Showing 135001 words to 138000 words out of 185502 words
nayi bacci na a nan."
Girgiza kai ya sake yi alamar a'a, kyab'e fuska tayi ta turo baki ba tace komai ba, kallon fuskarta yayi ganin yanda ta kyab'e a dole tayi hushi yasa shi aje wayar hannunshi ya mata cakulkuli yana dariya da fad'in "Haba dai gimbiya, kinga fuskarki kuwa yanda tayi? Sai kika zama kamar wata mage na jin bacci."
K'yalk'yalewa tayi da dariya bata sani ba tana bille-bille har ta fad'i kan carpet d'in tana zillewa, bin ta yayi ya mata rumfa yana fad'in "To yi min dariya sannan."
Cikin k'yalk'yalawa take fad'in "Na yi to, nayi ya isa haka, Abdul cikina zan mutu."
Dakatawa yayi yana dariya shi ma da kallon fuskarta, ba taee daya d'aga daga jikinta ba y'a kalli fuskarta yace "Ryam ina sonki sosai, ki yarda da haka kinji."
Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um! Ban yarda ba."
Kallon mamaki ya mata yace "Ya kike so nayi dan na tabbatar miki?"
Cikin murmushi tace "Da kaina zan tabbatar da haka."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ta ya ya?"
Kashe masa ido tayi ta d'an k'yata bakinta, sumbatar bakinta yayi sosai kafin ya d'agata yace "Tashi ki shirya mu tafi gida kafin dare yayi."
Kamata yayi ta mik'e tsaye ta suka shiga d'akin, a tsanake suka shirya suna raharsu har suka gama suka fito bayan ya rufe kowace k'ofa suka d'auki hanyar komawa gida.
Suna shiga cikin gari ta kalleshi a marairaice tace "Abdallah ice cream."
Ta gefen ido ya kalleta yace "Me ice cream yayi?"
Turo baki tayi tace "Zan sha."
Girgiza kai yayi yana murmushi yace "Hummm! Amma dai kinsan ba zan lamunci shan kayan sanyin nan ba ko?"
Dafa hannunshi tayi da yake tuk'i tace "Dan Allah fa, daga wannan ba zan k'ara ba."
Jinjina kai yayi yace "Shikenan, watak'ila fa yarona ko yarinyata ce a cikinki."
Da k'arfi tace "Me? Da wuri haka? Tabb'!"
Kallonta yayi yace "Kina mamaki ne da yin ubangiji?"
Girgiza kai tayi tace "A'a, amma dai ai yayi wuri."
Murmushin gefen labb'a yayi mata har suka tsaya daidai shiga wani alimentation, fita yayi zai rufo k'ofar ta d'aga masa hannun tace "A dawo lafiya."
Murmushi yayi yace "Wato ba zaki zo muje ba saboda ba kya son ki jera da tsoho."
Dariya tayi tace "Ba haka bane, ai na d'auka ba zaka so na shiga gurin nan ba."
Girgiza kai yayi ya rufe k'ofar ya juya ya shiga wurin, a hankali ta bud'e motar ta fito da k'afafunta kafin ta fita gaba d'aya, rufe k'ofar tayi ta tunkari shiga ita ma tana murmushin mugunta.
Ta b'angaren kayan mak'ulashe ta nufa tana hangenshi tana b'oyewa, kwando ta d'auka ta dinga loda kayan k'walam biscuit chacolat da saurensu, saida ta cika basket d'in ta nufo inda yake tsaye yana laluban aljihu, tana zuwa ta aje basket d'in tana murmushi ganin ya tsaya sororo yana kallonta da mamaki.
Murmushi ta masa ta kalleshi tace "Ga wanda na d'auko ta can."
Galala ya kalli matashin sai kuma ya kalleta ya matsa kusanta yace "Ryam lafiyarki k'alau? Wa ya ce ki fito?"
Murmushi ta saki tana takowa ta tsaya daf da shi tace "Kayan dad'i na siyo."
Iska ya furzo da tunanin ya zaiyi da ita, yana kallo ta shiga ciro kayan tana d'orawa kan kantar da za'a dubasu a musu kud'insu, yana kallon ikon Allah shi dai aka fad'a mishi kud'in ya biya aka saka musu a leda, zai d'auka tayi saurin d'auka tana fad'in "Lahhhh! Haba Abdallah ya zan bari ka d'auka?"
D'auka tayi suka fita yana kallonta shi dai, saida suka shiga mota ya fara tafiya ya kalleta yace "Ryam kinsan ina da kishi?"
Ba alamar damuwa a tare da ita tace "Na sani."
"Kuma kinsan zan iya yin komai a kanki?"
Kai tsaye ta sake fad'in "Na sani."
Kallonta yayi yace "To me yasa kikayi abinda kikayi?"
Marairaicewa tayi tace "Sorry."
Murmushi yayi tare da lak'ato hancinta yace "Nayi sorry yan matana, amma kar a sake daga yau."
Jinjina kai tayi tace "Insha'Allah."
Da hirarsu ta farin ciki suka isa gidan, ta falon Hafsat suka sake shiga kuma sunyi sa'ar samunta zaune tare da Aisha suna karatu, abun haushi shi ne kallon da Aisha ke musu shi da Mimi, gashi bai ji ta gaishe da ita ba sai ma Mimi ce tayi k'ok'arin fad'in "Aisha karatu ake?"
Amma sai ya ga ta mik'e ranta a b'ace tana fad'in "Amie saida safe."
Da kallo ya bi Aishar har ta shige, Mimi ma d'akinta ta nufa tana fad'in "Saida safenku."
Shigewa tayi ta barshi tare da Hafsat, shi ma yau babu fara'ar nan ya kalleta yace "Zan shiga ciki nayi wanka, kafin na fito ina buk'atar ganin duka yaran nan a falona."
Da fara'a ta amsa mishi da "Angama sheikh nawa."
Shigewa yayi ta bishi da kallo sai kuma tayi saurin mik'ewa ta je had'o mishi kan yaran da tunanin ko lafiya? Bai d'auki lokaci ba ya fito daga wanka ya shirya cikin jallabiya fara tas da ita, yana fitowa falon kam ya samesu dukansu har da Munzeer, mutmushi yayi na jin dad'in girmama maganarshi da Hafsat tayi, duk da abinda zai fad'a yanzun bai shafi Munzeer ba, amma da yace yaran duka saita tasoshi daga bacci shi ma, dan gashi nan kanshi a cinyarta tana daddab'ashi ya tashi saboda ganin sheikh ya fito.
Zaune yayi akan sofar yana kallonsu dukansu, had'e fuska yayi sosai cikin fad'a da muryar tashin hankali yace "Auren da nayi ne yasa nake gani raini k'arara a idonku ko kuma dama can akwai rainin tsakaninmu yanzu ne ya fito? Shin haramun ne na aikata da girmansa ya gawurta har zai iya janyo min rainin 'ya'yan cikina dana haifa? Me na yi? Akan me?"
Ya k'arashe yana kallonsu musamman ma Aisha da Heezam, duk sanda kawunansu sukayi hakan yasa shi d'orawa da fad'in "Auren da nayi? Ko kuma yarinyar ce bata muku ba? Bana son tashin hankali kun sani, amma daga auren yarinya har zaku fara min kallon hadarin kaji har wasunku ma zasu iya bud'a baki su min tambayar da duk ta zo bakinsu bayan na tabbata kuna da hankalin tauna magana kafin ku furtata, to akan me?"
Jinjina kai yayi tare da k'wafa yace "Da ba'a aure ai da ban haifeku ta hanyar aure ba, k'addarata ce ta kawo Mimi a Wanda k'arfina ya fara k'arewa, idan zamuyi adalci yarinyar ce abar dubawa anan, amma ku mahaifiyarku kawai kuka sani, ita kuke taya wa kishi kenan? Shin ita kunga tayi makamancin abinda kuka min ne a yau d'in nan? Haka kawai na tsaya gabanku kuna k'are min kallo cike da raini da son tantance me na aikata da matata a d'akinta."
Kallon Hafsat yayi a sanyaye yace "Qawwama bana da matsala da ke, na tabbata kina iya k'ok'arinki akan tarbiyar yaran nan, amma ki sani zanyi wani abu da ban san ko zai miki dad'i ba, kasancewata uba namiji dole na d'auki matakin gyara kan iyali tun yanzu, dan a yanda na fahimta idan lamarin nan ya gawurta wata rana zan iya shigowa gidan nan na samu d'aya a cikin yaran nan suna dakuwa da Mimi, musamman ma da suke ganin shekarunsu d'aya kumaa tsayinsu d'aya da ita."
Kallon Aisha yayi yace "Ki shirya ma aurenki ranar juma'a mai zuwa insha'Allah."
Kallon Heezam yayi yace "Zan gama kammala maka shirin tafiyarka Madina a satin nan, da zaran kaga d'aurin auren yar uwarka zaka bar k'asar nan."
Kallon Aswan yayi yace "Daga sallah magriba zuwa isha'i zaka fara darasi tare damu a majalisin su Anas, daga isha'i zuwa lokacin da zaka kwanta bacci zaka kasance a d'akin karatu na kana bitar karatunka."
Duka yaran kallonshi suke kowa kamar zaiyi kuka musamman Aisha data fara hawaye, amma sai suka sadda kawunansu k'asa Heezam na fad'in "Ka gafarcemu Abie, mun tuba ba zamu k'ara ba insha'Allah."
Aisha ma da sauri tace "E Abie, ka yafe mana dan Allah, ba zamu sake ba wallahi, zamu d'auki aunty Mimi kamar mahaifiyarmu."
Da mamaki ya kallesu yace "A ganinku saboda ita ne na yanke hukuncin nan? Kar ku min gurguwar fahimta mana, hak'ik'a Aisha sai bayan aurena ne da naji wasu kalaman a bakinki na yanke hukuncin aurenki, amma sauran ai dama na jima da fad'a muku ina da wannan tsarin, yanzu ne lokacin zartarwa yayi."
Cikin shahsek'ar kuka Aisha tace "Abie ka yafe min ba zan k'ara ba, ina so na kammala karatu Abie ba yanzu na ke son aure ba."
Harara ya dalla mata yace "A lokacin da kike buk'atarshi kuma saiki kirashi ya zo?"
Kallon Hafsat yayi da ita dai tayi shiru take kallon yaran, amma fa a zuciyarta kamar zata kama da wuta haka take ji, a gaskiya hukuncin yanzu bai mata ba, dan ita ma kawai ta ta'allak'a haka da aurenshi da Mimi ne, akan me zai yanke ma yaranta wannan hukuncin? Saboda sun kalleshi kawai? Ajiyar zuciya ta sauke sanda yace "Hafsat me kika ce akan haka?"
Girgiza kai tayi a sanyaye tace "Ba komai sheikh, Allah yasa haka shi yafi zama alkairi, Allah ya mana jagora a lamuranmu."
Wani tattausan murmushi ya saki yana kallonta, a gaskiya da zai bud'a zuciyarshi ya nuna mata irin girma da k'aunar da yake mata musamman halayen nan nata na karamci, tabbas da sai ta ji babu mace mai sa'a a duk duniya kamar ta, da zatayi rawa tayi tsalle ta buga k'irjinta a gaban dubbanin mata kan cewa babu kamarta. Kallon yaran yayi yace "Ku tashi ku je ku kwanta."
Mik'ewa sukayi jiki duk a sanyaye sai Munzeer daya shiga baccinshi a k'afar Hafsat, saida suka fita dukansu ya taso ya d'auki Munzeer d'in sannan ya kama hannunta ta mik'e, a hankali suka fita har suka k'arasa d'aki ya shinfid'eshi ya tofa mishi addu'a, d'aki ya rakata ita ma ta kwanta kafin ya mata saida safe ya fito.
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*45*
Yana shiga d'akin ya samu Mimi bacci ya d'auketa, saidai da alama baiyi nisa ba dan hannunta har yanzu rik'e da robar ice cream d'inta, karb'a yayi ya aje gefe ya tattare kayan ya aje sannan ya gyara mata rufarta dan tayi wanka ta saka kayan bacci.
*07:30*
A sanyaye take amsa wayar Hajia tana fad'a mata auren Aisha kamar yanda sheikh ya fad'a, cikin son kwantar mata da hankali na iya abinda zata iya kawai Hajia tace "Hafsat karki damu kinji, dama ai sheikh ya sha fad'a idan har ya tashi aurar da ita babu abinda zaiyi na bidi'a, kar ki bari shed'an ya raya miki cewa ya yanke hukuncin nan ne saboda auren da yayi, ki mata addu'a matsayinki na Uwa Allah yasa haka shi yafi alkairi kinji."
A hankali tace "Shikenan Hajia insha'Allah, yanzu ya maganar shirye shirye ko wani gyara?"
Murmushi Hajia tayi tace "Hafsat ai ke ce uwarta kuma kinfi sanin me ya dace da ita, kawai kiyi tunani sai ki tuntub'i Karima kuyi magana, na tabbata dai sheikh ba zai mata kayan d'aki ba dan shi baya cikin wannan tsarin."
A sanyaye tace "Haka yake fad'a Hajia, ba zaiyi kayan d'aki ba kuma ya baka 'ya sannan ya baka abincin da zaka ci, saidai yace a matsayin Anas naa d'alibin da yake ji da shi zai iya mishi kyauta tsakaninshi ne da shi wannan."
Hajia ce tace "To kin gani, kawai ki mata addu'a tunda yaran ke kanki kin tabbatar da yaron kirki ne."
A ladabce tace "Gaskiya ne Hajia, Allah ya tabbatar mana da alkairi."
"Ameen." Hajia ta fad'a kafin suyi sallama ta aje wayar ta fito dan shiga madafa ta taimakawa mai aikin da ke tayata aiki idan ta haihu.
Tun asuba daya tasheta ya tafi masallaci bata sake ganinshi ba, tana idar da sallah ta shiga gyaran d'akinta a nutse, duk da ba wani datti ko wani abun gyaran ke akwai ba, amma saida ta kimtsa komai tayi turaren ruwa dana wuta da kaskon na'ura, tana gamawa ta shiga wanka dan Alhamdulillah yanzu jikinta da sauk'i sosai, tana fitowa a wanka ta zauna ta d'auki ado kamar zata je gasar sarauniyar kyau, cikin wani leshi ta shige ta kashe d'aurin d'an kwali mai hawa-hawa.
Yanda tayi wani masifaffen kyau yasa ta kallon kanta a madubi har ta d'auki selfie, saida ta gama ta aje wayar ta tunkari k'ofar fita, yanda falonta ke ta tashin k'amshin turaren wutar data saka yasa ta fita a falon ta rufo k'ofar.
Falon Hafsat ta shiga da sallama a bakinta, Munzeer da Aswan ne suka amsa a tare suna kallonta, murmushi ta sakar musu tana k'arasawa da fad'in "Sannanku?"
Da ladabi da girmamawa Aswan yace "Ina kwana aunty."
Da fara'a tace "Lafiya lau Aswan, har an shirya tafiya makaranta?"
Da ladabi yace "E aunty."
Munzeer ta tarawa hannu tace "D'an Abbansa yaya? An shirya ne?"
Tasowa yayi da dariyarshi ya mik'a mata hannun, sunkuyawa tayi tana shafa kanshi tana murmushi tace "Ina mamanka?"
Madafa ya nuna mata yace "Tana ciki."
Murmushi tayi tace "Kunyi karin kumallo ne?"
Girgiza kai yayi yace "Shi muke jira."
Mik'ewa tayi daga sunkuyawar tace "Bari na shiga ciki to na kawo maka naka na musamman ko?"
Jinjina kai yayi yana dariya yace "To aunty."
Hanyar madafar ta nufa sai kuma Aisha ta fito tana gyara jakar makarantarta a bayanta da alama sauri take, ba tare da tunanin komai ba Mimi ta sauko da kanta tana fara'a tace "Ina kwana Humaira."
Kallonta tayi tana gimtse fuska, wani wawan tsaki taja ta ci gaba da takawa, ta gabanta ta wuce ta shiga madafar tana fad'in "Amie mun kusa makara fa, har yanzu baku gama ba?"
Girgiza kai Mimi tayi ta shiga madafar ita ma tana tab'e baki a ranta tana fad'in "Kinyi da yar halak yarinya, akan tsohon ubanki zaki min tsaki?"
Tana shigowa suka had'a ido da Hafsat dake aiki tuburan, dukansu murmushi suka ma juna inda Mimi tayi saurin fad'in "Ina kwana aunty?"
Da fara'a sosai ta amsa da "Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?"
Jinjina kai tayi tace "Lafiya lau, aiki ake?"
Cikin sakin fuska tace "Wallahi, kinga yau kamar an d'auremu na rasa me ya tsayar damu."
Murmushi tayi tace "Allah sarki, yau da gobe kenan, bari na taimaka muku."
Kamar daga sama Aisha tace "Amie indai wannan matar zata saka hannu a abincin da zamu ci yanzu wallahi saidai na hak'ura da shi."
Da sauri Hafsat ta kalleta hankali tashe tace "Aisha kina lafiya? Me yake damunii ne? Wannan wane irin iskanci ne?"
Turo baki tayi haar da bubbuga k'afafu tace "Lafiya ta k'alau Amie, akan ta ne fa Abie ya daina son m没 har zai min auren wuri."
Zaburowa Hafsat tayi zata kwad'a mata mari sai kuwa tayi hanyar fita, Mimi dake k'ofar tsaye tana kallon Aisha da mamaki bata ankara ba ta bangajeta tana fad'in "Dallah malama matsa min ni."
Yanda ta had'a kanta da bango yasa Mimi sakin siriryar k'ara tana dafe k'eyarta dan ta ji zafi sosai, da sauri Hafsat tayi kan Mimi tana tambayar "Subahanallah! Mimi kinji ciwo ne?"
Daurewa tayi ta mayar da hawayenta ta k'ak'aro murmushi ta girgiza kai tace "Ba komai aunty, ki k'yaleta dan Allah."
A tsawace tace "Na k'yaleta fa kika ce? Aisha yarinya ce da har zata min d'anyan kai a gidan nan?"
Fita tayi a madafar a hassale, a sanyaye Mimi ta k'arasa kusa da mai aikin da take gaisheta ta amsa sannan suka ci gaba da aikin.
Hafsat na fitowa a fusace Aisha na daf da k'ofar fita tana ta kumburo baki, nunata tayi da yatsa tana fad'in "Abinda zaki min kenan Aisha? Wannan ita ce koyarwar dana miki? So kike ki nunawa duniya ni malalaciya ce kenan? Kina so ki fad'a da babban murya cewa ban isa dake ba?"
Cikin turo baki tace "Kiyi hak'uri Amie, amma faa ke ma kinsan gaskiya na fad'a, duk saboda ita ne komai yake faruwa."
A zafafe tayi kanta sai kuma Heezam ya fito daga d'akinshi shi ma a shirye, da sauri Hafsat ta kalleshi tace "Heezam kamo min hannun yarinyar can?"
Aisha na jin haka ta fita a guje hakan yasa Heezam kallonta sai kuma ya kalli Hafsat yace "Amie lafiya? Me ta miki yanzu da safe? Ban tab'a ganin b'acin ranki irin haka ba?"
Kamar zatayi kuka tace "Dole ne Heezam, yanzu duk abinda mahaifinku ya fad'a muku jiya ace bai shiga kan Aiaha ba, har ta tsaya tana wa Mimi rashin kunya kuma a gabana."
Girgiza kai yayi cike da rashin jin dad'i yace "Kiyi hak'uri, ina ga fa dalilin da yasa Abie yace zai mata aure kenan, kinsan matsalar Aisha kafuwa."
D'aga kafad'a yayi yana feso iska yace "Ni dama a shirye nake da tafiyata Madina, dan gari ne da nake mafarkinshi kullum tun ranar da Abie ya labarta min zai turani can karatu, dan haka ban d'auki hukuncin nan da zafi ba, ya min dad'i ni kam."
Wata yar k'wallar tausayinshi Hafsat ta matso tace "Allah ya maka albarka, Allah ya taimakeka ya haskaka maka neman iliminka."
Murmushi yayi yace "Nagode Amie."
Takawa ya shiga yi yana kallonsu Aswan yace "Ku tashi mu wuce kunsan Abie baya so mu tsayar da dreba yayi ta jiranmu ko."
Mik'ewa sukayi inda Hafsat ke fad'in "To abun karin fa?"
Kallonta yayi yace "Amie lokaci ya k'ure, kawai idan munje zamu samu abinda zamu sa a cikinmu."
Jinjina kai tayi tace "To shikenan, Allah ya tsare."
Shafa kan Munzeer tayi tana masa murmushi tace "A dawo lafiya ko yarona."
Bye bye ya mata suna daf da fita Mimi ta fito da sauri tana fad'in "Ku tsaya ku tsaya."
Tsayawa duk sukayi suna kallonta, bred ne ta saka musu soyayyen dankalin turawa a ciki da k'wai da tomate fresh, ninkeshi duka tayi a tissus tana mik'awa kowannensu tana fad'in "Ai ba zaku tafi da yunwa ba, taya za'a fahimci karatu?"
A kunya ce Heezam ya kalleta dan gaskiya kwalliyar data cab'a sai ya gan ta wani wal-wal-wal,