Showing 132001 words to 135000 words out of 185502 words
ka saka mishi abokina tunda dai ai na ga ka girmeshi."
Yanda take maganar ita fa iya gaskiyarta take fad'a, takowa ya fara yi tare da aje ledar indomie hannunshi, jawo k'ugunta yayi ya had'a da na shi yana kallon fuskarta yace "Ya kike so ayi yanzu *sarauniyata*?"
Cike da sangarta tace "Kawai ka saka mishi aboki."
Karb'ar wayar yayi yana fad'in "Angama yan matan tsohonta."
Tana kallo ya shiga daddana wayar na yan dak'ik'u kafin ya nuna mata yace "Haka yayi?"
Dubawa tayi ta ga ya saka aboki, murmushi tayi ba tare da saninta ba tace "Ko kai fa."
Mik'a mata wayar yayi ta juya zata fita yana binta da kallo, wato indai ka auri yarinya dole ka zama yaro wani lokaacin kuma ka zama mai raino. Tana daf da fita kuma ta tsaya ta juyo irin da mamakin nan tace "Amma kuma ai sirikinka ne, ya zaka sakawa lambarshi sunan aboki?"
Numfashi ya ja yace "Bai yi ba shi ma?"
Marairaicewa tayi tace "Haka nake tunani."
Murmushi yayi yace "Yanzu ki fara kiranshi ku gaisa, kafin ki gama wayar zan tayaki tunanin sunan da zamu saka, hakan yayi?"
Jinjina kai tayi alamar e, fita tayi shi ma ya juya ya ci gaba da aikinshi yana tunanin sunan da zai saka ma lambar nan ya huta, dan alamu na nuna zai sha matsi akan sunan lamba kawai.
Zaune tayi akan kujera ta d'ora kafafunta sama ta cire kallabin rigar abaya ta aje gefe, tana jin tana ringin da sauri aka d'aga Abba na fad'in "Assalama alaikum akaramakallah."
Dariya tayi cikin ladabi tace "Wa'alaikum salam, Abba ni ce fa, Mimi."
Kamar a d'an tsorace yace "Mimi? Ke me kike da wayar sheikh yanzu da sassafen nan?"
Turo baki tayi tace "Abba ina kwana?"
A dak'ile yace "Lafiya lau."
Jin bai k'ara da komai ba yasa tace "Abba ina Mama? Ku bani ita."
Muryarshi ta ji yana fad'in "Rabi'a karb'i nan, uwata ce yanzu ta kira da lambar sheikh?"
Jim kad'an ta ji Mama a dak'ile ita ma tace "Ina jin ki?"
Numfashi ta sauke tace "Mama ina kwana?"
"Lafiya lau." Ta fad'a a tak'aice, cikin sanyin murya tace "Mama ina so na je gida wajenki, dan Allah Mama ki ce na zo kinji, bana da lafiya Mama ina son ganinki."
Shiru Mama tayi tana nazarin duka maganganunta, can daga bisani ta nisa tace "Mimi, yanzu ke fa ba yarinya bace, ina so na ga kin aje wannan shirmen kin rungumi sabuwar rayuwarki, ba k'aramin mutum kike aure ba fa, Mimi a yanzu idon jama'a dayawa zai sake hawa kan ki ne da son ganin kalar damun da zaki wa ta ki rayuwar ta yanzu, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, ajin nan dana sanki dashi da kuma tsafta, iya kwalliya da iya girki, Mimi na sanki da iya zama da mutane, na tabbata indai a b'angaren ladabi ne da girmama babba ba zaki samu ta biyu ba, ya kamata kiyi anfani da damarki kinji, sannan da kike maganar baki da lafiya, ya kamata kisan wacece ke, baki da k'anwa ko aunty da zasu iya taimaka miki a wasu abubuwan, tun yanzu ki fara koyon yanda zaki taimakawa kanki idan buk'atar hakan ta tashi, dan akwai gurin da ko giyar wake na sha ba zan iya tunkara ba da sunan taimaka miki, kin fahimta?"
Mimi da jikinta ya gama sanyi wata ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi kafin tace "Na fahimta Mama, nagode."
A takaice tace "Ba komai, ki kula da kanki."
Saida ta had'e wasu hawaye da suka taho mata kafin tace "To Mama."
A hankali ta kashe wayar tana sako da hawayen na jin zafin rashin mataimaki a rayuwarta, lallai zatayi kamar yanda Mama ta fad'a, zata koyi kula da kanta sannan ta fara koyon yaanda zata shanye damuwarta ita kad'ai, bugu da k'ari zata koyi yanda zata iya farantawa mijinta rai ita ma. Dan maganganun Mama ba iya wannan k'arfin gwiwar kawai suka k'ara mata ba, har da na d'amarar zama da sheikh ma, zata zauna da shi ta masa biyayya ta masa ladabi, saidai b芒 hakan na nufi ta zama sakara bane a gidan miji, kasancewarshi tsohon daya haifeta ba shi zai sa ta kwanta ya jata a k'asa ba, haka ma matarshi kasancesarta wacce ta haifi kamarta ba zata d'auki wani abun daga gareta ba, saidai ta yarda zata mata ladabi ta kuma bita sau da k'afa, kuma ta yarda ko a wayo ne zata iya wanketa ta shanye, dan haka tasan ba zata kara da ita ba ta kowane fanni, amma ita ma zatayi iya bakin k'ok'arinta.
Aje wayar tayi gefe ta gyara zamanta sosai tana kallon tvn, ta jima zaunen kafin ya fito hannunshi d'auke da wani k'aramin tangaren mai kama da kwano, akan table d'in tsakiyar ya aje tare da d'auko table d'in gaba d'aya ya dire a gabanta yana fad'in "Oya Hajia, ga indomienki."
Kallonshi tayi da girmamawa tace "Sannu da aiki."
Gefenta ya zauna yana murmushi, cokali mai yatsu ya d'auka ya saka a ciki ya tallabe kwanon a tafin hannunshi, d'ibowa yayi ya nufi bakinta yana fad'in "Bismillah."
Cike da kunya ta bud'a bakinta ta karb'a, jim tayi tana d'an taunawa a hankali tana son tantance abinda take ji, k'ura mata ido yayi yana murmushi yace "To ya kika ji?"
D'aga gira tayi ta kashe masa ido d'aya tace "Ba laifi, dama ka iya girki ne haka?"
Dariya yayi yace "Hakan na nufin na birgeki ta wannan fannin?"
Sunkuyar da kai tayi alamar kunya, sake d'ibowa yayi ya ci gaba da bata a nutse tana karb'a, tas ta cinye dan yunwa take ji dama kuma shi ma bai barta ba saida ta cinye, kakkaurar madara ya bata ta sha sannan ya b'allo maganin da Rakiya ta bayar yace "Yawwa yan matan tsohonta, yanzu wannan zaki sha sai ki samu bacci ko?"
Marairaicewa tayi tace "Abdul bana son magani wallahi, kaga dai wannan abubuwan biyu bana son su ko kad'an."
Kallon tuhuma ya mata yace "Menene su?"
Cikin turo baki tace "Allura da magani."
Wata yar harara ya mata yace "Da duka kuma? Kin manta kin ce ba kya son duka."
Da sauri tace "E hakane, da duka."
Girgiza kai yayi yace "To yanzu fad'a min, idan na jik'a miki maganin zaki sha?"
Kyab'e fuska tayi irin kamar zatayi amai tace "Tirrrrr! Amai zanyi."
Matsawa yayi daf da ita yace "To kinga bari kiga dubarar da zamuyi."
Gyara maganin yayi a yatsunshi biyu yace "Bud'e bakinki ki d'aga kan ki saiki rufe idonki sosai."
Had'e yawu tayi sannan ta rintse ido ta bud'e bakin kamar yanda yace, bata ankara ba taji maganin can k'asan mak'oshinta, kafin tayi wani yunk'uri kuma ya kora mata ruwa tare da saka yatsu biyu ya rufe k'ofofin hancinta, hakan ya tilasta mata had'e maganin da ruwan tana sauko da kanta k'asa, kallonshi tayi tana zazzaro ido shi kuma yana murmushi yace "Gashi har kin shanye."
Waro ido ta sake yi tace "Da gaske?"
Jinjina mata kai yayi, cike da mamaki tace "Duka biyun?"
Sake jinjina mata kai yayi alamar e, dafe k'irji tayi tana dariya tace "Yau ni na sha magani haka, kai Allah nagode maka."
Dariya yayi ya jawota jikinshi ya kwantar yana shafata yace "Kinga yanzu haka zamu dinga shan maganin kenan."
Sunkuyar da kanta tayi k'asa ba tace komai ba, gyara zamanshi yayi ya kwanta akan kujerar tana jikinshi ita ma, cikin sanyin murya yace "Ryam, kin yarda ina sonki?"
Shiru tayi kamar ba zata amsa ba sai kuma ta numfasa tace "Ban yarda ba."
Da sauri ya d'agota a jikinshi yana kallon fuskarta da mamaki da kuma tsoro yace "Baki yarda ba Ryam? Kina ganin zan miki k'arya ne."
Tab'e baki tayi ta d'auke kanta daga kan shi, cikin tashin hankali da jin zuciyarshi na bugawa ba daidai ba ya cabko wuyanta ya juyo da kallonta kan shi yana fad'in "Dake nake magana kin wani shareni, fad'a min na ji mana, k'arya na fad'a miki kenan?"
Fizge kanta tayi ta mik'e tsaye tana fad'in "Kawai ni na ce ban yarda ba."
Shi ma tsaaye ya mik'e ya jawota gaba d'aya jikinshi yana kallon fuskarta yace "Me yasa Ryam? Dan kin tabbatar ina son ki ne kike min haka?"
Mutsu mutsu ta fara na son k'wacewa tana fad'in "Ba so na kake tsakani da Allah ba, jikina kake so Abdul."
Da wani matsiyacin mamaki ya kalleta yana sakinta gaba d'aya ya girgiza kai, yanda bakinshi yayi nauyi yasa shi d'agawa da k'yar yace "Ryam...soyayyar tawa...ce abar wannan..wulak'antawar? Me yasa Ryam?"
Kawar da kanshi yayi kamar mai son b'oye hawayen idonshi, girgiza kai tayi ita ma cikin sanyin jiki tace "Ni ba k'aryatawa nayi ba, amma dai nasan jikina kafi so, sheikh na tabbata kana d'aya daga cikin mutanen da suke zargina da aikata zina, yanda kake min wani kallo, da yanda kake fad'in wasu maganganu akai na, da yanda ka zo min jiya, ni yarinya ce mai k'ananan shekaru, amma ba mahaukaciya ba."
Gyara tsayuwarta tayi tana kallonshi tace "Ka d'auka ni ballagaza ce shiyasa ka zo min a yanda babu wata budurwa da aka tab'awa haka, kawai ni yanzu so nake ka kaini gidanmu dan ina so nima a rakoni kamar yanda ake rako kowace mace."
Juyawa tayi zata fita a falon da niyyar ta zauna bakin k'ofar ya rik'o hannunta, hankalinshi tashe zuciyarshi ta makance ya jawota sosai, marairaicewa yayi cikin rawar murya yace "A'a Ryam, ba haka bane kinji, karki zargeni akan haka dan Allah, kuma maganar tariyarki na fad'awa Hajia kuma ta fad'awa Abbanki kin tare d'akinki, karki damu da wannan kinji."
Da mamaki ta kalleshi tace "Ban gane na tare ba? A hakan?"
Kamar zaiyi kuka yace "To miye a ciki? Dama ai ni ko mahaifinki ne ya kalata mu rakaki d'akinki, duk wannan shirmen da ake yi bidi'a ce Ryam, dan Allah ki kwantar da hankalinki kinji."
Kallonshi tayi tana had'e hawayenta, tuna maganar Mama da kuma tabbatarwa bata da wata madafa, sai kawai ta fizge jikinta gareshi ta koma kan kujerar ta zauna, zaunawa yayi shi ma yana kallonta ya buga tagumi, cikin raunin murya yace "Ryam ke ce jarabawata, dan Allah ki taimaka min ko na samu cinye jarabawar nan a sauk'ak'e."
Jan majina tayi saboda bata son yin kuka, ganin bata kulashi ba yasa shi jingina a kujerar ya jawota a hankali ya kwantar a jikinshi, hakan ne yasa ta fashewa da kuka tana cukuikuiye rigarshi tana fad'in "Abdul bana jin dad'i, jikina da zuciyata ciwo suke min, gashi kai kuma bansan me yasa ba bana iya maka tsayayya, dolena ne na girmama wanda iyayena ma suke girmamawa."
Shafata ya ci gaba da yi yana sumbatar kanta yana fad'in "Shiiiii! Ya isa haka Ryam, kiyi hak'uri kinji, bari na miki addu'a to."
Kwantar da ita yayi kan kujerar ya zura hannunshi ta saman rigar, a hankali cike da kissa da k'warewa ya shiga shafa nonowanta da suka k'ara kumbura, shiru tayi da mamakin wace irin addu'a ce haka? Tana ji tana saurarenshi yake ta shafawa yana lailayawa har saida ta ji sak'on ya fara isar mata, gaba d'aya ta ji tana wani bank'arewa tana neman shigewa jikinshi, jin abun zai fi k'arfinta sai kawai ta fashe da kuka ta matseshi tsam.
A hankali ya laluba ya kamo bakin kuka ya had'a da na shi ya shiga tsutsa hakan ne ya tirsasa mata yin shiru tana saurarenshi.
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*44*
Hannun da taji yana zurawa ta k'asan rigarta alamun akwai gab'ar da yake son kaiwa yasa ta saurin hautsinawa ta mik'e tsaye, kallon juna suka shiga yi kamar masu tuhuma ko zargin juna, sai kuma ta dafe gaban goshinta tana yatsina fuska tace "Aouch!"
Da sauri ya mik'e yana rik'o hannunta yace "Menene? Kina lafiya?"
Cikin yatsina fuska tace "Bana jin dad'in jikina ne, bacci nake so nayi."
Murmushi yayi ya jawota suka shiga takawa a hankali, d'akin daya shiga da ita yasa ta d'ago kanta tana k'arewa d'akin kallo, kwantar da ita yayi kan lafiyayyen gadon tare da shafa kanta yace "To kiyi bacci."
Lumshe ido tayi alamar to, mik'ewa yayi daga sunkuyawar zai fita sai kuma ya tsaya, a nutse ya haura kan gadon ya d'aga kanta ya d'ora kan k'irjinshi, shafata ya ci gaba da yi yana fad'in "Bacci...bacci...bacci...bacci."
Samun kanta tayi da d'oa hannunta na dama akan k'irjinshi ta rufe ido, sannu sannu sai kuwa bacci yayi gaba dasu dukansu.
Awa d'aya ya samu a baccin nan ya tashi saboda rashin sabo, falo ya dawo ya zauna yana gudanar da wasu harkokinshi, a k'alla awa biyu ya d'auka anan zaune kafin ya shiga madafar nan, kazar daya sa mai gadi ya kawo masa ya saka a cikin na'urar d'umama abu, kafin tayi zafi kuma kokombre ya saka a blender tare da na'a na'a da citta d'anya ya markad'a, da k'aramar rariyar roba ya tace ya saka zuma ya kai fridge, yana kammalawa ya ciro kazar tare da sakata a plate ya yankata yanda zatayi daidai da cin mutum a sauk'ak'e kafin ya d'ora plate d'in a babbar faranti, lemun nan ya d'auko ya d'ora akan farantin sannan ya d'auko fresh milk ya d'ora ya nufi d'akin baccin.
Baccinta ya samu take yi har yanzu, aje farantin yayi ya nufi ban d'aki ya had'a mata ruwan wanka masu d'umi, fitowa yayi ya zauna gefenta ya rik'o hannunta yana kallon fuskarta, a nutse ya shafa kumatunta tare da furta "Innar Issa."
A hankali ta shiga bud'a idonta tana mitsikasu, saida ta bud'e duka ta saukesu fes a kan shi, tashi tayi zaune tana murza idon ta juya dan neman agogo ta ga awa nawa ta d'auka, murmushi ya mata yace "Awa hud'u babu minti goma kika d'auka kina baccin nan."
D'an matse bakinta tayi tana k'ok'arin sauko da k'afafunta k'asa, taimaka mata yayi har ta mik'e tsaye tana jin bata jin k'warin jikinta, saidai ciwon jikinta ya ragu sosai, saida suka isa bakin k'ofar d'akin ya tsaya yace "Ki shiga kiyi wanka na gama had'a miki ruwa, kiyi alwala daga nan dan 12:30 tayi."
Jinjina kai tayi ta shige ban d'akin ya rufo mata k'ofar, falo ya koma shi ma ya shiga ban d'akin dake nan yayi alwala, dawowa yayi d'akin ya zauna bakin gado jiranta, ta d'an d'auki lokaci kafin ta fito d'aure da towel babba a jikinta, kanshi na k'asa a lokacin yana ganinta ya d'aga gaba d'aya, santala santalan cinyoyinta masu kauri da haske ya fara kallo, da k'yar ya had'i wasu yawu tare da kawar da kanshi saboda alwalar dake jikinshi.
Cikin shak'akk'iyar murya yace "Ryam gaggauta muyi sallah kafin k'arfe 01:00."
Jinjina kai tayi da sauri ta nufi rigarta zata d'auka yace "Ki duba cikin drower nan akwai kaya."
Da sauri ta nufi drower ta bud'a, duka abaya ne sai kuma kaya masu taushi na bacci da hijabai, d'auka tayi ta saka wata abayar ta d'auki hijab ta saka, gabanshi ta tsaya tace "Na gama."
Mik'ewa yayi yana tsaya sosai akan sallaya yana fad'in "Na manta rabon da nayi sallah jam'i a gida, yau dalilinki zanyi hakan."
Zaro ido tayi tace "Saboda ni? To ka je masallaci mana ni sai nayi a gida."
Murmushi yayi yace "Ai anan kusa ne babu masallaci, kuma na miki alk'awarin zama tare dake na tsawon wunin nan."
Kallonshi tayi ba tace komai ba ita dai har suka kabbara sallah tana daga gefenshi, a minti ashirin da d'aya suka gama sallah har Mimi ta fara tunanin ko k'iyamu-lail zai sa su yi, suna idawa ta mik'e ta cire hijabin ta aje kan gado, mik'ewa yayi shi ma yace "Zauna ga abinci."
Zaune tayi kamar yanda yace ya aje mata farantin gabanta, hannunshi ya sa ya fara bata a bakinta shi ma kuma yana ci. Har suka gama ya bata madarar tasha shi kuma ya d'auki lemun nan ya shanye.
*Wuni* ne na ban mamaki a wurin Mimi, wuni ne da zata iya cewa ya shiga tarihin rayuwarta, yanda ya mu'amulance ta ya tafi da ita sai abun ya tsaya mata cak a zuciya da tunani, yanda ya kula da ita ya riritata ya k'ara shagwab'ata, ko kare bai yarda ta d'auka daga nan zuwa can ba, komai shi ya yake mata saidai ta ci ta zauna suyita hira, duk da mamakinshi ya sa ko sakin jikin ta kasa yi da shi, amma dai ba laifi wunin nan yasa ya tsaya mata a rai har ta fara jin tsohon a k'asan zuciyarta. Saidai abu d'aya da bata sani ba shi ne dama ba tun yau take jin shi ba, can ma rashin bawa abun mahimmanci ne da shiririta yasa bata iya fahimta ba.
20:30 tana zaune kan cinyoyinshi biyu ya d'ora hab'arshi kan k'irjinta yana danna wayarshi ita kuma tana kallon tv, lumshe ido tayi ta sauke numfashi a hankali tace "Ab..yallab'ai."
Kallon fuskarta yayi yace "Um um! Ki kirani da Abdul."
Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um! Ni tsoro nake ji."
Girgiza kai yayi yace "Tsoron me kuma? Allah Ryam kin d'aukeni kamar kakanki."
Murmushi tayi tace "Ba haka bane, kaga idan na saba da fad'in Abdul idan a gaban mutane ne fa? Kaga su suna giramamaka idan na kira sunanka za'a kalleni marar tarbiya ne."
Murmushi yayi yace "Hakane kam, to ki canza min wani sunan mana mai dad'i."
Jim tayi ta d'aga kanta sama alamar tunani, sai kuma tayi saurin kallonshi tace "To idan na ce bawan Allah fa."
Wani sanyayyan murmushi yayi yace "Haka ma yayi, babu abinda zai sani k'ara k'ank'ar da ka茂na kamar na tuna ni d'in bawan Allah ne ba wata tsiya ba."
Murmushi tayi ita ma sannan tace "Abdul nan zan kwana?"
Kallonta yayi yace "Kina son hakane?"
D'aga kai tayi alamar e, sake matsata yayi jikinshi yana shinshina jikinta yace "Um um! Gida zamu koma, ba zan iya barinki a nan ba."
Turo baki tayi gaba tace "Ni dai kawai ka barni