Showing 75001 words to 78000 words out of 185502 words
dasu na girma, hakan yasa duk zaka gansu kamar rainon turawa, kowane da jikinshi masha'Allah kurtib'a kirtib'a dasu. Aisha data jima da lura da kallon da yake mata haushi ne yasa ta d'an jan tsaki, a hankali sheikh ya kalleta tare da bin wurin data harara ta d'auke kan ta, ido hud'u sukayi da Saminu da a lokacin yake kan kallonta, da nutsatsun idonshi ya aika mishi da sak'on a sauk'ak'e, a take wani bazawarin kwarjinin sheikh ya rufeshi, duk da dama dai a girme zai bashi yan shekaru amma ba wasu sosai ba da zasu jawo har ya ji wanan matsayacin shakkar tashi.
Bud'a k'ofar d'akin da akayi yasa duk kowa ya gyara tsayuwa yana zubawa k'ofar ido, ganin likitoci ne guda biyu sai kowa ya sake matsawa daf dasu dan jin me zasu fad'a, Asas na gaba kusa da likitan yana kallon bakinshi, inda sheikh ke tsaye a inda yake saidai ya kasa kunnuwanshi dan yaji me zai fad'a shi ma kuma tsaf yake lura da motsawar bakin likitan. A hankali likitan ya goge zufar fuskarshi yana k'are musu kallo yace "Kune danginta?"
"Eh mune." Abba da Asas suka fad'a a tare, numfashi likitan ya sauke yace "Alhamdulillah munyi nasarar ceto rayuwarta, saidai da mamaki yanda kamar wannan tasha wannan guba mai kaste hanjin ciki a lokaci d'aya, sa'a d'aya shine ba wani dayawa tasha ba bare ta gaggauta illatata, da yanzu fa wata maganar ake ba wannan ba."
Duk zaro ido sukayi tare da fad'in "Guba kuma?"
Jinjina kai yayi yace "Tabbas guba."
Sallalami aka shiga yi inda Asma'u tace "Amma garin yaya? Me ta ci a wurin?"
Salma ce tace "Cake ne ai sai lemu."
Asma'u ce tace "Amma ai mu ma mun ci, kuma gashi ba abinda ya same mu."
Cikin muryar kuka Zeinaba tace "To ai bamu sha lemu ba, saidai in a lemun aka saka."
Cike da tuhuma Asma'u tace "Ai yar uwarsu ce ta bata lemun."
Fanna ce ta harareta tace "Wace yar uwarmu kuma? Wannan mai rawar kan tsiyar? Kinga tayi kama da ahalinmu?"
Aisha ce cikin ladabi tace "Ai mun d'auka yar uwar aunty Mimi ce."
Asma'u ce tace "Basu had'a komai da ita ba, m没 ma nan kallon yar uwarku muke mata."
Asas ne yace "To kenan wacece?"
Duk tab'e baki sukayi suka ce "Uhum!"
K'wafa yayi kawai yace "Ba wanda ya santa kuma?"
Salma ce tace "Bamu santa ba gaskiya, amma ai ba'a rasa hotonta tunda tana ta shigewa jikin Mimi."
Da sauri yace "Na gani." Jiki na rawa ta shiga duba hotunan da suka d'auka inda sheikh ke hangen komai daga can yana jan tsakin ganin Salma, ita ma dai shigarta kamar ta sauran, amma dake ta fito da gashin dokin data saka ga kwalliyarta tafi ta kowace yawa, sannan ga wayar daya gani a hannunta sai yake ganin wannan ba k'awar k'warai bace, watak'ila ma ita ta lalalata mi shi Ryam "Mtssss!" Wani tsaki ya kuma ja yana kallon Asas daya ciro wayarshi ya d'auki hoton Feena sannan ya mik'awa Salma wayarta.
Sallalami suka shiga rabkawa har likita ya rab'asu zai wuce tare da wata a bayanshi Asas yayi saurin cewa "Yanzu babu wata matsala likita?"
Kallonshi yayi yace "Babu insha'Allah."
Zai wuce Abba ya sake bin bayanshi yana fad'in "Likita." Tsayawa yayi tare da kallon k'asanshi sosai ganin Abba ne yasa shi sunkuyawa cikin ladabi, cikin rad'a Abba yace "Likita yarinyar nan dake kwance da safe k'arfe 08:30 za'a d'aura aurenta, kana ganin ba wata matsala sosai za'a iya sallamarta?"
Cikin sakin fuska yace "Nayi tunanin haka dama dana ga d'an uwan sheikh tare daku, indai ba wani iko na ubangiji ba kuma a gaskiya munyi iya bakin k'ok'arinmu, kuma muna saka ran zata farka lafiya lau nan da asuba ma, allurar bacci muka mata dan ta huta, a shawarce Abba ku d'aura aurenta babu abinda zai faru."
Jinjina kai Abba yayi cike da gamsuwa yace "Nagode sosai likita, Allah yayi albarka."
Da murmushi likitan yace "Ameen Baba nagode."
"Zamu iya shiga mu ganta?" Cewar Abba, jinjina masa kai yayi yace "Zaku iya, amma dai kar a takura mata dan tana bacci ne, ta wahala sosai kafin amayar da gubar da tasha."
Cike da jimami ya jinjina kai alamar gamsuwa tare da nufa inda mutanen ke tsaye, malam ne yace "Ya kukayi da likitan? Ba komai dai ko?"
Cikin jin kunya ta suruki yace "B芒 komai malam insha'Allah, yace ma zamu iya shiga mu ganta amma kar a takurata."
Da sauri malam da Asma'u suka nufi d'akin har suna had'a kafad'a, tare suka shiga kafin Asas da Abba su bi bayansu, sai kuma Maimuna da Saminu suma suka shiga. Cike da tausayawa suke kallonta, kwalluyarta na nan a fuskarta sai jan bakinta ne kawai ya d'an fara b'aci, hannayenta dake cikin lalle ja ya k'ara fitowa akan fatarta, sai tayi wani masifar kyau kamar gawa, kowa bakinshi addu'ar tashin kafad'unta yake amma banda Saminu daya shiga k'are ma nonuwanta kallo da sukayi cirrr a cikin rigarta zuwa d'uwawunta da suka baje akan gadon tana kwance, tsabar jaraba bakinshi ne kawai yake bushewa yana lashewa, sai ya samu kanshi da jin wata mahaukaciyar sha'awar yarinyar da kuma jin mad'aukakiyar tsanar Asas da yake ganin shi ne zai mallaketa.
Haka dai suka fita aka bar d'akin Asma'u na kuka tana fad'in "Abba zan kwana a nan wurinta, ku barni a nan ba zan iya barin Mimi ba."
Cike da dattako Abba yace "A'a ba za'ayi haka ba yata, wuce muje gida Iya zata zo ta kwana tare da ita."
Cikin kuka kamar an ce ta mutu ne tace "To Abba kafin Iya ta zo waye zai zauna anan?"
Da sauri Saminu yace "Ba komai zan zauna, sai ku tafi tare da Maimuna gida a motata."
Kallonshi duk sukayi da mamaki musamman Asas daya bishi da kallon ban gane ba? Dan haka ya gyara tsayuwarsa ya kalli Abba yace "Abba, ku je kawai kafin Iya ta zo zan zauna a nan."
Wata harara Saminu ya wurga masa wacce tsaf Asma'u ta gani ta shiga mamaki, haka dai suka fita shi ma Asas ya fito tare dasu suna sallama, Hafsat na ganinsu ta mik'e da k'yar tana fad'in "Asas ya jikin nata?"
Da fara'a ya amsa mata da "Jikinta da sauk'i aunty Hafsy, kije gida ke ma ki huta insha'Allah zata samu lafiya."
D'an satar kallonshi sheikh yayi sai kuma ya d'auke kai, su Salma dake ta kallon sheikh jikinsu na b'ari na zumud'in ganinshi kamar su je daf dashi suke ji, haka duk suka fita a asibitin tare Asma'u dasu Salma duk a motar Saminu suka koma gida, Abba ma suna zuwa a nutse suka fad'a musu abinda ya faru, da sauri Iya ta tarkato ta taho dama tana nan gidansu Mimi, wata tsohuwa ma yayar malam ta so su je tare malam d'in ya hana yace tayi hak'uri.
12:30 sheikh ya dawo asibitin, saida ya tsaya k'ofar d'akin kuma saiya tsaya cak ya tambayi kansa "Me ya kawoka? Miye hujjarka na zuwa ganinta?"
Juyawa yayi da sauri kawai ya bar asibiti ya shiga mota, jingina kanshi yayi a sitiyari yana furta "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntum-mina zalumin, hasbunallahu wani'imal wakil, Allahuma ajirni fi musibati waklufli khairan minha."
Sai kuma ya shiga fad'in "Astagfirullah wa'atubu ilaikh, astagfurullah wa'atubu ilaikh."
Dan gaskiya ji yake ko wani laifin ya ma Allah ya jarabceshi da abinda yake ji a yanzun, har zuciyarshi yake son mantawa da ita, amma tunaninta na yawan addabarshi, gashi kuma awanni da basu gaza takwas bane suka rage ta zama matar shak'ik'insa. Ya jima zaune a motar yana istigfari da tunanin had'uwarshi da ita, fuskar nan ta ta mai matuk'ar kamala da nutsuwa, saidai kash *mage* ce mai *kwanciyar d'aukar rai*, wani wawan tsaki ya ja a motar tare da d'an dukan sitiyari yana fad'in "A kan me Ryam? Me yasa kika zama mai arha ballagazar matasan titi? Shitttt!"
Ji yayi kamar ya samu wani ya ciza dan haushi yake ji sosai na tuna abinda ya faru a ranar, da k'yar ya samu ya bar k'ofar asibitin zuwa gida, saidai dake Hafsat tana can gidansu Hajia suna ci gaba da aiki dan Abba ya tabbatar za'a d'aura auren, sai kawai ya shiga ta k'ofar baya ba tare daya ratsa ta falon ta ba.
*Safiyar juma'a*
Tubarkallah duk girman gidan nan nasu a tumbatse yake da jama'a ana ta shan biki tun kafin ma a d'aura auren, Hajia kam cikin kulawa tasa Salamatu tare da dreba da Aisha suka kai wa su Mimi abin kari a asibiti, sosai hakan ya birge Iya da jinjina dattakonsu, suma kuma zuwa k'arfe 09:00 aka sallameta a asibiti, ba abinda ke damunta saidai rashin k'arfin jiki kawai, Asas da kanshi ya aje su har k'ofar gida ya juya cike da begen amaryarshi.
Suna shiga ciki dangi aka shiga murna da tambayarta ya jiki? Jiki a sanyaye take amsawa da "Da sauk'i." D'aki ta shigata cire kayanta Sahura ta mata jagora ta shiga ban d'aki tayi wanka ta fito ta canza kaya, ta samu Asma'u a d'akin har ta zo dubata, da farin cikin ganinta take tambayar "Ya jikinki?"
Saida ta zauna kusanta a sanyaye tace "Jiki da sauk'i Asma'u."
Da fara'a tace "Allah k'ara kiyayewa." A hankali ta amsa da "Ameen."
Lumshe ido kawai tayi tana jin yanda zuciyarta ke wani tsinkewa tana gudu da sauri, a k'asan mak'oshinta ta furta "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntum-mina zalumin."
Su Zeinaba duk suna tare da ita a d'akin Shapi'a ta kawo mata abinci girgiza kai tayi tace "Um um aunty ban ci."
Kallonta tayi tace "Iya fa ta ce har abinci aka kai muku asibiti kuma baki ci ba."
Madara ta mik'o mata a roba tace "Daure kisha ko wannan to, kar yunwa ta hanaki tab'uka komai."
A hankali ta karb'a tare da bud'e robar, sanyi da dad'in madarar yasa ta d'an kurb'awa dan dama tana jin yunwa sosai, ba zata iya tuna rabonta da abinci ba har ta manta ita kam. Tana jin su Asma'u da Salma da suka zo suna sake tattauna maganar yarinyar data bata lemu, ita dai kallonsu take da ido kawai, ba ta da wanda zata zarga tace shi ne, hasalima ba ta tunanin gabarta da wani takai matakin da zai nemi rayuwarta haka, shiyasa kanta ya kulle ta kasa tuna komai.
02:08 Shapi'a ta shigo ta kalleta tace "Ke taso kiyi wanka."
Kallonta sukayi sai Rauda da tace "Mama har an d'aura auren ne?"
Cike da rashin tabbas tace "An d'aura mana, tunda ai k'arfe biyu ne yanzu kuma biyu ta gota."
A hankali Mimi ta mik'e Shapi'a ta kama hannunta suka fita, gud'a mutanen tsakar gidan suka saka har ta wuce zuwa ban d'aki, yan uwan Abba ne su uku a ban d'akin suna jiranta, nan suka mata wankan fita kamar dai yanda aka mata na farko, ana idawa aka d'auko sabon d'inkin da aka mata riga da zane na atamfa d'inki simple, abun ka da mai k'iba sai kayan suka kamata sosai suka mata kyau musamman zanin daya fito da mazaunanta, kallabinsu aka d'aura mata kafin aka bata takalmi silipas ta saka a fararen k'afafunta da kuma darar amare kalar ja, ruf aka rufeta da darar har aka fito da ita daga ban d'aki.
A daidai lokacin wayar Sahura na kuka, tana d'auka sai kuma a ladabce tace "Kai ashe Abban Mimi?"
Jim tayi kafin tace "To ga Iyar." Ta fad'a tana mik'awa Iya wayar, karb'a tayi ta nutsu tana saurarenshi, duk tsura mata ido akayi suna kallon yanayinta, saida ta d'an jima kafin a sanyaye tace "Allah yasa haka shi yafi alkairi, Allah basu zaman lafiya, shi kuma Allah ya jik'anshi da rahama."
Sahura da yayar malam ne suka kalleta da fad'in "Iya wa ya rasu kuma?"
Kallonsu tayi sannan ta kalli Mimi dake tsakiyarsu zasu rakata d'aki, sauke numfashi tayi kawai ba tace komai ba, Shapi'a dake kusanta ne ta aje tasar furar hannunta da za'a kai ma bak'in da suka shigo yanzu daga k'auye tace "Iya wa ya rasu dan Allah?"
Cikin danne kukan tausayin Mimi cikin jin haushi Iya tace "Yaron ne ya rasu, angon."
*Waiwaye*
11:00 Asas ya shigo da leda da hannunshi, abokan wasa na tsokanarshi yana dariya yace "Ban da lokacinku yau, duk kuyi ku gama matata ce zata rama min duk abinda kuka min."
Da haka ya shige b'angarenshi dan shiryawa, tsaf yayi wanka ya fito ya zauna ya linde jikinshi da mai ya fesa turare kamar ba gobe, inda kayanshi suke ya nufa ya d'auki wandon dakakkiyar shaddar ya saka ya aje towel d'in k'ugunshi, ya d'auki rigar zai saka kawai ciwon ciki yace salam Asas, da sauri ya saki rigar ya sunkuye k'asa yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, wayyo Allahna ciki Hajia, Hajia ciki zan mutu, wayyo Allah."
Yunk'urawa yayi da niyyar d'auko wayarshi saidai ina kawai ya fad'i a wurin jikinshi na saki gaba d'aya tare da d'aukar wani irin sanyi k'alau. Tun ana saka ran fitowarshi har dai aka ga ya jima, 12:28 Sadeeq ya shigo gidan tare da wani abokinsu cikin shirinsu sunyi tsaf, Hafsat suka gaida kafin Sadeeq yace "Auntynmu wai ina yaron nan yake ne? Shiriritarshi yawa ne da ita fa."
Nuna musu b'angaren tayi tace "Tunda ya shiga ina jin bai fito ba, ko shirin yake har yanzu?"
D'an tsaki Sadeeq yayi yace "Martala gareshi wallahi, yanzu nan fa sheikh sai kirana yake yana jadadda mana karmu b'atawa mutane lokaci, mu zo akan lokaci dan ayi komai a gabanmu."
Nufa b'angaren na shi sukayi dukansu biyu d'in Hafsat na murmushi dan sheikh ne zai karb'ar ma Asas auren ma'ana zai wakilceshi. Suna zuwa k'wank'wasa k'ofar suka fara yi suna kiran "Kai zaka fito ko sai na bankad'e k'ofar? Kaji iskanci ko kai ma kwalliya kake irin ta amaryar."
Shiru babu motsi ko alamar mutum, cikin jin haushi Sadeeq ya sa k'arfi ya tura k'ofar ashe ma bud'e take, abinda suka gani ne ya d'aga hankalinsu tare da sandarewa suna sake kallonshi, kamar an tsikaresu sai kuma suka tafi a guje suka durk'ushe suna kiran sunanshi, Sadeeq ne ya kalli d'ayan yace "Lamin dan Allah kira mutane a kai shi asibiti, ina jin ciwon cikinshi ne ya motsa."
Hankali tashe Lamin ya mik'e da gudu ya fita Sadeeq na ci gaba da jijjigashi yana fad'in "Dan Allah ciwon ciki ba'a wannan lokacin ba, kar ka shiga tsakaninshi da burinshi mana."
Rututu aka shigo d'akin har da Hafsat da tsohon cikin ta ta durk'usa tana kallon d'an uwanta, cikin rawar murya tace "Haka kuka sameshi?"
"Eh." Cewar Sadeeq, a hankali ta kai hannu a wiyanshi ta tab'a wajen shed'a, jin shiru yasa ta d'aga hannun sai taji yayi nauyi ya sake fad'uwa, a hankali ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."
"Lafiya?" Cewar Hajia a kid'ime, zaune tayi dangal dangal ta kasa cewa komai, Sadeeq kam kallon Lamin yayi yace "Kamashi mu kaishi asibiti."
Girgiza kai tayi ta musu alama da hannu kar su tafi, a tsorace Sadeeq ya kalleta yace "Kamar ya?"
A tausashe tace "Saboda wanda ya fi mu son shi ya karb'e abun sa."
Gaba d'aya d'akin aka d'auki salallami sai Hajia data fad'a kan gadon tayi zaman yan bori ita ma tana na ta salallamin, duk shiru sukayi a d'akin ana ta kallon kallo ana jimami babu mai magana, gasu ga gawar Asas kwance baya motsi, yayi kyau masha'Allah ga askin nan daya sha irin na zamani sumarshi ta asalin bafulatani an tara mishi ita a gaban tsaf, kukan wayar Hajia ne yasa su zabura suka kalli inda take zaune, sai suka lura kamar bata ma san ana kiran ba, matar kawu Saleh ce ta kai hannu a jakar Hajia ta d'auki wayar, tana dubawa sheikh ne mik'awa Hafsat tayi ta karb'a.
Cikin ruwan sanyi yace "Hajiayarmu, ina Asas?"
Wani murmushi ta saki mai kama da kuka tace "Asas ya amsa kiran ubangijinshi."
Sai kuma ta fashe da kuka, jim yayi yana jin abun kamar alamara ko tatsuniya, can kuma saiya nisa yace "Manga, Asas na ce yana ina, hud'uba zan fara yanzu gashi basu zo masallacin nan ba."
Cikin kuka tace "Sheikh ga Asas dai kwance a gabanmu amma baya motsi, ba zai iya anfanar kan shi da komai ba a halin yanzu, hatta da wanka ma sai an mishi."
A gigice sheikh yace "Ban gane ba Sawwama, me ya same shi wai?"
Wani kuka mai cin rai ta fashe da shi tace "Bamu sani ba mu ma, gawarshi kawai muka samu."
Wani bala'in sanyi ne gabb'anshi sukayi hakan ya sakashi sakin wayar daga hannunshi, da sauri d'an agaji tare da masu tsaronshi suka matso suna tambayar lafiya? B'alle d'amarar dake gaban rigarshi yayi ta alkyabba ya shiga firfita da hannunshi, lura kamar cikin tashin hankali yake yasa d'aya fad'in "Allah gafarta malam ko zamu koma gida ne?"
Da sauri yake jan numfashinshi kamar mai hawan jini, kiran sallah da aka kwad'a yasa shi d'an zabura yace "Astagfirullah, astagfirullah, Asas? ashraf? Astagfirullah."
A gigice ya juya ya tunkari masallacin ba maa tare da yasan me yake ba, saida ya shiga ya tabbatar ba abinda yayi niyya ya aikata ba, shi fa gida yake so yaje ya gasgata abinda suka fad'a, bud'a mishi hanya aka dinga yi yana ta wuce har ya kai gaba inda ya kamata ya hau mimbari, saidai kuma kawai gani sukayi yayi zaune a layin masu biyarshi, kallon kallo ake saidai ba wanda yace wani abu ana tunanin ko wata sabuwar sunnar ce.
Kawu Saleh da sukayi waya da matarshi ta sake fad'a masa abinda ke faruwa ne ya matsa a jerin sahun farko inda wasu malamai da sarakuna da manya suke, sheikh Bala ya ma magana kan ya wakilci sheikh dan shi yana cikin halin d'imuwa ne, shi ma abun dai ya razana shi tare da k'ara mishi tsoron Allah, haka ya hau mimbari ya fara gabatar da hud'uba a harshen larabci na minti sha biyar kafin ya d'an zauna na minti d'aya ya mik'e ya ci gaba da fassarawa a hausa, saida aka gama akayi sallah sheikh shi ma dai biya kawai yake, ana idawa ne aka gabatar da aure takwas da za'a d'aura.
Duk waliyai da wakilai sun matso dan ayi abunda ya kawo amarya d'akin mijinta, aure biyar aka d'aura kafin aka kawo ga na su Mimi, Saleh ne ya kalli sheikh da sam hankalinshi baya kansu yace "Sheikh ya