Showing 72001 words to 75000 words out of 185502 words

Chapter 25 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

486

Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif.

Kecup! Suka ji k'arar waya tare da hasken daya d'auke idonsu, da sauri suka kalleshi sai kuma kunya ta kamata ta sunkuyar da kai, murmushi yayi yace "Maah kin ga yanda kika had'u? Har saida na ji gabana ya fad'i tsabar razana."

A hankali ta d'ago matsakaitan idonta da suka sha eyeshadow a tausashe kamar mai rad'a tace "Me yasa gabanka ya fad'i?"

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Sadeeq yace "Saboda ganin kamar *matar manya* na d'auka, bana so na zama tururuwa uwar jaye-jaye."

A sauk'ak'e ta kalleshi tace "Wannan maganar kamar dani kake, kar kasa na ji ba dad'i mana."

Sunkuyar da kanta ta sake yi shi kuma ya kalli Sadeeq dake fad'in "Ba wannan ba ma abokina, na ga amaryar ta mu kamar jinin sarauta, dan Allah daga wace masauratar take?"

Yar dariya tayi cikin sanyayyar murya tace "Ni ba yar masarauta bace, hasalima ko gidan sarauta ban tab'a shiga ba daidai da gaisuwa, idonku ne kawai suke yaudararku."

Dariya sukayi sai Asma'u data rik'o hannunta tace "Mimi gaskiya ya fad'a, jininki da zubi na tsarin yanayinki kamar na wacce aka haifa a cikin masarauta ne."

Murmushi Asas yayi yace "Kin gani, k'awarki ma haka take gani, amma ba komai karki damu, gaba kad'an zan mayar dake kamar sarauniya."

Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta sosai, Asma'u ma dariya tayi tace "Allah yasa."

"Ameen." Ya fad'a yana gyara zamanshi, Sadeeq ne ya saci kallonta ta madubi yace "Ke ma da zaki bada dama ai gaban kad'an sai a mayar dake sarauniyar."

Dariya Mimi tayi tana sinne kanta wani dad'i na ratsata Asma'unta zata samu babban yaro, Asma'u kuma cike da zolaya tace "Wa zai mayar dani sarauniya bayan bana da suffar ko gimbiya?"

Dariya yayi yace "Gani, Allah da gaske nake Asma'u."

Kallon Asas yayi yace "Abokina fad'a mata mana."

Hararanshi yayi yace "Rainin hankali, ban tabbatar dana rik'e tawa a hannu ba zan zauna tayaka jefa k'uri'a? Kowa ya ji da kansa."

Da mamaki ya kalleshi yace "Au! Hakane kenan?"

"Eh d'in." Ya fad'a yana d'auke kai, jinjina kai yayi yace "Ba komai zan rama."

Sake kallon Asma'u yayi ta madubi yace "Asma'u kinji ko? Dan Allah ki bashi kunya mana ta hanyar amince min."

Kunya ce tasa ta sadda kanta k'asa tana wasa da yar wayarta a hannu, jin shiru yasa shi sake marairaicewa yace "Dan Allah *Asma'ul Husna* ki amince min kar na zauce."

D'aga kai tayi ta kalleshi da mamaki, ita ina zata kai babban yaro haka kamar Sadeeq? Bata tab'a saurayin daya taka ko da matakala ta farko na a b'angaren aji bare hawa na uku, ita kam ya zata ce mishu ne yanzu? Tabbas tunda suka san juna yake nuna mata kulawarshi da abubuwa masu wuyar fassara, ta d'auka mutumci ne kawai ashe abinda ke ransa kenan?

Mimi ce ta d'an tsamiketa a cinya hakan yasa ta fad'in "Washhhh!" Da sauri ta kama bakinta tana kallonta, da ido Mimi ta mata alamar ki amince mana, ita kuma ta mata alamar ni a wa? D'an tsaki tayi tare da yin kamar zata daketa, hakan yasa Asma'u jinjina kai tace "To zanyi tunani ko?"

Cikin murmushi Sadeeq yace "Ba matsala, zan jiraki har kiyi tunanin."

Bud'e baki sukayi da mamakin ashe ya ji me ta ce, da hirar raha da nishad'i har suka isa katafaren gidan daya had'u sosai aka k'watashi saboda hidimar da za'ayi.

Tabbas gidan ya cika mak'il da mata manya da yara ga kuma yan mata, saidai maganar gaskiya sun zo ne ganin zahiri da idonsu, tabbas su d'in ahali ne masu ilimi da sani sosai, amma fa suna da wani abu da saika rantse gidan jahilai ne, maganar talaucin gidansu Mimi a yanzu ba shine gabansu ba kamar da aka fad'a musu su waye iyayenta, sai suka zo tabbatarwa da tambayar kansu dame yarinyar tafi na su yaran da dayawa daga ciki aka so had'a Asas dasu amma ya k'i. Yan matan kansu suna so suga yarinyar ne dan su mata kallon hadarin kaji idan da hali ma har su yaga mata rigar mutumcinta.

Ai kuwa yamma na k'ara yin sanyi sai ga motocin angaye sun aje dangin Mimi, yanda suka fara shigowa harabar d'aya bayan d'aya yasa duk akaa kafesu da ido, su Shapi'a ne a gaba suka fara shigowa, hakan yasa wani gungu na 'yan mata kecewa da dariya ganinsu dunk'ul dunk'ul kamar yara amma kuma da fuskar dattijai, ajiyar zuciya Sahura ta sauke tace "Allah gamu gareka, nagode Allah da Mimi bata wurin nan da anyi b'atacciya."

Shapi'a ce tace "Ni kam fatana yanzu ta zo dan naga yanda zata ci uwar yarinya idan aka nemi wulak'anta mu."

Ido Sahura ta zaro tace "Rufa mana aisri Shapi'a, kai tsaye fa zata ce ta fasa auren d'an uwan nasu."

Cike da rashin dana sani Shapi'a tace "Idan tayi haka ma ai sai ta birgemu, wannan ai rashin sanin darajar d'an adam ne kamar ba gadon ilimi Sharif ya bar musu ba."

Murmushi Sahura tayi tace "Ya bar musu gadon ilimi, amma yayanshi kuma sun bar musu gadon dukiya, hakan ya jawo dayawa daga ciki dukiyar ce tafi aiki a tunaninsu."

Tab'e baki tayi tace "Allah ya kyauta musu."

Dogaye da gajeru ne suma haka duk suka samu wuri suka zauna ana d'an gaggaisawa sama sama, hakan ya jawo kowa ware nashi ya koma gefe ana k'us-k'us-k'us, tubarkallah farfajiyar ta cika har kujeru na neman yin k'aranci duk yawansu, dan kuwa kafatanin ahalin Sharif duk sun hallara, kama daga iyalin Aliyu Sharif, Usman Sharif, Salmanu Sharif da sauran abokan arzik'i, sosai Hafsat ke k'ok'arin ganin an samu sanayya da kuma fahimtar juna tsakanin danginsu da dangin Mimi, hakan yasa take ta nunawa iyayensu su Shapi'a a matsayin iyayen Mimi, wasu suna sakin jiki su karb'esu a gaisa, wasu kuma gaba da gaba suke yatsina fuska suna musu yak'e, hakan bai ma Hafsat dad'i ba amma ya ta iya, sharesu tayi ita ma tana fama da cikinta da wunin yau ta ji bai motsa mata ba ga wata muguwar kasala, jefi-jefi kuma sai taji gabanta ya fad'i kawai ba dalili, saidai bata bar ambaton ubangiji ba a bakinta da haka take jin sanyi sanyi a ranta.


Sanda motocinsu suka tsaya angayen ne suka fara fitowa suna shigowa filin, sai k'awayen Mimi da suka jera gwanin sha'awa suka sakata tsakiya tare da Asas dake ta doka murmushi, Mimi kan kanta na k'asa tana fama da rik'e jakar hannunta rigarta kuma na jan k'asa.

Kowa sake waro idanu yayi dan tabbatarwa kanshi abinda yake gani, dangin Mimi da dama sun san kayansu ba daga nan ba indai wajen d'aukar wanka ne da iya gayu, saidai yanda ta zama tamkar wata balarabiya ya k'ara birgesu da kashesu a game da ita.

Inda yan matan nan kuma suka shiga tamtama wai dama haka yarinyar take, sam babu wata makusa a tare da ita da zasu kushe, duk da kwalliya tana canza hallitar mace ta gyarata amma dai sun tabbatar zata yi kyau, na farko tana da dogon hanci ga ta jar fata, su kam idan aka barsu sai su ce wata baralabiya ce, duk sai suka kasa motsawa a wurin dan kwarjini ma suka ji tayi musu yarinyar, sai yan matan amaryar ne da angaye da suka dage suna ta d'aukarsu hotuna, da haka aka isar da Mimi kan kujerarta sai su Asas da suka bar wurin dan dama fa anyi ba dasu za'a yi hidimar ba.

A cikin taron yan matan nan akwai guda d'aya wacce ita ba fa abinda ya kawo kowa ya kawota ba, na ta k'udirin babba ne daya girmi na kowa dan kuwa sak'on Muttak'a ta zo isarwa, tasan kasada zatayi amma kud'in daya bata tare da yi mata alk'awarin aure yasa ta ji zata iya yin koma menene, tun shigowarsu Mimi ta mik'e ta shige zak'ewa akan komai tana kamkamba kamar wata yar uwa. Dangin Mimi kallonta suke yanda rawar kanta yayi yawa suna tunanin wata yar uwace makusanciya ta Asas. Inda suma dangin Asas suke kallonta wata marar hankali daga b'angaren Mimi take, da wannan kallon da duka kusurwoyin ke mata aka kasa samun wanda zaiyi mata maganar shishigewa da take musamman ta b'aangaren abinci.

Magriba na gabatowa Hafsat ta gabatar da masu ruwa da tsaki ayi kamun amaryar, ana idawa Hafsat tasa Aisha da su Fanna suka kawo cake dan ta yanka tunda ba wani abun ci aka ware mata ba ita, da taimakon Asma'u ta yanka Asma'u ta d'an saka mata a baki aka musu tapi ana dariya, *Feena* ita tayi babakere ta d'auki lemu ta tsiyaya a cup na glas, a hannunta dama akwai k'aramar k'waya babu wanda ya kula da tsiyarta bare ya lura har ta saka, mik'awa Asma'u tayi ita kuma ta mik'awa Mimi, amsa tayi ta d'an kurb'a zata aje Feena ta sake fad'in "Ki k'ara mana, ko ruwa baki sha ba fa."

Dayawa kallonta sukayi sai Mimi da take kallonta a matsayin dangin wanda zata aura, wannan kunyar tasa ta d'an k'ara kurb'awa kafin ta aje, Feena kam murmushi tayi duk da bata ji dad'i ba da bata sha sosai ba, amma dai tunda Muttak'a ya bata tabbacin guba ce mai had'ari sauta share kawai, a hankali ba tare da lurar kowa ba tayi kamar tana amsa waya ta fita a wurin.

Ana kwad'a kiran sallah magriba su Asas na dawowa d'aukar amarya, Hafsat ce ta rik'e hannunta sa茂 Asma'u a gefenta sauran yan mata a gaba wasu a baya suka nufi hanyar fita, Mimi dake jin matsanancin murd'awar ciki da jin kamar an rik'e mata numfashi ba tare da ankarewar kowa ba ta tafi baya luuuu! Ta fad'i a wurin, da sauri Hafsat ta kalleta tare da sakin hannunta tana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Mimi."

Asma'u ma da sauri ta durk'ushe tana kiran "Mimi, Mimi lafiya."

Take aka rufe wurin ana tambayar lafiya, cikin tashin hankali Hafsat ta d'ago kanta ta kalli Aisha tace "Eesha kira Asas a waje."

Mayar da kallonta tayi kan Mimi, a hankali ta lura da jinin daya fara b'ullowa ta hancinta, cikin tsananin tashin hankalin da take jin bata tab'a riska ba ta daure ta d'ora hannu a kai tace "Na shiga uku, me ya sameta?"

Da gudu Asas ya shigo tare da rakiyar zaratan mazan a bayanshi, suna zuwa suka bud'a musu hanya, da sauri ya durk'usa yana fad'in "Me ya sameta? Me aka mata?"

Shapi'a ce tace "Ba abinda aka mata, ni fa ina ganin ko mayya ce ta kamata a wurin nan?"

Dayawa daga cikin mutanen suka kalleta sai wata mace mai aji sosai da tace "Nan ciki akwai wanda ya miki kama da maye ne?"

Hafsat ce tace "Bana tunanin haka, mu kaita asibiti jini ne yake fita a hancinta fa."

Wata dattijuwa ce tace "To ko tana da iska ne?"

A sukwane Asas ya mik'e tsaye tare da tattara k'arfinshi ya d'auki Mimi cak ya fita da ita da gudu, duk rufa masa baya akayi hankali tashe da tunanin miye zai faru, yana sakata mota yaja da gudun tsiya zuwa asibitin sheikh data fi kusa dasu har da ma gidanshi duk yana kusa da masaukin bak'in na shi, duk tarin tilin motocin dake wurin kad'an ne suka bi su zuwa asibiti dan su san halin da take ciki.




*Gobe d'aurin aure fa*馃榿



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:55 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*25*



Sanda suka samu aka amsheta da gaggawa ganin iyalen sheikh, a lokacin wasu suka sake taso da maganar ana bibbikawa, inda Asas ya d'ora hannu d'aya a kai yana amsa kiran Hajia da labari ya risketa, cike da tsananin damuwa ya marairaice yace "Hajia ni ma ban sani ba, sun ce wai fad'uwa tayi suma basu sani ba."

Hankali tashe Hajia tace "To ko dai tana da aljanu ne?"

Saida ya d'an juyo yana kallon mutanen dake bayanshi yace "Hajia na tabbata ma bata da su, ban tab'a ganin alamunsu a gareta ba, kuma fa har sheikh sun had'u da shi amma babu abinda ya sameta, kuma kinfi kowa sanin baiwar da Allah ya masa."

Cikin son kwantar masa da hankali tace "To kaga yanzu dai ka zauna kusa dasu, sannan kar muyi saurin barin labarin ya fita tunda babu tabbacin me ke damunta."

A sanyaye yace "To Hajia, Hajiata."

Yanda ya kirata yasata cewa "Na'am autana."

Kamar zai fashe da kuka yace "Hajia ina tsoron ta mutu."

Da sauri tace "A'a autana, insha'Allahu babu abinda zai sameta, zata tashi da yardar Allah."

A hankali yace "Allah yasa Hajia." Da "Ameen." Ta amsa mishi ta yanke kiran.

Asma'u ma kiran Abban Mimi ne take amsawa da yaga magriba ta wuce basu dawo gida ba, gashi yana tsananin son ta had'u da dangin malam wanda suka yi niyya sa茂 gasu kwatsam sun shigo da yamma, sunyi farin ciki sosai na ganinsu amma gashi amaryar bata dawo ba, hankali tashe cikin kuka Asma'u ke fad'in "Abba muna asibiti, Mimi ce kawai ta fad'i jini na fita a hancinta, Abba kar na rasa k'awata ni ma mutuwa zanyi Abba."

Duk zuba mata ido mutanen sukayi cike da tausayinta da jin lallai ita d'in k'awa ce ta gari, Sadeeq kam ji yake kamar ya rumgumeta a jikinshi tsabar tausayi, cikin kid'ima Abba ya amsa da "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, hasbunallahu wani'imal wakil! Mimi kuma? Me ya sameta to? To gani nan tafe yanzu wace asibiti ce."

Cikin kuka tace " *Annur*." Ta fad'a a k'asan mak'oshi, k'it Abba ya datse kiran yana waige waige ya ma rasa ta ina zai bi, Abban Asma'u dake tare dashi ne ya tambayasa lafiya? Yana fad'a masa ya tashi motonta yace su tafi, zasu tafi kuma malam na fito a gidan dan tunda yayi sallah magriba yake tare da yan uwanshi da yake jin kamar ya goyasu, malam ma cewa yayi zai tafi hakan yasa mutan ciki basu san me ke faruwa ba malam ma ya samu taxi ya bi bayansu suka d'unguma asibiti.

Saminu ma tunda Maimuna ta fad'a mishi halin da ake ciki yace zai je idan komai da sauk'i saiya d'aukota su dawo gida. Hafsat ma haka hankali tashe tana sanyayyan kuka ta rud'e sosai take fad'awa sheikh "Wallahi sheikh bansan me ya faru da ita ba, kawai gird'ewa tayi ta fad'i shikenan fa sai jini a hancinta, ni na shiga uku sheikh ya zanyi idan wani abu ya sameta? Ni na je har gidansu na nemi izinin a barta fita a ranar nan, wayyo Allah na!"

Ta k'arashe tana sake fashewa da kuka, daddab'a kafad'arta Aisha tayi tana kallon mahaifiyarta da tausayawa, daga b'angarenshi kam jim yayi kamar ba zaiyi magana ba sai ma istigfari daya fara ambata a bakinshi, can sai kuma ya bud'a baki da k'yar yace "Su wa suka je taron? Me ta ci? Wa ya bata wani abu ta ci a wurin?"

Cikin kuka tace "Babu wani abu da ta ci sai d'an cake kawai da lemu, dukansu bata musu wani cin da zasu isa cikin cikinta ba."

Lumshe ido yayi ya ja numfashi, a sanyaye ya yanke kiran yana kallon matasan dake gabanshi, cikin dattako ya rufe littafin gabanshi yace "Zaku gafarce ni kad'an abokaina, kira ne na gaggawa daga ahali, suna buk'ata ta a asibiti yanzu, zamu d'ora karatunmu a sati mai zuwa insha'Allah."

Kallon wani matashin yayi dake gefen damanshi yace "Malam *Anas* ka kula mana da inda muka tsaya, zamu d'ora wani satin insha'Allah."

Cike da girmamawa da mutumtawa da ladabi ya sunkuya daga zaunen da yake yace "Insha'Allah sheikh, Allah ya tsare Allah ya sauk'ak'a lamura."

"Ameen ya Hayyu ya Qayyum." Ya fad'a yana mik'ewa tsaye, duk mik'ewa sukayi suma inda ya saka taklminshi k'afa ciki, rufa masa baya sukayi har ya fito inda masu tsaron lafiyarsa ma suka rufu a bayanshi, da sauri d'aya a cikinsu ya bud'e mishi inda zai zauna y'a shiga, da gudu suka ja motar suka bar harabar gidan gonar zuwa asibiti.


*Masha'Allah* duk da Mimi ba wasu babban ahali bane da sukayi suna, sai gashi a kad'an mutane a k'alla ashirin ne tsaye bakin d'akin da take ana ta jiran sakamako, saidai tun zuwan sheikh sai kallo ya koma kan shi, kwarjini da wani irin dattijantaka da dattijon had'a ga wani kyau da yayi a cikin fararen kayan da kuma kalar shud'i, wanda ko takalmin k'afarshi farare sai yar kwalliyar shud'i, shigar nan ce dai irin ta kullum babbar rigar malamai mai zubin alkyabba. Ya goya hannayenshi bayanshi a hankali yake d'an tattakawa dama yana tsaye a k'ofar shigowar ne, yanda yake tafiyar a hankali daga bango zuwa bango yana motsa yatsunshi alamar tasbihi, hailala, istigfari, tahmidi yake yi, sautin takalminshi dake fita wani gum gum gum ga fitinannen turarenshi daya had'e wurin duk sai aka zuba mishi ido.

Kallon Hafsat yake da take kuka tayi zaune da k'yar kan kujerar robar da Aisha ta samo mata, a hankali ya k'arasa gareta tare da yin tsuguno a gabanta ya rik'o hannunta, cikin taushi ba tare da duk wanda ke wurin yaji ba yace "Sawwama, kukan nan ya isa haka mana, ko kina so ki babbaka min zuciyata ne?"

Saida ta ja majina ta d'an girgiza kai alamar a'a, lusmhe ido yayi yace "To ya isa haka, karki sake kinji."

Jinjina kai tayi tare da had'e kukan tsaf kamar ba ita ba, sai yar shashek'ar da ba'a rasa ba. A hankali ya mik'e daga gabanta ya d'an karkato da niyyar juyowa, yanda ya samu ido a kan su ne ya dakatar dashi daga juyawar gaba d'aya, duka kallonsu suke da mamaki inda matan ke jin kamar su d'aukesu hotu su nunawa mazajensu dan ya zamar musu hujja, Alhaji Saminu kam kallon Aisha yake yana d'an lashe leb'enshi, dan gaba d'aya 'ya'yan sheikh irin jikin nan ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login