Showing 96001 words to 99000 words out of 185502 words

Chapter 33 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

513

ya dinga tayata k'awata burinta abin hamdala, amma gashi *tafiyar k'addara* ta sauya musu komai, cikin son danne abinda ke zuciyarta tace "Zan kashe waya, sai anjima, ki kula da kanki."

Da sauri Asma'u tace "Mimi."

Dakatawa tayi daga shirin kashe wayar, a hankali tace "Dan Allah ki nutsu kinji Mimi, na sanki farin sani fiye da kowa, kar ki sake yin abinda zai sa wani ko wata ya zargeki."

Marairaicewa tayi alamar rarrashi tace "Dan Allah kinji."

A sanyaye Mimi tace "Insha'Allah Asma'u, nagode."

Murmushi tayi kamar tan agabanta tace "Sai mun had'u kinji, wata rana zan zo na ganki."

Jinjina kai tayi tace "Shikenan, Allah ya yarda."

Kashe kiran sukayi inda Asma'u ta aje wayar, fita tayi ta koma falon ta sameshi yana tsakurar abincin, saidai kallo d'aya ta masa ta fahimci hankalinshi a tashe yake kamar akwai abinda ya shiga tunani har ya b'ata masa rai, sai kuma ta tuna wayar data fara gabanshi, hakan yasa ta tunnin ita ce silar b'acin ran nashi, a sanyaye ta zauna tana satar kallonshi, ganin yanda yake cin abinci kuma fuskarshi kamar zata tab'ashi ya fashe da kuka yasa ta cewa "Lafiya ko?"

Kallonta yayi lokaci d'aya kuma ya d'auke kanshi yace "Ba komai."

Ture plat d'in yayi ya mik'e yace "Ni zan fita, saina dawo."

Da sauri ta mik'e tsaye tana fad'in "Amma yau k'awaye na sun zo zasu zo min wuni."

Dakatawa yayi yana kallonta yace "To, da wani abun da kike buk'ata ne?"

Girgiza kai tayi tana sunkuyar da kai tace "A'a ba komai, dama na fad'a maka ne dan ka sani."

Lumshe ido yayi alamar shikenan, juyawa ya sak茅 yi zai fita tace "A dawo lafiya, Allah ya tsare."

"Ameen." Ya amsa yana ficewa a falon, saida ta ga fitarsa a gidan sanda mai gadi ke mayar da k'ofar yana rufewa kafin ta zauna ta k'arasa abincinta, tana idawa ta tattare kwanukan ta kai madafa ta dawo falon ta zauna dan ba shara bare goge goge da zatayi, kallo ta shiga yi a tsanake tana canja tashar da take so ga sanyin ac na ratsata ga kuma sanyayyan lemun data aje, lallai Allah kai ne Allah, wacce ta tashi a gidan mutane dayawa, dan a kad'an mutanen gidansu zasu kai ashirin da biyar idan lissafasu za'ayi, a haka fa dan akwai mata masu aure ga maza da ba zaman gidan suke ba. Yau gata a k'aton gida ita d'aya tana yanda take so, lallai tarayarta da Mimi alkairice a gareta dama danginta.


12:02 su Salma suka diro gidan, da murna ta fito daga madafa tana fad'in "Marasa mutumci, shi ne sai yau aka ga damar zuwa?"

Dariya suka saka sai Jamila data k'are mata kallo tace "Kinji wata tsifa kuma, ba shekaran jiya ne muka kawoki gidan ba."

Salma ce ta cire mayafinta tace "Rabu da ita, me take so muzo muyi a jiya? Mu zo cin kaza ko kuma gasa mata jiki?"

Dariya suka sake shek'ewa da ita Asma'u kula tab'e baki tayi tace "Ku zauna dan Allah ni bana son iskanci."

Juyawa tayi zata d'auko musu ruwa Ruky tace "Asma'u wai me mijin nan naki ya baki ne har kin fara sauyawa haka?"

Dungureta Salma tayi tace "Dan uwarki duk wanda aka kawo a wannan aljannar zai k'i canzawa ne? Ai sai marar rabo duniya da lahira."

Wata dariyar sukayi har da Asma'u data kawo musu lemu da ruwa, d'auka duk sukayi suka fara jik'a mak'oshinsu, zaune tayi tana kallonsu tace "Amma daga nan zaku je ku gano min k'awata ko?"

Da sauri Salma tace "Wa? Wai Mimi kike nufi?" Cikin d'aga murya ta tapa hannaye ta shiga fad'in "Ai Mimi zuwa na musaamman zan mata, ba dai ni ta dinga wa dariya zan auri tsoho ba mai k'aton ciki, wallahi idan na je gidan sai nayi dariya kamar cikina zai k'ulle, ke k'arshe ma saina kwaso mata shoki wallahi."

Tsaki Asma'u tayi tace "Ramawa zakiyi kenan? Amma dai kinsan mijinki yafi nata tsufa."

Da k'arfi Salma tace "K'arya ce wallahi, shekarun sheikh sun fi na mijina."

Ruky ce ta kai mata duka tace "Shegiya wai mijinta, yaushe aka d'aura muku auren?"

Hararanta tayi tace "Ke kauce dallah."

Jamila ce tace "Maganar gaskiya fa Salma karki fara, dan in gaskiya za a bi ko sheikh ya girmi Alhajinki amma sheikh ya fi shi kyawun jiki."

Ruky ce ta tintsere da dariya tace "Ai ko a majigi kika ga sheikh kinsan tsohon duniya ne wallahi, ke karfa kiyi mamakin idan yana d'aga k'arfe, dan a kujerar nan idan ya zaune haka zaki ga kafad'unshi a bud'e."

Jamila ma dake dariya cewa tayi "Ai shiyasa ni nace wallahi da ya so ni da gudu zan aureshi."

"Sai kuma ya zamaa rabon Mimi ba." Cewar Asma'u tana hararenta, Salma ce tace "Ko ma dai menene mijinta ya fi nawa tsufa, kuma sai na rama duk tsiyar data min wallahi."

Tab'e baki Asma'u tayi tace "Allah ya shiryaku to, ni na matsu ku shiga hannun wad'anan dattijan arzik'i ko sun bambamce muku zare da abawa."

Cike da salon shak'iyanci na yan mata suka saka mata dariya Salma na fad'in "Su Asma'u manya, wato har an shiga daga ciki ko? Da alama dai jarumi Asas ya gama aiki."

Girgiza kai tayi tace "Har yanzu babu wannan tunanin a tare damu, ba anan kusa ba b芒 kuma lokaci."

Kallonta sukayi kafin Ruky tace "Uhum! Ke dai bari muga kun shanye wannan satin tukuna, namiji da kinibibi ke kuma mace san kowa k'in wanda ya rasa."

Jamila ce tace "Ai tsaf zai manta da wata Mimi ya kwashi garar Asma'u."

Dariya sukayi sai Asma'u data girgiza kai tace "Ku wallahi baku da kunya."

Mik'ewa tayi tana fad'in "Bari na kawo muku abinci."

Da kallo suka bita har ta shige, da sauri Jamila ta kallesu tace "Ke ki dubi daula ki gani, wa ya san Asma'u zata auri mai kud'i? Ita da ko saurayin kirki bata da."

Ruky ce tace "Allah ya kareta daga sharrin tarikitan samarin ne saboda mijinta bai bayyana ba."

Salma kam cewa tayi "Ni ba wannan ba, wai yanzu ya zasu rayu ne suna auren yan uwan juna ita da Mimi bayan kuma abinda ya faru ranar auren nan?"

Cikin rad'a Jamila tace "Bari kedai, nima abinda na fi tunaani kenan, kuma fa har yanzu da alama k'awancensu na nan, kuna ganin hakan ba zai shafi alak'arsu ba?"

Ruky ce tace "Da zai shafi alak'arsu daya tab'a tun ranar, mazan dai na fi jiye ma, kinsan maza sun fimu rik'o fa, kar a zo tafiya tayi tafiya Asas ya kasa cireta a zuciyarshi."

Salma ce tace "Ai shi d'in ne, baiwar Allah kuma fa zata fuskanci matsi idan haka ta faru."

"Gaskiya kam." Cewar Ruky, jin fitowar Asma'u yasa Jamila saurin fad'in "Daga nan dai muyi k'ok'ari muje wajen Mimi, ina so naga tab'ara da iya hege."

Dariya sukayi har da Asma'u data fito tana fad'in "Ta daina ma na sani, babu abinda zaki gani Jamila."

Salma ce tace "Wacece? Mimin? Ai kuwa dana tsine mata, yo a zaman da zatayi gidan nan idan bata kafawa sheikh tarihi ba ai bata cika Mimin dana sani ba."

Ruky ce tace "Gaskiya kam, ko wajen iya d'aukar wanka ai Mimi zata rikita gafarta malam."

Tintserewa sukayi da dariya sai Salma da tace "Sai ma ta gifta ta gabanshi tana sittin saba'in."

Cikin dariyar mugunta Asma'u ma dake rik'e ciki tace "Wata rana kam zamu ga yayanmu babu hula a kai."

Da ire-iren hirar nan suka shiga cin abinci ana tapawa ana shewa, sosai suke nishad'i inda Asma'u ma ta ji dad'in zuwan nasu sosai duk da tana bak'i lokaci lokaci daga danginta zuwa mak'wabta, sai daf da magriba suka bar gidan dan girki ma su suka tayata yin shi ta gyara gidanta tsaf kafin suka tafi bayan sun karb'i lambar Mimi wacce ta kirata d'azu da cewa zasu kira su saka ranar da zasu tafi gidanta duk da bata tare ba.


*Mimi*


Tunda ta samu wayar nan ta shige d'aki ta shiga latse-latse, a k'arshe dai da taga wayar an loda mata kud'i sai kawai ta shiga yanar gizo, a take ta bud'e WhastApp duk da bata da lambar kowa, haka ta shiga man-hajar videmate ta dinga d'auko wak'ok'i na hausa na kallo dana saurare, kiran sallah azahar kawai ya tasheta a wurin tayi sallah kafin ta fito falo, ta samu Hajia na d'aki sallah sai kawai tayi zaune ta k'urawa tvn ido wacce ita dai ta fahimci kamar tasha d'aya suke kallo kullum wato *sunna tv*.


Da yamma da kanta ta shiga madafar duk da har yanzu bakinta bai sake had'uwa dana Salamatu ba, haka ta shiga had'a abinda ranta ke so kamar yanda Hajia ta bata wannan damar, Salamatu dai na kallon ikon Allah, gata k'aramar yarinya mai jikin yan hutu, amma yanda take takawa tana wani motsa k'ugunta kamar da gayya, sai taji kamar yarinyar zata shiga ranta sai kuma tayi saurin tunawa kanta abokiyar gaba ce fa. 馃ゴ a banza indai uwata ce.

Daf da magriba suka kammala ta kai komai kan tebur ta shiga d'akinta dan yin sallah, saida ta idar da sallah kafin ta shiga wanka, tana fitowa ta zauna a gaban madubi, wani karsashi take ji tare da jin bari fa ta cire komai a ranta kar ta zama wata 'yar k'auye. A sauk'ak'e ta shiga linde fuskarta da hoda ta ruwa mai haske sosai kalar fatarta, kafin ta zana gira da kalar maroon data fito da fasalin fuskarta, saida ta fara shafa eyeshdow a saman idonta ta shafa mascara kafin ta shafa jan baki kalar maroon mai duhu sosai a sama sai k'asa data shafa lips sannan ta shiga fitar da tsarin labb'enta da wata hodar mai haske amma mai d'an k'yalli.

Mik'ewa tayi ta kalli kanta a madubi ta kanne ido d'aya dan ta birge kanta sosai, k'arasawa tayi gaban drower kayanta, wata fitinanniyar rigar shadda ta d'auka wacce tana d'aya daga cikin kayan da Asas ya fara aikata mata, d'inkin ya bala'in haukata ta yayi kyau sosai, yanda kalar fatarta take sai kalar kore mai duhu, tsaye tayi gaban madubi kamar wasan yara ta laulaya d'an kwallin, a yanda tayi d'aurin zaka rantse kawai tayi ne dan babu yanda zatayi, amma ko da ta ja shi baya ya fito mata da goshinta tare da fito da gashinta a gaba, a baya ma ta fito da jelar gashinta sai yayi wani irin kyau kamar zama akayi na musamman aka d'aura.

Wayarta ta d'auka ta fita ko wuk'a aka d'ora maka zaka iya rantsewa matar wani shugaban k'asa ce dan wani d'aukar ido tayi wal wal wal, Hajia ta samu a falo tana kallon tv da kuma wayarta a hannu saidai da alamar damuwa a tare da ita, ganin Mimi ne yasa ta sakin baki tana kallonta, ajiyar zuciya ta sauke tare da tuna yanda Asas ke fad'a mata yana son mace yar gayu da iya ado, murmushi ta mata tana fad'in "Takwarata kin fito?"

Murmushi tayi ita ma tace "Barka da hutawa."

"Barka." Ta fad'a tana sake kallon komai na jikinta, a gaskiya ba dan taga gidansu ba sai tace ba daga nan ta fito ba, cikin fara'a tace "Yau fa kinsha aiki, dan na ga abinci jere akan table."

Murmushi kawai tayi tana sunkuyar da kan ta, cikin zolaya Hajia tace "Sai nayi tunanin ko cheif ce ke a wajen iya girki."

Da sauri tace "A'a Hajia, karambani ne kawai da sa kai, a wayar k'awaye na nake gani dama ko kuma a YouTube."

Da fara'a tace "Masha'Allah, ai karambanin mai kyau ne."

Cikin ladabi Mimi tace "Zan d'an zagaya farfajiya ne."

Da murmushi tace "Ba komai, ki kula." Jinjina kai tayi tare da fita a hankali, tana fita kai tsaye wajen ajiye motoci ta nufa, mota biyu ce a pake a wurin, tsayawa tayi ta fara d'aukar hotuna masu kyau.

Bud'e k'ofar gidan da taji anyi yasa ta juyawa dan ganin mai shigowa, tana ganin motar sheikh da sauri ta lab'e bayan motocin tana fad'in "Old man an taho, wai me yake kawoshi gidan nan ne kullum?"

Kusa da motocin aka paka motar, tana hange taga wani mai bak'ak'en kaya ya bud'e mazaunin baya, a sanyaye ya fito cikin k'asaita da nutsuwa, tab'e baki tayi tana kallo ya rufe motar, zai fara takawa sai kuma ya tsaya tare da juyawa bayanshi kamar zai kalli inda take, da sauri ta sake lafewa tana dafe k'irjinta, sake juyowa yayi ya kalli jami'in yace "Ku jirani a nan."

Gyara tsayuwa yayi yana hard'ewa wuri d'aya da bak'in glas d'in shi, takawa ya shiga ta b'angaren da take hakan yasa Mimi hanjinta motsawa kamar zasu fito waje, rintse ido tayi sosai data tabbatar wajenta ya nufo, saidai tana mamakin yanda yasan tana nan, ai kam gabanta ya tsaya yana k'are mata kallo daga k'asa har sama.

Cikin dakakkiyar muryar shan k'amshi da b'acin rai yace "Me kike yi a nan?"

Bud'a ido tayi tar a kan fuskarshi sai kuma tayi k'asa da su, cikin rawar baki tace "Um..dama..na zo shan iska ne."

A gajarce yace "Shan iska?"

D'aga kai tayi alamar eh, takawa yayi d'aya biyu na uku ya kai daf da ita, ja baya tayi dan sai taji ta kamar gaban wani basamude, tsaf ya rufe da girman jikinshi da kuma manyan kayanshi, d'ora hannayenshi duka biyu yayi jikin motar data jingina, hakan ya haifar da k'wak'waran kusanci a tsakaninsu kamar zai rumgumeta, d'auke numfashi tayi tana kallon fuskarshi da yanayin tsoro da kuma sakarci, fuskarshi a had'e sosai yace " *Ke yanzu matata ce, ba kamar matar kowane gaja bace, suturtata jikinki da kama min kanki ya zama wajibi a gareki, wannan kwalliyar ni kawai ya dace ki wa, gashinki kuma kar na sake ganinshi a waje.*"

D'auke hannayenshi yayi tare da k'urawa fuskarta ido yace "K'amshin nan haramun ne ki sa ki fito waje, ke Ryam ba zan yarda hakk'inki ya kaini wuta ba, wallahi ki kiyayeni kinji na fad'a miki."

K'wafa yayi tare da ja baya yace "Kuma ki zauna a nan karki fito har sai na bar gidan nan."

Zaro ido tayi dan sai lokacin kawai ta farfad'o daga halin daya jefata, maganganunshi sun shigeta ta sama musu muhalli tare da tunanin abinda yake nufi. Yanda ta zaro ido yasa shi fad'in "Kin ji me na fad'a?"

Da sauri ta jinjina kai cikin tsoro tsoro da firgici tace "Na ji, amma kuma..."

"Amma me?" Ya fad'a yana binta da harara, girgiza kai tayi alamar ba komai, jinjina kai yayi yace "Magana ta dake mai yawa ce, zan tarasu ne har ki sameni gidana."

Kyab'e fuska tayi tana neman fashewa da kuka tace "Ni wallahi ba zan je ba, haka kawai a wani kai ni gidan..."

Da sauri ya kalleta yace "Gidan me?"

Girgiza kai tayi alamar ba komai, zaro lata ido yayi yace "Me na fad'a miki akan k'arya?"

Da sauri ta fashe da kuka tare da fad'in "Ai dama cewa ne zanyi gidan old man."

K'ank'ance idonshi yayi yana kallonta da mamaki, bakinta data turo tana zuba shagwab'arta yasa yatsu biyu ya cabkoshi, gam ya rik'e hakan ya haddasa mata sakin k'arar data shiga dodon kunnen wanda ke gidan a lokacin, hankali tashe ba tare da tunanin zata iya yin haka ba ya had'ata da motar tare da yin wuf da bakinta ya had'a da...




*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*32*



Hankali tashe ba tare da tunanin zata iya yin haka ba ya had'ata da motar tare da yin yuf da bakinta ya had'a da tafin hannunshi ya taushe, zazzaro ido tayi haka shi ma dake kallonta da mamaki, da gudu jami'an suka tunkaro wurin dan su lafiyar sheikh ce nauyinsu, kuma basu san shi da waye a wurin ba, daga d'aki ma Hajia fitowa tayi tana kallon Salamatu data rigata tace "Kamar ihun Mimi ko?"

Jiki na mata rawa tace "Ni ma haka na ji Hajia."

"Me ya sameta to?" Ta fad'a tana nufa farfajiyar gidan, yanda jami'an suka fad'o bayan motar d'aya har ya ciro bindigar da gwamnati ta basu tare da izinin harbi idan suka ga had'ari, juyowa yayi ya kallesu tare da sakin bakinta, babbaketa yayi yana kareta wai shi a dole kar su ganta, fuska a had'e sosai yace "Me ye?"

Cikin girmamawa d'ayan yace "Yallab'ai mun d'auka da had'ari ne."

"Ba komai, ku tafi." Ya fad'a yana sake wani ciccijewa, juyawa sukayi zasu tafi sai kuma ga Hajia da Salamatu apujajen, sake matsawa yayi nesa da ita yana k'wala mata harara, cikin tashin hankali Hajia ta shiga kallonshi tana fad'in "Sheikh lafiya? Naji ihun Mimi."

Matse bakinshi kawai yayi da sauri Mimi ta tafi da sauri ta isa kusa da Hajia, da kallo ya bi bayanta yanda take tafiyar da sauri, zuciyarshi ce ta tambayi "Anya yarinyar nan ke da k'ugun nan?"

Numfashi ya sauke a hankali yana kallon Hajia na share mata hawaye tana fad'in "Me ya sameki? Wani abu kika gani?"

Girgiza kai tayi cikin kuka tace "Shi ne ya tsoratani."

Kasa d'auke idonshi yayi a kan ta duk da kallon da Hajia ke masa tana fad'in "Sheikh wani abu ka mata?"

Sai kuma ta kalli Mimi tace "Ko dai wasa ne yake miki?"

Cikin shagwab'a ta kalleta ta turo baki tace "Hajia kina nufin wasar kaka da jika?"

Da sauri Hajia tayi saurin rufe bakinta a bayyane tace "Kai."

Salamatu ma ta zazzaro idonta waje tayi, shi kuma sheikh daga tsayen da yake duk irin yanda ya kai da b'acin ran masu tsaron nan nasa sun wani zo masa a wajen da bai dace su zo ba sai ya tsinci kansa da sakin k'ayataccen murmushi, lallai ma Ryam abun na ta yanzun ya fara d'agowa kamar so take ta hassala shi, so take kawai ta ringa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login