Showing 174001 words to 177000 words out of 185502 words

Chapter 59 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

528

wuni?"


Rintse ido tayi tana d'an yatsina fuska ta amsa k'asan mak'oshi da "Barka."

Da murmushin shi a fuska ya d'ora da "Ya su Hafsy? Kwana biyu baki lek'a k'awarki ba?"

Bud'e ido tayi a hankali ba tare data kalleshi ba tace "Lafiya lau."

Mayar da kallonshi yayi kan sheikh dan ya fahimci bata cika son kulashi ba yace "Sheikh sai ina? Ko shak'atawa aka fito?"

"Um." Ya fad'a yana wucewa inda Mimi ta bi bayanshi yana fad'in "Zan sameka gida ne?"

Juyawa Asas yayi ya kalleshi yace "Yaushe?"

"Yanzu." Ya fad'a kai tsaye, da mamaki yace "Da gaske wai? To indai hakane saidai na tafi yanzu dan ku sameni."

Juyowa yayi ya kalleshi yace "Ba abun ujila bane, daga nan gidansu zan kaita, daga nan ne zan wuce da ita can." Da kallo ya bisu suka k'arasa fita kafin ya maayar da hankalinshi kan Hajia.


*Tsaye* suke k'ofar gidan cirko cirko kamar masu jiran fitowar wani, a karo na ba adadi kenan da sheikh ya kalleta yace "Ryam, yanzu a nan zamu tabbata a tsaye kamar wasu masu zance?"

Sake marairaicewa tayi tana d'an kukan shagwab'a tace "Ustaz ba haka bane, ni wallahi kunyar Mama nake ji, data ganni fa zata shiga k'are min kallo har sai ta gane ina da wannan."

Ta fad'a tana dafa cikinta, girgiza kai yayi yace "Ryam abun farin ciki ne fa, Mama zatayi murna da haka fiye da tunaninki, ita a wajenta hakan ya tabbatar mata lallai 'yarta ta girma, hakan yana mata nuni da cewa 'yarta ta zama babba, hakan na alamta mata ashe 'yarta tauraruwa ce ita ma a gidanta, hakan na nuna mata ke ma mijinki na kulaki, ba wai kara zube kike a gidan shi ba, Ryam Mama zatayi farin ciki zata samu jika daga gareki, ke 'yarta ta farko, duk soyayyar da take miki da wannan alkunyar kasancewarki 'yar data fara haifa, yanzu zata koma kan d'an dake cikinki ne, a da idan Mama bata kulawa da ke, a yanzu sanadin cikin nan zata zamo tana kulawa da ke fiye da yanda kike jaririya, dan Allah Ryam ki shiga mu gaishesu sannan ki nemi afuwarsu abisa komai kafin mu bar k'asar nan."

Jikinta a mace ta jinjina kai tana kallonshi tace "To muje."

Gaba tayi yana d'an binta a baya yana fad'in "Ki fara shiga sai ki fad'a musu tare muke."

"To." Ta fad'a tana saka k'afarta d'aya a cikin gidan, kamar an tsayar da ita kuma sai ta tsaya ta juyo tasa yatsarta babba a baki tana d'an cizawa tana kallonshi tace "Sheikh kasan wani abu? Kuma fa Mama ma..."

Sai ta nuna mishi ciki ta nuna cikin gidan alamar Mama ma ciki ne da ita, sai kuma tayi kamar zata fashe da kuka tace "Ni wallahi kunya nake ji."

Da k'arfi sheikh ya rik'e dariyarshi a zuciyarshi yana fad'in "Oh Allah." A zahiri kuma saiya gimtse ya kalleta yace "Ryam zan shiga masallacin nan na shelantawa mutane kina d'auke da ciki, kinsan dai zan iya ko?"

Zaro ido tayi da sauri ta shige cikin gidan tana fad'in "Sheikh."

Da sallama ta shiga Abba dake wanke hannaye ya gama cin tuwo ya amsa yana zuba mata ido, bai bari ta k'araso ba yace "To uwata shirmatu, yau kuma da wace aka zo mana?"

Murmushi tayi ta k'arasa kusa da shi ta durk'usa da ladabi tace "Abba na daina komai fa, ina wuni?"

Girgiza kai yayi yace "Za dai ki daina uwata, ni tunda na ga ruwan lalle basu sa kinyi hankali ba ai na sare da lamarinki."

Mama data fito daga d'aki ne ta kalleta tace "Ke kuma fa daga ina warhaka?"

Da girmamawa tace "Ina wuni Mama?"

Zaune mama tayi tana d'an shanye cikinta daya fito sosai a k'alla wata shida tace "Lafiya lau."

Mik'ewa Mimi tayi ta k'arasa kan tabarmar kusa da Mama ta zauna tana satar kallonta, kunya take ji sosai tana rufeta ita da ciki mamanta ma haka, sai kawai ta sunkuyar da kan ta tana d'an cije leb'e, Abba ne yace "Wai ke da wa kika zo a daren nan?"

Turo baki tayi ta kalleshi tace "Abba tare da shi ne fa." Kallon Mama tayi tace "Mama wai ina su Yaseen?"

A dak'ile Mama tace "Sun tafi gidan Iya na aikesu."

Mik'ewa Abba yayi yace "Kinga irinta ko? Kin gani, yanzu shigowa tayi ta baro waje ko a jikinta."

Ficewa yayi yana gyara zaman hularsa, jim kad'an ya dawo da sauri yana d'auko kujerar roba ya aje ya cewa Mama "Shigowa zaiyi ya gaisheki, kinji wai yana mahaukaciyar zai d'auka su tafi k'asar waje."

Kyab'e fuska Mimi tayi ta kalli Mama da ita ma ta kalleta, mik'ewa mama tayi ta d'auko d'an k'aramin hijabinta ta saka ta zauna tana takura kanta yanda ba za'a gane cikin jikinta ba, cikin nutsuwa da dattako ya shigo d'ai bayan d'ai cikin shigarshi ta kamala, a nutse ya zauna kan kujerar bayan yayi sallama Mama ta amsa, kanshi sadde k'asa yana kallon hannayenshi suka shiga gaisawa da Mama sosai, kafin daga bisani ita ma ya fad'a mata zasuyi tafiya ne su ka zo yi musu ban kwana.

Cike da dattijantaka Mama tace "Allah ya kiyaye hanya, a je lafiya a dawo lafiya."

Kallon Mimi tayi tace "Sai a kula kuma, ban da shiririta dan Allah."

Murmushi yayi a ranshi a furta "Akwai ta kam."

Mimi kuma turo baki tayi tana mamakin yanda duka iyayen na ta har yanzu suke ganinta da shirme bayan ita tasan ta daina yanzu.

Sun jima zaune kafin ya mik'e yace "Zamu wuce, sai anjimanku."

Mik'ewa Abba ma yayi yana fad'in "To shikenan, sai anjima, Allah kiyaye hanya Allah tsare."

"Ameen Ameen." Ya fad'a yana d'an satar kallon Mimi duk da ba hasken wuta ke akwai ba, Mama ce ta d'an zunguri Mimi hakan yasa ta mik'ewa a kasalance ta saka takalminta cikin shagwab'a tana fad'in "Abba, Mama ni dai ku yafe min duk abinda na muku, kunga dai jirgi zan hau ko? Ban son ko na sauko a raye ba."

Bata jiran amsarsu ba ta yi gaba sai sheikh ne ma ya bita a baya,a k'ofar gidan suka ci karo da su Yaseen sun dawo, tsayawa tayi da k'annanta suka gaisa tana fad'a musu zasuyi tafiya, ai da sauri Amir yace "Mimi ni dai ki kawo min irin moton nan na wasa."

Yaseen kam cewa yayi "Ni dai duk abinda kika kawo min ina so."

Dariya tayi tace "To shikenan zan kawo muku, amma ku kawo kud'i?"

Zazzaro mata ido sukayi suna kallo sai kuma suka saki murmushi Yaseen na fad'in "Idan kika siyo zamu biyaki."

Sheikh dake saurarensu ne ya kamo hannun Amir yana sunkuyawa sosai yace "Rabu da ita kaji, idan ma bata siyo ba ni zan siyo."

Hannunshi yasa aljihun babban rigarshi ya ciro sababbin kud'i a mik'e zar ya damk'a mishi yace "Wannan na kashewa ne idan zaka tafi makaranta."

Godiya yayi cike da jin kunya yana rik'e kud'in da hannu biyu, shigewa sukayi ciki su ma suka shiga mota suka nufi gidansu Iya, nan ma sun d'auki lokaci suna ta raha da tsokanar juna malam na fad'in ya yarda ya ara mishi amaryarshi su je su dawo, hakan yasa sheikh farin ciki sosai da jin wani sabon nishad'i, nan ma d zasu tafi kud'i a aje musu suka fito zasu tafi.

Iya ce ta rik'o hannunta cikin rad'a tace "Ke! Wai yanzu wata na nawa koke ciki ne? Bana son sai kinje can zaki fara awon farko."

Da mamaki Mimi ta kalleta tace "Iya watan me? Wane irin awo kuma? Na masu tamowa?"

Dak'uwa Iya ta mata tace "Na masu shan Inna dai, ina maganar k'warai zaki saka min shirme."

Turo baki tayi tace "To Iya ban gane me kike nufi ba ko?"

D'auke kai Iya tayi daga gareta tace "To na ji, cikinki na ce watanshi na nawa ne yanzu?"

Bud'e baki tayi tace "Lahhh! Iya kuma haka kika koma? To ni gaskiya ban sani ba."

Dungure mata kai tayi tace "Ke wai ba zaki cire shirme a rayuwarki ba, to karki sani bari na tambayi wanda ya sani."

Zaro ido tayi tace "Wa wai?" Nuna mata sheikh tayi dake tsaye bakin mota shi da malam suna d'an hira, ganin ta nufesu yasa ta rik'o hannun Iya tana fad'in "Kinga Iya ki daina bana so, a kan me zaki tambayeshi wai cikina, na fad'a miki ina da shi ne to?"

D'an gajeran hannunta ta kwad'a mata a kan ta tana fad'in "Sakeni ja'ira kawai, kin rainani dan kinga tsawona bai wuce k'ugunki ba ko?"

Ai kuwa fitowa Iya tayi ta tsaya daga bakin soron tana kallonsu da kunya tace "Yarinyar can wai nake tambaya watanta nawa ne yanzu? Ina so ta fara awo a nan gaskiya ba k'asar masu jajayen kunnuwan nan ba."

Kallonta sheikh yayi sai kuma ya kalli makullayen hannayenshi yana fad'in "E to, ina jin dai watanta na hud'u ne wannan."

Murmushi Iya tayi tace "Yawwa to ina ga tunda tafiyar ta ku jibi ne me zai hana gobe na rakata ta je awon fari, kenan idan kun dawo ta ci gaba da zuwa."

Da fara'a sheikh yace "Hakan ma yayi Iya, Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya."

"Ameen." Ta fad'a ta juya zata koma ciki Mimi kuma ta k'arasa fitowa, hararan juna sukayi ita da Iya tana murgud'a baki tace "Gaskiya ni a daina min haka, ina ce dai yanzu na bar miki tsohon mijinki tunda ni ma na samu nawa, to me ye na son cizgani a cikin mutane kuma?"

Kallon malam tayi dake ta k'yalk'yala dariya yace "Malam na tab'a fad'a maka wani abu ne tunda muke?"

Girgiza kai yayi yana ci gaba da dariyarshi, Iya kuma shigewa tayi tana fad'in "Idan jin ta kike dani ki bari gobe da safe na sameki gidan naki sai muyi."

Juyowa tayi tana kallonta tace "Iya kika je gidana da sassafe da angulu zan had'aki."

Dak'uwa ta mata tana dariya tace "Ta jima bata kasheni ba angulun, yar banza b'ulelliyar wofi."

Gwalo ta mata tace "Yo Iya kuma yaushe aka fara hassada da k'ibata? Yar mulmujewar dana fara yi har an fara saka mata ido."

Zagayawa tayi ta mota zata shiga ganin yanda malam da sheikh kamar zararri suke ta k'yak'yata dariya, Iya ma dariyar tayi a yanzu tace "Wannan k'ibar ce 'yar mulmujewa? Ai ina ga da kin haihu sai an ganki a d'auka ma ke ce uwar gida, dan jikinki bud'ewa kawai yake."

Saida ta bud'e murfin motar zata shiga tace "Na ji dai, ki ci kanki Iya."

Shiga tayi ta zauna tana ci gaba da kallonshi yana ta dariya, haka ya tayar da motar suka d'auki hanyar komawa, ba tare daya tsagaita da dariyar ba yace "Wasar Kaka da jika akwai dad'i, ina ma na wa kakan ko kakata suna raye, dana kwatanta irin haka da su nima."

Murmushi tayi tace "Hakan ya birgeka ne?"

Jinjina kai yayi yace "Sosai, kun birgeni matuk'a, kamar na zauna nayi ta kallonku."

Cikin zuba mishi ido tace "Idan zaka dinga biyanmu ai sai ka dinga kawoni kullum muna dramar a gabanka kana dariya."

Wata dariyar ya sake bushewa da ita yace "Ke mai wayo ko?"

Turo baki tayi tace "To miye a ciki, ai kowa yan...tsaya tsaya tsaya sheikh, dan Allah." Ta k'arashe tana kallonshi, da sauri ya taka birki bai shirya ba dan yanda tana tsaka da magana ta shiga fad'in ya tsaya ta sa gabanshi fad'uwa, kallonta yayi yana sake dudduba jikinta yace "Lafiya? Me ya faru Ryam?"

Nuna mishi mai baron da suka baro baya kad'an tayi tace "Bredi nake so, gashi nan baya."

Wata k'akk'arfar ajiyar zuciya ya sauke ya had'a kanshi da sitiyari yace "Hasbunallahu wani'imal wakil."

D'an dafa kafad'arshi tayi a sanyaye tace "Akaramako, kan ka ne ke maka ciwo?"

D'agowa yayi ya zuba idonshi cikin na ta da mamakin jin wai akaramako, girgizz kai kawai yayi ya juya ya kalli mai bredin dake tafiyarshi ya soma musu nisa, bud'e murfin motar yayi ya fita zai rufo sai kuma ya kalleta ya nunota da yatsa cikin muryar gargad'i yace "Ki jirani na dawo, idan kika fito a motar nan ranki zai b'ace."

Jinjina kai tayi alamar to, da kallo ta bi shi har ya siyo bredin aka saka mishi a leda ya dawo motar, mik'a mata yayi tana karb'a ta fara sincewa, tayar da motar yayi yace "Da fatan dai ba ciye-ciye zaki min a mota ba?"

Kallonshi tayi tana kwance ledar tace "Yawuna har tsinkewa suke, idan ka hanani wallahi hukumar kula da hakk'in yara zan kai k'ararka."

Murmusawa yayi yace "Ki ce na tauye hakk'in abinda yake cikinki?"

Nuna kanta tayi tana fizgar bredin mai laushin gaske ta kai bakinta tana taunawa tace "Ni dai, ni nake nufi."

Zaro ido yayi yace "Oh! Wai ke ce yarinyar dama?"

D'aga kai tayi alamar e, shi ma jinjina kai yayi yace "Lallai, Ryam zanyi addu'ar Allah yasa mace zaki haifa."

Da sauri ta kalleshi tace "Me yasa? Ni ma ai ita nake so na haifa."

Kallonta yayi yace "Me yasa kike son haifar mace?"

Cike da rashin damuwa tace "Na dinga mata kitso na saka mata ribom na mata kwalliya na saka mata riga da siket na kanti ko kula riga da wando sannan na tafi biki da ita."

Galala kawai yayi yana kallonta yana jin ba dan tuk'i yake ba da sai yayi tagumi ya k'are mata kallo, sai kawai ya girgizz kai a zuciyarshi yace "Allah ya miki albarka Sawwama, duk da shekarun k'uruciya aka had'amu, amma ban ga irin haka daga gareki ba."

Sake kallon Mimi yayi yace "Ni kuma saboda ta zama silar zamarki uwa ta gari nake son ki fara da mace."

Kallonshi tayi irin kallon na na fahimta na basira, sai ta d'auke kan ta a hankali tace "Zan zama, zan zama insha'Allah, da kuma taimakonka."

Murmushi yayi yace "Da taimako na, amma kuma da taimakon Qawwama, dan ta fini kula da yara yanda Allah da manzon sa suka fad'a."

Da fara'a ta kalleshi ita ma tace "Na ji dad'in kasancewata a cikinku."

Murmushi kawai ya sake mata da haka har suka isa gidansu Asas kamar yanda dama suka shirya zasu je suyi ban kwana da su, Asma'u ta ji dad'in ganin Mimi haka ta sako hijab bayan Asas ya shigo da sheikh ta cika gabansu da kayan ci, saidai babu abinda suka tab'a sai ruwa musamman ma Mimi data ci bredi ta k'oshi a mota, basu jima ba suka mik'e dan 10:00 na dare har ta wuce sosai, sallama suka musu tare da addu'ar Allah ya kiyaye hanya. Daga nan kuma gida suka wuce, dake dama kwana Hafsat ne kai tsaye d'akinta ya wuce yayi shirin bacci.

Tana kwance kan k'irjinshi hannayensu a had'e suna wasa da su, d'aya hannunta kuma k'irjinshi take shafawa tana fad'in "Sheikh nawa, ka ga dai zanyi kewarka na wata d'aya ko? Dan Allah kamar yanda ka min alk'awari ka dawo nan da wata d'aya, ina buk'atarka a kusa dani."

Sumbatar yalwataccen gashinta yayi dake ta tashin k'amshi yace "Na miki alk'awarin nan Mangata, insha'Allah zan dawo a kan lokaci."

Hannunshi dake sakale cikin na ta ta sumbata tace "Nagode mijina, duniyata, aljannata."

Da fara'a yana d'an lumshe ido yace "Madalla da mata ta gari."

Ita ma a sanyaye tace "Madalla da miji na gari."

A tare suka fad'i "A bisa koyarwar addinin islama."

Tallabo hab'arta yayi suka kalli juna yace "Ina sonki sosai Hafsat, ina sonki uwar ya'yana, Allah ya sani ke ce ni kamar yanda ni ma ni ne ke, ke ce farin cikin gidana kuma salama a cikin rayuwata, wani lokacin har tuna irin gararin da zan shiga nake yi idan aka ce yau babu ke a tare da ni, sai na tambayi kai na an ya kuwa zan iya ci gaba da rayuwa? Sai na tambayi kai na anya zan sake murmushi a fuskarta? Anya kuwa idan na rasaki daga ni har 'ya'yana ba zamu tagayyara ba?"

Da sauri ta d'ora yatsanta a labb'anshi tace "Shiiiii! Haka ba zata faru ba mijina, Allah yana tare da ku, insha'Allah muna tare ka ji." Ta fad'a tana k'amk'ameshi k'am a jikinta, numfashi a dinga saukewa a kan ta mai fito da zafi ya sake fad'in "Ina k'aunarki sosai."

A sanyaye ta furta "Ni ma haka." A hankali ya rad'a lata a kunne "Muje na miki wanka, kar ki yi bacci da najasa a jikinki."

Dariya tayi tace "To a d'aukeni mana."

Yunk'urawa yayi ya sauka a gadon ya d'auki towel ya d'aura ya kimkimeta tsaf suka nufi ban d'akin.




*Washe gari*


Sosai Iya ta ji dad'in yanda tunda safe ya tura mota sukutum aka je d'aukarta, saidai ga ta zaune falo tana jiran ja'irar ta bakinta ta fito bata gama shiryawa ba.

Sheikh ma dake kwance kan gadon tun shigowar Iya ya shigo tashinta, kallonta yake tana shiryawa a tsanake, da yaga dai shirin ba mai k'arewa bane yasa shi fad'in "Ryam Iya fa jiranki take, a k'alla ta d'auki minti ashirin zaune a falon nan ita kad'ai."

Yatsina baki tayi tace "Ai na fad'a mata tun jiya kar ta min sammako a gida, kuma ma awon sai ta wani rakani, salon muje tayi ta tona min asiri."

Dariya yayi yace "Ke da zaki jira layi a b'angaren masu ciki, ai kallon kallo zaku yi wa juna ke da su, da dukanku abu d'aya ya takaru, ta inda kika bi kika sameshi haka suma."

Juyowa tayi ta dakata daga shirin shafa jan bakin da take tace "Da gaske? Tabb'! Lallai zan sha kallo, wallahi sai na k'arewa kowace kallo, kuma idan kika min kallon da ban so b芒 na ce ni da ke duk kanwar ja ce."

Ban da k'yalknyala dariya babu abinda yake kafin yace "Amma dai kiyi a hankali kar ki ja fad'an da zaki daku fa a asibitin nan."

Murmushi ta masa tace "Karka damu ba zan yi ba."

Da son gasgatawa yace "Kin tabbata?"

"Na tabbata." Ta fad'a tana juyawa zata shafa jan bakin, mik'ewa yayi da sauri ya rik'e hannunta ya karb'e jan bakin yan fad'in "Kina da sani akan mutanen da Allah ya yarje ma ganin kwalliyarki kawai, amma me yasa kike son take saninki ne Innar Issa?"

Shagwab'e fuska tayi tace "Kayi hak'uri to, ka yafe min?"

D'aga kai yayi alamar ya yafe, mak'ale mishi tayi a wuya tana sumbatarshi, warware hannayenta yayi yana fad'in "Maza dan Allah, hanzarta Iya na jiranki."

Turo baki tayi tace "Ni fa na ga Iyar nan sai wani ji da ita kake, zan fara zargin ko son ta kake fa?"

Da mamaki ya kalleta yace "Yanzu ne ma zaki fara zargin? Ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login