Showing 36001 words to 39000 words out of 185502 words
suma kamar mamanta ne, cikin nutsuwa aunty Sahura tace "Mimi kin ji lokacin da mahaifinki ya tsayar da ranar aurenki?"
Girgiza kai tayi tana kallonta alamar a'a, jinjina kai tayi ta nuna mata kud'in hannunta masu yawa tace "Kinga wannan yanzu mahaifinki ya bayar da su, ya ce muje a rakaki kiyi siyayyar duk abun buk'atarki, dan gaba d'aya wata d'aya suka saka na auren."
Da sauri ta kalleta ta kalli mama tace "Wata d'aya mama? Bai yi kad'an ba kuwa?"
Kawar da kai mama ta yi saboda kunya ba ta tanka mata ba, aunty Shapi'a ce tace "Bai yi kad'an ba Mimi, me za'a tsaya jira tunda dai kin kai minzalin auren nan, sannan ba wani karatu kike ko wani abun ba na daban da za'a ce zai ja lokaci."
Sahura ce ta d'ora da "Ba komai kinji Mimi, kiyi addu'a Allah yasa haka shi yafi zama alkairi."
Ajiyar zuciya ta sauke ba tace komai ba, Shapi'a ce tace "Ranar alhamis baku karatu saiki shirya da wuri ki zo gidan Sahura ki same su, sai mu wuce kasuwa daga nan ki siyo duk abinda ya danganci sutura."
Jinjina kai tayi tace "To insha'Allah." Mik'ewa tayi zata koma d'aki Sahura tace "Sannan Mimi, dan Allah a cikin waccen akwatin da kike da na kaya har guda biyu, an fad'a min shak'are suke da kaya dan baki da aiki sai d'inki, kiyi k'ok'ari kafin alhamis ki zauna ki ware kayanki sabbi masu kyau, saiki ajiye su gefe ki je dasu d'akin mijinki, ko ba komai zasu anfaneki suma."
Jinjina kai tayi sai Shapi'a da tace "Ki godewa Allah miji kika samu d'an babban gida mai karamci, ya ce ke ya gani yana so kuma ke kad'ai yake da buk'ata, tsinke baya so a kai miki."
K'uri ta musu da ido tana kallo da tunanin anya kuwa! Hakan ba zai jawo mata abinda ta tsana ba? Wato *raini* a wurin danginshi, ta sani ne dole ta fuskanki k'alubale daga garesu, a yanda ta fahimta shi d'in d'an masu hannu da shuni ne, ita kuma yar talaka, sannan ita ce doguwa, amma dayawa ahalinta duk wadanni ne, ta sani ne ita kanta bata cire rai da haifar yara masu irin halintar iyayenta ba, saidai hakan sam ba zai zama abun k'yama a gareta ba, to amma dangin mijin da zata aura fa? Numfashi ta sauke mai nauyi tana tunanin idan mahaifinta ya zo zata mishi magana, gaskiya a mata kayan d'aki ko kad'an ne, dan ba zataa iya ji da wulak'anci da gori har biyu a lokaci d'aya ba, *yar talakawa*! *'yar wadanni*! Shigewa tayi d'aki tana lalubo wayarta a akwati ta kunna, duk da hankalinta na kan wayar amma tana jin yanda ake ta shiga da fice a gidan, daga yanda makwabta ke ta shigowa zaka san ana shigowa dan ganin gaske dai Mimi ce aka kawowa kaya jiya babu wanda aka fad'a ma? Sannan da aka ce million d'aya da rabi da gaske?
*Masha'Allah*
Assalamu Alaikum
Masoyanmu da fatan kuna lafiya.
Muna mik'o maku godia da fatan alkhairi masu matuk'ar yawa a yadda kuka nuna mana kara da kauna wajen siyan littafinmu na kud'i.
Alal hak'ik'a munji dad'i kuma mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i.
Muna kuma k'ara kira ga masoyana wadanda basu siya ba dasu garzayo su siya domin muhimman darussa rayuwa, ilmantarwa da nishadantarwa dake cikin littafin. Dukkan wanda yaji taken littafin na *AURE YAKIN MATA* yasan littafi ne mai cike da ilmantarwa da bude ido akan irin rayuwar zaman auren da muke a zamanin yanzu don haka babu dana sani a siyan littafin.
Yadda kuke siyan littafin yana k'ara mana k'warin guiwa wajen yi maku typing din littafinmu na *KOMIN NISAN JIFA* da *Matar Mutum*, muna fatan zaku cigaba da siye don mu samu k'warin guiwar yi maku typing din littafin na kyauta akan kari ba tare da b'ata lokaci ba.
Mun yarda daku mun aminta da irin k'aunar da kuke mana, nasan kuma zaku siya littafinmu mai take *AURE YAK'IN MATA.*
*MUNA SONKU SOSAI MUNA ALFAHARI DA KASANCEWA A CIKIN DUNIYARKU.*
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke mana don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna muna kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafinmu馃グ
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:52 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*13*
Saida ta shiga gidansu Asma'u kawai ta samu damar amsa wayar Asas, sun jima suna hira wacce duk rabinta hange-hangensu ne na yanda zamansu zai kasance da kuma bikinsu, mafi yawa kam shi ne yake fad'in tsarinshi da yanda yake so ayi, ita kuma da ta ga yana fad'in duk wani abu da ita ma take da burinshi ne sai take amsa mishi da hakan ma yayi, saida ta ji sallah isha'i ta tabbatar Abba yanzu zai shiga gida sukayi sallama ta dawo gida.
*Sheikh*
A hankali ya d'aga idonshi ya sauke a kan ta yana murmushi, da kallo ya bita yanda take takawa a cikin doguwar rigarta ta bacci da cikinta daya fito sosai, saida ta zo daf da shi ta sunkuya ta aje farantin hannunta tana fad'in "sheikh na wa, ga shayinka."
Ba tare daya d'auke murmushin ba yace "Nagode, Allah ya miki albarka."
Saida ta nufi wajen wadrob d'in kayanshi tace "Ameen, nima nagode."
D'aukar kofin yayi ya shiga had'awa kan shi lipton d'in a tsanake, ita kuma gyara zaman kayanshi ta ci gaba da yi cike da fara'a da son wahaltawa mijin na ta, tana cikin gyaran ya kalleta yace "Ki had'a mana kayanmu mana, mun kusa tafiya ai."
Juyowa tayi tace "Angama sheikh, yanzu kuwa."
Murmushi ya mata ya ci gaba da kurb'an shayin, juyowa ta sake yi tace "Wannan karan ma ba zamu tafi da ko da *Saifil islam* ba?"
'Yar harara ya cilla mata yace "Rashin samun isashen lokacinki fa yasa nake ware miki k'arshen watan nan, idan muka tafi dashi me zamuyi?"
Da murmushi a fuskarta tace "Me za muyi to dama? Na d'auka hutu zamu tafi."
Wani malalacin murmushi yayi yace "Za muyi yak'i ne."
Girgiza kai tayi ta juya tana dariya tace "In an girma a san an girma, ka fa tuna miji kake nemawa Eesha, kuma ka ce ko yanzu ka samu wanda ya dace zaka aurar da ita ne."
D'an zaro ido yayi yace "To auren Eesha zai hana nawa auren farin ciki ne? Haihuwar Eesha ba zai hanani sake yi miki wani cikin ba idan kika sauke wannan, saidai ku haihu tare da 'yarki."
Zaro ido tayi tace "Lahhh! Har da surukin na mu sai yaga mun haihu?"
Jinjina kai yayi yace "Ai da gani na yasan banyi tsufan da zan kasa abinda zai iya yi ba shi ma."
Girgiza kai tayi sosai tana dariya tace "Gafarta malam, gyaran kimtsi."
Kallonta yayi ba fara'a a fuskarshi yace "Gafarta malam, ina ma laifin ki ce Abdul."
Da sauri ta juyo tana fad'in "Wace ni? Ka rufa min asiri malam, ai fad'in wannan suna yafi k'arfin bakina."
Murmushi yayi yace "A haka kuma babu wanda ya kai ki sani na."
Murmushi jin kunya tayi tace "Wannan kuma ai daban ne ko sheikh na wa."
Girgiza kai yayi yana sakin murmushi kawai saboda tuna wacce kai tsaye tace masa Abdul, Abdul! Har yanzu sunan na mishi amsakuwa a kunnenshi, duk da a cikin rud'u da kid'imewa da tsoro ne ta fad'a saboda tsoron mahaifinta, amma dai sunan data kira yayi tasiri sosai ta yanda har yanzu idan ya tuna ya kan saki murmushi shi kad'ai.
*Asas*
K'atuwar sanda ce a hannun Hajia ta d'aga tana fad'in "Ashraf zan buga maka sandar nan a kai idan baka shanye magasin nan ba kaban kofin."
Yatsina fuska ya sake yi ya kalli Hajia dake tsaye gabanshi ta zaunar dashi ta tisashi a gaba, a hankali ya kalli kofin data jik'a maganin na gargajiya a ciki, kamar zaiyi kuka yace "Hajia wai dole sai na sha ne? Ki aje min har a jima mana."
Girgiza kai tayi tace "Ko kad'an, ai dole ka shanye ka bani yanzu yanzun nan, kasan daga ina nasa aka amso min maganin nan?"
Sake had'e fuska yayi yace "Wallahi ni dai Allah yana gani na gaji da shan maganin nan."
Buge mishi baki tayi tana fad'in "Uwa ka, mutumin banza kawai, god'e-god'e da kai amma baka san shan magani, kuma kafi kowa sanin larurarka, yanzu da ka sa aka nemo maka auren 'yar mutane haka zaka sakata titseyeka kasha maganin?"
Turo baki yayi yace "Hajia ni Mimi ma nasan ba zata titseyeni da sanda ba ai, zata lallab'ani ne har na shanye saita bani sweet na sha."
Yanda yayi maganar da kanne ido d'aya yasa ta dungure masa kai tace "Maza bani kofin na gaji da tsayuwar nan."
Rufe ido yayi yasa yatsa biyu ya rufe hancinshi ya kifa kofin a baki, da k'yar ya shanye kamar zaiyi amai kafin ya mik'a mata kofin ya mik'e ya nufi fridge, zaune tayi tana aje sandar hannunta tace "Shan magani ya zama aiki, kamar ba namiji ba."
Dariya yayi ya kurb'i ruwa ya fita waje yana kuskure bakinshi, dawowa yayi yana fad'in "Hajia magani fa ba dad'i ne dashi ba, ai ke k'ok'ari ne dake da har kike zuba guda biyar a bakinki lokaci d'aya."
Girgiza kai tayi tana tab'e baki, kallonta yayi yace "Hajia zan fita, saina dawo."
Kallonshi tayi ita ma tace "To ina aka nufa yanzu? Nasan dai ba'a zuwa zance da yamma haka."
Dariya yayi yace "Zan je zance amma sai anjima, yanzu zan je gidansu " Sadeeq ne ya kirani yace babu mota a hannunshi."
Jinjina kai tayi tace "Yayi kyau, amma ni yaushe zaka kawo min surukuwar ta wa ne na ganta? Ko sai randa ta shigo gidan zamu ga juna."
Dariya yayi yace "Hajia karki damu, da zaran na je yau zan mata magana, idan iyayenta sun amince saina kawo miki ita ta wuni."
Jinjina kai ta sake yi tace "A'a ba sai ta wuni ba, ni da bana da wasu yara yan mata a gidan, kaga ai indai mai kunya ce ko numfashi ba zata sauke ba har sai tabar gidan nan, tsawon wuni d'aya kuwa ai akwai takura."
Jinjina kai yayi yana shafa sumar kanshi yace "Shikenan Hajiata, yanda mukayi da ita zan fad'a mki."
Jinjina kai tayi ta bi shi da kallo har ya fita, daga nan b'angarenshi ya wuce ya shirya ya fita ya bar gidan bayan yasha gargad'i a wurin Hajiar ce wa kar ya jima a waje ya dawo.
*Mim-Sas*馃槣
Ana idar da sallah isha'i ta hana kai da kawon su Yaseen ta k'unshesu a d'aki suna karatu, ta k'alk'ale gidan tsaf ta kawar da komai yanda ya samar da fili kuma a tsaftace, kujeru ta aje guda biyu na roba kafin ta bankawa d'akinsu turaren tsintsiya, wanka ta shiga a k'alla minti ashirin ya d'auketa ka rantse canza fatarta take yi a ciki, haka ma a gurin shafa mai da tsantsara sassauk'ar kwalliyar data fito mata da tsarin ainihin kakkauran fuskarta, wata galleliyar rigar shadda ta saka wacce bata jima da d'inka ta ba da kud'in data yafata hannun wani Alhaji Bukar, tunda ta karb'i kud'in ta yi bloqu茅n lambarshi ta rufe duk wata k'ofa da zasu had'u. Wani shara-sharan mayafi ta d'auka ta shafeshi da turarenta mukhalat, fitowa tayi farfajiya ta d'auki jug d'in data wanke sabuwa da sai azumi mama ke aiki da ita, zata shiga d'akin ta ji wani sassauk'an numfashin mota a k'ofar gidan, da sauri ta kalli k'ofar ta tabbatar a nan mota ta tsaya, shigowa tayi d'akin ta kalli Yaseen da suke binta da kallo tace "Fita waje ka gani idan shi ne sai ka masa iso ya shigo."
Gyad'a kai yayi shi dai ya mik'e ya fita, mik'awa mama jug d'in tayi tare da d'auko d'an k'aramin bokitin data had'a jus a ciki a abarba ta saka k'ank'ara tace "Mama juye min shi a ciki."
Karb'a tayi ita ma tana kallonta kawai ta shiga yin abinda tace, dan tunda rana take wannan kimtse kimtsen da shirin tarbanshi, abinci ma yau da kanta ta girka na musamman inda mama tayi ta mamakin inda ta iya sarrafa wannan abu data ga ta had'a, domin kuwa kud'i ta kashe sosai wanda ta amsa a hannun maman ita ma wanda Abba ya bata ne tayi abun buk'atar ta.
Mayafin ta d'auka ta rataya a kafad'a tana k'ara kallon kan ta a madubin, d'aurin d'an kwalin ya zauna mata a kai yayi kyau dan irin mai hawa-hawan nan ne ta yi sai kuma ta ja shi baya sosai ta yanda ya bayyanar da cikon dandazon gashinta bak'i, kallonta mama tayi tace "Ki d'ora mayafin da kyau mana, haka zaki je masa?"
Kallon mama tayi tace "Mama, ai haka shi ne daidai, kinga had'uwarmu ce ta biyu, waccen lokacin da hijab ya ganni, kuma kinga ai addini ya yarda ka fito yanda mai son aurenka zai kalleka ya tabbatar komai ya masa yanda yake buk'ata."
Galala mama tayi da baki ta sake d'aga kan ta da kyau ta kalleta dan a tsaye take tana k'ara gyara fuskarta tace "Kenan idan ya shigo zaune zaiyi ke kuma a tsaye kina jujjuyawa yana k'are miki kallo?"
Murmushi tayi tace "A'a mama ba haka ba kuma."
Girgiza kai tayi tana fad'in "Allah ka shirya mana zuri'a." Da murmishi Mimi tace "Ameen mama."
Daga farfajiyar suka ji murya a tausashe a nutse a hankalce ana sallama a sirrince, Yaseen dake gaba ne ya sake amsa mishi yana fad'in "Suna ciki, bari na musu magana."
D'akin ya shigo da sallama shi ma yana fad'in "Mama gashi nan ya shigo."
Zaro ido tayi tace "To ya zanyi? Ni zanje muyi zancen?"
Dariya Mimi tayi murya k'asa k'asa tace "Mama ki shirya da kyau dan zaki fito ku gaisa."
Girgiza kai ta shiga yi alamar a'a, d'an turo baki tayi tace "To nan zan shigo dashi ya gaisheki."
Takalminta ta saka kalar ruwan hoda da suka dace da shaddar da kuma gyalenta, a hankali cikin tako kamar d'awisu ta shigo takowa tana fitowa harta yaye labulen ta fito bayan ta d'an sunkuya gaba d'ayanta, tarr! Idonsu suka sark'e dana juna domin kuwa akwai hasken fitila a k'ofar d'akin, a tare suka saki murmushi kowa na sake kafe d'an uwanshi da kallo.
Shi kan shi saida ayar nan ta sake fad'o masa a rai da take magana akan buwayar Allah, mai fitar da matacce a jikin rayayye, ya kuma fitar da rayayye a jikin matacce, Allah mai yin yanda ya so, mai yin sakamako ba tare da hisabi ba. Yanda ta fito kamar wata yar sarkin Istanbul, ko waye kai ka had'u da ita a waje ba zaka ce ta tab'a shiga wani wai gidan k'asa ba, amma a ciki take rayuwarta, kuma bata kunyar a san da haka.
Ita kan ta irin kyawun da yayi sai take tabbatarwa kan ta lallai ta ciro *fure a cikin k'aya*, dan kuwa irinsu Asas bibiyarsu ake kamar a yi farautarsu, da k'ok'on bara yan mata ke neman irin su, yanzu data samu sai take ji kamar tayi hannun riga da kwanciyar hankali kenan, dan tasan dole tasha fama wajen tsare da kula da mutumcinshi, musamman a yanda ita ma ta kula mazan wasu, dan ita tana da ma tsari da idan ka nace mata ne zata kula ka. A nutse ta k'araso gabanshi ta tsaya kamar yanda shi ma yake tsaye cikin wata dakakkiyar shadda bak'a k'irin sai k'yalli take tana d'aukar ido kamar zaka matsata mai ya fito, ya had'u sosai yayi kyau a cikin shaddar da ke d'auke da d'inkin zamani.
Sunkuyar da kan ta tayi cikin jin kunya murya k'asa k'asa tace "Barka."
Murmushi ya sakar mata yace "Barka madame Asas, gani na zo."
D'an d'ago da idonta tayi ta kalleshi da fara'a tace "Barka da zuwa kurkukun mu."
Lumshe ido yayi yan ci gaba da murmushi yace "Kurkukun dake d'auke da mace kamar Mimi ta a ko ina yake zan iya nemanshi na zauna a ciki."
Murmushi tayi har yana bayyanar da hak'oranta tace "Ka zauna to."
Cikin kafeta da ido yace "A ina kenan?"
Nuna mishi kujerar tayi tace "A nan." Murmushi yayi yace "Tabarma nake so, domin na zo nan ne da niyyar na ci abinda kika girka min da hannayenki."
Rarraba ido tayi tace "Tabarma kuma?"
Jinjina kai yayi yace "E, tabarma." Murmushi tayi tace "To me kake so ka ci?"
Rumgume hannaye yayi yana kallon fuskarta yace "Me kika dafa min na tarbena?"
A sanyaye tace "Tuwon masara, miyan kuka."
Wani sanyayyen murmushi yayi shi ma yace "Masha'Allah, abunda na wuni ina buk'ata kenan yau, kawo min tabarma da tuwo na ci Maah, yunwa nake ji."
Da mamaki ta kalleshi da son gano wai gaskiya yake fad'a kuwa, cike da tabbaci yace "Ki kawo min mana."
Rarraba ido ta shiga yi dan yau