Showing 108001 words to 111000 words out of 185502 words

Chapter 37 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

506

kiran sunan Kabir, idan kika sake kuma wallahi kinji na rantse saina taune bakinki."

Cikin wahala taa jinjina kai alamar to, sakin leb'en nata yayi tare da shigewa gaba yace "Saki nikab d'inki ki biyo bayana."

Hannu d'aya ta d'ora a kai ta fashe da kukan da babu sauti tace "Wayyo Allah na ni Maryam, wannan ita ce jarabar da nake gudu ta auren tsoho, sam bai san miye soyayya ba bare ya nuna min, sai wasu dokoki da sharud'ai kawai yake gindaya min, yanzu ni gidan uban wa zan kai wannan hijab?"

K'wank'wasa k'ofar da yayi yasa ta zabura ta juya, tsaye yake yana jiranta da sauri ta fita a d'akin ya rufe kafin suka fita, da kanshi ya bud'e mata mota ta shiga ya rufe kafin ya shiga shi ma suka sake d'aukar hanyar asibiti.

Shirun daya ratsa motar yasa Mimi sauke numfashi a hankali, d'an kallonshi tayi da idonta dake waje cikin sanyin murya tace "Ni fa ba jahila bace, kuma Abbana ba a banza yake biya min kud'in laraba ba, ina da ilimin addini daidai gwargwado, karambani ne kawai da bud'ewar ido na 'ya'yan yau da aka haifemu ba'a haifi halinmu ba, iyayena a tsaye suke kan tarbiyata, ni ce kawai nake ja musu zagi da zund'e, amma na tabbata duk wanda ya zageni iyayensa ya zaga, dan ni ban yi wa iyayena rainin da har zanyi cacar bakin da zata kaini ga zaginsu ba."

Duk da maganarshi ta so tsaya mishi sai yayi gaggawar kawar da ita a rai ya d'an tab'e baki yace "Kin tabbata ba asara ake yi ba?"

Kallonshi tayi rai b'ace tana sako hawaye tace "E, na tabbata."

Wani shak'iyin murmushi yayi yace "A Alk'ur'ani mai girma Allah yana fad'awa manzonsa cewa " Qumi-llaila illa k'alila, (suratul muzammil, aya ta 2) me ye fassarar hakan?"

Kallonshi tayi tana malalacin murmushi tace "Ka tsaya a kowane dare sai kad'an kawai."

D'orawa yayi da "A wata ayar yana cewa, Yah ayyuha-llazina amanu qu anfusakum wa'ahalikum nara'waquduha-nasu walhijara,alaiha mala'ikatun gilazun, shidadun-laya-asunallaha ma'amarahum wayaf-aluna ma'yu'umarun (suratul tahrim, aya ta 5)."

Ba tare data daina kallonshi ba dan mamakinshi take a yanzu kam tace "Yah ku wad'anda sukayi imani, ku kare kawunanku da iyalenku daga shiga wuta-wacce mutane da duwatsu ce makamashinta'a cikinta kuma mala'iku ne masu tsananin k'arfi da basa sab'a umarnin Allah kuma suna yin abinda aka umarcesu."

Ba tare daya kalli sashen da take ba yace "A wata ayar cewa ake, Wa'iza sa'alaka ibadi anni'fainni qarib-ujibu da'awati-da'i iza'da'an, falyastajibuli-walyu'uminubi-la'alahum yarshudun (suratul baqara aya ta 185)."

A kaikaice ita ma ta amsa da "Idan bayina suka tambayeka a game dani ka fad'a musu ina kusa da su, ina amsa rok'on mai rok'o a a sanda ya rok'eni, ku rok'eni kuyi imani dani i..."

Kallon daya mata da sauri yasa tayi shiru tana d'auke kallonta daga kanshi gaba d'aya, sake d'auke idonshi yayi yana jin zuciyarshi na wani daka da k'arfi k'arfi, cikin k'arfin hali da son rikitata ya fita a b'angaren Alqur'ani ya koma hadisi ta hanyar fad'in "Fawallahu lazi-la'ilaha gairuhu, ina ahadakum-laya'amaluahalin-janna hatta'mayakunu bainahu-wabainaha illa'zira'un, fayasbik'u'alaihul kitab faya'amalu ahalin'nar fayadakulaha..."

Kallonshi Mimi tayi a ranta tana fad'in "Wato ita zai wa wannan jirgen?"

Cije leb'en k'asa tayi kafin tace "Hadisi na 4 mai taken ahwalul insan, Abi Abdul-Rahaman Abdullahi bin Mas'ud ne Allah ya yarda dashi ne yake fad'a, fassarar kuma ita ce na rantse da Allahn da babu wani bayan shi, lallai d'ayanku yana aikata aiki irin na yan aljanna harsai ya kasance tsakaninshi da ita saura zira'i d'aya, sai a rufe littafinshi sai ya dinga aikata aiki irin na yan wuta, kuma sai ya shigeta...Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi."

Kallonta yayi cike da gatse yace "Wane hadisi ne a gaban wannan?"

Murmushi tayi tace "A wane littafin hadisin???"

Yanda ta gama harbo jirginshi yasa shi saurin kallonta da ido cirrr kamar zai had'eta, d'auke idonta tayi daga kanshi tace "Idan a matin-l'1arba'una nawwiya fi ahadisin-lsahiha nabbawiy, hadisi na 6 shi ne hani akan bidi'a,, wanda uwar muminai uwar Abdullah A'ishata Allah ya k'ara yarda a gareta tace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa yace "Duk wanda ya zo mana da wani abu cikin lamarinmu ba'a cikinmu ba to mun mayar mishi" Bukhari da Muslim ne suka ruwaitoshi, a cikin wata rawaya ta muslim kuma yace "Wanda ya aikata wani aiki ba'a cikin lamarinmu ba to mun mayar mishi."

Wani nauyayyen numfashi ya sauke a sirrince yana jin abun wani iri kamar mafarki, to dama tana da sani haka take sanin ne tayi take tsula tsiyarta? Kafin ya samu gamsashiyar amsa dreban ya kutsa hancin motar cikin asibiti, a inda motocin suke da farko yanzu ma aka paka, yana shirin bud'ewa tayi saurin cewa "Abinda nake yi ai baiyi kama dana jahilai ba, kuma bai aikata abunda ya sab'awa shari'a ba bare har kayi tunanin rashin ilimi ne ya jawo hakan."

Saida ta bud'e motar zata fita ta sake kallonshi tace "Yana daga cikin kyautata musuluncin mutum ya bar shiga abinda bai shafeshi ba, hadisi ne ingantaccen, idan ka manta ka tuna hakan."

Ficewa tayi ta shiga takawa da sauri tare da d'age nikab d'in ta kwanceta gaba d'aya har ta shige duk da bata san d'akin da zata shiga ba, tana shiga ta corridor suka had'e da Alhaji Saleh ya fito zai tafi, gaisheshi tayi har k'asa ya amsa da fara'a ya nuna mata d'akin, wucewa tayi da sallama aka amsa da bata izinin shiga, a hankali ta bud'a k'ofar tana mai sauke idonta akan Hajia, k'arasa shiga tayi daga Asma'u sai Hajia sai kuma wata matashiya da bata san ta ba tare da Aisha da kayan makaranta a jikinta.

Da fara'a Hajia tace "Mimi sai yanzu? Nayi taa jiran shigowarki ai."

Murmushi tayi tana sunne kan ta, Asma'u ma murmushi tayi tace "Da alama gida ta koma ta canza hijabi."

D'aga kai Mimi tayi ta kalleta tare da satar kallon Asas dake kwance yana bacci, d'auke kallonta tayi daga kan shi ta kalli Aisha dake fad'in "Aunty Mimi ina kwana?"

Da sakin fuska cike da jin kunya tace "Aisha sannu."

"Yawwa." Ta fad'a da fara'a, d'ayar ce tace "Ina kwana aunty."

A sanyaye tace "Muna lafiya?"

"Lafiya lau." Ta fad'a da sakin fuska ita ma, Hajia ce tace "Mai aikin gidanku ce ai, Hafsat take kama ma aiki."

Sunkuyar da kai tayi a ranta tana fad'in "Gidan mu dai, ni ba zan zauna da tsohon nan ba, d'an rainin wayo ne."

Yanda tayi maganar a zuciyarta yasa har bakinta saida ya motsa, mik'ewa su Aisha sukayi tana fad'in "Hajia ni zan wuce makaranta dreba na jirana a waje."

Tab'e baki Hajia tayi tace "To Umma ta gaida Aisha mana."

Kallonta Aisha tayi tace "Kuma dan kin samu ma na miki magana?"

"Kar ki min mana." Ta fad'a tana d'auke kai, murmushi tayi tace "Nasan me ye matsalarki, idan na dawo zamu zauna dake Hajia."

Zasu fita shi kuma ya bud'o k'ofar da waya a hannunshi, juyawar da tayi yasa suka fara had'a idonsu, da sauri ta janye nata gabanta na fad'uwa da sauri sauri, takawa tayi ta koma bayan Hajia ta lab'e tare da yaye hijabin ta baya ta d'orashi akan kafad'unta, hakan yasa bayanta ya bayyana a waje.

A sanyaye ta ji yace wa Aisha "Har yanzu baki tafi ba?"

Da ladabi kanta a k'asa tace "Abie Amie ce ta aikoni tare da Assia muka kawowa su Hajia abinci."

Lumshe ido yayi tare da kaucewa a k'ofar suka fita, k'arasa shigowa yayi yana kallon yanda ta yaye hijabin, wato har tayi halin? Girgiza kai yayi ya kalli Hajia dake fad'in "Hajiarmu, mun gama shirin tafiya komai da komai, insha'Allah yau da k'arfe 08:00 na dare jirginmu zai tashi."

Kallonshi tayi da mamaki tace "Yau kuma? Da wuri haka?"

Lumshe ido kawai yayi alamar eh, jinjina kai tayi daan ta fahimci ya gama kenan, a sanyaye tace "To da wa zaku tafi?"

A dak'ile yace "Ni, da kuma shi."

Nan ma jinjina kai tayi ba tace komai ba, juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya, kallon Mimi yayi da ita ma ta kalleshi ganin ya tsaya, nunota yayi da yatsa yace "...



_Nasan kunsan da gani posting da wuri ya nuna komai ya tafi zan-zan, hak'ik'a comment k'arfin gwiwa ne da kuzari馃榿 dan gashi allurarku ta sokeni da kyau, a ci gaba da gashi._



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:56 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*35*


Nunota yayi da yatsa yace " *Maamah* wallahi idan baki gyara hijabin nan ba saina ajeta hulata gefe na miki abinda baki tsammani."

Wani bazawarin murmushi ta saki tare da yin durk'ushe bayan kujerar Hajia tana fad'in "Hajia ai kinsan tun ina yarinya bana son zafi, shiyasa Mamana ma a waje take min shinfid'a ina kwana, wannan hijabin zai iya kasheni saboda girmansa yayi yawa."

Hajia daketa rik'e dariyarta rufe baki tayi da tafin hannu, Asma'u kam kallonta tayi tace "Yaushe haka ta fara faruwa?"

K'wafa sheikh yayi ya juya zai fita Mimi dake hararan Asma'u ta sake fad'in "Sheikh baka bani wayata da ka ce ba."

Da sauri ya juyo jin ta kimkima wata k'aryar, kallonta ya shiga yi irin mai nuna "Ke Mimi dan Allah zo ki kasheni ki huta."

Jinjina kai yayi yasa hannu aljihu ya ciro wayar dan dama tana tare dashi, mik'a mata yayi yace "Gashi."

Karb'a tayi tana washe baki har kunne, juyawa yayi ya fita da sauri ta zagaya kusan Asma'u ta zauna tana bud'e wayar, abubuwan data fi damuwa da su ta fara dubawa, saidai mummunan gani tayi dan komai ya shafe hotunanta da girki kawai ta gani, sannan an yi d茅sinstaller WhastApp d'inta alamar ba'a son ta dashi, gumtse baki tayi ta kalli Asma'u kamar zata kifa mata mari tsabar takaici.

Zuwa k'arfe 10:20 aka sallamesu a asibitin, har gida suka rakasu saidai daga cikin mota Hajia ta musu sallama ban da Mimi dake kunyar had'a ido da Asas, dan shima kunyarta yake ji fiye da yanda ita take jin kunyar shi ma, suna shiga gidansu su kuma dreba ya wuce dasu gida.



*07:00*

Cike da son danne kewarta ko na ce buk'atuwar mace ya sake matseta a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske, tun ranar da ifiritiyar yarinyar can ta tashi boma-bomanshi sun kasa kwantawa, dan ya fahimci Hafsat bata jin dad'i sosai, dan haka bai ma nuna mata buk'atar hakan ba, lumshe ido yayi yana sake jin komai na dad'a mik'e mishi tsaye cikin muryar dake nunawa duk mai hankali halin da mamallakin muryar yake ciki ya shiga rad'a mata "Zzzanyi...kewarki manga na, ki kula min da kanki."

Sake d'an rumgumeshi tayi ita ma tana yatsina fuska saboda rik'ewar da bayanta keyi tace "Insha'Allah, ka kula min da kanka kai ma, Allah ya tsare mana ku ya kareku."

Kasa amsa mata yayi sai wuyanta daya shiga shinshinawa yana goga mata gemunshi a kafad'a, cije leb'e tayi tana rintse ido dan sosai take da buk'atar zama, hannu tasa ta dafe cikinta da sauri ya d'ago ya kalleta yace "Lafiya?"

Murmushi ta sakar masa tace "Ba komai." Da alamar tuhuma yace "Kin tabbata?"

Jinjina kai tayi, ajiyar zuciya ya sauke yana rik'e da hannayenta yace "Ki tayamu da addu'a muje a sa'a da fatan dacewa, idan kika ji jikin nan ya matsa miki dan Allah kiyi k'ok'ari ki kai min kanki asibiti, Hafsa ba'a son zaman nan naki a wannan halin."

Jinjina kai tayi tace "Insha'Allahu zan je."

Jinjina kai yayi shi ma yace "A d'aki na aje miki katin banki na gida, sannan akwai makulin mota guda biyu na bar miki wanda zaki iya buk'ata."

Murmushi tayi tace "Allah ya saka da alkairi, zanyi kewarka."

Sake rumgumeta yayi tare da manna mata sumba yace "Nima haka."

Sakin juna sukayi a hankali yana rik'e da hannunta suka fito falon, yaran suka samu suna tilawar karatu, duk mik'ewa sukayi suna binshi da addu'a, shafa kawunansu yayi dukansu ya sumbaci goshinsu har Aisha kafin ya musu addu'a ya fita zuciyarshi cike da kewar iyalinshi musamman ma matarshi da yake matuk'ar tausaya mata.


*Asa-Ma'u*


Fashewa tayi da kuka duk da bai fad'a mata kalmar so ba, amma dai yanda ya nuna mata jin dad'inshi da godiya akan martaba da kimarta data kawo masa, had'e da jinjina mata akan irin bajintar da tayi a darensu, madadin ace yana kula da ita sai ya zama ita ce ta kula dashi har ta kasa bacci a wannan daren saboda halin da yake ciki. Ganin yayi rarrashin amma ta k'i yin shiru yasa shi aje jakarshi k'asa yace "Shikenan to tunda ba kya son tafiyar, bari na kira sheikh saina fad'a masa kawai na fasa tafiyar saboda ba kya so, kinga sai na zauna a gidan tare dake, amma fa kiyi hak'uri dan kullum zan dinga suma miki a guda."

Da sauri ta rik'e wayar da yake k'ok'arin cirowa aljihu tana fad'in "A'a baan ce ba."

Kallonta yayi ya sauke numfashi yace "To me kika ce yanzu?"

Sunkuyar da kai tayi tana share hawaye tace "Ka tafi Allah ya bada sa'a, Allah ya baka lafiya kamar kowa."

Tallabo hab'arta yayi tare da fad'in "Sannan na dawo miki gida mu d'ora shagalinmu daga inda muka tsaya."

Duk'ar da kai tayi cike da kunya tana Murmushi da sauri ya tallabota ta fad'a jikinshi, rumgumeta yayi sosai yana furta "Na fad'a miki wata magana."

A k'asan mak'oshi tace "Um." Sake matseta yayi yace "Zaki yarda dani idan na fad'a miki?"

"Um." Ta sake fad'a a sanyaye, cike da k'warin gwiwa yace "Ina sonki a zuciyata *Husna*."

Da sauri ta d'ago kanta daga k'irjinshi tana kallon fuskarshi, kamar wanda aka ce mishi zata hango burbushin sauran son Mimi da har yaanzu ke zuciyarshi sai kawai ya sunkuyar da idonshi k'asa, sautin murmushinta ne yasa shi kuma kallonta, cikin raha tace "Kamar ba gaske ba."

Da alamar tuhuma yace "Kenan baki yarda ba?"

Girgiza kai tayi tace "Na yarda mana, kawai dai ina ji ne kamar a mafarki."

Murmushi yayi yace "To ba mafarki bane, zahiri ne wannan."

Murmushi tayi mai k'ayatarwa tare da gyara zaman hijab d'inta, rik'e hannunta yayi yace "Muje dreba na jiranmu a waje."

Jinjina kai tayi tare da bin shi a baya duk da yana rik'e da hannunta d'aya hannun kuma jakarshi yake ja, tare suka nufi airport dan suna so suga tafiyarsu kafin su juyo su dawo.



*Mimi*


Kwance take akan gado tana ta karatun muktasur-lakhdari da ta samu a wayar, ba kuma shi kad'ai bane ta samu ire-iren litattafan nan dayawa a wayar wanda ta tabbatar shi ya saka mata su.

Da sauri Hajia ta shigo d'akin hakan yasa ta tashi zaune tana kallonta, hijab ne hannunta tana ta k'ok'arin sakawa tana fad'in "Mimi tashi mu tafi ki rakani, na tabbata yanzu suna filin jirgin nan."

Da mamaki tare da wani fad'uwar gaba da taji a sirrince tace "Hajia tare zamu tafi?"

Saida ta gyara hijab d'in a fuskarta tace "E mana, ina so ne na samu abokin tafiya, ko ba zaki je ba?"

Sauke numfashi tayi a fili ta furta "Shikenan zan je."

Saukowa tayi a kan gadon tare da nufa wurin kayanta, har ta d'auki hijab sai kuma ta yatsina baki ta mayar dashi tace "Dare ne fa, wa zai kula dani ma."

Wani arnen mayafi ta d'auko shara-shara kalar fari kamar yanda fari yafi yawa a atamfar jikinta, riga da siket ne dai kamar mafi yawan lokuta d'inkin zamani, gidan nonuwan nan ya fito cas da shi haka siket d'in ya bi jikinta ya fito da mazaunai da wajen gwiwa ma ya ciresu daban, takalmi ta d'auka masu tudu hakan yasa ta shiga bada sautin d'as-d'as-d'as.

Gaban madubi ta tsaya ta d'an gyara d'aurin kallabin irin kawai zahra Buhari tare da shafe jikinta da turarenta mukhallat, masha'Allah yanda wuyanta ya fito sai kuma ta d'ora mayafin a kafad'u ta rik'e wayarta ta fito.

A mota ta samu Hajia tana amsa waya da alama kuma da Hafsat suke waya, dan haka Hajia bata kula da shigarta ba ta dai ji k'amshin turarenta kawai, saida ta kammala ne ta juyo ta kalleta tana fad'in "Daga nan zamu wuce gidanku na ga jikin Hafsat, da alama bata jin dad'i..."

Dakatawa tayi sakamakon ganin Mimi kamar wacce zata je bikin walima, zaro ido tayi tace "Takwarata da mayafin naan kika fito?"

Tsareta tayi da ido tace "E." Ajiyar zuciya ta sauke ta furta "Ya Hayyu ya Qayyum."

Jinjina kai tayi ta kasa cewa komai ba, dan badan sauri da take ba da sai ta canza mayafin nan, kar sheikh ya d'auka ita ke d'aure mata gindi ma take wani abun.

Basu jima ba suka isa dan sun fi dukansu kusa da filin jirgin, ko da motarsu ta paka wajen ta hangi na shi motocin da kuma ta Asas saidai babu kowa a wurin, fita sukayi saidai a yau Mimi jin ta take a sake kamar sanda tana budurwa, dan ta kwana biyu rabonta da mayafi ma, gaba Hajia ta wuce Mimi na bayanta suna tunkarar shiga cikin filin da mutane dayawa ke ciki sun rako ahalinsu a iya inda kujerun zama na farko suke, wasu kuma kai tsaye suke wucewa wajen kejuru na biyo wanda aka tanada domin masu tafiya.

Hajia na shiga suka kallo wajen kamar wacce ta k'wala musu kira, saidai kuma a take kallo ya koma sama wau shaho ya d'au giwa, " *Mimi*?"

Shi ne kawai abinda ya furta tare da damk'ar hannun Asas d'aya hannun kuma gam a k'irjinshi, lumshe ido yayi yana son ambatan sunan ubangiji amma yau sai ya samu kan shi da kasa furta komai. Kallonshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login