Showing 54001 words to 57000 words out of 185502 words
addu'a, amma dayawa kuwa sun iya taka rawarsu daidai da kid'an ta yanda komai dubararka ba zaka iya gane takonsu ba. "
Abba ya kawar da kansa daga duban da Mimi ke masa yace "Ni kam ki duba min ita Hajia, kin ga bana son na mutu da hakk'in kowa gasu nan da yaron da magabatansa idan aka yi komai a gabansu shikenan!"
Mik'ewa Hajiar tayi tana mai yiwa Mimi maganar cewa ta tashi su shiga ciki.
Asma'u kam kuka take sosai gaba d'aya ta bi ta tsurewa wannan lamari, ta sani ba tare suke kwana da Mimi ba, amma tana iya k'ok'arin bugar k'irji da hallayen k'awar tata, a bar Mimi da caje aljihun gara amma sam wancen harka ba halinta bane.
Jiki a sanyaye ta mik'e tana kallon Abba, cikin tsawa yace "Zaki wuce ko saina ragargaza miki fuska, yar banza mai kama da aljanu."
Idonsa da sukayi ja ya d'ago a hankali haka kawai ya sauke a kanta a lokacin da ta bada baya tana tafiya dukkan wani lamari nata na motsawa daidai da takun tafiyarta.
Da sauri ya kuma sadda kansa yana mai jan "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'ne." Cike da fad'uwar gaba ya shiga korar shed'an a hankali ya sauke dubansa a kan Asas daya sauko k'asa ya had'e hannayensa yana hawaye harda shashek'a yace "Ya sheikh dan Allah koma mecece koma me tayi ni ina son aba ta, ni ba wai wannan nake so ba ni ita nake so, wannan zamani kuwa ba ita ce ta farko ba kuma ba zata zama ta k'arshe ba a fannin cin kud'in maza, wasu da haka suka gina gidaje da motoci da komai, ni kam ina sonta a haka dan Allah."
Muryar Abba ne cike da tausayawa yana kallonsa yace "Yaro, halayan fa? Idan yau aka shaida mana ta banzatar da kanta ya ya tarbiyar 'ya'yanka? Ban tab'a sanin uwata ta kai cen ba har ta iya b'oye min waya, ina bada misalai da tarbiyarta? Ina saka baki idan ana maganar 'ya'yan wasu da suke irin haka, ashe tawa na kwance tamkar macijin kumba."
Cikin ladabi Asas ya kalleshi yace "Abba na tabbata ko da an sameta da laifi wallahi yanayin rayuwa ne, ni fa gaskiya zuciyata bata gamsu da abinda kuke tunanin ta aikata ba, ta yaya yarinyar da bata jin kunyar fad'an ko ita wacece a gaban kowa zata aikata haka? Mimi fa yarinya ce mai aji ba ballagaza ba."
A hankali ya kuma sadda kanshi k'asa maganganun nan suna hawa masa kai sosai, shi sai yanzu ne ma yake sake tantance yanda zuciyarshi ta wani d'aukaka yarinyar a matakin da baiyi tsammani ba.
Abba kam gyara tsayuwa yayi yana fad'in "Ban sani ba ko dan Allah yayi ta kyakyawa ne? Amma ta yaya na zama sakarai haka a gaban yarinyar Ddna haifa?"
Da sauri sheikh ya kalleshi da mamaki, sai yaji shi kanshi fa sunanshi kenan inda a gaban Mimi ne, domin kuwa ta mayar dashi wani sha-tara har ya kasa ganota.
*A ciki* kuwa suna shiga Hajia Gambo ta umarceta ta cire pant d'inta ta kwanta akan gadon, sarewar da tayi a lamarin yasa Mimi ba gardama tayi abinda ta ce, tana kallo ta saka shafa ta likitoci a hannunta ta matso kusanta, kaallon fuskar Mimi tayi tace "Mimi, garin yaya kika bari har irin wannan zargi ya shiga tsakaninki da mahaifinki?"
Hawaye ne suka sak茅 sulalo mata ta rintse ido tace "Tsautsayi, k'addara, da kuma rashin jin maganata."
Girgiza kai tayi tace "Kenan da gaske kin zama babbar mace tun a waje Mimi?"
Wani sakaran murmushi tayi tace "Ke da zaki tabbatar yanzu, me yasa zaki tambayeni kuma?"
Murmushi ta mata tare da d'an gyara k'afarta tace "Hakane."
Yanda take jin hannunta na neman shiga gabanta yasa ta k'amk'ame jikinta tana sake lik'e ido gam, tana jin hannun na daf da shiga tayi saurin rik'e hannunta ta sauke k'afafunta ta kwantar dasu, bud'a idonta tayi suka kalli juna, Hajia Gambo ce tace "Mimi ki fad'a min gaskiya mana, idan kinsan baki san namiji ba kar ma a fara shigar da wani abun da zai kawowa budurcinta rauni."
Kawar da kan ta tayi hakan yasa Hajia Gambo ci gaba da aikinta, yatsanta biyu kawai ta saka amma saida ta nemi shid'ewa, ganin kawai zata wahala a banza ya cakata cire hannayenta tana murmushi tace "Ki ci gaba da tsare mutumcin kanki Mimi, a wannan duniya budurci ya zama kamar shine macen ma, kindai gani me ya faru, iyayenki ma sun kasa yarda dake, bare kuma mijin da kika aura ko zaki aura."
Saida ta cire safar ta saka a kwadon shara tace "Tashi ki saka pant d'inki."
A hankali ta tashi ta d'auki pant d'in zata saka Gambo tace "Nasan dai za'a sha dangwarma Mimi a daren farkonki, dan wannan kafin ki bada kai bori ya hau sai an nemi ji miki ciwo."
K'ala ba tace mata ba saida ta saka ta gyara rigarta, Gambo na juyawa zasu fita ta rik'o hannunta, tsayawa tayi tare da kallonta da mamaki, durk'usawa tayi cikin magiya da neman alfarma tace "Hajia dan Allah na rok'eki ki rufa min asiri, karki fad'awa mahaifina komai a gaban mutanen can, ina jin kunyarsu bana so na ci gaba da tozarta a gabansu."
Tsam ta kalleta sai kuma ta jinjina kai tace "Shikenan ba komai, muje."
A sanyaye suka fito hakan yasa dukansu suka saki ido suna kallonsu, saidai banda sheikh da hannayensa ke jimk'e yana ta karanta hasbunallah wa'ni'imal wakil! Da sauri Abba ya taresu yace "Ya ake ciki Hajia Gambo?"
D'an bud'a baki tayi sannan ta kalli Mimi, a hankali ta d'auke dubanta daga kanshi tace "Abban Mimi kayi hak'uri dan Allah, zuwa safe zan zo gidan na maka bayanin komai insha'Allah."
Abun ka ga marar tsayi d'an duk'ul, ba wanda ya lura sai zamanshi suka gani a k'asa b'ingil yana tapa hannaye yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Oh Allah na Mimi kin kasheni, kin gama dani a duniyar nan."
Da sauri kuma ya wulk'ita ya mik'e tsaye ba zato ba tsammani kawai ya ja k'afar Mimi ta dama, yanda abun ya zo mata yasa ta fad'uwa irin fad'uwar nan ta yan bori tippp! Ta daki k'asa, "Ahhhhhhhhh!"
Wannan k'arar data saki ta saka sheikh da Asas zabura a tare suka mik'e tsaye sa茂 sheikh daya had'a da jimk'e hannunshi gam, da gudu Asas ya rik'e k'afar Abba dake shirin hawa jikin Mimi ya takata, cikin magiya ya kalleshi yace "Abba karka kasheta, wallahi zan aureta a haka na ji na gani Abba, karka ji mata ciwo dan Allah."
Cike da k'una Abba ya sake yin zaune ya fashe da kuka yana fad'in "Mimi ni kika tozarta haka? Ashe duk ladabin da kike mana da girmamamu duk na banza ne wawaye kika d'aukemu? Yau kinsa na ji ni tauyayye ni a cikin hallita, yanda nake d'an tsirit a cikin k'asa haka k'wak'walwata ma da tunani na, ke kad'ai mace amma na kasa kula da tarbiyyarki, uwata me na miki da kika min haka? Talaucinmu ne ya jawo?"
Da sauri Asma'u da jikinta ke rawa ta sunkuya ita ma tana kuka tace "Abba wallahi wallahi wallahi ni dai nasan Mimi bata bin maza, Abba karka yanke hukunci ka tsaya kayi bincik..."
Tsawa ya mata yana fad'in "Binciken uwaki zanyi, ke da ita ai duk kanwar ja ce, tunda kullum tare kuke manne da juna."
Nunawa Asas Asma'u yayi yace "Kaga yarinyar nan da zaku tafi gidanku cewa nayi su tafi tare, amma a k'arshe suka zagaye ita ta dawo ita kuma ta tafi ita kad'ai, to nasan niyyarta da tayi maka tallar kanta ne tunda taga kai aure ne a g..."
Cikin wani matsanancin kuka Mimi tace "Abba...abba ka daina ci min mutumci haka, wallahi ban aikata abinda kake zargina ba, ni ba 'yar iska bace Abba."
Cikin muryar data fara shak'ewa Abba yace "Wacece ba 'yar iskar ba? Ke fita..."
A tausashe cikin son danne abinda ke ranshi kamar an mak'ureshi yace "Dan Allah ko zaki iya barin maganar nan har kuje gida?"
Cike da girmamawa Abba yace "Me zai hana sheikh."
Wani rank'washi ya kai wa Mimi yace "Wuce muje."
Da k'yar ta yunk'ura ta mik'e ga zafin da take d'an jin a k'asanta sakamakon hannun da aka so turbud'a mata, yanzu ma d'an kwalinta a hannu yake dan duk a rikice take a gigice, suna fitar k'ofar gidan kusan shi ne a bayansu sai Mimi dake bayanshi.
Kamar daga sama sukaji muryarshi yace "Daure ki rufe kanki, hakan ba kyau."
Dukansu saida suka kalleshi har da ita data fara k'ok'arin gyara kallabin ta d'ora a kai, yanzu ma dai duk a motar sheikh suka koma gida sai Asas shi kad'ai a motarshi, amma zuciyarshi zallo take sosai yana jin sirikin na sa na neman b'ata mishi rai.
*Idan na ga ruwan comment gobe zaku ga uku ma (peut 锚tre)*馃槑
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:54 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*19*
Duk zaune suke akan tabarma guda sai Asas da sheikh dake kan kujerun roba farare duk da ba sababbi bane, mama kanta na sadde a k'asa dan bata so zama a nan ba saboda kunya da takaici, Mimi daf da k'ofar shiga d'aki take zaune ta had'a kai da gwiwa tana ta shashek'ar kuka, Asma'u na gefenta ta rik'e hannunta gam tana ta murzawa alamar rarrashi, cikin nutsuwa da dattako sheikh ya kalli Abba a nutse yace "Yaran da muka haifa wata rana sukan koya mana darasin rayuwa da bamu tab'a karanta ba, hakazalika wani lokacin sukan sa muji kamar su suka haifemu ba m没 muka haifesu ba, idan har Allah ya bawa mutum haihuwa dole wata rana sai ya zama tamkar jami'in binciki na k'asa da k'asa, wata rana kuma saiya koma kamar lauyan dake gaban wanda ake tuhuma, wani zagayen kuma rigar malunta zaka ara ka yafa dan yi musu nasiha a tsanake sannan su fahimci karatu, akwai lokacin da dole uba sai ya zama mai zafi da kausasawa ga yaranshi, kafin wata rana ka zama mai taushi kamar audiga sannan mai sakin jiki dasu dan suma su shiga jikinka. Amma fa duk wannan matakan tsaron zasu biyo bayan addu'ar nema musu shiriya ne, duk yanda zaka kai ga saka ido ko tattare al'amarin yaranka idan Allah bai nufesu da shiriya ba to fa zasu baud'e maka ne, dan haka malam kayi hak'uri ka b芒 wa zuciyarka hak'uri, idan har ta b'acin rai zaka bi tabbas zaka iya ganin bayan yarka, idan haka ta faru kuma wace akayi kenan?"
Numfasawa yayi yace "Kayi hak'uri, ga Asas nan yace har yanzu yana son ta da aure, ni nan zan tsaya masa har naga hakan ya tabbata, mu musu fatan alkairi da zaman lafiya mai d'orewa kawai."
Jinjina kai malam yayi ya sauke numfashi yace "Gaskiya ka fad'a sheikh, ni shaidane akan k'wak'waran darasin da uwata ta koyar dani, kuma kamar yanda ka rok'a mata alfarma na yafe mata duniya da lahira, Allah ya tabbatar da alkairi,Allah ya shirya mana zuri'a baki d'aya."
"Ameen ya Allah." Suka amsa malam da Asas, kallon Mimi yayi da niyyar ya mata nasiha mai ratsa zuciya ya ja mata ayoyi da haddisai, sannan ya umarceta ta nemi gafarar iyayenta da ta ubangiji, amma tuna abinda ya faru da abinda likitar nan ta fad'a, alamu ne kenan na eh ta zubar da mutumcinta, sai zuciyarshi ta sake maimaita mishi kalmar nan "Kamaninta bata da suffar cutar da kowa, yanayinta bai nuna hakan ba."
Da sauri ya d'auke kanshi kawai ya mik'e yana fad'in "Saida safenku."
Mik'ewa duk sukayi banda Asma'u da Mimi suka fita sai Mama data shiga d'aki, suna ganin haka Mimi ta d'ora kanta a kafad'ar Asma'u cikin shashek'ar kuka da raunin murya tace "Asma'u kin gani ko? Kinga rashin jin maganarki me ya ja min? Asma'u Abbana ne yake zargina fa."
Dafa kanta tayi tana shafa mata gashinta ita ma tana shashek'ar kukan tace "Kiyi hak'uri kinji Mimi, komai zai wuce insha'Allah."
Ajiyar zuciya duk suka shiga saukewa har Abba ya dawo cikin gidan, a k'ofar shigowarshi ya ci karo da jakarta data jefar a nan, da k'afa yayi cilli da ita hakan yasa yar jakar buguwa a bango ya bayar da k'ara mai d'an nauyi dake nuna bana jakar bane, da sauri ya taka tare d'aukar jakar ya bud'e, ciro wayar yayi yana kallonta yana jujjuyata, sake jifa yayi da wayar ya kalli su Mimi da duk suka sunkuyar da kawunansu, dogon tsaki yaja tare da sake fita y'a bar gidan.
A hankali Asma'u ta zame kan Mimi daga kafad'arta ta mik'e tace "Mimi zan tafi gida nima, saida safe kinji, kiyi hak'uri kuma kar kiyi kuka zai iya haddasa miki ciwon kai."
Jinjina kai tayi ta bita da kallo har ta fita, wata irin k'aunar k'awarta ta take ji a ranta, lallai ita yar halak ce kuma ta cancanci ta so ta, a hankali ta yunk'ura ta mik'e ta shiga d'akin, zaune ta samu mama zugum sai su Yaseen dake rik'e da littafin karatunsu amma da gani kasan suma suna cikin alhini, a hankali ta durk'usa gaban Mama ta d'an rik'o zaninta tana fad'in "Mama, dan Allah kar kiyi kuka a kai na ba kyau mama, kina so Allah yayi hushi dani ne? Mama kin gani wallahi ban tab'a issss..."
Kasheta tayi da mari tare da fizge k'afarta, hak'ik'a duk da basu da tsayi mutanen amma Allah ya basu wata baiwa, wannan baiwar kam ita ce ta k'arfi, k'ashi d'aya garesu da idan suka rik'eka zaka sha mamaki, hakan yasa Mimi k'arasa zaucewa taji wani zuuuuuu! A cikin kanta, da k'yar ta dafe kuncinta tana jin muryar Mama a cikin matsanancin kuka tana fad'in "Mimi a dalilinki fa aka mana wannan terere! Yanzu ke ko kunya baki ji ba domin Allah, yarinya kamar ki Mimi, ina miki kallon k'aramar yarinya ashe ke ma babbar macece ke tunda har kin iya d'aukar namiji, Mimi har ke ce wai za'a baki kud'i da abu dan ayi anfani dake?"
Wani kuka ta kuma fashewa dashi tana zama kan kujerar tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Allahuma ajirni fi musibati, waklufli khairan minha."
A hankali Mimi ta muskuta ma su Yaseen da zasu fita daga d'aki saboda ganin har yanzu rigimar bata k'are ba, mik'ewa Mama ma tayi tare da yin k'wafa ta bar mata d'akin, hakan yasa Mimi fashewa da kuka marar sauti kamar zata shak'e kanta ta mutu.
A ranar dai kam bata sake jin motsin Abba b芒 dan a masallacin unguwar ya kwana, Mama kuma ko shinfid'a bata fitar waje ba a kan gadonta ta haye saidai ita ma ba bacci tayi ba kamar Mimi dake k'asa kwance.
*Sheikh*
Cikin nutsuwa ya sake gyara zamanshi yana kallon Hajiar da alama kalamanshi sun fara ratsata ya ci gaba da fad'in "Hajiarmu, ai sun gama kyau da daraja tunda Allah ya hallicesu a 'yan adam, domin kuwa fad'ar Allah ne cewa *lallai an hallici mutum cikin mafi kyawun hallita*, ita kuma wannan hallitar Hajia ubangijin daya hallici ta wa hallitar shi yayi ta ki, haka kuma shi ne dai yayi tasu hallitar, hakan ba dan baya son su bane ko kuma sun mishi wani laifi, hakan ganin damarshi, haka ya so kuma babu wanda ya isa ya hana, dan ya fad'a mana a littafi mai tsarki a suratul buruj aya ta goma sha shiga cewa *yana yin abinda ya so ne*, Hajia karmu k'yamacesu dan hallutarsu, mu k'yamace dan munanan d'abi'unsu ko halayensu, kuma mun tabbatar babu su Hajia, hallitarsu hallita ce ta Allah wanda idan ya so yanzun nan zai iya mayar dani irinsu, ko kuma cikin dake jikin Hafsat ta haifo mai kama dasu, duk yin ubangiji ne wannan, Hajiarmu, *shin da wace ni'imace kuke k'aryatawa*? Ni dai ba'a da ja akan cewa Allah ba zai iya salwantar da hallitata ba, ban sani ba ko ke Hajiarmu?"
Da sauri ta girgiza kai tace "A'a sheikh ni a wa? Ni ma bana da ja, dama tun farko raina ya b'aci ne saboda babu wanda ya sanar dani kalar jinsinsu, sai kuma yarinyar da naga zubinta yafi k'arfin yanayin iyayenta a yanda aka fad'a min, bugu da k'ari Salamatu ta fad'a min ta gansu suna fad'a har ana kiranta da karuwa."
Girgiza kai yayi yana fad'in "Subhanallah, astagfurillah! Wannan shaci-fad'i ne na mutane, dama ai babu inda za'a fara maganar aure ba'a samu masu kushewa ba, Hajiarmu Asas yana son yarinyar nan tunda har kika ga ya sameni gida da sassafe haka ya ce na sameki, ki musu fatan alkairi a matsayinki na uwa hakan nada matuk'ar tasiri akan su fiye da yankan wuk'a."
Jinjina kai tayi cike da gamsuwa tace "Shikenan na amince, Allah ya tabbatar da alkairi."
Murmushi yayi yace "Ameen Hajia, nagode da wannan alfarmar da karamci, Allah k'ara girma da lafiya."
"Ameen." Ta fad'a cike da son suruki kuma d'an d'an uwan mijin nata, mik'ewa yayi yana mata sallama ya fita a falon inda ya samu Asas a bakin motarshi da alama shi yake jira.
Yana zuwa cike da zumud'i yace "Ya ake ciki sheikh? Dan Allah ka ce min ta amince?"
D'an zuba masa ido yayi da fari sai kuma ya jinjina kai ya lumshe ido yace "Ta amince, ka je ka ci gaba da shirye shirye."
Rumgumeshi yayi yana fad'in "Alhamdulillah, gaskiya na ji dad'i."
Murmushin yak'e kawai ya masa amma har zuciyarshi wani suka yake ji kamar ana soka mishi allura, ga wani irin mataccen yanayi daya taru ya baibayeshi saboda abinda ya zo mishi wanda bai tab'a tsammani ba, da kuma rashin baccin da bai samu ba a daren jiya ko na minti d'aya,