Showing 114001 words to 117000 words out of 185502 words
akayi sallah asuba ta gama duk azkar kafin ta kwanta rama baccin da bata yi ba.
*06:10*
Kiran wayarta ya tasheta, da k'yar ta bud'a idonta da sukayi mata nauyi sosai dan baccinta baiyi nisa sosai ba, ba tare data duba lamba ba kawai ta d'ora a kunne a magagin bacci da tunanin cikin k'awayenta ne tace "Hello, dallah miye haka zaki katse min bacci na? Wannan ai shiga hakk'i ne."
Sautin k'ayataccen murmushi ta ji a cikin wata tausashiyar muryar data sakata bud'a ido sosai yace "Ki gafarce ni yan matana, na d'auka a daidai lokacin nan kina azkar ne, amma baccin na ki ma samun nutsuwata, a huta lafiya zan sake kira anjima."
Cikin muryar rad'a yace " *Ina k'aunarki*."
K'it! Ya datse kiran ita kuma sororo ta bi wayar da kallo, wata ajiyar zuciya ta sauke tana tashi zaune ta gyara zama, murmushi tayi tana girgiza kai tace "Wai yana k'aunata, ko kunya baya ji ya haifeni yake fad'an wannan maganganun."
Tab'e baki tayi ta yatsina fuska tace "Tsoho kawai."
Kaikatawa tayi da niyyar komawa ta kwanta sai kuma aka k'wank'wasa k'ofar d'akin, mik'ewa tayi tana d'aukar kallabi ta d'ora a kan ta, tana bud'ewa taga Hajia da shiri da alama fita zatayi, da girmamawa tace "Inaa kwana Haji."
Da kulawa ta amsa da "Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?"
Ita ma da kulawa tace "Lafiya lau, Hajia fita zakiyi ne yanzu?"
Cike da jimami tace "Fita zanyi Mimi, Hafsat ce jikin nan sai a hankali, zan je dai yanzu dole zan tisata gaba muje asibiti, dama dan na fad'a miki idan kin tashi ki d'ora abinda zaki ci ne dan tare da Salamatu zamu tafi."
Da yanayin alhini tace "Ayya Allah bata lafiya, insha'Allah zan d'ora."
Da fara'a tace "Yawwa to, kuma zan kiraki idan ma zamu iya jimawa a can dan kiji halin da ake ciki."
Jinjina kai tayi tace "Zan ji dad'i idan ya zama babu wata matsala."
"Allah ya tabbatar." Ta fad'a tana d'orawa da fad'in "Anjima kkawarki zata zo Asma'u, dan naga ba zata ji dad'in zama a can ba shiyasa na ce ta dawo nan."
Da fara'a tace "To shikenan, Allah kawota." "Ameen." Ta fad'a tana wucewa, bin bayanta tayi saida ta rakata har farfajiya, ido biyu kawai sukayi da Salamatu a k'asan mak'oshi tace "Na kwana." A zuciyarta ta k'arasa da cewa "Lafiya."
馃ぃ _Ku fahimta fa, ba gaisheta tayi ba fad'a mata tayi ta kwana lafiya._
Salamatu dai da kallo ta bita dan ita yarinyar tafi mata kama da masu shafar aljanu, saida ta ga fitarsu a gidan kafin ta koma ciki a falo ta zauna ta kunna tv.
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:57 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*37*
Daga kallon nan bacci ne ya d'auketa dan saida ta bincike receiver nan amma tashoshin nan dai ne tsiraru, 09:45 daddab'ata Asma'u tayi da shigowarta kenan, bud'a ido tayi a nauyaye tana kallonta, da k'yar ta yunk'ura ta tashi zaune tana sake kallonta, tunawa fa jiya ta cizgata dayawa sai kawai ta d'auke kan ta, zaune Asma'u tayi a inda ta d'auke k'afafunta tana fad'in "Bacci kike sha a bin ki?"
Kallonta tayi kallon dake nuna ina jin haushinki, murmushi Asmaa'u tayi tace "Haba Mimin Asma'u, kiyi hak'uri mana komai ya wuce ai."
Turo baki tayi gaba tace "Kin tabbata ba zaki sake ba?"
Dariya tayi tace "Wannan shagwab'a haka kamar ana gaban sheikh, to na tabbata ba zan kuma ba."
Harara ta galla mata tace "A gaban carbi nake iyakar sheikh."
Mik'ewa tayi zata shiga d'akinta dan yin wanka Asma'u tace "Dan Allah me kika dafa da zan iya ci ne? Yunwa fa nake ji."
Juyowa tayi tace "Baki ci komai a gidanki ba?"
Girgiza kai tayi tace "Ban ci ba."
Tab'e baki tayi tace "Ni ma kuma ban dafa ba, in zaki shiga madafar da kanki to."
Girgiza kai Asma'u tayi tace "Naki salon karb'an bak'in kenan?"
Juyowa tayi tace "Ke ce bak'uwar? Ai nan gidan sirikarki ne, ko kin manta ne?"
Murmushi kawai tayi tace "Hummm!" Dan bata so su tado maganar data shafi ranar d'aurin aurensu ko kuma baya, d'aki ta shiga tayi wanka har Asma'u ta kai kayan data zo dasu d'akin da Mimi take, fitowa tayi ta shirya cikin doguwar rigar kanti mai kyau da d'an kwalin daya dace da ita.
Tana fitowa ta samu Asma'u zaune tace "Me kika dafa mana?"
Zaro ido tayi tace "Me na dafa? Me kuwa zan dafa daga zuwana?"
Tsaki tayi tace "Karki dafa d'in, shiga zanyi yanzu na had'a sauce na k'wai da doya, ko kallona kikayi ina ci Allah ya isa zan miki."
Mik'ewa tayi ta bi bayanta tana fad'in "Tare zamu je ai ki dafa a gabana na gani, kinsan babu abinda nake da buk'atar k'warewa a kan shi yanzu kamar girki."
Ba tace komai ba har suka shige madafar dan in zata iya tunawa tasan waye Asas a wannan fannin, yanda yake so matarshi ta zama yar kwalliya haka yake so ta zama gwanar girki, shiyasa ta dage a lokacin ta dinga koyon sababin kala na yan zamani, saidai kash ta auri old man da ta tabbatar tuwo ne cimar sa.馃槑
Mimi na fasa k'wai Asma'u na yanka albasa suka shiga hirarsu ta rayuwa, saidai dukansu babu wacce ta tab'o hirar bikinsu ko kuma mazansu kamar dai kowa da abinda yake b'oyewa a zuciyarshi, Mimi na cikin soya sauce d'in ta wayarta ta shiga kururuwa, jim tayi dan a take tayi tunanin shi ne, juyawa tayi ta koma falo inda ta bar wayar, tana dubawa sai ta ga lambar Hajia ce data saka mata lambar sanda suka dawo daga asibiti, d'auka tayi da ladabi tace "Assalama alaikum."
Daga wajen Hajia ta amsa da "Wa'alaiki salam, Mimi."
"Na'am." Ta fad'a a sanyaye, d'orawa tayi da "Dama dan na fad'a miki ne gamu a asibiti har yanzu..."
Da sauri tace "Hajia lafiya? Jikin nata ne?"
Amsa mata tayi da "Lafiya lau Mimi, Hafsat dai gata ma har ta haihu."
Da d'an k'arfi tace "Haihuwa kuma? Cikinta ya isa haihuwa dama?"
Da murmushi kamar tana gabanta tace "Bai isa haihuwa ba tunda ko wata bakwai bai shiga ba."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Allah sarki, me aka samu?"
A raunane tace "D'iya ce gata can a kwalba an sakata dan bata kai haihuwa ba."
Cike da tausayawa tace "Ayya! Allah ya rayata akan sunna, Hajia to kuna buk'atar abinci ne?"
Cike da jin dad'in karamcinta tace "Kinga kam kamar kinsan ina tunaanin yanda zamuyi."
Da 'yar fara'a tace "Shikenan Hajia dama nima yanzu kad'ai na shiga madafar, bari na k'arasa sai mu je mu kai muku."
Da fara'a tace "Asma'u ta zo kenan?"
"E Hajia ta zo." Taa fad'a kai tsaye, Hajia ce tace "To shikenan dreba yana nan idan kun kammala sai ku ce ya kawo nan asibitin sheikh."
Jim ta d'anyi da tunanin dama yana da asibiti ne? Sai kuma ta tab'e baki tace "To Hajia."
Da haka suka yanke kiran ta shiga da sauri madafar suka k'arasa aikinsu tare Asma'u, hibajinta zumbulele na wajen sheikh ta saka saidai duk da Asma'u tace "Ki d'aura nik'ab mana."
Sai kuwa ta d'aga kafad'a tace "Na k'i d'in, idan ya dawo ki fad'a masa."
Dariya tayi tace "Wahalar fad'a masa ma zanyi? Ai zai ji a jikinsa kuma zai matsi mutum wallahi a hannu."
Sak'e tayi tana kallonta da alamar rashin yarda da kai tace "Me kike nufi? Ko dai shi ne ya fad'a miki?"
Dariya Asma'u tayi tace "Kin tsargu kenan? Ke ma ai kinsan ko gaisuwa da k'yar mukeyi bare magana irin wannan."
Tab'e baki tayi suka fita a gidan indz Kabiru ya d'aukesu zuwa asibitin.
*Tunisie*
Zaune yake k'afa d'aya kan d'aya yana danna wayarshi jefi jefi kuma ya d'an kalli Asas dake kwance gadon duba marasa lafiya da likitan ke dubashi duk da a rufe wurin yake da labule, yana kuma jin tambayoyin da yake masa har da tambayar yana da aure? Yaushe yayi auren? Mayar da duban yayi kan waya yana son kiran Hafsat saidai kuma baya son shiga hakk'in likitan, aje wayar yayi tare da zubawa wani hoto dake bayan kujerar likita mai d'auke da sassan kayan cikin mutum, motsin daya ji yasa shi saurin kallon wurin, likitan ne ya zauna akan kujerarshi yana kallon Asas dake saka rigarshi, saida ya zo ya zauna kafin ya kalli sheikh.
Likitan ba wani babba bane dan sheikh ma zai iya yin k'ane dashi, cikin wani kwarjini da sheikh d'in ke masa ya sassauta muryarshi a harshen turanci yace " Matsalar ta shi na ga ba kamar yanda nayi tunani ba, da nasan haka ciwon na shi yake da ban bari kuyi wahalar zuwa ba, a magani kawai zan d'orashi daga can ma."
Gyara zama sheikh yayi cikin k'wamewa sosai yace "Ba wata matsala bace? Suma fa yake idan ciwon ya tashi, ya jima yana wahala."
Murmushi yayi yace "A gaskiya abinda bincike na ya nuna min kenan, gashi har jininshi da aka d'iba da kuma scanin da aka masa duk ban ga wata matsala ba."
A hankali sheikh ya kalli Asas shi ma kuma ya kalleshi, numfashi suka sauke a tare kafin likitan yace "Zan d'orashi a magani na kwana bakwai, na tabbata zai warke daga ciwon nan har abada, idan kuma bai samu lafiya ba to gaskiya saidai ku hak'ura da larurar nan."
Kallonshi sheikh yayi yana jinjina al'amarin bayahude, wato ba zai ce a kaishi wurin wani ba yana ganin shi ne k'arshen k'warewa? Wata ma'aikaciyar lafiya ya kira wacce ita ta musu jagora zuwa d'akin da za'a kwantar da shi, kaya ta bashi ya canza na jinya kalar shud'i kafin ta fita, jim kad'an ta dawo tare da likitan da d'an haranti a hannunta d'auke da magani, suna kallo Asas dake zaune likitan ya b'alli magani yasa a k'aramin kofi mai kama da tangaran, maganin dake gari ne dandanan ya jik'a, sirynge yasa na allura ya daidaita daga bakin 5 cl ya zuk'a, mik'awa ma'aikaciyar yayi ta d'ora a faranti sannan ya mik'awa Asas na cikin kofin ya shanye, fita sukayi yana sake jadaddawa ma'aikaciyar da k'arfe 05:00 na yamma ta bashi sauran maganin, kuma ta kula haka zata dinga mishi zai dinga dubashi lokaci lokaci.
Suna fita kira ya shigo wayar sheikh, yana dubawa yaga Hajia sai bai d'auka ba dan yasan za'a ja kud'i sosai, saida ta tsinke sannan ya maida kira, a gaggauce ta d'auka a lokacin dan zasu tafi da Hafsat asibiti ne, yanda ya ji muryarta yasa shi saisaita nutsuwarshi yace "Hajiarmu, nutsu ku fad'a min abinda ke faruwa?"
Daidaita nutsuwarta ta tayi tace "Sheikh Hafsat ce ba lafiya, ina so na kaita asibiti ne."
Lumshe ido yayi yana jin zuciyarshi ta canza bugawa, wani sanyi yaji jikinshi yayi lak'was kafin a raunane yace "Hajiarmu na damu akan cikin nan nata, ina yawan fad'a mata ta je asibiti sai ta ce to kawai, dan Allah Hajia a kaita asibiti a dubata."
"To, to yanzu dama can zamu." Ta fad'a alamar a gigice take, yana aje wayar Asas dake kallonshi yace "Lafiya? Me yake faruwa da Hafsy?"
Kamar zai fashe da kuka yace "Bata da lafiya, zasu kaita asibiti ne."
Cike da tausayawa yace "Ayya! Allah bata lafiya."
"Ameen." Ya fad'a a hankali, mik'ewa yayi daga kujerar da yake zaune yace "Ni zan fita, kaga sun ce ba sai na zauna tare da kai ba, zasu kula da komai."
Yar dariya Asas yayi yace "Salo ne ai na cin kud'in mutane."
Hararenshi yayi yace "Kuma kaga salon ya min, tunda zai bani damar fita na je yawona."
Waro ido yayi yace "Au! Dama wahala kake tunanin zakayi? Lallai ma zan fad'a ma Hajia."
Tab'e baki yayi ya nufi hanyar fita, cike da zolaya Asas yace "Ashe dama da shirin shak'atawa ka zo shiyasa na ganka yau cikin k'ananan kaya."
Girgiza kai yayi yana murmushi bai ce komai ba ya fice, yana rufo k'ofar wata tsohuwa na rik'e rigarshi ta fashe da kuka cikin harshen french take fad'in "Dr. Yarinyata zata mutu, muje ka duba ta."
Galala yayi yana kallonta sannan ya kalli jikinshi daga k'asa har sama, bleue rigar daya saka shemise ya tank'wasa hannayen zuwa gwiwar hannu da bak'in wandon daya saka na lallausan yadi sai kuma bak'ak'en takalmi k'afa ciki su ne suka sakata kiranshi likita? Tab'e baki yayi tare da bin bayanta dan tuni taja rigarshi alamar dai a rud'e take, suna shiga d'akin na kusa da su takawa yayi har daf da gadon da matashiyar ke kwance kamar gawa, wani madanni ya danna hakan yasa ya d'anyi k'ara kad'an girrr! Ko minti d'aya ba'ayi ba sai ga ma'aikaciyar jinya ta shigo d'akin da farantin magani, yana ganin ta fara duba yarinyar kawai ya fice a d'akin yana fatan samun waraka ga kowa.
Bayan minti talatin yana zaune a wani k'aramin shagon shan coffee ya sake kiran Hajia, labarin haihuwar Hafsat kawai ta fad'a masa, da mamaki yace "Hajia ta haihu fa? Amma ai cikinta ko wata bakwai baiyi ba."
Da fara'a tace "Ai kam dai ta haihu, saidai abinda aka haifa yana cikin kwalba."
Lumshe ido yayi a sanyaye yace "Ya Manga take?"
Murmushi tayi tace "Lafiya k'alau take babu wata matsala, bacci dai take."
A tausashe ya furta "Alhamdulillah ala kulli hal."
*Niger*
Suna zuwa asibiti sun samu d'akin da take kusan a cike da mutane, haka kawai Mimi ta samu kanta da jin kunya da kuma jin dad'i data zo da wannan hijabin, ajiye kwanukan sukayi suka samu wuri suka zauna a kan tabarma inda su Aisha suke, tunda suka shigo ta kasa kallon Hafsat ta furta ko da kalmar a, kanta na sadde k'asa taji Hafsat tace "Mimi sannu da k'ok'ari, hada wahala haka?"
Da sauri ta kalleta, tun ranar kamu rabonta da ita, ta d'auka idan suka had'u zata shak'i wuyanta ne ta mata d'an banzan duka ai, sake sunkuyar da kanta tayi tana mirmushi mai d'auke da kunya tace "Ba komai aunty Hafsat, ya jikin?"
Da murmushi sosai a fuska tace "Jiki da sauk'i sosai."
Daga haka basu sakewa juna magana ba, haka dangi suke ta kai da kawowa ana ta hira, Asma'u da Mimi kuma dake bak'i ne a cikinsu su dai suna saurarensu kawai, wani abun suyi dariya wani su murmusa, Mimi kuma kunya da takaici ke rufeta idan aka nunawa wasu ita aka ce ga matar sheikh, musamman da wata abokiyar wasa ta kalleta tace "Kai kai kai! Wannan ce sheikh ya kwasa, gaskiya yan mata karki yarda, ya za'a had'aki da tsohon gwangwani wanda ya kusa ritaya a duniya ma ba'a aiki ba, ke kika yarda? Lallai da ni ce ke saina nunashi da bakin wuk'a nace ya sakeni."
Dariya wasu sukayi sai Hafsat da tace "Ke dai kina jin haushin rasa mijinmu da kikayi."
Kallon Mimi tayi tace "Kinga Mimi kafin tayi aure ba irin asirin da batayi ba dan mijinmu ya aureta, da k'yar ta shafa masa lafiya har kotu aka shiga tsakaninsu."
Dariya aka yi sai Hajia da tace "Yanzu *Karima* d'an nawa ne ma gwangwani? Kinsan fa da a gabansa kike ba zaki iya furta a ba."
Cikin d'aga murya Karima tace "Hajia ai gaskiya na fad'a, shi ma tunda ya zama malamin duba ne ya asircemu indai muna gabansa bama iya d'aga kawunanmu mu kalleshi saboda cuta."
Kallon Mimi tayi tace "Ke k'anwata bari in fad'a miki, yana dawo ki ce ya maida ke gidanku kinji, daga shi har Asas d'in banga wanda ya dace dake b芒 tubarkallah dake, idan kuma kikayi wasa yana dawowa nan da wata tara bikin sunan d'anki ko d'iyarki zamu zo, kinga kenan dai kin tabbata a *matar tsoho*."
Sunkuyar da kai ta sake yi inda Hafsat tayi murmushin yak'e sakamakon tunawa yanzu fa duk yanda suke da sheikh ko dan sauke hakk'in yarinyar nan sai yaje mata, sanyayyan numfashi kawai ta sauke aka ci gaba da hira ta raha da nishad'i har su Aisha suka zo ganin k'anwarsu bayan dawowarsu daga makaranta.
Bayan sallah la'asar Rakiya data kula da Hafsat ta shigo tana fad'in "Hajia zaku iya tafiya gida, ba wani abun yanzu insha'Allah."
Take idon Hafsat suka kawo ruwa da tunanin tafiya da zatayi ta bar yarta anan, kallonta likitar tayi tace "Ayya madame! Kiyi hak'uri karki damu, ko ba yarinyarki bace ai zamu kula da ita saboda abinda sheikh ya d'aukemu muyi kenan, bare kuma 'yar sheikh guda?"
Murya a raunane tace "Dan Allah yaushe zan iya zuwa ganinta to?"
Shiru ta d'anyi dan gaskiya ba dan tana ita ba a tsari da dokar asibitin nan da wata biyu da yarinyar zatayi ba zai wuce ta zo ta ganta sau uku ko kad'an da haka ba, amma dake ita ce sai tace "Madame zamu iya yi miki alfarmar zuwa ganinta sau uku a kowane wata."
Da sauri Hafsat ta kalli su Hajia ta kalli Rakiya tace "Sau uku kawai? Amma kuma taya zan rayu nesa da 'yata."
Murmushi tayi tace "Karki damu madame, zata kasance cikin kulawarmu."
Kamar zata fashe da kuka tace "To amma Rakiya ina so 'yata tasha nono ko kad'an ne."
Da fara'a tace "Wannan ba matsala bane madame, duk sanda kika zo ma idan kina so za'a iya tatsa mata nonon na ki sai a bata."
D'an murmushi tayi ta jinjina kai alamar to, da haka ta mik'a musu katin maganin da za'a siya kafin ta fita, haka suma suka mik'e suna shirin tafiya, Hajia ce ta fara kallon Mimi tace "Mimi ku zaku wuce gida ke da Asma'u, idan kunje saiku d'ora abinda zaku ci ko? Zuwa dare zan dawo nima."
Jinjina kai sukayi a