Showing 42001 words to 45000 words out of 185502 words

Chapter 15 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

494

baisan tana iskanci ba ana bata kud'in kashewa, kuma ai har IPhone gareta ma."

Duk kowa babu wanda yace wani abu saboda mamaki, sai Abba dake jin knashi na sara mishi da k'yar yace "Wace irin IPhone kuma?"

D'aya daga cikin yan matan ne wata tace "IPhone dai daka sani, waya salula ba."

Zurum ya fad'a cikin gidan hankali a tashe, anan kam wannan hayaniyar suka ci gaba da yi inda muryar Kaka ta karad'e unguwar tana cin zarafin Saminu, saidai ya shiga mota ya barsu amma fa yayi niyyar sai sun bar unguwar nan, dan ta tab'a masa Mimin sa ba kuma zai lamunta ba.

Abba na fad'awa gidan a d'aki ya sameta ta cire hijabi tana share k'walla, kalmar karuwar nan ta mata zafi sosai, Mama kam kallonta tayi tace "Ke da wa kuma?"

Majina ta ja amma ba tace komai ba, tana shirin zame rigarta dan ta watsa ruwa Abba ya shigo d'akin b芒 sallama, saida ta tsorota ganin yanda ya shigo d'akin, wani kallo ya tsareta dashi ya jefa mata tambayar "Da gaske kina da waya?"

Zaro ido tayi tana sulalewa k'asa ta shiga rarraba ido, dafe cikinta tayi daya shiga murd'a mata tana addu'a a zuciyarta, a tsawace ya sake fad'in "Ba dake nake magana ba kina ji na kinyi shiru?"

Da sauri tace "K'arya ce Abba, bana da waya ni."

Da sauri yace "To IPhone d'in da ake magana a kai fa ta uban wacece?"

Cikin alaamar rashin gaskiya tace "Abba...IPhone kuma? Ni wa ya bani IPhone ? Ban tab'a ganinta a zahiri ba wallahi."

D'an gajeran yatsanshi ya nuna mata yace "Uwata, wallahi fa duk randa na kamaki da waya a hnanu zaki ci ubanki a gidan nan."

Tare suka kalleshi ita da mama, mamaki suke yanda ya b'angaro wannan ashar haka shi da ba mutumin ashar ba, jinjina masa kai tayi alamar to hakan yasa shi ciro k'aramar tecno d'in shi ya mik'a mata yace "Ki kira ki fad'a masa, idan kin gama wayar sai kije ki tambayi iyayen Asma'u idan zasu barta ku tafi tare."

Karb'a tayi da ladabi tana fad'in "To Abba."

Saida ya fita kafin ta zauna bakin gado tana saka lambobin Asas, ta jima tana kururuwa kafin aka d'aga tare da sallama, murmushi ta saki tana amsawa taare da fad'in "Na d'auka ba zaka d'auki kiran bak'uwar lamba ba."

Murmushi yayi shi ma yace "Wane ni? Ban cika d'auka ba kam, haka kawai na ji wannan kiran na musamman ne saboda yanda zuciyata ta shiga bugawa."

Yar dariya tayi tana satar kallon mama tace "Da baka d'auka ba ai da na ce na fasa auren."

Jin haka yasa mama mik'ewa ta bar mata d'akin cike da kunya, Asas kuma d'orawa yayi da cewa "Maah da kin kasheni ashe, kinsan burin da na ci akan auren nan namu kuwa?"

Yar dariya tayi tace "Idan na kashe Asas ai Mimi ma mutuwa zatayi, ka d'auka zan rayu ne babu kai?"

Wani k'asaitaccen murmushi yayi yace "Mimi kar kisa na kuma durk'usawa gaban Abba na ce ya jawo lokacin aurenmu nan da sati."

Dariya kawai tayi mai d'an sauti b芒 tace komai ba, a hankali cikin sanyayyar murya yace "Naanah wannan lambar waye?"

A hankali ita ma tace "Lambar Abba ne, ya bani ne na kiraka dan na sanar da kai ya amince na je na gaishe da mama, saidai yace bayan gidanku da gidan yayarka kar na k'ara gaba sai gida kawai."

Wani murmushi ya sake yi yace "Na ji dad'i sosai maah, hakan kuma yayi kyau sosai, ba komai zamuyi yanda Abba yace, yaushe zaki shirya."

A tausashe tace "Abba yace gobe." Murmushi yayi mai sauti yana fad'in "Kinsan da kuwa yanzu haka na dawo daga gidan aunty Hafsat, kuma ina zolayarta ina fad'a mata gobe zaki zo, har take tambaya ta wai me zata dafa miki? Ni kuma na ce mata ta yanka miki bijimin sa."

'Yar dariya tayi tace "Ni kam ina zan kai bijimin sa? Ai zaka sakani na tafi da babbar jaka dan na yi wa 'yan k'annaina guzurin abinda suka jima basu ci ba."

Wani d'an siririn murmushi yayi cike da tausayin yarinyar a ran shi, a tausashe yace "Ina wayarki? Me yasa zaki cinyewa Abba katinshi?"

Murmushi tayi tace "Abba ne ya bani ai saboda ta wa babu caji, amma idan na saka a caji zan kiraka."

Jinjina kai yayi kamar yana gabanta yace "Shikenan ina jira, kuma fa karki manta dani."

Girgiza kai tayi ita ma tace "Wace ni na manta da angona? Ai sai na ji sammacin kotu ban shirya ba."

Yar dariya yayi yace "Mimi girmanki ai ya isa kiyi laifi kuma babu mai k'arfin halin hukuntaki."

Murmushi tayi tace "Zaka fasa min kai na fa, yanzu dai sai na kiraka d'in."

Da haka sukayi sallama ta kaiwa Abba wayarshi a tsakar gida yana kallon mama dake tsintar shinkafa, tana durk'usawa ta mik'a mishi ta mik'e ta koma d'aki, kayanta ta cire ta fito da d'aurin k'irji da hijabi saboda kunyar uban ta shiga dan watsa ruwa, jim kad'an ta fito ta shiga d'aki doguwar rigar kanti kawai ta saka ta fita a gidan zuwa gidansu Asma'u, duk da kallo suka bita sai dai mama ta k'asan ido take kallonta saboda kunya.

Saida ta fice Abba ya sauke ajiyar zuciya y'a kalli mama yace "Ina zaune lafiya da kowa a unguwar nan, ina k'ok'arin kiyaye hakk'in mak'wabtaka, wallahi duk ranar da yarinyar can ta sake kira min 'ya da karuwa sai nayi shari'a da ita a kotun musulunci, ba zan lamunta ba wallahi dan na yarda da 'yata."

Mama kam a sanyaye tace "Ayi hak'uri dai malam, Allah ya kyauta kawai."

K'wafa Abba yayi yana jinjina kai bai ce komai ba, ita kam mama a ranta take jin zafin maganar kamar zatayi kuka, ko da da gaske ne abinda suka fad'a ai akwai cin zarafi da tozarci, ita kan ta bata jin zata iya yin shiru idan aka sake maimaita haka gaskiya, dan 'yarsu mutumcinsu ce, babbar darajarsu kuma Mimi ce.


*Mim-Ma'u*


Labarin fad'ansu da Maryam babu inda bai shiga ba, shiyasa ma tana shigowa gidansu Asma'u suka sakar mata ido aka yi shiru, ita kam dake ta saba da irin wannan kallon dama sai bata kula da tsiyar kowa ba, maman Asma'u kawai ta kalla tace "Mama Asma'u fa?"

Nuna mata d'akin tayi tace "Yanzu ta shiga ciki."

Wucewa kawai tayi ba tace da ta jira izinin shiga ba, samunta tayi tana saka kaya da alama wanka tayi ita ma, cire hijabi tayi ta jefa kan gadi ta zauna tana fad'in "Asma'u wurinki Abba ya aikoni."

Kallonta tayi tace "Wuri na kuma? Me y'a faru?"

Saida ta kalleta da kyau tace "Asas ne ya nemi izinin na je na ga Hajiarsu, shi ne Abba ya amince amma dole sai in tare zamu je da ke."

Da mamaki Asma'u ta zauna kan kujera tana gyara rigarta da fad'in "Da gaske Abba ya amince? Yaushe ne tafiyar?"

Yatsina baki tayi tace "Gobe."

Da fara'a tace "Ba komai Mimi, zan fad'awa mamanmu insha'Allah sai mu tafi."

Gyara zama tayi tace "Asma'u, bana so ki je gaskiya."

Da mamaki ta tsareta da ido tace "Ban gane ba? Me yasa?"

Cikin rad'a tace "Kin gane Asma'u, shi fa Asas ni kawai ya buk'ata sannan ni ce zai gabatar a gaban mamanshi, Abba dai nasan tsoron faruwar wani abu suke, insha'Allah zan kare kaina babu abinda zai faru."

Da mad'aukakin mamaki tace "Yanzu Mimi tsarin na iyayenki ne bai miki ba? Ina laifin kariyar da suke son baki ma?"

Yatsina fuska tayi tace "Ban ce bai min ba Asma'u, kawai dai ina so ne na tafi daga ni sai shi, bansan wace kalar tarba zan samu ba idan na je."

Cikin tsareta da ido Asma'u tace "To kinsan da haka me yasa kika zo kika fad'a min?"

Ita ma idonta cikin nata tace "Saboda tare zamu bar gidan nan."

Da mamaki tace "Kamar ya?"

Gyara zama tayi tana wani malalacin murmushi tace "...



*Muna barar addu'arku yan uwa? Allah ka bawa Khadija lafiya. Kwate na ma Allah ka k'ara mata lafiya mai inganci*



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:52 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*15*



"Zamu fita daga nan muje gidan Iya Delu, ke zaki zauna a nan ni kuma saina wuce."

Girgiza kai tayi tace "Mimi kina ganin ba matsala? Ya zakiyi idan Abba ya ganeki? Gaskiya ni dai ina jin tsoro ba za'a yi haka dani ba."

Cike da tabbaci da tsaurin ido tace "Babu abinda zai faru Asma'u, kwantar da hankalinki kawai."

Da alamar jimami sosai a fuskarta tace "Zamu ci amanarsu kenan? Yaudarar Abba zamuyi fa Mimi."

Girgiza kai tayi tace "Ba yaudara bace, Asma'u ki fahimceni mana, kinga yanzu idan..."

D'aga mata hannu tayi tace "Matsalata dake taurin kai, indai kikayi niyyar abu babu mai hanaki."

Mik'ewa tayi ta fara k'ok'arin d'aura zanenta bata sake tankata ba, ita ma mik'ewa tayi ta d'auki hijabinta a hannu ta fito dan tasan sunyi fad'a kenan ko zasu shirya sai sun had'e a islamiyyar yamma, takalminta ta saka a k'ofar d'akin ta wuce tana k'ok'arin saka hijab d'in, da kallo yayan Asma'u ya bi k'ugunta yana murmushi, lura da hakan yasa kishiyar maman Asma'u (mahaifiyarshi) cewa "Kai!"

Wannan tsawar data daka mishi tasa har Mimi juyowa ta kalleta, kallonta shi ma yayi yana zazzare ido, cikin jin haushi tace "Dan ubanka me kake kallo baki sake?"

Yatsina baki Mimi tayi ta juya ta saka hijab d'inta ta wuce ta barsu tana jin yana fad'in "To wai mama bani da ikon kallon abinda na ga dama ni da ido na?"

Ita kuma cikin fad'a take fad'in "Dan ubanka duk zalamarka waccen tafi k'arfinka, na d'aya dai kaga taxi ce ita da kowa ma shigarta yake, na biyu ba kowa take kulawa ba sai wanda taga akwai mamora a jikinsa."

Mimi kam ko fa a kwalar rigarta sai ma fita da tayi daga gidan, ita indai ita zaka tab'a kai tsaye to bata da matsala da kai, ka dai saka iyayenta ne ko da ta hanyar zaginta ne bata lamunta ko kad'an, dan taana da tabbacin ko mijin aurenta zata iya tsinke fuskarshi da mari idan ya nemi fad'a ma iyayenta magana.


*Sheikh*


Cikin nutsuwa ya sake tank'washe k'afafunshi yana had'e tafukan hannayenshi ya ci gaba da fad'in "A duk inda zaku shiga a fad'in duniya, a duk halin da zaku tsinci kanku a ciki yarana kada ku yarda kuyi wasa da addininku, addininku shi ne gatanku, addinin islama shi ne alk'iblarku, addinin nan shi ne madogararku, dan haka duk inda zaku samu kan ku kuyi alfahari da addininku, kada bambamcin yare ko k'abila yasa ku ji kunyar nuna kanku a matsayin musulmi, kada wani rud'i na duniya ko kuma muzgunawa tasa ku wofantar da addinin daya baku madafa a sanda baku da tudun dafawa, addinin musulunci rahama ne a garemu kuma alfarma."

A hankali ya kalli Aisha yace "Aysha, ke ce babba a gidan nan, ina sake gargad'inki da ki kula sosai da yan uwanki ki tayasu rik'e sallarsu ta farilla, kada ki barsu suyi wasa da ita a kowane hali, nasan macece ke kuma a halin yanzu kowane lokaci zaki iya shiga d'akin mijinki, amma hakan ba zai hanani sake jadadda miki rik'o da zumuncinku ba, a duk inda aure ko ratuwarki ta gaba zasu kaiki, zaki iya tsayawa tsayin daka wajen ganin kun rik'e zumuncin nan, ko bayan babu ranmu zaku zama gatan junanku."

Cikin tsareta da ido yace "Kin fahimta?" Jinjina kai tayi alamar eh cikin sanyayyar murya tace "Eh Abie, insha'Allah zamu rik'e zumuncinmu, wannan alk'awari na ne a gareku iyayena."

Jinjina kai yayi yace "Masha'Allah, sai kuma kai *Heezam*." Ya fad'a yana kallon k'annan Aisha mai bi mata, a nutse yace "Bana da d'ar a kan ka dan na saka maka ido sosai ina lura da duk wani tako da motsinka, a tak'aice kuma a yanzu dai banga wani abu daya nuna shagala akan sallahrka ba, haka kuma ban ga alamar wasa a cikin karatunka ba, kamar yanda banga wani b'ataccen aboki da zai iya b'ata tarbiyarka ba, saidai hakan ba shi zai sa na zuba maka ido ina kallonka haka kawai ba, Heezam."

Ya kira sunanshi cikin dakakkiyar murya, amsawa yayi a ladabce yace "Na'am Abie."

D'orawa yayi da "Daga yanzu zamu fara fita tare da kai zaman majlisi, sannan ina so kai ma ka fara wani k'ok'ari akan matasa yan uwanka dan bayar da ta ka gudummuwar."

Da ladabi ya jinjina kai yace "Insha'Allah Abie."

Kallon *Aswane* yayi ya saki murmushi yace "Manya masu gari, macijin k'aik'ayi kenan sari ka nok'e, wato yarona Aswane duk gidan nan babu wanda ya kai ka karatu, haka kuma babu wanda ya kai ka iya shegantaka."

Duk dariya aka d'auka a wajen har Hafsat dake shafar cikinta saboda juyawar da yaron cikin ke yi mata, cikin muryar laushi tace "Akwai son gayu fa kamar ya ga ubanshi Asas, amma kuma yafi kowa tsanar irin shigar da matasa keyi ta k'ananan kaya."

Dariya sheikh yayi sosai yana fad'in "Wannan ikon Allah yana bani mamaki, wai kai ka saka riga da wando na zamani ka d'aure k'ugu da ceinture (belt), amma idan ka fita waje ka ga wani matashi zai wyce da shiga irin ta kai saika gyara tsayuwa ka tsayar ka dinga yanko mishi hadisai da ayoyi harda karatun d'ab'ia na d'an adam ma kana nuna mishi rashin dacewar haka."

A sanyaye ya kalli Aswa'ne daya d'aure fuska tamau yace "Sheikh Aswane ya kake nufi ne to? Shin kana so ka koyar da hallacin shigarka ne ga matasa a aikace? Ko kuma dai kana son su k'yamaci abinda kai suka ga kana yi ne?"

Saida ya sauke ajiyar zuciya ya shafa tarin sumar dake kan shi a gaban yace "Abie, ai ni ba irin waccen shigar nake yi ba da ake zazzago wando ana takawa, kuma nima ina so na daina saidai Allah ne ya saka min soyayyar kayan a raina, kuma sun fi yi min kyau idan na saka."

Girgiza kai yayi yace "Kash! A gaskiya tunani da idonka sun fad'a maka k'arya yarona, taya kake tunanin suturar yahudawa zata fi yi maka kyawu fiye data ka suturar? Wa ya fad'a maka kawai kana son su ne saboda Allah ne ya saka maka soyayyarsu? Aswane magana ta gaskiya sutura ta hausa ita ce cikakkiya kuma kamilalliyar sutura, na yarda idan ka ce sun fi maka kyawu a jikinka, to amma kamala fa? Ita ma suna fito maka da ita ne?"

Shiru yayi kan shi a k'asa hakan yasa shi girgiza kai ya gyara zama tamkar zaiyi magana da d'an shekara ashirin ba wanda shekarunsa duka goma sha biyu bane yace "Aswane, wannan suturar da kake sakawa ta hayudu ce, manufa ce dasu data sa suka k'irk'iri wannan suturar, kuma sun cimma burinsu tunda har suka yi nasarar ribatar ire-irenku, amma ka sani cikar kamala na cikin tufafin hausa, fito da asalin haiba da kwarjinin mutum sai tufafin bahaushe, da wannan nake kira gareka d'ana ka siyawa kanka mutumci ta hanyar yafa shigar mutumci a jikinka."

Jinjina kai Aswane yayi yace "Insha'Allah Abie, zan kiyaye."

Jinjina kai yayi ya kalli d'an k'aramin yace "Wannan shi ne autana kuma ba autana ba, *Munzeer* yaron kirki ne, ba ruwanka da rigima ko fad'a, karatu kawai ka saka a gaba ko yaron kirki?"

Cike da jin dad'i yaron mai shekara biyar ya jinjina kai alamar eh, dafa kanshi yayi yana jinjina kai da murmishi yace "Allah muku albarka, Allah ya k'arawa karatun albarka, Allah ya k'ara had'a kanku, Allah ya wadataku da lafiya mai anfani."

Gyara zama yayi yace "Ku tashi ku tafi." Mik'ewa sukayi bayan sun amsa a ladabce, duk da kallo suka bisu har suka b'ace ma ganinsu, saida suka shige ciki kafin ya mik'e shi ma, hannun Hafsat ya kama yana fad'in "Muje ki kwanta ki huta, dare yayi fa."

Murmushi tayi tana ci gaba da shafa yaron cikinta daya dunk'ule wuri d'aya kamar baya motsi, suna shiga d'akin ta fahimci yau kenan zai kawo mata ziyara, dan baya zaune sai mace ta sameshi d'akinshi, da kanshi yake zuwa inda kike sannan ya lallab'aki ya amshi hakk'inshi, dan haka saita daure sosai ta saki jikinta bata yarda ta nuna bata jin dad'i ba, saida ya tayata yin wanka kafin suka k'arasa gadon girma, duk da tana jin d'an cikinta ya dunk'ule mata a mara haka ta jure bata nuna bata ra'ayi ba, har tambayarta yake ya isa haka saita sunkuyar da kai tace "Sai ka gamsu."

Shi kuma a duniyar Allah yana matuk'ar son mace mai raki, rakin ma irin na tsiyar nan, wallahi a duniya yana son y'a ga mace dake mayar da masassara ciwon kai, wacce zata dinga billi tana kuka akan abinda bai kai bai kawo ba, yana so wata rana Hafsat ta gwada yin haka ko sau d'aya ne, da zai yi zaune ya aje hularsa da babban riga da hirami ya dinga mata hidima yana rarrashinta. Da k'yar ya samu gamsuwa ya taimaka mata ta tsarkake kanta ta dawo ta gyara shinfid'ar ta kwanta a matuk'ar wahale.


*Washe gari*


Tana tsaka da tsantsara kwalliyarta a fuska ta ji wayarta dake cikin k'aramar jakar da zata fita da ita tana vibrations, saida ta d'an d'aga labulen d'akin ta tabbatar suna waje suna harkar gabansu kafin ta ciro wayar, zaro ido tayi ganin lambar sheikh ce wacce tsabar mahimmancin data bata har ta iya hardaceta a kan ta, ita kan ta bata san ta bashi wannan mahimmancin ba. Sam bata son d'aukar wayar a lokacin, amma abun mamaki lambarshi kanta kwarjini

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login