Showing 51001 words to 54000 words out of 185502 words

Chapter 18 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

488

da zuciya d'aya na so samunki a matsayin matar aurena? Ni ba yaro ba ne tunda har ina da 'ya kamarki, ni ba zauna gari banza ba tunda ina da aiki, daidai gwargwado zance ni ba mutumin banza bane, ana girmamani ana ganin darajata a k'asashe da dama bare kuma k'asata."

Da k'arfi ya sake juyowa kanta a hassale sosai cikin daka tsawa yace "To a kan me zaki maidani wawa da bai san me yake ba?"

Wani matsanancin kuka ta fashe dashi ta sake yin k'asa da kanta tana fad'in "Kayi hak'uri ka gafarta min, har zuciyata ban yi haka da niyyar cutar da kai ba saidan ganin kai d'in babban mutum ne, har zuciyata nake jin rashin dad'i idan ina son fad'a maka gaskiya, dan Allah kayi hak'uri karka cutar dani."

Wani iska ya shiga furzowa mai zafin gaske na tsananin b'acin rai, bai sake magana ba sai kallonta kawai da yake, d'an tsaki yaja k'arami ya fita daga motar ya rufo mata k'ofar da k'arfi ya zauna mazaunin dreba, da k'arfin tsiya ya figi motar har saida ta gwara kanta a k'ofar da take zaune, kuka take kamar zata mutu ba k'akk'autawa, sosai take jin zafi a zuciyarta na jefa babban mutumin nan cikin wani hali marar dad'i. Shi kuma ko juyowa bai sakeyi ba har saida ya ja pakin a k'ofar gidansu ya tsaya, tashin hankalin da take ciki ya mantar da ita Asma'u da sukayi mahad'a da ita, tashin hankalinta yasa ta manta wayarta a jakarta kuma a kunne take saidai a vibrations.

Shiru tayi bata bud'e motar ba bare ta fita ta k'ura mishi ido ta baya tana kallo yanda ya had'e fuska kamar hadarin gabas, saida ta sake share k'walla tayi k'arfin hali ta bud'a baki cikin dakusashiyar muryar kuka tace "Dan Allah ka gafarceni, karka rik'eni a zuciyarka, wallahi bana jin dad'i a zuciyata."

A sanyaye kuma a ladabce kamar ba shi yayi maganar ba yace "Shiru! Mak'aryaciya kawai."

Da sauri tace "Wallahi gaskiya nake fad'a maka."

Girgiza kai yayi ba tare daya juyo ba yace "Alamar k'arya kika fad'a kenan, wannan rantsuwar da kikayi.".

Saida ta gyara zamanta sosai cikin magiya tace " Abdul gaskiya nake fad'a maka, maganar nan daga zuciyata take fitowa, bana jin..."

Wani kallo ya watso mata ta madubi na mamaki, suna had'a ido ta sunkuyar da kanta saboda kwarjininshi, a hankali ta jinjina kai cikin sanyin murya tace "Ni ma haka kawai nake jin bakina yace Abdul, kayi hak'uri dan Allah."

Yanda fuskarta tayi gwanin tausayi tasha kuka gashi ta sunkuyar da kai, hakan ya bashi damar sakin murmushin gefen labb'a tare da d'auke idonshi a kanta, a dak'ile sosai yace "Na yafe, amma ki kula ki daina k'arya, ba kyau Ryam."

Jinjina kai tayi da sauri tace "Insha'Allah."

Matsawa tayi jikin k'ofar ta bud'e murfin a hankali ta sauka tare da rufo mishi murfin, ta glas d'in motar ta k'ura mishi ido tana takawa zuwa cikin gidan, ta gabanshi ta wuce hakan yasa shi saurin rufe idonshi, abayar ta fito da k'irar jikinta sosai kuma da yake ita d'in yar duma duma ce hakan ya wanzar da wani tasiri a zuciyarshi, ga kallabin rigar dake shirin fad'uwa a kan ta wanda yake nuna mishi lallai zatayi gashi a kan ta ko ba sosai ba, saidai yana so yasan su d'in wace k'abila ce? Mahaifinta bak'i ne sosai kuma gajere dake manne da k'asa, saidai kakanta daya haifi mamanta dogo ne sosai, amma kuma ita bata d'auko mahaifinta ba ta ko ina. Yana cikin tunanin ya sake bud'e idonshi a k'ofar gidan, a lokacin tana daf da shigewa ciki ta sake juyowa, a hankali ta d'ago hannunta ta mishi bye bye tana sakar masa murmushi.

Da sauri ya kuma lik'e idonshi yana dafe gaban goshinshi ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."

Yanda shed'an ke ta k'awata mishi ita a zuciya ne yake son yakicewa, so yake ya manta da komai ya rik'eta surukarshi matar k'annanshi, saidai shed'an sai hura mishi wuta yake a kan yarinyar komai tayi sai yaji zuciyarshi na fad'a mishi " *Komai na ta yanda kake so*."

Cak a daidai bakin k'ofar ta tsaya sakamakon komai nata daya daina aiki, Abba zaune dangalgal akan k'asa ba takalmi a k'afafunshi, ga kuma Mama zaune a gefe kan kujera sai Asma'u ita ma durk'ushe gefen Abba tana share hawaye, tunda ta ga haka ta san yau wannan rana bak'a ce k'irin a gareta, yau ranar kam babu sa'a a gareta, me ya faru? Me kuma zai faru?

*Tun* bayan tafiyarsu ba jimawa Abba ya dawo daga masallaci ya samu Muttak'a a k'ofar gidan, ba yabo ba fallasa suka gaisa inda Muttak'a ke fad'in "Abba dama na zo wajen Mimi ne, saboda ina ta kiranta bana samu shi ne na zo naji ko lafiya."

Da matsanancin mamaki Abba ya d'aga kai sosai ya kalleshi dan shi ma a tsaye yake ba ko rusunawa yace "Kiranta kuma? Dame kake kiran nata?"

Da mamakin tambayaar yace "Da wayarta mana, ina ta kirane shiru ba'a samu, ko ita wannan wayar ta samu matsala ne? Idan ta lalace sai na sake mata wata ai ba damuwa bane."

Jim Abba yayi yana kallonshi yana jin mamakin kalamanshi, ba tare da yabi ta kanshi ba kawai ya juya a fusace ya shiga cikin gidan, Mama data idar da sallah ya tsaya bayanta akan tabarma yace "Ke kinsan *Maryama* tana da waya ne?"

Da sauri ta juyo da mamakin jin yau sunan mahaifiyar ma tashi ya kama haka, tabbas yana kiranta Maryam wasu lokuta, amma dai jin sunan Maryama ba dai a bakinshi ba, cikin rashin sani tace "Waya kuma? Wace irin waya malam?"

Wani dogon tsaki yaja tare da kutsawa d'aki ya shige, akwatinta guda biyu duka ya jawo a k'ark'ashin gado, bud'esu yayi ya shiga ciro kayanta d'aya bayan d'aya yana zazzagewa yana dubawa, har k'ananan kayanta daya ci karo dasu pant da bras da cotton saida yayi cilli dasu a tsakiyar d'akin, jikinshi har rawa yake kamar mazari. Ganin bai samu komai a nan ba yasa shi jawo jakunkunanta na hannu sama da guda goma duk k'anana na yan zamani, a tsanake ya shiga dubasu yana bud'a kowane gida a cikinsu, babu waya babu alamarta, saidai ya samu layiyyika (sim) a k'alla guda bakwai, ga poshet na waya wanda take cirewa ta sake wasu suma har guda biyar, ga kuma tsabar kud'i daya samu a wata k'aramar jakarta har jaka ashirin da uku, wata irin juwa ta d'ebeshi ta kayar akan kujerar robar dake d'akin, wannan k'arar ce tasa Mama tashi da gudu gudu ta shiga hankali a tashe, tana k'arasawa ta shiga kiran sunan "Malam, malam lafiya? Wai me yake faruwa ne?"

Bud'a ido yayi a matuk'ar wahalce ya kalleta, zunbur ya tashi tsaye yana sake kallon hannayenshi, nuna mata yayi amma bai ce komai ba saboda nauyin da bakinshi yayi, rab'a Mama yayi ya fito da sauri ya saka takalminshi ya fita a gidan.

Yanda yake saurin zaka rantse dungurawa zaiyi ya fad'i saboda yanayin hallitar, amma kuma haka yake tafiyar yana sauri dan isa gidan Iya Delu, yau kam yasan sai yayi abun kunya gidan surukai, amma fa babu mai hanashi karya Mimi idan sukayi ido takwas takwas.

Suna barin k'ofar gidan Abba na kawowa hakan yasa ya had'e da Asma'u da zata tafi gidansu Jamila, a tsawace sosai yace "Ke tana ina?"

Duburburcewa tayi ta shiga rarraba ido, matsowa yayi zai kamo hannunta ya durk'usar da ita sai tayi saurin ja baya tace "Abba sun tafi."

"Ina?" Ya fad'a da jin haushi, cikin rashin gaskiya tace "Can, wallahi Abba ni babu laifina, saida na fad'a mata mu tafi tare tace wai..."

Shiru tayi saboda tausayin k'awarta tasan yau kam saita Allah Mimi, nuna mata hanya yayi yace "Wuce muje, zataa zo gidan ta sameni, zaku fad'a min abinda kuke shiryawa da bamu sani ba."

Da sauri ta wuce har tana had'awa da gudu Abba ma biyarta yake da saurin kamar zai had'a da gudu shi ma.


Mimi dake tsaye ta rasa yanda zatayi, ta koma da baya ne ta nemo taimako a gidansu Iya? Ko kuma dai tayi k'undumbala ta shiga? A gaskiya bata son abinda zai tab'a mata lafiyar jikinta, bata son jin duk wani abu daya danganci rad'ad'i a jikinta, muciyar data gani gefen Abba kuma irin muciyar nan ce mai kama da ice irin na yan damagaram, ta tabbatar da ita yake shirin dukanta. Ajiyar zuciya ta sauke a b'oye tana ci gaba da rarraba ido, d'agowa yaayi ya kalleta idonshi jajir kamar wanda yayi kuka yace "Shigo."

Marairaicewa tayi ta durk'usa a wurin tace "Abba kayi hak'uri dan Allah karka dakeni, ka tambayeni da baki zan fad'a maka komai."

Wuntsi Abba ya wulk'ita ya tashi tsaye yana sake d'aukar muciyar a hannunshi ya nuna mata gabanshi yace "Maryama ki zo nan indai ni na haifeki, in kuma kina so ki nuna min ke babbar mace ce da kika isa da kan ki to ki bar gidan nan."

Fashewa tayi da kuka tana girgiza kai ta kalli Mama da kanta ma ke k'asa, cikin rikicewa tace "Abba karka dakeni dan Allah, zan maka bayanin komai wallahi da dalilina na yin haka, Abba karka dakeni ka ji, zan zo yanzu amma ban da duka."


Sheikh da har yanzu bai guda daga wurin ba ne ya fara jin kamar hayaniya, sai zuciyarshi ta raya mishi ko dai jimawar da tayi ne ya sa tayi laifi haka, a hankali ya bud'e motar da tunanin ko sallama ne yayi ya fad'i dalilin jimawar, a hankali cikin kamala da dattako ya shiga takawa izuwa k'ofar gidan, a nan ya tsaya ganin Mimi durk'ushe tana magiya.




*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:54 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*18*




Abba saida ya k'ara tamke fuskarsa yace "Mimi idan baki k'araso inda nake ba na damk'e ki saina fasa maki baki da hannuna."

D'an mudil mudil d'in hannun sheikh ya bi da kallo kafin yake d'an k'ara k'arasawa yana son yin magana amma yanayin da mahaifin nata ke ciki saiya d'an dakata yana sauraronsa.

Abba ya rasa ina zai saka ransa, kwata kwata bai kula da cheikh ba hakan yasa yayi taku ya kai goma yana kai kawo a d'an wajen da ba girman kirki ne da shi ba ga mama kanta sadde jikinta har yanzu b'ari yake cike da alhinin wannan tashin hankali.

Su dukansu basu shirya ba suka ga Abba ya hau dutsin dake kusa da Mimi wanda ta durk'usa kad'an kusa da shi bata kai tsayinta kaf ba amma ta rage tsayin nata sosai ya d'aga wannan hannu nasa dugul ya wanka mata marin da ya sakata zabura daga d'an durk'ushen da tayi ta falla ihu ta shiga dira tana rik'e gefen kuncin nata tana kururuwar a taimaketa Abba zai kasheta.

Rai b'ace ya d'aga muciyar nan zai kuma doka mata ita da sauri sheikh ya rintse idonsa yana jin wani irin rad'ad'i a zuciyarsa tamkar shi aka doka ba ita ba.

A hassale Abba yace "Yanzu Mimi kece da wannan rayuwar? A gidan wa kike samu wayar dake hannunki da kud'in dake nanik'e cikin jakarki? Wato kin banzatar da kanki ko? Biye biyen maza kike da suke baki wannan d'in ko me?"

Gaba d'aya ya bud'e idonshi zuwa yanzu yana jin wata zufa na son karyo masa da girmansa da komai haka kawai kan rigimar budurwar yar da bai san haka cikinta yake ba.

Mimi kam tana dire diren nan ta tsaya da sauri jikinta na rawa ta had'e hannayenta tace "Abba na rantse da sarkin dake busa numfashi bana haka, sam ban san wannan hanyar ba, Abba ban tab'a aikata zina ba tunda mama ta haifeni, wallahi wallahi wallahi ban iya ba."

Abba ya kuma matsowa yanzun da take tsugune ya damk'i kunnenta na hagu yace "K'arya kike uwata, wannan zamani da ya zama na bala'i me kike tunanin kina iya fad'a min na yarda dake? Ba zai yiwu ba wuce mu tafi wajen Hajia Gambo, wuce!"

Zuwa yanzu mamanta kanta hawaye take sharewa a tsugunen da take kuma ita sarai ta ga sheikh wanda gaba d'aya ya jinginar da bayansa jikin garu yana jin juwa na d'ibansa na wannan abu dake faruwa.

Mama dake son dakatar da shi dan kar a yi wannan abin a gaban mutane idan har abinda yake zargin kenan su tonawa kansu asiri muryarta na rawa tace "Malam, ka ga sheikk ne a tsaye fa, na san sallama yake."

Malam ya kai dubansa inda take nuna masa, sai a lokacin ya ganshi, shi da kansa sai da gabansa ya k'ara fad'uwa cike da tsoron shikenan ta tabbata ta gama janyowa kanta tashon hankali mai yiwuwa maganar fasa auren ta kawo shi nan shima ya lumshe idanuwansa cike da tashin hankali muryarsa zuwa yanzun ta k'ara yin sanyi yace "Nasan abinda ka ji kenan ka zo wajena ko sheikh? Sai dai ka ganta nan ban san rashin jin nata ya kai cen ba, Innalillahi wa'inna ilaihi raju'une ban san cewa tana rik'e da wayar salula a hannunta ba har ta tara kud'i irin wannan a jakarta ba, ka ganni nan talaka ne mai wadatar zuci haka mahaifiyarta, sannan irin yadda muke taka tsantsan a kan shige da fitarta bamu san ta waye haka ba, idan ka ce kun fasa ba zan k'ullaceku ba domin ni kaina yanzu ban yarda da mimi ba. Zan kaita gidan Hajia Gambo cen layin likita ce ita ke duba mana mararsa lafiyar anguwa ni baba take ce min muna mutunci sosai da ita domin mai d'akina ke mata tuyar wainar juma'a, zan kaita ta duba min ita idan ta rigaya ta gama lalacewa shikennan sai a fasa ta dawo ta zauna..."

Irin yadda Abba ke maganar gaba d'aya hankalinsa a tashe ransa a b'ace, Mama kuwa kunya da tashin hankali ya sakata shigewa ciki da saurinta, Asma'u kuwa hawaye take wani na korar wani inda mimi gaba d'aya bakinta ya gama mutuwa tana tsugune ne gaba d'aya jikinta na mata rawa hankalinta ya gama tashi.

Sheikh yayi iya yinsa ya aro dukkan jarumtar da ta rage masa da k'arfin addu'a sannan ya gyara tsayuwarsa da shigarsa ta kamala ga k'amshin da yake ta fitinar hancin kowa da shi mai dad'in gaske ya tausasa muryarsa yace "Ba za'a yi haka ba malam, a yi hak'uri, na zata ko dan ta yi dare ne na zo na fad'i cewar shi wanda aka saka masu ranar ne ya je asibiti shi yasa na kawota, aman ina ga mai zai hana a shiga ciki a tattauna a nutse ta yadda komai zai shiga cikin haske ba tare da rayuka sun b'aci ba."

Cike da girmama shi Abba yace " Akaramakallah, ba zaka gane wacece mimi ba, idan bamu je ba ba zan tab'a samun nutsuwa ba , kuma idan kuka fasa aurenta ba zan tab'a jin haushinku ba domin tsatso mai kyau ake wawa ba sakarya ba!" Ya k'arashe yana harararta.

Zuwa yanzu ta gama gane cewar ashe duniya banza ce? Yar gajeruwar k'afarsa ya saka ya hanb'areta yana fad'in "Tashi muje, mutuniyar banza kawai."

Tana ji tana gani mahaifinta ne gaba da aminiyarta da mutumen da zata iya rantsewa cewar bata tab'a jin nauyi da kunya da darajar wani d'an adam mai saka wando da zariya bayan mahaifinta irin na wannan bawa ba, sai gashi a yau sanadiyar yan samari da take kulawa, da d'an karb'ar abin hannayensu ba tare da iyayenta sun sani ba ta b'allowa kanta ruwa, an tisota a gaba za'a kaita wajen likita a ware k'afafunta a dubata ita ba mai shirin haihuwa ba ita ba mai rashin lafiya ba.

Gaba d'aya ta nemi wani kukan ta rasa, haka kuma baki d'aya ta zama wata sukuku tana ganin ikon Allah har suka ja suka tsaya a k'ofar gidan wanda sheikh ne ya nemi a sirrinta shi kam in ba dan wani irin girman dattijon mahaifin Maryam ba da ba zai yarda a aikata wannan lamari da shi ba.

Suna fitowa suka ga motar Asas wanda ganin shigarsu mota yayi gaba d'ayansu ya saka shi fasa tsayar da tasa ya karkata ya bisu dan a yadda ya ga da k'yar Abbban sahibarsa ya cibcib'a ya wuntsila cikin motar da irin yadda da k'yar ya shiga baya ga sheikh da kansa ke tuk'in sai ya ga kamar ba lafiya ba.

Daga motar ta fito wannan karon d'an kwalin abayarta a hannunta yalwatacen gashin kanta ya bayyana bak'i sid'ik da shi har wajen gaban goshinta.
Gabanta ne ya buga a lokacin da suka yi ido hud'u da Asas a hankali ta lumshe lumsasun idonta wasu hawaye suka zubo mata.

Cire dubanta ta yi tana ganin yaron daya fito yake shaidawa Abba cewar su shiga, kasancewarta likita tana samun bak'i maza da mata ta ko ina a kowane lokaci.

Cike da tausayawa take kallon Mimi bayan Abba ya gama kora bayanin abinda yake buk'ata, uwa uba sheikh dake zaune kansa sadde k'asa tunda ya shigo ta rasa ina zata saka kanta dan murna domin har k'asa ta duk'a ta gaishe shi dan kuwa a duniyarta wa'azi idan ba nasa bane bata jin dad'insa, nutsuwarsa, kamalarsa ya saka take son wa'azinsa domin a sanyaye yake isar da sak'on Allah.

Sai Ashraf da ya zabura jin bayanin Abba yana kallon Abban, da Mimi da du wanda yake wajen yana son k'arin bayani amma ba hali domin sheikh ya had'e fuskarsa.

A nutse Hajia Gambo tace "Ayya Abban Mimi, ai kam Mimi akwai nutsuwa duk da baka shaidar d'an yanzu amma bana tunanin idan har zata zubar da mutuncinta haka ba, ka san ba duka 'yan matan namu suka zama d'aya ba duda abin yanzu ya zama na tir sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login