Showing 48001 words to 51000 words out of 185502 words
komai ta gani ba, yanzu ne zata yi kallo uya son ranta, mai gadi na bud'e musu suka shiga ciki, a gaban wata jibgegiyar reng rover bak'a ya tsayar da motar, a hankali ta shiga fitowa tana sake kallon girman gidan lai d'auke da tsaki da kyan gaske, wani irin iska ne ta gauraye gidan na shukoki mai sanyin gaske da saka bacci.
Gaisawa Asas yayi da jami'an sheikh dake jiranshi ya fito, gaba ya shiga ita kuma tana take masa baya tana kuma satar kallon gidan, suna zuwa k'ofar falon ta kalli kanta ta madubin dake k'ofar, tura k'ofar yayi daga ciki ya shiga, ita ma a hankali ta cire takalminta ta taka k'afarta akan pause pied d'in dake bakin k'ofar mai taushi kamar bargo, a sanyaye ta lumshe ido ta furta "Masha'Allah."
Falon akwai girma amma kuma an cikeshi da kujerun alfarma kujerun dake birgeta, wanda take da burin lallai in zatayi aure dole Abba ya siya mata royal, ga ni'imtaccen k'amshi da kuma sanyi dake fita, yaran da mahaifiyarsu duk zaune suke a nutse sai hira da suke k'asa k'asa.
Da farin ciki da kuma karramawa duk suka mik'e suka nufi Mimi yaran na fad'in "Aunty sannu da zuwa."
Hafsat kuma tana fad'in "Sannu da zuwa yar uwa."
Turo baki Asas yayi yana fad'in "Yau kuma a gidan nan babu wanda zai min lale?"
Murmushi Eesha tayi tace "Kayi hak'uri tonton, na yau dai ka barwa auntynmu wannan ranar."
Mayar da kallonta tayi kan Mimi tana jin ta samu k'awa tace "Aunty Mimi barka da zuwa."
Da murmushu tace "Anwuni lafiya."
Kama hannunta Eesha tayi suka zauna kan kujera, kallonta Hafsat tayi tace "To fa sarauniyar gwandagi, wato kin ga k'awa ko? To ai zaki kawo mata ruwa ko."
Mik'ewa tayi da murmushi ta nufi wata kusurwa, ita ma zaune tayi kusan Mimi tana fad'in "Mai sunan Mama ya gida?"
Sunkuyar da kanta tayi tace "Ina wuni."
Gaisawa sukayi sosai, su Aswane ma gaisheta sukayi ta amsa, a kadabce ta kama hannun Munzeer dake k'arami tana fad'in "Ya sunanka?"
A hankali yace "Munzeer."
Da fara'a tace "Masha'Allah, suna mai dad'i."
Shafa kan shi tayi sai Aswane da yace "Aunty ni baki tambayi sunana ba? Yafi na shi dad'i fa."
Dariya tayi tace "Ya sunanka?"
"Aswane." ya fad'a yana murmushi, girgiza kai Hafsat tayi tace "Allah ya shirya."
"Ameen." Mimi ta fad'a tana satar kallon matar mai matuk'ar dattako, gata cikin shirin doguwar riga ita ma abaya tayi tsaf duk da ba kwalliya ce a fuskarta ba, haka ma cikin jikinta ya mata kyau dan b芒 wani girma ne dashi ba. Muryar Asas ce ta dawo da ita daga kallon Hafsat yana fad'in "Wai ina shehi ne kuma ya shige? Nan fa yake ta zura min kira kamar zan sameshi a k'ofar gida yana jirana."
Dariya Hafsat tayi tana kallon Eesha data aje faranti a gaban Mimi tace "Nan yake zaune ma, yanzu ya shiga ciki amsa waya, da alama wani wurin zai je mai mahimmanci, dan na ji yana k'orafin ba zai fita da masu tsaron ba yau."
Murmushi Asas yayi yace "Ustaz kenan, shi fa idan tashi ne yayi ta tafiyarshi sakaka a gari."
Ita ma murmushin tayi tace "Ni kaina na fi son haka, duk abinda Allah ya rubuta zai faru ai shi ne zai faru, babu abinda zasu iya tare masa wanda aka rubuta zai same shi."
Jinjina kai duk sukayi sai Asas da yace "Duk da haka, kula da lafiyar yana da kyau."
Kallon Munzeer tayi tace "Munzeer, shiga librairie (labrary) kaga Abienka ya gama wayar."
Jinjina kai yayi tare da nufa kusurwar da zata sadashi da d'akin karatun sheikh d'in, zai bud'e k'ofar shi kuma ya bud'e ya fito bayan ya gama wayar, dama shi da Muddaseer ne da yake k'ara kwatanta mishi gidansu Ryam d'in shi, dan yanzu can zai nufa dan ganawa da iyayenta.
Sanyayyan k'amshin turarenshi mai matuk'ar tsada ne tr茅sor ya fara musu maraba, bud'add'en alkyabarshi irin ta malamai fara k'ar wacce ya d'ora akan farar shaddarshi mai k'yalli, fararen takalmi k'afa ciki da kuma farin hirami daya d'aure hular dake kanshi, siririn farin glas ya saka duk da bai cika sakawa ba, amma dake yau ranar ta musamman ce saiya saka.
Takowa yayi ba tare da ganin fuskarta ba dan ta bashi baya ne daga inda take, saidai yana kallonta yaji fad'uwar gaba tare da tsanantawa da gudun jinin jikinshi, fararen hannayenta masu kauri yake kallo da take shafar kan Munzeer.
Saida ya zo daf ita kusa da Hafsat ya tsaya, kafin kowa yace wani abu Asas yace "To malam ga amaryata dai na kawo maka."
Murmushi yayi tare da kallon fuskarta dake sunkuye, a lokacin Asas yace "Maah ga sheikh da nake baki labari."
A hankali, a ladabce kuma a nutse ta d'ago da innocent fuskarta, *ido biyu* sukayi k'uru k'uru suna kallon juna, dukansu babu wanda bai firgita ba haka kuma kowanensu ya kad'u. Da sauri tayi k'asa da kanta ta rintse ido sosai tana ambatar "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."
Saida ta maimaita sau uku, a take wata irin kunya da matsananciyar nadama ta rufeta a gurin, bata tab'a tsammanin haka zai faru da ita ba, ko a mafarki bata tab'a jin cewa zata iya hakaito haka ba, me kenan yake shirin faruwa da ita? Me ta aikata haka data tsinci kanta a wannan halin? Duk sanyin wurin saita samu kanta da jin wani irin gumi na tsatsafo mata, gashi komai na jikinta ya daina aiki hatta da jinin jikinta ma, ta kasa motsawa bare ta fita a guje ta bar gidan.
Sheikh kam da kanshi ke neman yin bindiga gaba d'aya saiya rasa me zaiyi tunani a kai, a dai lokacin kam babu ta yanda zai fara tunanin lamarin, sai kawai yayi k'arfin halin cewa "Sannu ko?"
Shiru Mimi tayi dan bakinta ya mata nauyi ta kasa furta komai, muryar Asas ce ta samar mata d'an k'wari k'wari yana fad'in "Sheikh gashi zaka fita, mu ma kuma tafiya zamuyi yanzu."
Da k'yar da sud'in goshi ya k'ak'aro murmushi yace "Hakane, amma ai zaku iya zama, da alama ma tafiyar ta fasu, dan dama zan je ganin wani muhimman bak'o, amma ganinku ya tuna min da wani abu."
Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi, sai kuma ta sunkuyar da kanta tana d'an ciza kakkauran leb'enta, wasu hawaye masu zafi na takaicin halin data samu kanta ciki kawai taji sun zubo mata, a hankali tasa bakin kallabin abayarta ta share cikin dubara.
Mik'ewa Asas yayi yana fad'in "Aunty Hassu, zamu wuce fa dan b芒 jimawa zamuyi ba dama."
Mik'ewa tayi tana fad'in "Da wuri haka? Amma dai zaka sake kawo min ita ta wuni ko?"
Murmushi yace "Gaki nan gata nan kuyi magana, idan ta amince ni mai sauk'i ne."
Kallonta Hafsat tayi ta matso kusanta sosai tace "Mimi zaki sake dawowa ko?"
Shiru tayi kanta a k'asa tana kuma jin yanda idanun sheikh ke yawo a kan ta, ta tabbata kallon mamaki yake mata da al'ajabi, ita kam ina zata saka kanta ne yanzu? Shikenan aurenta da Asas ya gama rugujewa, ta gama samun lasisin rabuwarsu kawai, kallonta Asas yayi yace "Maah."
A hankali ta kalleshi shi kanshi wata kunyarshi take ji, a sanyaye yace "Muje ko?"
Da ido ta amsa da "To." A hankali ta yunk'ura ta mik'e tsaye tare da Hafsat, Eesha ce tace "Gaskiya tonton ka sake kawo mana aunty, ko ruwa fa bata sha ba."
Murmushi ya mata yace "Ki shirya duk randa kike so saina kaiki wurinta."
Da farin ciki tace "Yawwa tonton nagode, zan tambayi Abie sai na je."
Kallon Eesha Hafsat tayi da ido ta mata alama, amsawa tayi tare da juyawa ta shiga d'akin uwar, jim kad'an ta fito da tsaraba ita ma ta mik'awa Asas tace "Tonton inji Mamie ka bawa aunty Mimi."
Karb'a yayi yana fad'in "Mutanen nan kirkinku kad'an ne fa, babu wanda ya tab'a bani wata leda sai yau da na zo da bak'uwa."
Hararanshi Hafsat tayi tace "Idan ka ji haushi mana ka daina zuwa kai kad'ai."
Hannu ya saka aljihu yana lalubar wayarshi dake k'ara yana fad'in "Dole ai, daga yanzu tare zamu dinga zuwa."
D'ora wayar yayi a kunne, daga yanda ya amsa wayar zaka san wani abu ya faru na tashin hankali, hakan yasa yana kashe wayar hankali a tashe ya juyo ya kalli Mimi yace "Mimi akwai matsala, masu min gyara gida ne wallahi wani wai ya samu mummunan rauni, zan wuce asibitin ne yanzu na ganshi, zaki bini muje?"
Sak'e tayi tare da tuna maganar Abbanta, a haankali ta girgiza kai da k'yar a karo na farko tun bayan fitowar sheikh tace "Gaskiya Abba ya hana, yace na koma gida kawai."
"Hummmm!" Suka ji sheikh ya fad'a daga bayansu, kallonshi Asas yayi yace "Sheikh mi ye abun yi yanzu, suna buk'atar kud'i a asibitin wallahi da gaggawa, gashi ita kuma bata so tati dare."
A hankali ya shiga takowa hakan ya haddasa fad'uwar gabanta sosai, jikinta har wata rawa ya d'auka saboda jin yana kusantota, saida ya tsaya inda yake hangen fuskarta kafin yace " *Zan mayar da ita gida* idan Abbanta zai amince, dama yanzu can unguwar zan tafi."
Da farin ciki Asas ya rumgumeshi kafin ya kalli Mimi da take jin kamar tace "Mutuwa." Ita kuma ta amsa mata yace "Maah, na yarda dashi, kiyi hak'uri kuje tare kinji, insha'Allah komai dare na dawo zan sameki a gida na fad'awa su Abba abinda ya faru."
Idonta taf da hawaye ta kalleshi tace "...
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:54 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*17*
Idonta taf hawaye ta kalleshi tace "Tsoro nake ji ni dai."
Murmushi yayi yace "Tsoron me? Ba mugu bane ba fa." Ya fad'a yana satar kallon sheikh da a lokacin yake kallon fuskarta, shi wallahi maamaki ma yarinyar ke bashi, ta ya ya k'aramar yarinya kamar wannan tayi abinda tayi? Me yasa ta aikata mishi haka? Me ye burinta a duniya ko a rayuwa?
Da takon k'arfi ya juya da hanzari ya fita daga falon dan har ga Allah zuciyarshi tafasa take, musamman idan ya tuna shi ne aka wa wannan shak'iyancin, da sauri Asas ya kalleta yace "Muje."
Bin bayanshi yayi da sauri inda Mimi ta shiga takawa da k'yar tana sab'a rigarta a hannu da take jin ta mata nauyi, Hafsat da yaran kam daga baya suke binta suna mata addu'ar Allah ya tsare, duk da dai Hafsat tana jin wani abu a zuciyarta, da fari yanayin mai gidanta kawai ta kalla a lokacin da yake kallon Mimi ta fahimci akwai wani abu, uwa uba daya ce zai mayar da ita gida, saidai dake tasan waye mijinta kuma ta yarda dashi, sam bata kawo komai a ranta ba musamman mummunan zargi, daga bakin k'ofar suka tsaya ita ta wuce wajensu, tsaye suke sheikh na shirin shiga mota ta kalli Asas tana sako hawaye tace "Ka mayar dani gida da kanka, na fad'a maka tsoro nake ji."
Tsayawa yayi dan sarai yaji me ta fad'a, kallonta yayi irin kallon naan na ban tsoro duk da idonshi a cikin glas suke, cikin muryar da bata saba ji ba ko a tv yace "Me kike ji ma tsoro? Kina da laifi ne da ba kya son tafiya tare da ni?"
Kallonshi tayi tana girgiza kai hawaye na zubowa a idonta, a sanyaye Asas yace "Wuce ku je maah."
Hannu tasa a idonta ta shiga murzawa sosai tana fashewa da kuka cikin siririyar muryarta harda bubbuga k'afafu tana fad'in "Ni wallahi bana so, kawai ka san yanda zakayi da ni."
Baki bud'e Asas ya shiga kallonta da matsanancin mamakin shagwab'ar da take bugawa. Inda a wajen sheikh kuma yayi saurin d'auke kanshi yana furta "Hasbunallahu wani'imal wakil."
Cije leb'enshi yayi na k'asa tare da lumshe ido, ya d'auki minti d'aya haka kafin ya juyo ya kalli Asas yace "Ba sauri kake ba?"
Jinjina kai yayi yace "Wallahi ina so naje naga halin da bawan Allahn nan yake."
Da ido ya fara masa alama kafin yace "Je kawai."
Jinjina kai yayi tare da kallon mimi, k'yabta mata ido yayi ya wuce bai ce komai ba, saida ya saka ledar da Eesha ta bashi kafin ya ja motar ya bar gidan. Tunda ya ba Asas umarnin tafiya ta kama bakinta ta rab'e wuri d'aya. Juyowa yayi ya kalleta a mugun dak'ile ya mata alama da hannu ta shiga, jiki na rawa ta matso daf da shi ta rab'ashi ta d'aga k'afarta ta wuntsila cikin motar, rufe k'ofar yayi tare da kallon dreban ya tara hannu alamar ya bashi makulli, mik'a mishi yayi ya karb'a tare da fad'in "Zan dawo yanzu, ku jirani a nan."
Bud'a mazaunin dreban yayi ya shiga, a tsanake kuma a hankalce ya tayar da motar ya shiga janta har suka fita a gidan, shiru motar ta d'auka babu ko sautin numfashi bare redio, a sanyaye yake tuk'i sai d'an sautin ac kawai da sanyayyen k'amshin dake fita.
Daga bayan nan da take hangenshi kawai take tana k'are masa kallo, hak'ik'a yanayinsa kalar fuskarsa, saidai a zahiri da bad'ini yana da b'oyayyen k'wanji, ga kuma iya d'aukar ado da k'wallisa da kuma kyau. Had'e hannayenta take a tsakanin cinyoyinta saboda fitsari take ji sosai, kayan cikinta yamutsawa kawai suke yi ga kuma fad'uwar gaba.
Daidai babban hanyar dake d'auke da titi biyu a hannun da suke ya ratse gefe yaja birki ya tsaya, dum dum dudum! Gabanta ya shiga dokawa da mugun k'arfi, sake k'amk'amewa tayi sosai tana rintse ido hawaye na silalowa, a ranta take fad'in "Tabbas da tare nake da Asma'u, da haka bai faru ba, wayyo Allaana k'awata."
Da sauri ta bud'e ido jin k'arar bud'e motar, tana kallo ya fito a nutse ya rufe k'ofar ya bud'e inda take, ganin ya bud'e k'ofar da take zaune yasa ta ja baya da k'arfin bala'i tare da kama d'aya k'ofar zata bud'e, wani kallo ya watsa mata duk da akwai duhu yace "Kina fita a nan zan had'ani da karnuka."
Dakatawa tayi tare da fashewa da wani sabon kuka irin na tab'ara saidai kuma da gaske take yin shi, hannayenta biyu ta d'ora a kai tana fadin "Na mutu na lalace ni Mimi? Dan Allah dan annabi ka yafe min sheikh, na tuba wallahi b芒 zan sake maka k'arya ba."
Ba tare daya daina kallonta ba ya shiga ya zauna yaja murfin ya rufe, shi kanshi sai yaji abun wani iri saboda rashin sabo, idan ba Hafsat ba babu macen da ya tab'a zama da ita haka a mota, gyara zama yayi sosai yanzu suke fuskantar juna, muryar a dak'ile ya shiga wurga mata wani kallo yace "Me yasa kika min k'arya? Akan me kika maidani shashasha? Akwai gaba a tsakanina da wani naki ne?"
Girgiza kai tayi cikin matsanancin kuka tace "Wallahi babu, ni ma ba'a son raina bane haka ta faru, wallahi a lokacin..."
"Shiru." Ya fad'a a matuk'ar tsawace, a harzuk'e ya kalleta yace "Taya kuka had'u da Asas? Wane irin so kike masa?"
Cikin kukan tausayin kanta baki na rawa sosai tace "Ni wallahi ina son shi da zuciya d'aya, amma idan ka ce na daina kulashi zan daina daga yau, kuma ni na manta inda muka had'u."
"Kin manta?" Ya tambaya yana mata tuhumammen kallo, cikin in'ina tace "Eh to...ina ga..kamar dai a hanya..., ni wallahi na manta ina ne, a rikice nake Abdul..."
Duk da ta kai k'arshe sa茂 kuma tasa hannaye biyu ta rufe bakinta tana k'walalo ido, ita kanta bata san me yasa take son kiranshi da sunan ba musamman idan suna tare. Duk da wani mugun dad'i ne ke kasheshi ganin rud'ewarta da duburburcewarta had'e da kukan nan, ga kuma sunan data kira daya kwana biyu yana mararin sak茅 ji daga bakinta, daurewa yayi sosai ya had'e fuska yace "To me yasa kika amince na je gidanku yau?"
Cike da makirci ta dafe cikinta tana fad'in "Cikina ciwo yake, ka ajiye tambayoyin zan amsa maka su a gaba idan mun sake had'uwa, yanzu ka kaini gida nasha magani."
Wani k'ayataccen murmushi ya saki yana mamakin Mimi da ya ga sam bata d'aukeshi da girman da kowa ya d'aukeshi ba, jinjina kai yayi ya sake kafeta da ido yace "Fad'a min gaskiya, zaki iya zama da Asas domin Allah?"
Da sauri ta kalleshi tace "Wallahi zan..."
Nunata yayi da yatsa yace "Kika sake min rantsuwa a wurin nan kafin magana saina tsinka miki mari Ryam, tabbacin k'arya zaki fad'a shiyasa kika min rantsuwa akan k'arya."
Girgiza kai tayi tana dafe kumatunta da hannu biyu, wata harara ya kuma wurga mata yace "Yi magana ina jinki?"
Gyad'a kai ta shiga yi kamar k'adangaruwa tace "Ina son shi, zan zauna da shi."
Lumshe ido yayi tare da jingina bayanshi a kujerar yasa hannun dama ya cire glas d'in fuskarshi, "Hasbunallah wani'inal wakil, La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntun minna zalumin."
Abinda ya dinga maimaitawa kenan kafin ya bud'e idonshi tar a kan titi, cikin d'aga sauti yace "Astagfirullah, Allah na tuba ka yafe min zunubaina, Allah ka gafarta min laifukana, nasan ni d'an adam ne kuma ajizi, bansan yaushe kuma a ina ba, amma ina neman gafararka ubangiji."
A hankali ya girgiza kai ya juyo ya kalleta, kanta a k'asa tana share hawaye ga wani mugun tausayin mutumin da taji ya dirar mata, fuskarta sam ba tayi kama da wacce zata iya aikata abinda ta aikata ba, sam *kamaninta bata da suffar cutar da kowa*, saidai shi ta cutar da shi sosai, ta raunata zuciyarshi yanda har takai matakin babbakewa k'urmus. A hankali cikin amon murya mai d'auke da alhini da jimami yace "Ban tab'a tsammanin haka zai iya faruwa dani ba."
A hankali ta d'ago ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kai, d'orawa yayi da "Ryam idan kinsan ban miki ba me yasa kika b'ata min lokaci? Ko kinsan cewa