Showing 102001 words to 105000 words out of 185502 words
zuwa falon saidai kash wani babban tashin hankali da abun kunya ne ya bayyano a jikinshi, sai yaji kamar ya cire hiraminsa yayi walki da shi ko zai rufe mishi sirrinshi, da k'yar yayi dubarar dan jan rigar har ya k'arasa ya zauna akan kujera.
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*33*
Da girmamawa Asma'u ta sunkuyar da kanta ta rusuna sosai tace "Ina kwana."
Da sauri Ashraf ya rik'e hannunta wanda yin hakan ya haifar mata da wani fad'uwar gaba da kuma tashin tsigar jiki, kallonta yayi cike da gargad'i cikin rad'a yace "Baya amsa gaisuwar ina kwana ko ina wuni, sallama kawai."
Wasu yawu ta had'e sannan ta kalleshi, sai taga kamar ma bai san da zamansu ba kan shi a k'asa kamar yana wani tunani, zaman Hajia akan kujera ne yasa shi saurin d'aga kanshi ya kalli inda suke zaune, shiru yayi bai ce komai ba har saida ya tabbatar sun gaisa.
D'aga kan shi ya sake yi ya kalli Asas cikin wata tsumamiyar murya yace "Ashraf, zan iya sanin dalilin da yasa tunda aka d'aura aurenka baka zo ka ga Hajia ba sannan baka d'aga kiranta?"
Rarraba ido Asas ya fara yi yana kallon Hajia da sigar "Ki rarrashe shi dan Allah, ba zan iya da masifarsa ba a halin da nake ciki."
D'auke kai Hajia tayi kamar bata fahimci me kallonshi yake nufi ba, sunkuyar da kai yayi sosai yace "Kuyi hak'uri dan Allah, ina cikin damuwa ne shiyasa."
A tsawace kuma a hassale yace "Damuwa? Asas wace irin banzar damuwa ce ta gidan duniya da zata sa ka manta da mahaifiyarka? Har ita ta nemeka a waya amma ka k'i d'aga kiranta, kasan girman laifinka kuwa?"
Wani wawan tsaki ya ja ya juyar da kan shi gefe sannan ya ci gaba da fad'in "Shin k'addarar aurenka ce ka kasa d'auka a matsayinka na musulmi? Ko kuma dai *Ryam* dana aura ce har yanzu baka cire a zuciyarka ba? Idan hakane ka fad'a min, yanzun nan a gabanka zan saketa sai ka aura inhar hakan zai sakaka farin ciki."
Da sauri duk suka kalleshi har da Asma'u dake ganin kwarjininshi, da sauri Asas hankali tashe ya girgiza kai yace "A'a sheikh, wallahi na hak'ura har abada, na rumgumi k'addarata da hannu biyu, kuma insha'Allah zan ci gaba da rik'ewa."
Wani nauyayyan numfashi ya sauke a sanyaye yace "Daga mu mazan har matan ya kamata mu d'auki wannan auren a matsayin k'addararmu, dukanmu babu wanda yayi hasashen hakan zai faru, babu wani mahaluki daya zauna ya tsara hakan, yin ubangiji ne, haka ya so ya kasance, shin da wace ni'ima ce muke k'aryatawa? Ikonshi ya fi gaban wasan bawa, komai yahudancin mutum idan mu'ujizarshi ta faru dole ya kan karya zuciya, saidai kawai mutum ya k'i gaskiya amma fa ya tgidanmu akan k'arya yake. Mu musulmi ne Ashraf da muka yarda a jerin rukunan imani guda shida akwai yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau, tunda muka amsa sunan musulmi mu yarda da duk jarabawar da zata samemu, ko kana so ko baka so dole ta zo, ta maka dad'i ko bata maka dad'i ba dole a jarabceka, saidai fa mu sani duk jarabawar da za'a wa mumini matuk'ar yayi imani kuma yayi hak'uri, to yana da sakamako mai tsoka. Yanzu wane gata ne ya fi wannan? Wane addini ne ya zo da irin wannan alkairan ga mabiyansa? Zazzab'i zakayi mai mugun zafi da zai saka ka fita hayyacinka, amma daga sanda ka kwanta har ka tashi lada ce mala'uku ke rubuta maka na sannan ana kankare zunubanka, da wannan zan rok'eka kayi hak'uri da jarabawarka sannan ka rik'e 'yar mutane da amana, ban da cin zarafi da halayen mata wato gori, watak'ila yarinyar nan ita ce warakarka da kake yawan fad'a mana."
Sosai jikinshi yayi sanyi har yana share k'wallar dake taruwar masa, dan gaskiya da ya so yayi sati kafin ya zo gidan nan, sannan Asma'u ya so ya zauna da ita dumkum d'in nan har sanda zata gaji tace sallameni, amma yanzu sai yaji wata sha'awar son zama da ita na shigarshi da kuma kyautata mata.
A tausashe sheikh ya sake fad'in "Mahaifiyarka da shaid'an ya zigaka har kake ganin ta maka ba daidai ba har da tagomashin hukuntata ta hanyar nesanta kanka da ita, ka bata hak'uri yanzun nan ka kuma nemi yafiyarta, sannan karka sake maimaita min irin wannan kuskuren dan ba zan d'auka ba, uwa daraja ce da ita, kima ce da ita da babu wani abu mai daraja da zamu iya had'awa da ita, munyi sa'a Allah ya bar mana ita, ita muke zuwa mu fad'a ma kukanmu da farin cikinmu, Ashraf kayi sa'a kai ta ka mahaifiyar ma tana raye, ni ina tawa take a yanzu? Nayi imani da zata dawo yanzu a duniyar nan na minti d'aya kawai ta umarceni da na auro biyu akan biyun da nake da a yanzu, wallahi tallahi zanyi dan farin cikinta, ita ta tsaya min na taka matakin da nake kai yanzu, ita ce k'ashin bayana da har na iya zama da d'uwawuna, addu'arta ce har yau take tasiri a gareni, kullum fata da burinta shi ne na zama babban malami kuma babban mutum."
Wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi ya sa bakin hiraminsa ya share k'wallar data tarar masa a gefe, ya d'an jila yana shashek'ar kuka kafin yace "Sanda na fara hawa matakin da take da burin ganin na hau, sai Allah ya karb'i rayuwarta gaba d'aya ta bar duniyar, na d'auki hakan a matsayin jarabawata mafi girma, har yanzu ina kukan rashin mahaifiyata, ina kewarta, ina neman sa war albarka daga bakinta."
Sake duk'ar da kai yayi dan sosai kukan nan ya ci k'arfinsa, mik'ewa yayi da sauri ya nufi hanyar fita, da kallo suka bishi jikinsu duk a tsume Hajia har da kuka ita ma, da sauri Asas ya taso ya zo kusanta ya zauna k'asa ya rik'e k'afarta yana magiyar "Dan Allah Hajiata, dan girman Allah ki yafe min, Hajia kar na mutu a yau kina hushi da ni, Allah k'onani zaiyi Hajia ki yafe min."
Rik'e hannunshi tayi tana share k'walla tace "Ba komai Ashraf na yafe maka, ai tun jiya ma sheikh yasa na yafe maka."
D'ora kanshi yayi a cinyarta yana sauke numfashi yace "Nagode Hajiata, Allah k'ara miki lafiya da nisan kwana."
"Ameen." Ta fad'a tana kallon Asma'u da tayi shiru jikinta yayi sanyi ganin sheikh na kuka, da hannu Hajia ta mata alamar ta zo, mik'ewa tayi tana gyara hijabinta ta zauna k'asa ita ma, dafa kanta tayi tace "Allah ya miki albarka Asma'u, kuyi hak'urin zama da junanku kunji."
A tare suka jinjina kai kafin ta rik'o hannayensu ta had'a wuri d'aya, a take suka kalli junansu sabida yanda ta had'a hannayen nasu, cikin fara'a tace "Zaman lafiyarku shi ne farin ciki na, ku girmama junanku ba tare da tuna ta yanda aurenku ya kasance ba, na tabbata akwai abinda Allah yake nufi da auren na ku, komai k'ank'antar alama a cikin tarayyarku zamu d'auketa mu rik'e a matsayin abinda Allah ya hukunta, dan haka kuyi hak'uri ku tallafi junanku wajen samar da kyakyawan sakamakon da zamuyi nuni da shi."
Jinjina kai sukayi sosai kafin ta saki hannayensu, kallon Asma'u tayi tace "Ki shiga ciki k'awarki na nan."
Da murmushi ta mik'e ta nufi inda Hajiar ta nuna mata, da sallama ta shiga d'akin tana tura k'ofar. Mimi da har lokacin take zaune a k'ofar ban d'akin da sauri ta mik'e jin saallamar Asma'u, bud'ewa tayi ta fito suka hada ido, wani kukan ta fashe da shi tare da tahowa a guje ta rumgume Asma'u tana fad'in "Asma'u mugu ne, ki tafi dani dan Allah ki kaini gidanmu, cire min kayana yayi."
Cikin tashin hankali da rashin sanin inda zancen ya nufa Asma'u ta d'ago tana fad'in "Ya cire miki kaya? Wanene?"
Cikin turo baki tace "Waccen malamin mana."
Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke, kama hannun Mimi tayi suka zauna kan gado, a tsanake ta kalleta tace "Mimi me ya faru? Nasan dai haka kawai sheikh ba zai miki rashin kirkin da har zaki kirasa da mugu ba idan ba ke kika tsokano shi ba."
Share hawayenta tayi dan zuwan Asma'un yasa duk ta ji babu wannan tsoron da k'uncin, cikin rashin damuwa tace "Ke ni bansan me na masa ba, kawai dai ya hau ni da masifa da tijara."
D'an guntun tsaki tayi tace "Kinji fa yana malami amma yake fad'in idan iskanci zaiyi a niger zan d'auka shi kad'ai ne ya iya iskanci, hmmm."
Ta fad'a tana mik'ewa tsaye, da kallo Asma'u ta bita tace "Ai gaskiya ya fad'a miki, mahaddacin Alk'ur'ani masanin sirrin yahudu da nasara kina ganin akwai wani abun ne da zai shige masa duhu?"
Tab'e baki tayi ta d'auki dogon towel d'inta ta d'aura a k'irji sannan ta k'arasa cire rigar gaba d'aya, matsowa tayi kusan Asma'u cikin rad'a tace "Ke har da tab'a min d'uwawu yayi, wallahi ki fad'a masa yayi na k'arshe."
Dariya Asma'u tayi tace "Ai sadakinsa ya biya, kad'an ma kika gani yarinya kafin ki tare."
Sake tab'e baki tayi ta shige ban d'akin Asma'u na fad'in "Ke tare da shi fa muke zaki wani shanya ni a nan?"
Tsayawa tayi ta juyo tare da kallonta tace "Tare kuke? Wani gurin zaku je?"
Girgiza kai tayi tace "Ke bakiyi mamakin gani na ba a yanzu? Jiya ne dama yace sheikh ya ce mu zo nan."
D'aga mata gira tayi tace "Wani abu ya muku?"
Girgiza kai tayi tana fara'a tace "Nasiha ya mana mai shiga zuciya."
Yatsina fuska tayi tace "Ki gaishe shi to." Ta fad'a tana shigewa ban d'aki dan yin wanka, girgiza kai Asma'u tayi ta mik'e tana murmushi ta fita a falon, jiranta ta samu Asas na yi tana zuwa yace "Muje."
Yanda ya mata magana d sakin fuska sai ya bata mamaki, sallama tayi da Hajia suka fice a gidan, tun a mota ya so kasheta da mamaki sakamakon hannunta daaya rik'o yana matsawa yana sakar mata murmushi, yanda take sunkuyar da kai yasa shi kallonta yace "Wai kunya kike ji? Lallai ma *Naanah* gwara ki daina, dan babu abinda zai hanani yau dai na sa ki amsa sunanki a matsayin *Asma'ul-Husna* matar Ashraf."
Gabanta ya shiga wani irin lugude yana fad'uwa, sake duk'ar da kai tayi ba tace komai ba sai rawa maa da bakinta ya d'auka, da haka suka k'arasa gida saidai bai sake fita ko ina ba, tare suka wuni kuma sosai suka samu wata irin fahimta da shak'uwa, dan yanda ya fahimceta shi ne ita d'in bata d'auki duniya da zafi ba, duk abinda aka mata ko ta samu zata karb'a da hannu biyu tayi godiya ga sarkin daya nufeta da samun wannan d'in, hakan yasa shi fara jin ta daban a zuciyarshi tare da mata wani kallo na matar aurenshi wacce zai iya yak'i a yanzun dan kare martabarta.
*Yammacin litinin*
Fitar Hajia yasa Mimi shigewa d'akinta ta kunna wak'a a wayarta, duk da ita d'in ba gwanar rawa bace amma sai gashi ta zage tana tik'ar abarta a d'akin tana kuma gyaran d'akin, dan in kid'a ya kai mata har tsayawa take a gaban madubi ta cashi abarta kafin ta ci gaba da aikin.
Sheikh ma na shigowa gidan da niyyar daya bata sak'onta ya wuce gida, dan litilin d'in yau ta zama mai sauk'i aiki a gareshi a ofishi, dan haka yayi saurin baro ofishin ya fara biyowa ta gidan, Salamatu na gad'a mishi Hajia ta fita sai kawai ya wuce d'akin kai tsaye, duk da kuwa zuciyarshi na kwab'arshi k'walwarshi kuma na tuna mishi had'uwarsu ta safe, d'aure fuska yayi ya bud'a k'ofar da tunanin sai fa ya gyara mata zama dole yarinyar nan.
Ai kam turus yaja ya tsaya sakamakon jin kid'a da kuma ganin k'anwar *shakira*馃ぃ, da d'an k'arfi ya furta "Hak'ik'a daga Allah muke kuma gareshi zamu koma."
Waro ido yayi da kyau dan shi ko cikin yaranshi a k'iriniya ta yara bai tab'a ganin haka ba. Jin sautinshi ya fargar da ita da sauri ta tsaya tana kallonshi, pik'i-pik'i ta tsaya yi da ido tana neman hanyar dakawa a guje, takowar daya fara yi ce ta sa ta ja baya tana fad'in "Dan Allah malam dan soyayyarka da Allah karka dakeni, kaga dai Hajia amanata ta bari ko?"
Yanda ta k'arashe maganar da nunashi da yatsa irin a dole tambayarshi ne take cikin yanayin yi mishi hannun ya mai sanda sai ta so bashi dariya. Tara mata hannun dama yayi yace "Bani wayar nan?"
Galala tayi tace "Iyee?"
Fito da idonshi yayi yace "Na ce ki bani wayarki?"
Da sauri ta d'auka ta mik'o mishi tana sake fad'in "Malam ai ku an ce ba kwa hushi saboda magada annabawa ne ku, dan Allah kar ka rabani da wayar zan daina daga yau."
Sama da k'asa ya kalleta ya mik'a mata k'atuwar ledar hannunshi, hannu biyu tasa ta karb'a shi kuma ya d'ora da fad'in "Wannan ita ce zata zama suturarki idan zaki fita."
Juyawa yayi kawai ya fita yana sake hangota tana ta kiciniyar rawa a shigowarshi, girgiza kai kawai yayi ya fita a falon, saida ya shiga mota dreba na jan shi ya shiga duba wayar, irin tarikitan hauka daya gani saida yaji kanshi ya fara ciwo, vid茅os na wak'ok'i da girki da kwalliya da shirme da shiririta na dariya, hotuna na d'inki da matan da bai ma san dan d'inki ne aka aje hoton ba ko kuma dan kwalliyarsu, tsaf ya tattara komai ya goge ban da girki da yake ganin zasu anfani mace, sai kuma hotunan ta daya samu barkatai wanda ya tabbatar zuwan k'awayen nan nata zata samesu, kallon hotunan ya shiga yi yana murmushi, idan ya ga wani style d'in sai kawau ya tintsire da dariya shi kad'ai, lallai kawai ya gama yarda yarinyar yar zamani ce, da wannan ya isa gida inda suka zauna a duka babban falon shi da ahalinsa suka shiga hira da raha ana tsokanar juna, a sauk'ak'e kuma iyayen ke fahimtar wani kuskure na kalma a tare sa yaran sai su d'orasu a hanya.
Bayan fitarshi kuma Mimi ta bud'e kayan nan, hijabbai ne zumbula zumbula har k'asa ko hannaye basu da, sai nikab da safar k'afa. Kecewa tayi da dariya tana fad'in "Wayyo Allah na akaramakallah, yo wannan ka d'auka ni d'in wata aljana ce? Tabb' lallai ma!"
Tattaresu tayi ta zuba akan gado ta shiga harkar gabanta da tunanin ta yanda zai dawo mata da wayarta ma, dan ita tafi damunta kam.
*Asa-Ma'u*
A wajen amaren kula yau fa daren na musamman ne dan sosai Asas ya zage damtse wajen kwasar amarcin shi da matarshi, kamar yanda yake hari matarshi ce zata zama silar warakarshi hakane ta kasance.
Sosai Asas ya rik'e wuta akan baiwar Allah Asma'u, tun tana jin kunyar nuna gajiyawarta har ta fara mishi kukan tab'ara tana magiyar ta gaji haka, mamaki yake yanda ya kasa sararawa 'yar mutane, jikinshi k'ara rik'ewa yake yana d'aurewa, hakan yasa suka galabaita daga shi har ita. Wata masifaffiyar zufa ce ta shiga tsatsafo masa sanda ya sauke wani curarren abun daya tarar mishi a mara, take kuma sai jikinshi ya kwashi b'ari sosai, cikin tashin hankali Asma'u ta yunk'ura ta shiga tureshi a jikinta saboda ganin yana wani shure shure kamar zai mutu, fashewa tayi da kuka tana jan zanin jikinta da k'yar tana fad'in "Assss...a..." Gaba d'aya sai ma ta manta sunan da zata kirashi da shi.
Tsaf ta ga ya daina numfashi bare motsi, a firgice baiwar Allah duk da azabar da take ji a jikinta sai ta manta, da gudu ta shiga ban d'aki da zanin rufa a jikinta ta rufe jiki ta d'ebo ruwa ta shafa mishi, shiru ba alamar Asas zai dawo, ai da sauri ta bud'a kayanta ta d'auko doguwar rigar atamfa ta saka ta fito wajen gidan, cikin tashin hankali take k'wala kiran "Mai gadi, mai gadi."
Kamar daga sama yaji kiran sunan shi ma a kid'ime ya fito yayo kanta, da gudu ta juya ta koma tana fad'in "Muje ka taimaka min, bashi da lafiya."
Da gudu ya bi bayanta suka shiga d'akin, ganinshi kwance babu kaya a jikinshi sai zanin gadon data ja ta rufa mishi, juyawa yayi yana fad'in "Hajia saka mishi ko duguwar riga, bari ni saina kira lambar Hajiarshi."
Fita yayi a d'akin da sauri tana matsar k'walla da cije leb'enta dan sosai take jin ciwo a jikinta, kawai dai tashin hankali ne wani yafi wani, da k'yar ta saka mishi dogon wandonshi na bacci da doguwar farar rigar, zaune tayi ta sakashi gaba tana kallo tare da rik'e hannunshi, babban abinda ke ranta a lokacin bai wuce "Kar a zo *sanadin takaba* ne yasa aure na da Asas ya tabbata, Allah ka tashi kafad'unshi kasa kar ya mutu ya barni, duk da ba son shi ne a zuciyata ba amma zan so ya zama mutumin da zai ci gaba da abonda ya fara."
Mintuna ashirin da biyar suka kawo Hajia gidan tare da drebanta, tana shigowa d'akin Asma'u ta mik'e tana sake fashewa da kuka, cike da dagiya Hajia ta dafata tace "Me ya sameshi Asma'u."
Cikin kuka tace "Hajia ban sani ba nima, kawai...kawai fad'uwa yayi haka."
Sake kallonshi tayi ta kalli gadon, da sauri ta d'auke idonshi daga birbid'in jinin data gani a kan zanin gadon dake jikinshi, saidai tana mayar da idonta k'asa sai kuma akan pant d'in Asma'u, cikin dattako da hangen nesa ta