Showing 87001 words to 90000 words out of 185502 words

Chapter 30 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

500

rik'e hannun Hajia tace "A'a, a'a Hajia, bana so, bana son zuwa asibiti, ki ce yayi zamansa dan Allah na rok'eki."

Zaune tayi gefenta tace "To banda abun ki Mimi an tab'a zama da ciwo haka? Zazzab'i bala'i ne takwarata, tsaf yanzu zai rabaki da jininki sai an koma tarbata ana k'ara miki."

Sake jimk'e hannun Hajia tayi tace "Ni dai idan kika zuba min ruwa a jikina ma zanji sauk'i, bana son zuwa asibiti wallahi, kana zuwa allura suke maka."

Komai Hajia ba tace ba sai mamatsa hannun Mimi data dinga yi, a k'alla minti ashirin ya kawoshi gidan, kai tsaye d'akin ya shigo da sallama a bakinshi, da sauri Hajia ta amsa sai Mimi da tayi ram da k'ugun Hajia cikin muryar galabaita tana fad'in "Karki bari ya kaini asibiti kin ji uwata, bana so wallahi na tsani allura, idan kika bari ya tafi da ni ba zan zauna gidanki ba."

Yanda take cumimiye k'ugun Hajia yake kallo ita kuma tana ta murmushi, kujerar gaban madubi yaja ya zauna yana kallon Hajia, ita ma kallonshi tayi tace "Ya zamuyi yanzu? Tace bata son zuwa asibiti."

Wani kallo ya wurga mata duk da ba fuskarta yake gani ba yace "Dama ba dan tana so zamu kai ta ba."

Kallon Hajia yayi yace "Ku shirya sai mu tafi."

Dariya Hajia tayi tace "Ba dani zaku tafi ba, dan har yanzu akwai bak'in da basu tafi ba."

Kallon Mimi tayi data dunk'ule tace "Tashi ki gyara hijabinki sai ku tafi."

Girgiza kai tayi alamar a'a, wani kallo kawai ya shiga bin ta da shi, cikin muryar da babu wasa a ciki yace "Jiranki fa nake, ina da abun yi."

Gabanta ne ya shiga fad'uwa da k'yar ta yunk'ura ta d'ago, a kan shi ta sauke idonta wanda shi ma a kan ta na shi idon suke, da sauri ta sinne kan ta saboda wata irin kunya data kamata, ko a tv bata tab'a ganinshi da kaya irin na yau ba, zallar d'inki ne kawai riga da wando tazarce sai hula a kan shi.

Ganin kallon da yake mata yasa Hajia mik'ewa tace "Bari na sama mata ko madara da zata saka a cikinta."

Fita tayi ba tare da ta ji me zai ce ba, rawar da jikinta ke yi ne ta k'aru sai ta rasa yanda zata yi ta sauka a kan gadon, murya a dak'ile yace "Jiranki nake malama."

Hijabi tasa tana murza ido cikin kukan shagwab'a tace "Ni bana son zuwa asibiti, na warke fa babu abinda yake damuna."

Mik'ewa yayi tsaye yace "Ke." Da sauri ta kalleshi dan indai y'a ce ke dole ka kalleshi, da sauri kuma tayi k'asa da kan ta sanda yake fad'in "Sauko a gadon nan kafin na tsula miki tsumagiya, kinsan haushinki ne dani ko?"

Da sauri cikin rashin k'arfin jiki ta shiga saukowa a kan gadon, saida tayi tsaye k'afafunta na mata rawa sosai ta kalleshi tace "Abdu..." Gumtse bakinta tayi sai kuma tace "Yallab'ai, dan Allah idan munje karka bari su min allura."

Wani firgitacen kallo ya mata daya razanata yace "Har a baki sai na ce a miki ko zaki daina yin k'arya."

Da sauri ta shiga nuna mishi da hannayenta tace "Na daina ai tun ranar, wallah..."

Sake zaro mata ido yayi shi yasa tayi shiru saai kuma tace "Tun waccen ranar na daina, ba zan sake ba Allah ko."

Yatsina fuska yayi yace "Wuce muje."

Silipas d'inta dake gaban gadon ta zura k'fafunta tayi gaba jikinta na rawa gab-gab-gab kamar ba zata iya tafiyar ba, saida ta kusa kaiwa k'ofar fita yace "Miye wannan kuma malama?"

Juyowa tayi sai taga ashe yana tsaye inda yake, dudduba jikinta ta shiga yi ganin bata ga komai ba saita kalleshi da alamar tambaya, cikin murtuke fuska yace "Wannan hijabi ne a jikinki?"

Duk'ar da kanta tayi tana kallon hijabin daya saukar mata har wuce gwiwoyinta, d'agowa tayi da mamaki tace "Hijabi ne mana."

A take cike da gatsali yace "Bai min ba, canza shi."

Galala tayi da baki ta kalleshi, ganin bata da niyyar yin abinda yace yasa shi cewa "Na ce ki canza shi ko?"

Turo baki tayi cikin sangarta tace "Ai duk sauran ma haka suke, kuma ba duka kayana bane aka d'auko."

Tab'e baki yayi yace "To nik'ab fa?"

Baki bud'e ta kalleshi tace "Nik'ab kuma? Ni da ba lafiya gareni ba?"

Cikin wurga mata harara yace "Dan baki lafiya sai aka ce jikinki abun talla ne?"

Gumtse bakinta tayi ta sinne kan ta, sama da k'asa ya harareta yace "Shi waccen sharb'eb'en da kike sakawa sai kina son nuna ta Allah ce ke ko?"

Takowa yayi da sauri yana fad'in "Muje, amma ki sani dole ki canza tsarin shigarki, dan wannan bata min ba."

Kaucewa tayi da sauri ya bud'e k'ofar ya fita sannan ta bi bayanshi, tana fitowa haka tayi ta jan hijabinta tana rufe fuskarta saboda bak'in dake nan wasu na ta haramar komawa inda suka fito, gaishesu tayi a ladabce suka amsa tare da fatan sauk'i a gareta. Tana fitowa daga falon ya shiga hangenta daga zaune da yake a motar, kamar wai ba ita ce yake jira ba take wata tafiya kamar wahainiya, yo shi ko Hajia ma ta tab'a sashi jiranta kamar haka kuwa? D'auke kai yayi daga kallonta yanaa d'an jan guntun tsaki.

Baya ta kama zata bud'e ya juyo ya kalleta, saki tayi ta koma gaba ta bud'e ta shiga, kakkauran hannunshi ta kama wanda agogon hannun ta cikashi dam, d'auke idonta tayi a ranta tace "Hummm!"

Saidai yanda ta fad'i humm! D'in yasa shi kallonta dan ta fito, saida ya juyar da kan motar zasu fita ya kalleta yace "Miye?"

Kallonshi tayi tace "Ba komai."

B芒 tare daya kalleta ba yace "Ban son k'arya, ki tabbatar kinsan me zaki dinga fad'a min kinji ko."

K'wafar da yayi yasa ta saurin cewa "To." A ranta kuma tana sake k'iyasta yanda ta wani shiga mota d'aya da mijin aurenta, mijin ma kuma tsoho sa'an babanta, yanzu nan a ganta da k'uruciyarta sai kawai ta ce shi ne mijinta, wasu k'walla ne ta ji sun taho mata tare da saka yatsarta ta share kawai tana kallon titi ba mai ma kowa magana.

Yana paka mota kamar jira take tayi saurin fita ta tunkari asibitin, cikin dak'ilalliyar murya yace "Ke!"

Lumshe ido tayi a ranta tace "Ohhh! Wai wani ke! Miye haka dan Allah."

Juyowa tayi a hankali tana kallonshi a ladabce, da ido ya mata alamar "Tsaya a gefena."

Take fuskarta ta nuna alamar rashin jin dad'i, juyawa tayi ta d'an shiga kallon mutanen dake kai kawo, tana cikin yatsina fuska kamar yasan me take tunani yace "Kunya kike ji a ga kin jera da *tsoho a matsayin mijinki*?"

Kumbura fuska tayi da baki tare da jan hijabinta ta rufe daga bakinta har zuwa hanci, k'wafa yayi tare da wucewa gaba yana fad'in "Bansan rashin kunyarki ta kai haka ba Ryam."

Ita dai biyarshi take yi a baya yana shiga lungu da sak'o na asibiti, ganinshi a asibitin yasa duk ma'aikatan da suka ganshi suke gaisheshi da girmamawa, wani matashin ma'aikaci ya tambaya Dr. Rakiya? Dan haka da kan shi ya musu iso zuwa ofishinta dan tana tsaka da duba mata da suka kama layi, sanda zai shiga ofishin ne ya kula bata bayanshi, juyawa yayi saiya hangeta nesa dashi sai wani rufe fuska take, jinjina kai yayi a zuciyarshi yana fad'in "Ba dai ni kike jin kunyar jerawa dani ba? Zaki gane baki da wayo."

Shigewa yayi ofishin ya zauna yana karb'an gaisuwar Dr. Rakiya, saida suka gama gaisawa kafin Mimi ta shigo da sallama k'asan mak'oshi, Rakiya ce kawai ta amsa tana sakar mata murmushi, sosai take kallon yarinyar wacce jiya labari ya karad'e gari sheikh ya aura ko kuma an aura ma sheikh ita, dan har hotonta ta gani wanda aka had'a ita da Asas amma Allah bai nufa ba. Tsaye tayi tana kallon kujerar da zata zauna wacce ke fuskantar sheikh dake zaune, hannu ta kai zata ja kujerar baya taa zauna sheikh yace "To ke da zaki fad'a mata abinda ke damunki, ya kuma zakija baya *Mari*?"

Kallonshi tayi kamar ta gaura masa mari domin ta fahimci so yake ya cizgata a gaban mutane, kaikaitawa tayi ta d'an tsoma mazaunanta tana kallon likitar, murmushi ta sakar mata tare da d'aukar katin marasa lafiya tace "Madame sunanki?"

Saida ta ja hijabinta sosai kafin tace "Mimi...au! Maryam."

K'ura mata ido yayi kamar mai burin rikitata yana sakin murmushin mugunta, Mimi kam data fahimta ko kallonshi ba tayi ba har likitar tace "Sunan mahaifi?"

A sanyaye tace "Uban kowa."

Da sauri ta d'aga kai ta kalleta haka ma sheikh daya sake kafeta da ido, sai kuma yayi murmushi ya d'an d'ago daga jinginar da yayi tare da kai hannunshi ya lalubo hannun Mimi a cikin hijabi ya rik'o, a razane ta kalleshi tare da k'ok'arin k'wacewa, sai kuma ya jimk'e hannun gam yana mata murmushi, ba tare daya daina wannan murmushin ba yace " *Innar Issa*, sunan Babanmu zaki fad'a mata kinji, ki daure ki fad'a mata."

Kyab'e fuska Mimi tayi ta fashe da kuka dan ta lura kawai ci mata mutumci ne ma zaiyi, wai babansu? Sa'an Abba ne fa amma yake cewa babansu, d'auke kanshi yayi daga kallonta ya kalli likitar yace "Dr. Ki saka Maryam Adam Shehu, shekaru 18."

Da sauri ta fizge hannunta tace "Abdul ban kai 18 ba fa, 17 ne wallahi."

Da sauri sheikh ya cije leb'enshi na k'asa sakamakon dariyar data nemi kubce mishi, hannu ya kai akan hab'arshi yana d'an saita kanshi tare da rik'e dariyar. Rakiya kam zaro ido tayi a ranta tace "Tofa! *auren yarinya* kenan."

Duk'ar da kanta tayi tana rubuta abinda ta tambaya, d'agowa tayi ta mik'owa Mimi abun d'aukar zafi, karb'a tayi tare da marairaicewa tace "Dan Allah ba zaki min allura ba ko?"

Murmushi ta mata tace "Ba zan miki ba indai zazzab'inki bai kai matakin ba."

Sheikh dai na kallonta sai k'ok'arin saka abun awon zafin take, saidai dake tun kayan jiya ne jikinta da suka matseta sai hannunta ya k'i shiga bare ta saka abun ya zauna mata a hammata.

Lura da haka yasa Rakiya fad'in "Ko ki zage zip d'in rigar? Dan naga kamar ta kamaki sosai."

A hankali ta aje abun d'aukar zafin ta zura hannayenta baya ta fara kiciniyar cirewa, sheikh kam takaici ne ya kamashi da tunanin haka take saka kayan kenan ita ma kamar dai 'yan zamani. Kamar da wasa sai ko yasa hannu biyu ya jawo gaba d'aya kujerar da take zaune wanda hakan ya haddasa bayar da k'ara akan tiles d'in 'kiiiiiiii! Zaro ido Mimi tayi ganin yanda ya jawota kamar wata beby duk da girmanta, bata gama sarewa da lamarinshi ba saida ya zura hannayenshi a cikin hijabinta ya kaisu a bayanta ya shiga lalubawa inda zai ji zip d'in. Tuni Mimi ta fara kakkaucewa tana babbank'arewa, zafin da yaji a jikinta yasa shi jin kamar ya cire mata rigar gaba d'aya ya rumgumeta a jikinshi ko ya samu damar d'auke mata zafin, saida ya ji ya rik'e zip d'in ya ja shi a hankali tare da sake matsawa daf da ita a kunne ya rad'a mata "Tsofaffi ba ruwansu tunda ba sha'awa garemu ba, miye na d'aga hankali daga cire zip na riga."

D'aukar abun awan zafin yayi tare da d'aga hannunta ya soka mata ya had'e mata hannun sannan ya ciro hannayenshi daga hijabin, Mimi kam addu'a take kar Allah ya d'auki ranta da mamakin tsohon nan, wata tambaya ta jefawa kan ta "To wai me yake nufi ne?"

Gemunshi kawai ta k'urawa ido mai d'auke da farin gashi d'ai-d'ai, saida taji tinnnn! D'in abun awon zafin ta d'an zabura ta kalli likitar data tara mata hannu, cirowa tayi ta mik'a mata ta duba, mik'ewa tayi tana fad'in "Bari mu gwada jininki mu gani."

K'ura mata ido Mimi tayi ganin ta d'auki d'an shud'i abu k'arami ta cire a gidanshi sai kuwa tsinin allura ya bayyana, zabura tayi ta mik'e tsaye tana saka kukan shagwab'a da fad'in "Bana so ni dai na fad'a miki tun farko, Abbana, Abba ma ya san bana son allura wallahi."

Ganin tana shirin zabgawa da gudu yasa shi mik'ewa ya tura kejarar baya, hijabinta ya rik'e yana kallon fuskarta duk ta rud'e yace "Innar Issa ya haka? D'an tsikara miki ne fa za'ayi ba zafi, haba mana *'yan matan tsohonta*, so kike a mana dariya ne."

Dariya Rakiya keyi inda Mimi ta shiga tsatsare k'aramin bakinshi da ido wanda bak'in gashi ma yake hanashi fitowa da kyau,wasu hawaye masu zafi ne suka taho mata akan kumatu, ba tare data d'auke idonta a cikin nashi ba murya a raunane tace " *Bawan Allah*, amma dai ai saida na fad'a maka bana so ko?"

Wani daban yake ji shi wallahi a lokacin a wani sake sakayau, ga isashen lokaci ga kuma wata k'uruciyarshi da yake jin ana neman dawo masa da ita baya, babu masu fad'in gafarta malam, babu ranka shi dad'e, babu sheikh ko malam, babu kurantawa da girmamawa mai cike da kambamawa, babu amsa umarninshi cikin d'aukakawa. Hasalima a nan shi ne ke k'ak'arin rarrashi, kai tsaye ake kallonshi ana fad'a masa abinda akayi niyyar fad'a, yau gashi har yake iya bada umarni sau biyu, bugu da k'ari ma har yayi magana kai tsaye aka ce a'a ba haka bane, wanda ko cikin wa'azi da dubannin mutane ke kallonshi da saurare aka samu akasi da ajizanci na d'an adam ya fad'i ba daidai ba kai tsaye ba'a katseshi, wani saidai bayan an tashi ya fad'a ko kuma a kirashi a waya ko kuma dai a rubuta mishi wasik'a.

Wani k'ayataccen murmushi ya sakar mata tare da jawota gaba d'aya ta kusa fad'awa jikinshi, d'an kashe mata ido d'aya yayi yace "...




_Sadaukarwa ga duk 'yan *duk nisan jifa* da kuma *matar mutum*_



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*29*



Wani k'ayataccen murmushi ya sakar mata tare da jawota gaba d'aya ta kusa fad'awa jikinshi, d'an kashe mata ido d'aya yayi yace "Kin fad'a min 'yan matana, amma ai lafiyarki tafi komai a wajena."

Kallon ka tausaya min ta bishi da shi sharrr hawaye na dararowa a idonta, Rakiya dake kallonsu ce tace "Malam ko dai a bata magani ne? Dan naga kamar ba zata bari mu d'auki jininta ba bare muga zazzab'i me take."

A hankali ya kalli Rakiyar saidai bai ce komai ba dan abinda ya fahimta shi ma kenan, kuma shi dai ba zai iya dagewa ya matseta a jikinshi ba, ganin haka ya tabbatarwa Rakiya me yake so, dan haka ta koma ta zauna mazauninta ta shiga duba magunguna da dama ake ajewa wasu na zazzab'i ne na rigakafi, Mimi dai na kallonta a ranta fad'i take "Shi ma ba sha zanyi ba, dan kin bar abinki ma kin bawa wani."

Sheikh ta mik'a tare da fad'a mishi yanda zata sha, godiya ya mata ya mik'e hakan yasa Mimi mik'ewa ita ma, shigewa yayi gaban yayi da Mimi ke fad'in "Sai anjima."

Da fara'a Rakiya tace "Sai anjima madame, daure a sha magani fa."

Murmushi kawai tayi ba tace komai ba har suka fice, yanzu ma dai nesa da shi ta tsaya har saida ya shiga mota kafin ta k'arasa da sauri ta shiga ita ma, a d'an hassale ya kalleta yace "Wai kunyar me kike ji na jerawa tare da ni? Ryam abun k'yama ne a jikina?"

Da sauri ta zaro ido baki bud'e tace "Ni? Wallahi ba ha..."

Hannu ya kai kamar zai bugi bakinta yana fad'in "Komai zaki fad'a sai kinyi rantsuwa, me yasa babu gaskiya a lamarinki ne wai?"

Mar-mar-mar! Tayi da idonta tare da nok'e kanta kamar wata mage tace "Kayi hak'uri to na daina."

K'wafa yayi ya aje mata ledar maganin a cinyarta yana yi wa motar key, kallonta ya sake yi sanda yake k'ok'arin hawa kan titi yana fad'in "Ni ne kika kalli idona a gaban kowa kika kira tsoho ko?"

K'wafa yayi yana jinjina kai, cikin turo baki ta d'anyi gunguni hakan yasa shi hararanta yace "Me kika fad'a?"

Girgiza kai tayi alamar a'a, wani mugun kallon ya mata yace "Na fad'a miki ki koyi fad'an gaskiya, bana son k'arya Ryam ina tsanar mai yin ta, dan alamomi a cikin alamar munafiki."

A hankali ta jinjina kai alamar gamsuwa, saida ya d'auki hanya kamar an bar zancen sai kuma ya kalleta yace "To yanzu fad'a min me kika fad'a?"

A d'an gigice ta kalleshi a ranta tana fad'in "Matsalar tsofafin nan fa kenan jinini."

A zahiri kuma cewa tayi "Ina tsoron na fad'a kayi hushi."

K'uri ya mata da ido yana kallo sai kuma ya d'auke kanshi yace "Ba zanyi ba, zan kwatanta halin annabi Muhammad (S.A.W), har ma na had'a miki da halin dattijon arzik'i sahibin fiyayyen halita Abubacar Siddiq, bayan banyi hushi ba har sai na yafe miki ma sannan na miki kyauta."

Baki sake tace "Dukana zakayi?"

Kallonta yayi yace "Bana duka, saidai akwai hanyoyin da nake ladabtar da marasa jin magana irinki."

Kallon titi tayi tana d'an kumburo baki, kamar daga sama ya sake fad'in "Ina jinki fa."

Kallonshi tayi tasa hannu da hijabinta ta rufe bakinta, cikin muryar rad'a tace "Dama kawai...cewa nayi..ai sa'an Abbana ne."

Da sauri ya kalleta ita ma da saurin ta fashe da kukan shagwab'a tace "Ai ka ce min ba zaka dakeni ba, kuma kai ka ce na daina yin k'arya."

K'ank'ance idonshi yayi tare da d'auke kai yana girgizawa, kawai ya tabbatarwa kan shi wannan bata cika shekara sha takwas ba, shi kam ya zaiyi da ita yanzu? Shiru sukayi suka ci gaba da tafiya har ta gaji da kukan sakarcin ta daina, saida yaji tayi d'ip ya d'an saci kallonta, yanda ta rakub'e tare da dunk'ule jikinta tana kallon titi zai tabbatar maka har yanzu bata jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login