce."
Dariya ta k'yalk'yale da ita ta d'aga k'afafunta sosai ta rad'a masa a kunne cewa "Shiyasa nake so na kama girmana, dan ni d'in ba matar yaro bace."
Dariya yayi ya bata hannu alamar su bige yana fad'in "Gaskiya ne matar old man."
Farin cikonsu suka ci gaba da yi kamar babu abinda ya so faruwa yanzun. Saidai a daren bayan fitar sheikh da su Heezam zuwa masallaci, Hafsat da Aisha basu fito cin abinci ba, Mimi kuma bata damu ba hasalima ita ma tana b'angarenta, sai kusan 10:54 na dare suka dawo gidan, da kan ta ta zubawa su Aswan abinci suka ci sannan ta d'iba ta kai wa sheikh falonta shi ma ya ci.
Saida kowa yayi bacci a gidan baka jin komai sai k'arar panka da ac, a lokacin sheikh ya mik'e ya nufi d'akin Aisha, cikin nutsuwa ba tare da tunanin komai ba ya bud'a k'ofar d'akin, ganinta kwance akan gadon tana bacci a nutse ba k'aramar salama ya sama mishi a zuciya ba, dan sosai yake tsoron zamanin nan da mutanen cikinshi, k'arasawa yayi gaban gadonta ya tsaya ya daddab'ata, cikin magagi ta bud'a ido ganinshi yasa ta yin zunbur ta tashi zaune tace Abie?"
Yanda ya tsaya gabanta k'ik'am yasa ta sauka daga kan gadon tana lalubar hijabinta kan gadon, sakawa tayi ta b'oye rigar baccinta tana zaunawa k'asa.
Zaune yayi bakin gadon ya had'e hannayenshi yana kallonta, saida ya gama mata kallon tas kafin ya d'aga hannunshi ya kwad'a mata mari, a gigice a rikice ta dafe kunci tana sakin k'ara.
Kallonshi tayi tana sako hawaye inda shi kuma ya nunata da yatsa cikin taushin murya yace "Wannan marin dana miki tun ranar da kika ma Mimi rashin kunya da safe ya dace na miki shi, ya kamata ki sani ita ma uwarki tunda ni ke aurenta, darajar aure ya siya mata darajar da zaki kalleta kamar uwa, addininmu ya koya mana yanda zamu mutumta d'an adam ko baka san shi ba bare wanda kake da alak'a dashi."
Kama kunnenta yayi a cikin hijabin cikin sigar fad'a yace "Aisha har na zauna na nuna ga yanda za'ayi saboda gudun matsala amma ke ki nuna ba haka, da kika ma yan uwanta fitsara me kike so ki nuna musu kenan? Ke *tantiriyar gidana ce*? Haka kawai zaki tarwatsa min farin ciki da zaman lafiyar gida, tunda kike kik tab'a ganin b'acin ran mahaifiyarki a zahiri? Ko kin tab'a ganin ta kalli idona ta fad'a min abinda ke ranta kai tsaye? Sai yau kuma duk a dalilinki."
Jinjina kai yayi sanda take neman tashi daga zaunen tana rik'e kunnenta tana fad'in "Abie zafi zafi, kayi hak'uri na tuba wallahi."
Mik'ewa yayi ya sake nunata da yatsa yace "D'aurin aurenki ba fashi Aisha ranar juma'a, ko ki shirya ma hakan ko karki shirya duk d'aya, amma ki sani kin fara sani tunanin ko dai kin san me aure yake nufi shiyasa kike kishi da wata wacce kike ganin ita ma ta rab'i jikin ubanki, to koma a ya ya dai kika d'auka ki sani hakan ne."
Yana fad'a ya wuce ya barta nan tana wani kukan tare da gyara zamanta a k'asan ta had'a kai da gwiwa.
Daren yau ma sheikh ya so ratsa gonar Mimi amma ta buga kai k'asa tace bata warke ba, dole ya hak'ura ya d'anyi wasa da ita kamar dai jiya sannan yayi wanka ya shiga karatun Qur'ani.
*Da* safe ma haka yara suka shirya suka fito, saidai Aisha kai tsaye ta wuce farfajiya sai su Aswan