Showing 45001 words to 48000 words out of 185502 words
take mata ta yanda ba zata iya share kiran ba, hannunta da zuciyarta na kakkarwa ta d'aga kiran tana jan sallama, a sanyaye sosai ya amsa da "Wa'alaiki salam."
Shiru ne ya d'an ratsa na dak'ik'u kafin yace "Ki gafarce ni Ryam na sake kiranki, zuciyata azalzalata take a game da lamarinki, dan Allah ki fad'a min idan Abbanki ya dawo na zo na ganshi."
Wani sanyayyan murmushi ta saki a ranta tana fad'in "Allah mai iko, ni Maryam ba kowa ba kuma ba 'yar kowa ba, yau ni ce har babban malami kamar wannan yake min magiya haka?"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da tunanin ai Abba ya karb'i lefenta har da ma kud'in aurenta, dan haka tasan duk girmanshi Abba ba zai yarda yayi magana biyu ba, dan haka ta saki murmushin jin dad'i tare da bud'a bakinta tace "Abba ya dawo jiya, dama na rasa yanda zanyi na kira ne."
Wani sanyayyan murmushi yayi shi ma har tana jin sautinsa yace "Na ji dad'i sosai Ryam, zan zo gidanku yau insha'Allah."
Cikin rashin jin dad'i a zuciyarta ganin yanda zata sakashi zama wani wawa haka tace "Shikenan, Allah ya amince."
Da fara'a yace "Ameen, nagode, sai anjima."
A k'asan mak'oshi tace "Uhum." Tana aje wayar ta kalli agogon screen d'in, da sauri ta aje wayar ta shiga gaggawar k'arasa shirinta, ta mik'e kenan tana gyara zaman rantsetsiyar abayar data saka bak'a wulik wacce ta fito da hasken fatarta ta yana kallabin y'a mata kyau sosai, Asma'u ce ta shigo da sallama mama ta amsa, tana shigowa suka kalli juna suna murmushi, ko gyara kayan data barbaza batayi ba ta d'auki jakarta tace "Muje kinji."
Fitowa sukayi Asma'u na fad'in "Wa zai d'auke waccen kayan kuma?"
Kafin tayi magana mama da taji ta tace "Ta bari jakarta ta d'auke mata mana."
Dukansu dariya sukayi kafin Mimi tace "Mama zamu wuce gidan Iya, kinga idan ya gaishesu ita da malam sai mu wuce."
Jinjina kai tayi tace "Allah ya yarda, ku kula dan Allah kunji."
"Insha'Allah." Ta fad'a tana kama hannun Asma'u suka fita daga gidan.
Kamar dai kullum zaka rantse da Allah wata 'yar hamshak'in mai kud'i ce, hatta takonta d'aukar hankali yake yanda duk da duhu ne ana k'are mata kallo, ga k'amshin da take bari a duk inda ta gifta ta wuce, da haka suka isa gidansu Iya D'茅lu, da raha suka shiga zolayar juna ita da kakanin nata data samu malam na cin abinci, kamar yanda tun a kan hanya ta fad'awa Asas dan haka suna zuwa ba jimawa ya iso.
Da kan ta ta fito ta mishi iso zuwa cikin gidan, sosai suka gaisa har malam na fad'in "Ai bansan zaka zo ba da ban yarda ka sameni ba."
Cikin shagwab'a Mimi ta kalleshi tace "Angona."
Dariya yayi tare da shafar kumatunta yana fad'in "To ai bana so ya gane kishina ne a kan ki, zan iya cakumarshi yanzun nan mu hau sama."
Dariya sosai Asas yayi yana sunkuyar da kai cike da kunya, Iya Delu ce tace "Ni kuma farin ciki nayi dana ganeshi, dan a take naji na samu miji nima mai jini a jika."
Kallon Mimi tayi tace "Ba kullum cika baki a kan ni na tsufa bane ke kuma sabon jini? To ni ma na k'wace miki miji."
Dariya sosai ake yi har Asas yace "Gaskiya ne, ni ma yanzu dana ganki na ji bana buk'atar sabuwar jinin, dan kuwa da tsohuwar zuma ake magani."
Da irin rahar nan suka musu sallama suka fita tare da Asma'u, saidai a k'ofar gidan ita suka rabu inda Mimi ta sake jadadda mata "Asma'u ki zauna gidansu Jamila, idan na zo zan kiraki a waya saiki fito waje mu k'arasa gida, kin gane?"
Jinjina kai tayi tace "Na gane, sai kun dawo."
Murmushi ta mata tace "To." A raunane tace "Dan Allah Mimi ki kula da kanki kinji."
Jinjina kai tayi alamar to, gidansu Jamila ta nufa ita kuma ta bud'e motar ta shiga, kallonta yayi yace "Ba tare zamu tafi da ita ba?"
Girgiza kai tayi tace "Dama akwai inda zata je, hanya ce kawai ta had'amu."
Jinjina kai yayi tare da tayar da motar suka d'auki hanya.
A k'alla sun d'auki minti talatin kafin suka isa gidan, a sanda ya shiga gaba yana mata jagora zuwa babba kuma k'ayataccen falon, tsoro, fargaba, al'ajabi da kuma kunya ne suka taru suka baibayeta, da haka suka shiga falon Asas na fad'in "Hajiata, fito ga sarakuwarki na kawo miki, zo kiga yar beautyna."
K'asa ta sake yi da kanta tsabar kunya tana sake rik'e jakarta tamau a hannu, da fara'a da kuma al'ajabin ganin kyakyawar yarinyar mai kama da larabawa ta shiga takowa tana fad'in "A'a masha'Allah, yau kam autana ya cika alk'awari."
Tana zuwa ta ja Mimi a jikinta ta rumgume wacce ke neman sulalewa k'asa, sosai tayi mamakin yanda mahaifiyarshi ta tarbeta, bata zame da ita ko ina ba sai kan teburin cin abinci, zaunar da ita tayi tana k'walla kiran "Salamatu! Salamatu."
"Na'am Hajia." Aka amsa daga ciki ana fitowa, tana zuwa Hajia tace "Kinga bak'uwa na yi, ki kawo mana abinci."
Saida ta kalli Mimi da kanta ke k'asa, d'an k'ara lek'a fuskar tayi da son gano a ina ta san fuskar, tunawa da tayi yasa ta jinjina kai ta kalli Asas, murmushi ta k'ak'aro tace "To Hajia."
Juyawa tayi ta koma tana mamakin shi kuma yallab'ai Asas me ya had'ashi da yarinyar? Ita ce zai aura? Wacce ake kira da karuwa, karuwar ma ta samarin unguwa, bugu da k'ari kuma 'yar wada, dan kuwa duk fad'an nan da akayi na jiya a gabanta, ita ce ma suka zaburo suka rabasu sanda suka kacame da fad'a. Haka ta gama duk abinda ya dace ta kawo ta kuma kula da komai amma bata daina kallon Mimi ba, gashi taga daga Hajiar har Asas d'in sai hira suke jan ta da ita da raha alamar dai ta samu karb'uwa a wurinsu sosai.
Saida ta gama ta koma ciki Hajia ta kalli Mimi tace "Takwarata, ci abinci kinji, nan gidan fa ba bak'onki bane."
Murmushi ta sake yi ta sunkuyar da kanta k'asa, da zolaya Asas yace "Kunyar Hajia wai kike ji? Kinga yanzu fa ke ce autarta ko, ni na bar miki yanzu dan na girma, tunda nan gaba kad'an zaki haifa min yara."
Satar kallonshi tayi da mamaki baki bud'e, sai kuma tayi shiru kawai kan ta k'asa tana jin Hajia na fad'in "Matsalata da kai kenan rashin kunya."
Jawo kujerarta tayi ta koma kusa da Mimi ta d'ebo abincin zata kai bakinta, sinne kai ta sake yi cike da kunya tana murmushi, tallabo hab'arta tayi tace "Maryam, ni ma fa mahaifiyarki ce, kinga bana da 'ya'ya dayawa sai guda biyu, ki saki jikinki dani kinga zaki shigo ahalin nan ba da jimawa ba."
Jinjina kai tayi alamar to, sake kai mata cokalin tayi a baki haka yasa ta karb'a cike da kunya, duk yanda ta so zillewa bata samu dama ba haka ta dinga ciyar da ita da hannunta, tana tsaka da cin abincin ne ta kalli Asas tace "Kaga takwarata sai tayi kama da *Fanna*, ko dai 'yar uwarta ce?"
Girgiza kai yayi yace "Bana jin ma sun tab'a had'uwa."
Kallon Mimi tayi tace "Takwarata, waye mahaifinki? Ina ne gidanku?"
Da sauri Asas ya kallesu yana neman k'warewa, to shi dai bai wani zauna ya fad'a mata wacece Mimi ba, yasan danginshi kuma farin sani zasu iya kawo mishi tangard'a, gata ita kuma bata b'oye komai daya shafi asalinta yasan tsaf zata fad'a mata komai.
Mimi ma satar kallonshi tayi kafin tayi k'asa da kanta tace "...
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:54 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*16*
"Mama ni ba 'yar kowa bace, mu talakawa ne da muke fafuta akan abinda zamu ci, sannan iyaye na..."
"Mutanen kirki ne." Cewar Asas da sauri yana tsare Hajia da ido, duk kallonshi sukayi da mamaki sai Hajia data d'an basar ta kalli Mimi tace "Ke 'yar talakawa ce?"
Jinjina kai tayi ba tare data kalleta ba, a hankali Hajiaa ta aje cokalin hannunta tare da yab'awa fuskarta yanayin rashin jin dad'i, kallon Asas tayi ta mik'e tace "Ka sameni a d'akina."
Lumshe ido yayi irin na ohh shiit d'in nan tare da kallon Hajiar bai ce komai ba, da kallo suka bita har da Mimi dake al'ajabi da mamaki, kallonta yayi ya mik'e yace "Ina zuwa Maah, karki damu kin ji, ki ci abincin."
Da kallo ta bishi kafin ta kalli farantin gabanta, hak'ik'a tana son cin wannan gara da aka wadata gabanta da ita, saidai zalamarta bata kai wannan matakin ba, da taga fuska ne ma zata iya d'iba ta kai wa 'yan k'annanta su goge hak'ora, amma daga yanda ta ga fuskar matar kam tasan sai ta Allah aurenta da Asas yayi wu.
*Suna* shiga a zafafe ta juyo tana fad'in "Asas dama yarinyar nan 'yar talakawa ce?"
Cikin rashin karsashi yace "Hajia miye dan 'yar talakawa ce? Shikenan mu dake da hali ba zamu iya auren 'ya'yan marasa k'arfi ba dan a tallafawa juna."
A kausashe tace "Kaga Asas ba kasancewarta 'yar talakawa ba yasa nake maka maganar nan ba, babbar matsalar shi ne dama ba daga ahalinmu ta fito ba, dangi zasu ga laifina ne na barka ka auri yarinyar da ba nasabarku d'aya ba sannan yar talakawa, kafi kowa sanin yanda ake son had'aka da 'ya'yan dangi amma ka k'i, larurarka tasa na ce a rabu da kai zaka zab'a da kanka, shi ne yanzu zaka zo min da waccen yarinyar."
Sanyaya murya ya sake yi sosai yace "Hajia ta, dan Allah karki hanani auren Mimi, ina sonta da zuciya d'aya ba zan iya rabuwa da ita ba."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Yanzu ka je kusa da ita ka zauna, idan ta kammala ka kaita gidan auntynka tunda an fad'a mata zaku je can."
Marairaicewa yayi yace "Hajia ba zaki hanani aurenta ba?"
Yatsina fuska tayi tace "Ka je kawai zanyi tunani."
Sake shagwab'ewa yayi yace "Hajia haka zaki tarbi bak'uwarki?"
D'an murmushi ta k'ak'aro tace "Muje to."
Da fara'a ya biyo bayanta suka fito falon, yanda suka barta haka suka sameta, bata yarda ta had'a ido da ko d'aya daga cikinsu ba, zaune sukayi Asas na fad'in "Maah, mun barki ke kad'ai? Kiyi hak'uri."
Murmushin yak'e tayi haka ma Hajia murmushin yak'en ta shiga yi, jim kad'an ya kalli Mimi da kanta ke k'asa bata cin abincin yace "Kina lafiya ko?"
Jinjina kai tayi ta kalleshi tace "Abba yace kar na jima."
Murmushi yayi ya kalli Hajia yace "Hajiata zamu wuce gidan Aunty Hafsat."
D'an kallon Mimi tayi tace "To Allah ya tsare, ku gaishesu da kyau."
Mik'ewa Mimi tayi hakan yasa shi ma ya mik'e haka ma Hajia, k'wala kiran Salamatu tayi tana zuwa ta sunkuya tace "Hajia gani."
A gadarance tace "Ki d'auko min sak'on nan dana ware dan bak'uwata."
D'an d'aga ido Mimi tayi ta kalli Hajia, a kuskure kuma idonsu suka had'u ita ma tana kallonta tana mamakin yanda tace yar talakawa ce ita amma fatarta wata irin fresh da ita, uwa uba ga abayar jikinta wacce ta shekarar bara ta siyowa Hafsat su dayawa da shegiyar tsada, to a ina ta samesu kenan? Bayan tace talaka ce ita. Tana wannan tunanin Salamatu ta kawo manyan ledojin kalar pink guda biyu, ajewa tayi k'asa tana fad'in "Gasu Hajia."
Cike da wulak'anci tace "Ki bata, zasu mata anfani."
D'agowa ta sakeyi ta kalli idon Hajia tsaf kallo na ki fahimceni naa fahimceki, Hajia kan ta saida ta ji wani shakkun yarinyar saboda yanda ta kalleta babu tsoro a ciki da kuma rashin d'aukar raini, mik'o mata ledojin Salamatu tayi tana fad'in "Gashi k'aramar Hajia."
A yangance ta kalli Salamatu ta yatsina fuska dan hakan d'abi'arta ce kafin tace "Nagode, Abbana ya hanani karb'an kyauta irin wannan."
Da mamaki Hajia ta kalleta, sai kuma ta tab'e baki ta kalli Asas tace "Ka d'aukar mata kayan, watak'ila kunya take ji."
Girgiza kai tayi a hankali tace "Bana so Abbana ya min fad'a sakamakon aikata abinda ya haneni."
A ladabce ta juya zata fita tana fad'in "Nagode da karramawa, sai anjimanku." Da kallo Hajiar ta bita haka ma Salamatu, Asas kam tuni ya juya zai bi bayanta Salamatu tace "Alhaji ka d'aukar mata kayan mana, ina ga fa kunya ce kamar yanda Hajia ta fad'a, ai b芒 kyau mayar da hannun kyauta baya."
Murmushi ya mata tare da d'aukar ledojin nik'i-nik'i ya bi bayanta da su, cikin al'ajabin lamarin yarinyar Hajia ta juya zata zauna kan kujera tana fad'in "Amma yarinyar nan akwai yar rainin hankali, wacece ita? Me take tak'ama dashi?"
Cikin ladabi kamar wata jakadiya Salamatu ta bi bayan Hajia tana fad'in "Ai ni banyi mamaki ba Hajia, bansan yarinyar ba ko kad'an, amma bansan me yasa jiya muka had'u da ita ba."
Kallonta tayi tace "Kun had'u da ita ne? A ina?"
Zaune tayi k'asan k'afafun Hajiar tace "Hajia zaki tuna jiya kin aikeni gidan Kubra karb'o turarukan da kika saka a ledojin bak'uwarki?"
Jinjina kai tayi alamar eh, d'orawa tayi da "To ai unguwar take basu da nisa sosai, a titi na gansu suna fad'a ita da 'yan makarantarsu Hajia, dambe kamar maza wallahi haka na ganta, kuma kalaman da abokiyar fad'an take fad'a mata sune suka fi d'aga hankali, dan bata musa ba sai dai kuka da take."
Gyara zama Hajia tayi tace "Uhum! Ina jinki."
Tas Salamatu ta kwashe duk abinda ta ji kuma ta gani ta fad'a mata, hankali a matuk'ar tashe Hajia ta zaro ido tace "Wada fa kika ce? Kina nufin ubanta wada ne?"
jinjina kai tayi tace "Wallahi wada ne Hajia, da idona naga sanda ya shiga da ita cikin gida."
Mik'ewa Hajia tayi a hassale ta juya zuwa d'akinta tana fad'in "Ina! Ba zai yiwu ba wallahi, yar wada? Shin ina hankalinshi ya tafi ne da zai jawo min wannan iskancin, baisan cewa wannan larurar jini take bi ba, ko ita ba kalarsu bace kuma ta auri dogo zata iya haihuwar irin ubanta."
K'wafa tayi ta shiga d'aki dan d'aukar waya ta kira k'anninta wanda su suka karb'o mishi aurenta, shi ma bai fad'a mata komai ba kawai yace dai mutanen kirki ne, bayan haka babu wanda yace mata komai uwa uba kuma sheikh da tasan dama babu abinda zai fad'a mata na aibun mutanen.
*Mim-Sas*
Sam sai taji aurenshi ya fita a ranta, kawai tasan ma aurensu ba zai yiwu ba daga yanda mahaifiyarshi ta nuna mata d'in nan. Saidai tasan zata rasa namiji da yayi daidai da muradinta, numfashi ta sauke a hankali tare da d'an k'amk'ame jikinta saboda sanyin ac, d'an tab'e baki tayi data tuna a gidan ma ac ce ga mota ac, shiyasa masu kud'in nan zaka ga jikinsu ma daban yake da saura, wani taushi da laushi zaka ga fatarsu na fitarwa na musamman kamar dai yanda a ido ne kawai take ganin fatar Asas d'in zatayi wannan taushin.
Lura da yanayinta ya sakashi fad'in "Mimi, ni kam wace k'asa ke birgeki a duniyar nan?"
Kallonshi tayi ba yabo ba fallasa tace "Me yasa ka tambaya?"
Da fara'a yace "Ina so ne na sani dan na fara nema miki visa, dan a can zaki ci amarcinki."
Wani farin ciki ne ya kamata tare da yin murmushi ta sunkuyar da kai, shi ma murmushin yayi yace "Ina jinki."
Saida ta tsagaita tace "Umm! K'asar Madina, sannan k'asar Saudia."
Jinjina kai yayi yace "Da kyau, kinga kenan zaki jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya, zaki sha amarcinki sannan zakiyi aikin hajj."
Wani murmushin ta sake yi kawai ba tace komai ba, shi kam dan ya sa ta saki jikinta yasa shi cewa "Akan maganar bikinmu, abokanaina sun fara hura min wuta wai dole na musu wata walimar tare da 'yan mata, me kika ce a kai?"
Numfashi ta sauke tace "Duk yanda kayi d'aya ne."
"Da gaske?" Ya fad'a yana satar kallonta, jinjina kai tayi tace "Da gaske."
Jinjina kai shi ma yayi yace "Shikenan, zanyi tunanin abinda ya dace, matsalar da zaran mun d'auko maganar party sheikh zai taka mana burki, bansan ya zanyi ba gaskiya."
Kallonshi tayi da mamaki da son jin waye sheikh d'in nan? Na biyu kenan tana jin sunanshi a bakinshi, a hankali tace "Wane sheikh?"
Da mamaki shi ma ya kalleta yace "Wane sheikh? Kina nufin baki sanshi ba? Shi ne fa wakilina a wajen d'aurin aurenmu, kuma shi ne yake auren yayata Hafsat, banda kamarsa a cikin abokai da ma yan uwa."
Jinjina kai tayi tace "Da alama yana da mahimmanci a gareka?"
Murmushi yayi yace "Fiye da tunaninki, zan iya yin komai saboda sheikh, ina sonshi fiye da yanda nake son kaina, shi ma kuma yana so na sosai."
Murmushi kawai tayi ba tace komai ba, kallonta yayi yace "Wai da gaske baki tab'a jin sunan sheikh Abdul w..."
K'arar da IPhone d'inshi ta d'auka yasa ka shi yin shiru yana d'aukar wayar da dubawa, murmushi ya mata yace "Kinga shi yake kirana ma."
Ya fad'a yana nuna mata wayar, saman kawai ta gani sunan daya fito b'aro-b'aro wato *d'an uwa na*, yana d'auka ita dai tana jin yana fad'in "Allah sheikh gamu nan a hanya, kad'an ya rage ka ganmu gabanka."
Bata ji me aka fad'a b芒 amma taga yayi dariya yace "OK sai mun zo."
Aje wayar yayi yana girgiza kai yace "Ya min alk'awarin tarbanshi da kanki ne, shiyasa ya matsu mu iso dan akwai inda zai je."
Jinjina kai tayi tana murmushi tace "Allah sarki."
Da haka suka isa k'ofar tamk'amemen gidan, irin ginin nan ne na zamani mai d'aukar ido, gashi had'e da masallaci abun gwanin birgewa, ga hasken fitilu masu kyau wanda suke ship ship a cikin shukoki, ita dai baki ta saki tanaa kallon ikon Allah, wato can data bud'e ido tana kallon gidansu Asas ashe b芒