Showing 138001 words to 141000 words out of 185502 words

Chapter 47 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

500

d'auke kanshi yayi yana fad'in "Ina kwana aunty."

"Lafiya lau." Ta fad'a sanda take mik'a mishi ta d'ora da "Antashi lafiya?"

"Lafiya lau." Ya fad'a yana karb'a da fad'in "Nagode."

Dukansu godiya suka mata kafin ta mik'awa Aswan tace "Ka mik'awa Aisha wannan."

Hafsat dake murmushi tana kallonsu ne tace "Ai da kin barta ja'ira ta je da yunwar."

Murmushi tayi tace "A'a aunty ayi hak'uri."

Ganin sun fita suna fad'in "Sai mun dawo Amie, sai mun dawo Aunty." Yasa su dukansu suka bisu da "A dawo lafiya, Allah ya tsare."

Suna ficewa Hafsat ta kalli Mimi tace "To me kika girkawa mai gidan? Iya fa yaran kawai muka d'orawa su da zasu tafi."

Murmushi tayi cike da kunya tace "Aunty ai duk abinda kika fad'a shi za ayi."

Girgiza kai tayi tace "A'a fa uwata, karki manta girkinki ne yau da gobe da jibi ke har nan da kwana biyar, dan haka wannan alhakin yana wuyanki, muje dai na taimaka miki da wani abun."

Cike da kunya ta sinne kai ta bi bayan Hafsat d'in, suna shiga ta tsare da tambayar me zata dafa mishi, dan haka kawai tace bari tayi sauce na k'wai da doya.

*Duk* abinda ya faru daga sanda Hafsat ke fad'awa Heezam abonda ya faru har k'arshe duk a idon sheikh daya shigo falon ta k'ofar dake fitowa daga falonshi, jin abinda ya faru yasa shi jin ba dad'i sosai, sai kawai ya share ya koma falonshi ya zauna.

Saida ta kamalla aikin nan tsaf Hafsat ta kalleta tace "Ki je b'angarensa ki ga ko ya dawo daga masallaci, ya kan jima dama bai shigo ba wani lokacin."

Jinjina kai tayi da ladabi ta nufi hanyar, a tsoro tsoro ta k'arasa ta k'wank'wasa tare da bud'ewa a hankali ta tura tana kuma fad'in "Salam."

Dake babu hasken fitila sai ta shiga waige waige, yana zaune kan kujera mai zaman mutum d'aya yana kallonta, saida ta sak茅 furta "Salam."

Mik'ewa yayi a hankali yalallab'a yayi ramda k'ugunta, hakan ya haddasa mata sakin k'ara a tsorace, da sauri ya rufe mata baki da hannunshi yana fad'in "Shiiii! Ni ne."

Ajiyar zuciya ta saukea hankali ta kalleshi, had'a goshinsu yayi wuri d'aya ba tare daya d'auke hannunshi a bakinta ba yace "Banda abun *Marya* a duk duniyar nan waye yake da lasisin tab'a jikinki bayan ni?"

Lumshe ido tayi a hankali ta bud'e ta kalleshi, hannunta tasa ta d'auke hannunshi a bakinta tace "Ni ma kuma waye yake da hurumin tsoratani a garin nan idan b芒 tsohona ba."

Dariya yayi ya shiga neman bakinta saida ya kamoshi ya had'a da nashi ya shiga tsutsa, shiru tayi tana saurarenshi ita dai saida tana yana neman zage mata zip d'in riga tayi saurin ja baya tana fad'in "Abdallah abinci na zo yi maka tayi fa."

Rik'o hannunta yayi yana sumbatar kuncinta yace "To ai sai na yi wanka ko?"

Jinjina kai tayi tace "To kayi wanka saika fito."

K'ugunta ya sake rik'ewa yace "To muje a tayani wankan ko?"

Zaro ido tayi baki bud'e tace "Lahhh! Ni d'in? Gaskiya kunya nake ji."

Murmushi yayi y'a lak'aci hancinta yana fad'in "Kunyar me? Shin ni ba naki bane? Ko kin manta mun zama d'aya ne."

Mak'ale kafad'a tayi tace "Gaskiya ni dai kunya nake ji."

Cak ya d'auketa ya nufi uwar d'akin da ita yana fad'in "Ba wani nan, idan baki taimaka min ba to zan fasa wankan ma."

Wutsil wutsil ta shiga yi da k'afafu tana fad'in "Abdul ka saukeni k'asa dan Allah kar na fad'o fa."

Murmushi ya saki yana fad'in "Ryam zan iya zagaye garin nan dake a haka babu abinda zai sameki."

Kallon fuskarshi tayi ta sagala hannayenta a wuyanshi tace "Da gaske?"

Girgiza kai yayi yana murmushi, dan sosai take bashi mamaki idan yayi magana tace wai da gaske? Sai yaji wani daban a zuciyarshi yana jin wani nishad'i, tunda har shi ma zai iya yin magana ayi tamtama gaskiya ya fad'a ko akasin haka. Jinjina mata kai yayi alamar eh, ita ma jinjina kai tayi tace "Shikenan, ni kuma yau sai ka goyani ma nayi bacci a bayanka."

Suna shiga d'akin ya sauketa yana fad'in "Ko zamu jaraba ne ki gani."

Tattare siket d'inta tayi ta taka gadon sannan tace "To juyo bayanka."

Da dariya ya tsaya kusanta ita kuma ta haye bayanshi, takawa ya fara yi da ita a tsakar d'akin yana fad'in "Kinga a haka sai na zaagaye k'asa d'ari ba d'aya dake."

Dariya tayi ta d'ora hab'arta a kafad'arshi tace "Kenan gari na d'ari d'in ba zaka iya ba?"

Dariya yayi ya duk'a da ita kamar zata fad'a ta gaba yana fad'in "Ke ko? To me zai gagareni indai a kan ki ne?"

D'an bubbuga bayanshi tayi tace "Wai baka jin ciwo a bayanka?"

D'an d'ago kanshi yayi ya kalleta yace "Me yasa kika tambaya?"

Sunkuyar da kai tayi tace "To ai naga irinku..." Dariya tayi ta kwanta a bayanshi sosai kamar zatayi bacci tace "Shikenan dai."

Girgiza kai yayi yana dariya yace "Tsofaffi iri na kike nufi ko? Ryam ban tsufa ba yanda kike tunani, amma sannu kad'an zan tabbatar miki da haka."

Duk'o kanta tayi ta kafad'arshi tace "Ta ya ya akaramakallah?"

Kamar daga sama ta ji ya juyo da ita gabanshi da k'arfi kuma ya rik'eta gam tare da yin k'asa da ita kamar zata fad'i k'asa, rintse ido tayi ta k'amk'ameshi sosaai, cikin kunne ya rad'a "Kin amince na nuna miki?"

Girgiza kai tayi ta bud'e ido tace "Na yafe, na tuba Abdul."

D'agata yayi ya direta k'asa ya jata zuwa ban d'akin yace "To muje a min wanka Innar Issa."

Binshi tayi suka shiga ban d'akin, yanda ya tilasta mata yasa ta b'alle mishi botiran jallabiyarsa shi kuma ya cire, rintse ido tayi sosai tace "Abdallah fita zanyi waje kafin na suma a nan."

Rik'eta yayi yace "Babu inda zaki je, ki suma a nan na gani."

Da k'yar ta samu ta kubto ta baro ban d'akin, a haka ma cewa yayi ta fito mishi da kayanshi da zai saka, wurin kayan ta bud'a saai ta rikice ta rasa wanda zata d'aukar masa, da k'yar ta ciro wata shadda bleu ta d'auko hula da hiramin da takalma duk sa suka dace da kayan ta aje, feshesu tayi da turare ta zauna bakin gadon jiranshi.



*Watak'ila mun shiga hutun sallah insha'Allah*



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*46*




Fitowarshi tasa ta yin zunbur ta mik'e tsaye tana kawar da kanta daga kallonshi dan d'aure yake da towel, kallonta yayi ya kalli kayan data fito mishi da su yana goge ruwan jikinshi yace "Inna Issa ya akayi kika san kayan da zan saka?"

Kallon kayan tayi tana murmushi amma ba tace komai ba, matsowa yayi kusanta yace "Na gane, wato ke ma kina so na ko? Hakan na nufin zuciya da tunaninmu d'aya ne."

Da sauri ta girgiza kai tace "A'a ba haka bane."

Wani kallo ya bita da shi yace "To ya ya ne?"

Sunkuyar da kai tayi a sanyaye tace "Ba komai."

Daf da ita ya tsaya kamar zai had'eta yace "Baki so na Ryam?"

Cikin turo baki da rashin bawa abun mahimmanci tace "To ai ni ban ma san ya so d'in yake ba."

Kallon tuhuma ya mata yace "Amma kuma a baya kika fad'a min kina son Asas?"

Da saurita kalleshi saikuma ta sunkuyar da kai, jawo k'ugunta yayi ya had'a da nashi yace "Hakan na nufin k'arya kika min?

Da sauri ta girgiza kai cikin sanyin murya tace " Ba k'arya bace sheikh, kayi hak'uri kaji, muje ka ci abinci."

K'arasawa yayi gaban kujera ya zauna ya d'auki mai ya fara murzawa a nutse, tana kallonshi har ya gama ya d'auki kayan ya saka, duk da turaren data fesa musu tana kallo ya d'auki wata k'aramar kwalba ya kuma shafawa a bayan kunnenshi sannan ya d'an murza a tafukan hannayenshi ya murza sosai sannan ya d'auki hula ya mik'a mata yace "Oya Hajia d'ora min."

Karb'a tayi tana dariya tace "Ai naga yanda Abba yake d'orawa na yi."

Murmushi yayi tare da sunkuyowa sosai tsayinsu ya daidaita sannan ta d'ora mishi hular, kallonshi tayi ta saki murmushi tace "Umm! Kayi kyau."

D'aga mata gira yayi yace "Da gaske?"

Jinjina kai tayi alamar eh, nuna mata k'ofa yayi yace "Muje to."

Wucewa tayi gaba ya bi bayanta yana fad'in "Ryam wannan kwalliyar wa ya miki?"

Dariya tayi ta juyo ta kalleshi tace "Ni na yi."

Rik'e hannunta yayi yace "In kuwa hakane zan bayar da kud'in siyan wasu kayan kwalliyar dan a ci gaba da canccara min ita ina kallo."

Dariya tayi cike da jin kunya har suka fita falon, Hafsat na zaune tare da mai aikin, gaisheshi sukayi a ladabce ya amsa a mutumce shi ma, k'arasa yayi wajen cin abincin ya zauna, Hafsat da Mimi ma k'arasawa sukayi sai mai aikin data koma madafa ta zauna, Mimi ce ta zuba musu abincin ta aje ma kowa sannan ta zauna ita ma da na ta a gabanta.

Cikin raha da farin ciki suka gama cin abincin, Mimi na kallonsu suna buga mata soyayyar manya, duk da Hafsat d'in na nuna kunya amma sheikh k'arara yake fad'a mata maganar soyayya ko ya rik'e hannunta, kallonsu ita dai take tana mamakin sheikh d'in. Ya rigasu gamawa ya mik'e, saida ya tsaya gaban kowace ya sumbaci goshinsu ya d'ora da fad'in "Allah ya muku albarka, Allah k'ara mana fahimtar junanmu da zama lafiya."

Gyara rigarshi yayi yace "Zan fita." Kallon Hafsat yayi yace "Nasan kinsan yau juma'a bana dawowa gida da rana."

Jinjina kai tayi tana murmushi tace "Hakane, Allah ya tsare."

Lumshe ido yayi yace "Ameen."

Mimi ma a d'arare tace "A dawo lafiya."

"Allah yasa." Ya fad'a yana kallonta, mik'ewa Hafsat ma tayi ta juya ta nufi d'akinta tana fad'in "Bari na barku kuyi sallama."

A kunyace Mimi ta mik'e tana fad'in "A'a...amma..."

Shiru tayi ganin har ta bud'e k'ofar d'akinta ta shige, kallonta yayi yana murmushi yace "Duk abinda kika ga *yar aljanna* tayi to da dalili, tafi kowa sanin bana yarda mace ta rakani bakin k'ofa fita saboda mazan dake gidan nan,iya falon nan ne kawai zamuyi sallama dake, kuma tasan waye mijinta shiyasa."

Jiki a sanyaye ta d'aga kai alamar gamsuwa, kamo hannunta yayi yana kallon fuskarta yace "Kinyi kyau Ryam, kamar na zauna tare dake ina kallonki."

K'asa tayi da kanta alamar kunya, tallabo hab'arta yayi yace "Fad'a min ciwonki ya warke ne?"

Cike da kunya ta sake sunkuyar da kai ta jinjina alamar eh, sumbatar goshinta ya k'ara yi yace "Jiya ai ina shiga na sameki kinyi bacci, sam ban ji dad'i ba da baccin nan ya hanani jin dad'ina."

D'ora hannunta tayi a k'irjinshi ta d'ora goshinta ta rufe fuskarta tsabar kunya tana murmushi, shi ma murmushin ya shiga yi yana rad'a mata a kunne "Da gaske nake fad'a miki, kin kuwa san irin duniyar da kika kaini daren can Ryam?"

Tallabo kanta yayi ya kalli fuskarta yace "Wani irin dad'i ne daya fi zuma gigita tunani, d'and'ano ne marar misaltuwa Innar Issa, yau d'in nan zan..."

Duka ta kai mishi a k'irji tana sake nutsa kanta cikin rigarshi tana fad'in "Dan Allah ka daina fad'a, baka jin kunya ne wai?"

Shi ma dariya yayi yana sake rumgumeta a jikinshi, cikin muryar nishad'i yace "Kyautar da zan iya baki ita ce ki ci gaba da rik'e katina na banki kina aiki dashi duk sanda kike so, kyauta ta biyu kuma da zan iya yi miki ita ce..."

Nuna kanshi yayi yace "Ni ma yanzu na zama na ki, na zama mallakinki Ryam, dan Allah ke ma ki bani kanki da zuciyarki, kinji?"

Sinne kai ta sake yi tace "Ni dai kayi sauri ka tafi dan Allah, wallahi kunya kake bani."

Dariya yayi yana sakinta ya gyara kayanshi da kyau yace "Shikenan tunda korata kike, zan tafi kuma sai dare zan dawo, dan yau ina da abubuwa da dama a gabana."

Da mamaki ta kalleshi tace "To a ina zaka ci abinci?"

D'aga kafad'a yayi yace "Duk inda na yada zago."

Girgiza kai tayi tace "A'a gaskiya ban yarda ba, a duk inda ka yada zago ka sanar dani zan tura a kai maka."

Wani k'ayataccen murmushi ya saki yace "Da kamar wuya Ryam, Hafsat ma ta jaraba yin hakan amma ban amince saboda abun dayawa."

Bubbuga k'afafu ta fara yi tana kukan shagwab'a da fad'in "Ni dai wallahi idan baka amince ba nima ba zan ci abinci yau ba sai ka dawo gidan nan."

Tallaba kumatunta yayi da hannu biyu yace "To wai ni da aka ce ba'a so na me, me ye kuma na damuwa dani haka?"

Kallonshi tayi da fuskar yarinta tace "Lahhh! Ni fa ban fad'a ba."

Lak'ace hancinta yayi yace "Zaki fad'a nan kusa *mai tsada*, ki shirya ma hakan."

Kallonshi tayi sanda ya nufi hanyar fita yana fad'in "Saina dawo."

Bye bye ta masa tace "A dawo lafiya."

"Allah yasa." Ya fad'a yana fita, saida ta matsa daf da k'ofar tana kallon yanda jami'an da mai gadi da mai bawa shukoki ruwa suke ta gaisheshi yana amsawa da fara'a, zagayeshi sukayi yana magana yana ta nunawa da hannu, saidai yanda yake maganar a nutse da kuma sakin fuska su kuma suna jinjina kai suna fara'a zai tabbatar maka da nasiha ko kuma dai gajeran wa'azi yake musu, bud'e mishi motar akayi ya shiga suka rufe kafin jerin gwanon motocin ukun suka fita a gidan.

Wata nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana juyawa tace "Allah ya tsare mana kai."

Rarraba ido ta shiga yi kamar wacce ta tuna wani abu, sai kuma ta d'aga kafad'a tace "Ai hakan ba yana nufin so bane."

D'akinta ta nufa ita ma tana fad'in "Nayi yaya ma na so shi ni kam?"


*10:20* ta fito kai tsaye madafa ta nufa inda ta samu mai aikin nan, da taimakonta suka shiga had'a girkin rana, sunyi nisa sosai Hafsat ta samesu madafar, da mamaki ta k'arasa shiga tana fad'in "Kai! Mimi wai ba dai aiki ne kuke ba?"

Dariya tayi cike da ladabi tace "E aunty, har mun kusa kammalawa ma."

Murmushi tayi tace "Kai amma sannunki da k'ok'ari."

Murmushi tayi ta amsa da "Yawwa aunty."

Ci gaba sukayi da aikinsu, hakan yasa 12:00 na bugawa suka kammala komai suka jere a table, d'akinta ta shiga dan yin wanka ta shirya, tana shiga wayarta na kururuwa da sauri ta d'auka ta d'ora a kunne ganin sheikh ne.

Daga b'angarenshi ya fara fad'in _"Amincin Allah ya tabbata a gareki Innar Issa."_

Murmushi ta saki tana jin wani farin ciki na daban ta amsa da _"Allah yasa muyi tarayya a cikin amincin daka rok'a min *old man*."_

Dariya yayi yace _"Ni ko Ryam? Ni ne old man?"_

Turo baki tayi tana zafe zip d'in rigarta tace _"To yi hak'uri."_

Numfashi ya sauke yace _"Na yi to tunda ai mun zama d'aya ni dake dama."_

Murmushi tayi tace _"Ya aiki?"_

Saida ya sauke numfashin da har ta ji sautinshi sannan yace _"Ba dad'i Ryam, so nake na zo gida cikin iyalina na zauna amma ba hali. "_

D'an murmushi tayi kawai mai sauti dan gaskiya har zuciyarta ita kanta zata so ya zauna kusa da ita, dan zaman gidan idan da shi a kusa zata fi jin dad'i, a sanyaye ya d'ora da _" Ryam kina lafiya?"_

Jinjina kai tayi kamar yana gabanta sannan tace _"Lafiya k'alau."_

D'orawa yayi da _"Babu abinda ke miki ciwo yanzu?"_

A sanyaye ta furta _"Babu Abdul, dan Allah ka daina tambaya ka ji, kunya nake ji."_

Murmushi ya mata mai sauti yace _"Dole na tambayeki Ryam, ina tsananin buk'atarki ne kuma bana so na sake ji miki ciwo."_

Cikin jin kunya ta sunkuyar da kai tana murmushi tace _"Ni dai bana so ka k'ara."_

Dariya yayi yace _"Ke ma kinsan ai baki isa ba, tunda kika barni na fara lasa zumar nan dole na ci gaba da lasawa ko na mutu."_

Hira suka sha sosai har saida shi da kan shi yace _"Ryam hutuna ya k'are, zan kashe waya, watak'ila sai dare idan na dawo gida."_

Marairaicewa tayi tace _"Kenan baka so na aika maka abinci?"_

Ajiyar zuciya ya sauke yace _"Na yau na yafe miki, amma daga gobe zaki fara insha'Allah."_

Jinjina kai tayi tace _"Shikenan Allah kaimu."_

_"Ameen."_ Ya fad'a yana d'orawa da _"Ki kula da kanki kinji, ina sonki sosai."_

A sanyaye tace _"Insha'Allah."_ Da haka sukayi sallama ta shiga ban d'aki tayi wanka tare da d'auro alwala ta fito ta canza kaya tayi sallah.

Saida ta gama komai a tsanake ta sake fita ta samu Hafsat, tare da duka yaran suka ci abinci saidai babu wani armashi dan ba hira suke ba. Suna gamawa kamar a kan k'aya take ta koma d'akinta ta kwanta abin ta.

Tasha baccinta saida kiran sallah la'asar ya tasheta, a gaggauce tayi alwala tayi sallah ta fito dan d'ora girki.

Falo ta samu Hafsat zaune da littafi a hannu tana karatu, zaune tayi kan kujera tace "Aunty barka da hutawa."

Da fara'a ta amsa da "Barka Mimi, an fito?"

Da fara'a ita ma tace "E aunty, zan shiga madafa ne dama d'ora girki, me za'a dafa ne?"

Kallonta tayi cike da k'auna da jin dad'in tambayar da ta mata tace "Mimi ni kike tambaya? Kije ki d'ora abinda ranki yake so ko kuma mijinki."

Yar dariya tayi tace "A'a aunty ku dai ku fad'a min."

Jim tayi tana murmushi alamar tunani, can ta numfasa tace "To kinga ki d'ora nama, dan sheikh yana son romo sosai, sai kisan dubarar da zaki masa."

Mik'ewa tayi tana murmushi tace "Shikenan aunty."

Tana shiga madafar ta samu mai aiki tayi shara tana guga, a nutse ta d'auki nama a fridge ta fara aikinta, mai aikin na gama guga ta kama mata da yankan albasa da tumatir da b'are tafarnuwa da saurensu, suna aikin suna yar hira sama sama har Mimi taji hayaniyar yaran sun dawo daga makaranta, saida ta daidaita komai ta fito a madafar bayan ta kalli mai aikin tace "Ki duba min dan Allah zan je na d'anyi shara a d'akina kafin magriba."

Jinjina kai tayi tace "To aunty."

Fitowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login