Showing 12001 words to 15000 words out of 185502 words
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*6*
Saida ta ji kiraye kirayen sallah kad'ai ta mik'e ta sake lek'awa, ido ta zaro samakkon ganin ya fito daga motar shi yana alwala, girgiza kai tayi tace "Na shiga uku, wannan jaraba da me tayi kama? Na tabbata ya kirani baya samu ne shiyasa ya zo ya girke mana a k'ofar gida."
Tana kallo ya kammala ya juya ya shiga kwanar da zata sadashi da masallaci, ai da sauri ta shiga takawa har ta k'arasa gida, tana shiga ko sallama ba tayi ba mamanta ta jefeta da harare tace "Daga ina kike?"
Tsuru ta mata da ido tare da yin tsuguno saboda ita tana tsaye ne, a hankali ta kalleta tace "Mama Yaseen bai fad'a miki bane?"
Cikin tsawa tace "Ke ba ruwana da shiririta, na tabbata k'arya kike dan daga yanda suka fad'a min ya tabbatar ke kika saka su fad'a."
D'an sosa kan ta tayi tace "Mama ba inda naje fa, wani ne na gani a k'ofar gidan nan shiyasa ban shigo ba."
Jinjina kai tayi tace "Ko da naji, Allah yasa ba wani abun kika masa ba."
Girgiza kai tayi tana kallonta ta k'arasa saman tabarma ta saka hijab ta kabbara sallah, da sauri ta shiga d'aki ita ma bayan ta duk'a kafin ta shige, kayan ta canza a gaggauce ta fito tayi alwala ta kabbara sallah. Tana idawa bata tsaya yin azkhar d'inta ba ta mik'e da saurita saka takalmi zata fita dan ta samu ya bar k'ofar gidan nan, tana juyawa suka kwatse da mahaifinta yana binta da kallo.
Da sauri ta duk'a tana fad'in "Abba gaisuwa."
Saida ya k'araso yana gyara carbinshi a hannu cikin fad'a yace "Mimi waye a waje yake nemanki? Wanene shi da ban san shi ba?"
Sunkuyar da kai ta sake yi tayi shiru, a zabure yayo kan ta yana sake fad'in "Ba dake nake magana ba? Mimi naga nema kike ki fi k'arfina ko? Kullum da kalar da zai zo nemanki gidanki."
Daga tsugunnon ta ja baya tana fad'in "Abba kayi hak'uri, wallahi ba ni na fad'a masa gidanmu ba, bansan zai zo ba."
A hassale yace "To ki je ki fad'a masa ya bar nan, kuma ya fita a sabgarki dan ni da mahaifin yaron nan mun tsayar da magana za'a saka muku rana."
Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi sai kuma ta sauke idonta k'asa, jinjina kai tayi alamar to tare da mik'ewa jiki a sanyaye ta fita, da wayarshi a hannu yana dannawa ko da ya ganta ya sauke ajiyar zuciya, shi sam ba wai gidansu ko ganin mahaifinta bane ya dameshi, hasalima ba wannan ne a ganshi ba, ita d'in dai ita yake so kuma ya ji ya gani zai iya. Murmushi ya sakar mata yana fad'in "Mimi dama zan iya ganinki? Ai har na cire rai da zan tafi."
Fuskarta a had'e ba alamar wasa tace "Me ya kawoka nan? Wa y'a fad'a maka gidanmu?"
Murmushi ya sake yi ya rufe motar ya gyara tsayuwarshi yace "Tunda na turo miki kati jiya ina ta kiranki ba kya d'agawa, yau ma tun safe nake kiranki Mimi amma shiru, shiyasa na nemi gidanku aka fad'a min, dan dama na fad'a miki ni aurenki nake so nayi."
Waina idonta tayi tare da sauke ajiyar zuciya tace "Kaga, dan Allah kayi gaggawar barin nan, kaga mahaifina bai sanka ba kuma sam bai ji dad'i ba, haka nima ban ji dad'in wannan ziyarar bazatan ba."
Cikin rashin jin dad'i yace "Kiyi hak'uri kinji Mimi, wallahi na damu ne sosai shi ya sa, zan tafi amma ki d'auki wayarki zan kiraki."
Cikin k'aguwa tace "Bana da waya yanzu, ta fad'i."
Wani murmushi ya saki yace "Haba Mimi, yanzu dan wayarki ta fad'i har zaki yarda ki kwana babu waya a hannunki."
Nuna mata wayarshi yayi yace "Wannan ta miki?"
Kallon wayar tayi a tafin hannunshi, saida taji wani murmushi zai sub'uce mata, a ranta ta ambaci "IPhone." A zahiri kuma d'aure fuska tayi tace "Ta ya zan karb'i wayar hannunka? Bana so gaskiya."
Murmushi yayi yace "Shikenan, yanzu fad'a min ina zamu had'u zuwa gobe da safe saina kawo miki wata."
Kallonshi ta yi tana tunanin abun yi, ko ba komai ai zata iya siyarwa, idan kuma iPhone ya siya mata ta samu ta d'aukar kan ta selfie da vid茅o, bugu da k'ari duk k'awayenta idan aka cire *Salma* bbu mai iPhone, ita ma dan zata auri mai kud'i ne. Nulfasawa tayi tace "Zuwa goben na kiraka na fad'a maka."
Juyawa tayi tana fad'in "Sai anjima." Shigewa tayi ya bita da kallo yana murmushi, a ranshi ya furta "Allah kai damo ga harawa." Saida ya soka wayar aljihu kafin ya shige motar ya bar k'ofar gidan.
*Litini*
Kasancewar yau zai shiga ofishin gwamnati ne yasa shi fita kan lokaci saboda bin dokar aikin da yake yi dan al'umma, saida ya fara biyawa ya ga jikin Ashraf kafin ya wuce, cikin ikon Allah kam yana zuwa aiyuka ya samu tari guda a gabansa da kuma bak'in daya bawa lokacin da zasu zo ganinshi, haka ma akwai wanda suka zo da fatan samun lokacinshi ko da ba yau d'in ba. Kaf wayoyinshi kashesu yayi idan ka cire fax d'in dake ofishin da kuma k'aramar samsung d'in da duk wani daya shafi aikinsa zai iya kiranshi ko sak'o.
Sauri yake ya kammala ko ya samu damar barin ofishin da wuri, so yake ya yi yak'in da kan shi ta hanyar neman gidansu, amma abun ka ga babba sai ya zamana yana aiki ne kuma yana karb'ar bak'untar wasu manyan bak'in da sun fi k'arfin a sharesu, wasu kuma tausayinshi da karrama d'an adam ke saka shi tsayawa sauraren kokensu. Madadin sauka k'arfe 01:00 na hutu sai gashi har k'arfe 01:16 sannan ya tsaya cin abinci, yana tsaka da cin abincin sakataranshi ya shigo dan a lokacin waya ma ana yanke sadarwarta ne dan bashi damar hutawar yana fad'in "Yallab'ai, kayi bak'o."
Lumshe ido yayi yana feso iska a bakinshi, bud'e ido yayi ya kalleshi yace "Waye?"
Cikin ladabi yace "Ya ce a fad'a maka Muttak'a ne, wanda kukayi magana a kan passepord d'in nan."
Da sauri ya kalleshi yace "Oho! Shigo da shi dan Allah."
D'aga kai yayi alamar to tare da juyawa ya fita, aje d'an take away d'in yayi ya d'auki tissue yana goge jajayen leb'unansa, jim kad'an ya shigo da sallama yana fara'a, da ladabi kamar zai sunkuya ya shiga gaishe shi yana amsawa shi ma da fara'a, cikin fara'a sheikh yace "Ina so ne nasan tsarin fitar da marar lafiya a station d'in ku?"
Da fara'a shi ma yace "Sheikh ai ba wani matsala bane, ana had'a visarshi ne tare da takardar shaidar rashin lafiyarsa da kuma asibitin da zai je gani, idan ciwon yayi k'amari da baya iya tafiya, ana iya tanadar masa wurin zama a vip, kamar yanzu ga mai buk'ata yana biyan kud'in vip ne, sannan zamu so sanin kalar rashin lafiyar, idan wacce bata da tsanani ne zata iya tafiya da yanayin jirginmu, awwanin da za'a d'auka a wajen tafiyar da kuma yanayin da marar lafiyar zai shiga idan jirgin ya tashi, idan akwai wata barazana dan mu sani da wuri mu kuma d'auki mataki."
Ajiyar zuciya sheikh ya sauke yace "Nagode sosai, insha'Allah zan gabatar maka da duka abinda kuke buk'ata, ko ba ni ba zan iya aikawa."
Da ladabi yace "Shikenan sheikh, ina jira." Lumshe ido yayi ya bud'e yace "Masha'Allah, insha'Allah."
Da haka ya mik'e ya fita ya bar shi, har zai d'auki abincin shi ya kalli agogonshi data nuna masa 01:32, da sauri ya danna madannin da zai kawo masa sakarantashi a take, wanda dama dan kiran gaggawa aka yi shi, yana shigowa ya bashi take away d'in yana fad'in "Akwai bak'i ne a waje?"
Da rusunawa yace "Eh yallab'ai, akwai wasu dattawa guda biyu da suka zo tun d'azu, sai kuma professeur *Yacoub Sumana* da ya zo yanzun."
Sa茂da ya kalli gabanshi yace "Ka shigo da dattawan."
Jinjina kai yayi tare da ficewa a ofishin, da irin haka fa aiki ya rik'e sheikh bai yi abinda yayi niyya ba, gashi kuma dolenshi ya halarci karatun *Umdatul ahkam* da yake gabatarwa duk ranar litinin da k'arfe 07:00 zuwa 08:00 na dare.
*Maryam*
Tun a hanyarsu ta dawowa ta rok'i Asma'u ta mata alfarmar da zata fita daga gida, da k'yar ta yarda tace za tayi amma ba zasu jima ba, suna zaune tare da mama a farfajiyar gidan tana gyara mata alaiyahu Asma'u ta shigo da sallama, har k'asa ta duk'a ta gaishe da mama dan haka ta ga k'awarta ma na yi, da sakin fuska ta amsa mata tana tambayarta mamanta? Da murmushi tace "Lafiya lau suke, sun ce na gaisheku."
Da fara'a tace "Ina amsawa." Jim tayi tana satar kallon Mimi da ta sunkuyar da kai kamar bata ganta ba, kallon mama tayi tace "Mama, dama anjima zan tafi gidan aunty *Rayya* ne na ce bari in fad'a miki ina so Mimi ta rakani."
Kallonta tayi sai kuma ta kalli Mimi, d'an jinjina kai tayi ta kalli Asma'u tace "Ba zaku kai magriba ba dai ko?"
Girgiza kai tayi tace "A'a mama, nima haka mama ta ce kar na kai magriba."
Jinjina kai ta sake yi tace "Shikenan Asma'u, na amince kuje Allah ya tsare, ko da mahaifinta ma ya dawo ya tambaya zan fad'a masa."
Da fara'a tace "To mama mun gode."
Kallon Mimi tayi tace "Mimi ki shirya da anyi la'asar sai mu tafi."
Gyad'a kai tayi alamar to tare da fad'in "Na ji, nima dai da ina da aunty haka zan dinga jan ki muna tafiya."
Dariya Asma'u tayi tace "Sai dai idan kinyi aure su Yaseen su je gidanki, ke kam sai hak'uri."
Dariya Mama tayi tana girgiza kai har Asma'u ta fita a gidan, Mimi kam farin ciki kamar zata zuba ruwa k'asa ta sha dan murna, dan haka ta dinga aikinta da sauri amma ba yanda Mamar zata gane tana gaggawa ba. Suna kammalawa saida ta share gidan tas ta wanke ban d'aki kafin ta shiga wanka ganin la'asar ta gabato, kafin ta fito aka fara kiran sallah dan haka tayi alwala ta shiga d'aki, mai ta shafa da sauri ta d'auki wata watsetsiyar doguwar rigar leshe wacce aka yi ta sak da zubin bubu, gaban rigar zuwa wuya a tamfatse yake da duwatsu, hijabi ta saka ta shara yin sallah a nutse, tana idawa mama ma ta idar ta k'ara gyara zaman hijabinta tace "Mama zan tafi, sai mun dawo."
Kallonta tayi tace "Ina d'an kwalin kayan kuma?"
Nuna mata k'aramar jakarta tayi tace "Gashi nan ciki, mama kinsan leshe yana da cin rai musamman lokacin zafi."
Jinjina kai tayi tace "Sai kun dawo, karki manta kuma ku dawo kafin magriba."
Saida ta d'auko wasu takalmi confence da suka dace da kayanta da jakar tace "To mama." Fita tayi tana sake gyara zaman Jakarta a kafad'a. Gidansu Asma'u ta shiga ta gaishe da mamanta sosai kafin ta fito suka wuce, taxi suka shiga abun mamaki Asma'u sai taji Mimi tace a kai su *nouveau marcher*, ko da taji haka tasan gidansu Salma zasu je, dan haka kawai ta biye mata suna hira dan karsu fara fad'a yanzu yanzu.
A bayan kasuwar aka aje su suka k'arasa cikin gidan, kyakyawar budurwa na zaune tana cin kwad'on dambu, tana ganinsu ta mik'e da sauri ta zo ta rumgume Mimi tana fad'in "Bestyna, daga ina haka?"
Da farin ciki Mimi tace "Daga gida mana." Raba jikinsu sukayi inda suka shiga gaishe da matan gidan, wanda cikin sauk'i zaka fahimci yanayin zaman, dan da alama uwar Salma ita ke buga mulki a gidan, watak'ila yanayinta ko yarenta ya jawo haka, dan kuwa daga ita har yaranta fatarsu jajir take kamar wasu larabawa, sannan gata 'yar caras sab'anin guda biyun da suke da k'iba mai yawan gaske. Ciki suka shige inda ta musu masauki a d'akinta, suna shiga Mimi ta cire hijabin ta jefa kan gado ta cire jakarta ta zazzage kayan ciki, kallon Salma tayi tace "Besty taimaka min da kayan kwalliyarki, ni ban d'auko ba saboda mama zata gane."
Dariya tayi ta juya ta d'auko mata jakar kayan tana fad'in "Muguwa, wani wuri zaki tafi shine baki fad'a min ba."
Saida ta zauna da kyau ta kanta a madubi da alk'alamin zana ja-gira (crayon) ta shiga bin tsatsaren girarta da bata da yawa sosai kuma ba siririya ba tana zanawa, kallonta suka shiga yi inda Salma ke nuna mata sababin vid茅o d'in data samu na wak'ok'i, jin wata wak'a dake birgeta sosai ta wani mawak'i da suke gari d'aya da shi wato Niamey mai sunan *Auta mg boy* tayi saurin cewa "Besty bar min wak'ar nan."
Aje mata wayar tayi gabanta tace "Besty kinsan da jibi za'a kawo kayana kuwa?"
Da sauri ta kalleta tace "Dan Allah? Da gaske?"
Cike da tabbaci tace "Allah kuwa."
Cikin farin ciki tace "Kai amma dole na yi waya kafin ranar, dan wallahi ni zan zama farko da zata fara had'a hotunan kayan lefenki."
Dariya tayi tace "To ina wayarki?" Yatsina fuska tayi sanda take saka conciller tace "Dama ai na fad'a miki bana son Samsung d'in nan, ya rasa wayar da zai bani sai Samsung ? Samsung d'in ma duos."
Tab'e baki tayi sai Salma da tace "To ai ke besty ba'a gane gabanki ne wallahi, kin ga fa har abokin 'ya'yana yace yana sonki ki fad'a min na fad'a masa ya ma fita harkarki, wallahi dan baya son raini ne amma har yanzu yana son ki, ke nan fa saida 'ya'yana ya fara min mad'e a kan ki yana nuna min son ki yake, ko da na fara tuntub'arki da lamarin kika kalli idona kika ce bai miki ba."
Wata shak'iyar dariya tayi sai Asma'u dake saurarensu tun tuni tace "Tsakani da Allah? Yayanki fa?"
Kallon Asma'u tayi tana gyara yaloluwar rigarta data fito mata da 'yan tsirarun nonuwanta tace "Wallahi haka ya faru, bansan wane irin namiji take so ba?"
Tab'e baki Asma'u tayi tace "Ai indai Mimi ce namiji zai tsallake jarabawar tantancewar fara kula ka ne idan ka haye wad'anan matakan, na farko ka zama dogo ne da ka iya d'aukar ado da tsafta, na biyu ka zama wayayye d'an zamani da zaka iya aje ta gaban mota ku zaga gari, idan ta kama har k'asar waje ka dinga fita da ita dan shak'atawa, na uku ya zama matakin karatunka mai zurfi ne yanda zaka iya cireta kunya a ko ina kuka shiga, na hud'u ka zama mai d'an abun hannu da zaka iya d'aukar d'awainiyarta, ko da baka kasance d'an babban gida ba ita wannan bai dameta ba, na biyar kuma shi ne ka tabbatar *shekarunka daga talatin* ne k'asa da haka, dan ita a tunaninta a wannan k'adamin ne yake ganiyar k'uruciyarsa, duk zai iya yin wad'ancen abubuwan dana lissafa ne idan wannan ne adadin shekarunshi, sama da haka tana ganin ya jima da tsufa a duniya, ita dama bata damu sai kyakyawa ba, indai kana da wancen to an wuce wajen a wurinta."
Wani nauyayyen numfashi Salma ta sauke ta kalli Mimi da har tayi nisa a kwalliyarta tace "Lallai besty burinki babba ne, ko ni da zan auri mai kud'i ban saka ran ya dinga fita da ni ba."
Jinjina kai tayi sai kuma tace "Indai hakane kenan duk sanda kika ganni tare da alhaji na dariya kike min?"
Mimi kam bushewa tayi da dariya dan gaskiya abin da ke faruwa ta fad'a mata, ganin haka yasa Salma hararenta tace "Allah indai hakane zan hanaki halartar bikina."
Tsagaitawa tayi da dariyar tace "Haba besty wa ya fad'a miki? Ni na isa na wa mijin da zaki aura dariya."
Hararanta tayi tana turo baki tace "Allah yasa gaskiya kika fad'a."
Dariyarta kawai ta ci gaba da k'yalk'yalawa can kuma saita kalli Salma sanda take shafa man leb'e tace "To wai besty me yasa zaki aureshi? Dubeki ki dubeshi, wallahi wannan tsaf zai kasheki da tumbinshi a daren farkonku, kuma fa zai kai hamsin mutumin nan."
Waro ido Salma tayi tace "Ke Mimi bansan wulak'anci, wallahi arba'in da hud'u yake, haka ya fad'a min da bakinshi sanda na yi shagalin murnar k'arin shekarata."
Asma'u dake ta dariya ne tace "Wato Mimi ke dai idan kika k'i abu kina da hanyoyi dayawa na kusheshi."
Salma ce tace "Gane min hanya dai yar uwa."
Kallon Salma tayi tace "Baki yarda ba kenan?" Shiru tayi sai kuma ta kalli Asma'u tace "Yar uwa fa tayiwu dan baki san shi bane, gaskiya ta fad'a indai zan cire son zuciya, ina jin fa Allah ne yayi ni d'in matarshi, dan nima da fari babu yanda ban yi ba dan mu rabu, dan gaskiya idan na tsaya kusanshi yanda kika san gwiwa ce da kaza."
Wata dariya suka kuma tintsirewa da ita har Asma'u, hakan yayi daidai da mik'ewar Mimi ta shiga kashe d'aurin d'an kwali kamar wacce ke koyar da kwalliya, kuma a haka duk ta koya ne ta hanyar kalle kalle a waya da saka kai, hakan yasa k'wandalarta bata shiga hannun mai kwalliya ko mai lalle, indai tayi niyya zata zauna tayi abun ta, kitso ma ta iya tsaf kan ta dai ne bata yi wa, kuma a haka bata d'aukeshi sana'a, a ganinta ajinta ya wuce nan gaskiya, tun mama na mata fad'an tayi har ta daina, mama kawai take ma sai Iya Delu sai kuma k'awayenta idan ta so. Sassauk'an d'auri tayi ta d'auki gyalenta ta rub'ashi biyu ta d'ora a kafad'a d'aya, turarenta ta d'auka ta fesa sosai kafin ta kalli Salma tace "Besty kira min