Showing 3001 words to 6000 words out of 185502 words

Chapter 2 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

476

bredin ta dinga yi har ta mik'e ta wanke hannayenta da sabulu ta koma d'aki, kayan jikinta ta cire ta saka doguwar riga mai taushi ta yadi, tana fitowa tayi zaune mamarta tace "D'ebo ruwan fa sai yaushe?"

Da sauri ta kalleta kamar zata fashe da kuka, saida ta turmuza k'afafunta alamar an takurata kafin ta mik'e bazar bazar ta d'auki bokiti tana gyara kallabin rigarta ta fita.

Har zai wuce akan babur cikin sanyayyar murya tace "Ina wuni *Bello*."

Tsayawa yayi tare da juyowa yace "Mimi, kina lafiya?"

K'asa tayi da kanta tana murmushi kamar ba da hushi ta fito ba tace "Lafiya lau."

Kallon bokitin hannunta yayi yace "Ya na ganki da bokiti? Wani wuri zaki tafi?"

Cikin muryar shagwab'a da take da tabbacin tana kayar da mazan yanzu tace "Wallahi Mama ce ta aikeni d'iban ruwa, kuma kaga dare yayi yanzu babu kowa a wuri, shine nake tunanin shiga gidanku na d'ebo."

Wani murmushi ya saki yace "Haba Mimi, kamar ki ace zaki d'ebo ruwa ki d'auko a kan ki bayan gamu a garin nan? Kinga koma gida ki zauna, dama gidan zan shiga yanzu idan na shiga zan saka yara su kai muku ruwan."

Da farin ciki tace "Kai amma naji dad'i, nagode sosai."

Murmushi ya mata yace "Ba komai." Juyawa tayi shi ma ya tayar da b芒bur d'in ya wuce gidansu da gida hud'u ne tsakaninsu, tana shigowa ta aje bokitin mamanta tace "Ina ruwan? Mimi ban san iskanci fa, yanzu cewa za kiyi babu ko kuma sun rufe gida."

Dariya tayi tace "Mama ki zuba ido ki gani za'a kawo miki ruwa adadin da kike buk'ata."



*Ahalin Aliyu Sharif*



Babban masallaci ne da a k'alla yake d'aukar dubbanin jama'a, ana sallahr juma'a da sallah eid a ciki, ginin ya tsaru sosai ya k'awatu, a duk ranar asabar masallacin kan cika tantsam da mutane saboda babba kuma shahararren malamin dake tafsirin Alqur'ani a wannan ranar, mutane daban daban kan zuwa dan sauraren wa'azi daga gareshi, a ciki har da manyan yan siyasa dan dama masallacin a unguwarsu yake a cikin gidan *Gaddafi*, da kuma manyan attajirai manyan k'usoshi a gwamnati da saurensu. Ac dake wuri da panka ya hana mutanen gurin yin gumi duk da ba yanayin zafi a ke ciki ba.

Teburin dake gabanshi tare da mai ja bak'i dake gefenshi a ciki yake da wayoyi manya da k'anana ana d'aukar recoding, sai d'an agaji guda a bayanshi da kuma wani mai tsaron lafiyarshi guda cikin bak'ak'en kaya da bak'in gilashi. A zahirance kyakyawa ne ajin da ba zai gaza hawa matakin farko ba, saidai kasancewarsa bafulatani yasa kana ganin zaka gane haka, a k'alla shekarunsa *arba'in da bakwai*, dan gemunshi ma har fari ke akwai wanda ya k'ara k'awatashi. Yanzu ma cikin raha da hankali da nutsuwa yake musu sharhin suratul *Noor*.

Kiran wayarshi aka yi dake hannun mai tsaron lafiyarsa ya kuma d'auka saboda ganin lambar daga babban gida ce, yana d'aukar muryar Hajia cikin kuka tace "Sheikh, kana ina ne? Jikin *Ashraf* ya tashi fa, ga mu nan clinique de *gazobi*."

Da sauri jami'in yace "Hajia muna tare da sheikh yana darasi, amma zan fad'a masa yanzu."

Cikin tashin hankali tace "To dan Allah kayi sauri."

Kashe kiran tayi hakan yasa jami'in matsowa ya sunkuyo kusan kunnenshi ya fad'a masa, da sauri ya kalleshi sai kuma ya sunkuyar da kan shi, ya jima haka kafin ya d'ago yayi gyaran murya, cikin nutsuwa da muryarshi mai taushi da sanyi da harshenshi mai gurgiri yace "A bisa wani babban uzuri daya taso min yanzu, zamu dakatar da darasinmu a nan saboda hali na ujila, da fatan zaku gafarceni, kira ne daga gida kan d'an uwana da baya da lafiya, muna barar addu'arku."

K'ok'arin mik'ewa yayi yana jin yanda masallacin aka d'auki hayaniya ana jefo mishi addu'a ta fatan samun lafiya ga d'an uwanshi, ta hanyar baya suka nufa tare da d'an agajin da kuma mai tsaronshi, suna fita ta k'ofar wasu daga cikin mutanen har sun zagaye k'ofar, kowa hannu yake mik'o masa yana son sai ya jajanta masa baki da baki, wasu kuma lambarshi suke son amsa saboda a dinga kiranshi. Dake hakan ba sabon abu bane saiya shiga k'ok'arin zillewa amma ina dole saida ya gaisa da wasu, da k'yar ya samu ya shiga mota dreban ya ja shi zuwa asibiti.

Suna zuwa asibitin kud'in clinique de gazobi suka fita a motar suna take mishi baya, saida aka fara fad'a musu d'akin da aka kwantar da shi kafin suka rankaya can, daf da zasu shiga ciki ya juyo tare da d'aga musu hannu alamar su jira shi, tsayawa sukayi suka hard'e a bakin k'ofar shi kuma ya shiga ciki.

Su hud'u ne a d'akin, mahaifiyar Asharf da shi Ashraf d'in, sai kuma yayar Asharf d'in wacce mata ce ga Sheikh d'in sai kuma k'annan Hajia, amsa sallamarshi sukayi inda idonshi ke kan Ashraf dake bacci hannunshi d'auke da k'arin ruwa, cikin nutsatsiyar murya yace "Ya jikin na shi?"

Cikin kuka Hajia tace "Jikinshi da sauk'i, sheikh wai yaushe ne za'a fitar da shi? Jikin Asharf ya fara bani tsoro fa, yanzu ciwon yana yawan taso mishi ba kamar da ba."

A hankali ya matsa kusa da ita ya rik'o hannun yace "Kiyi hak'uri Hajia, insha'Allah zai samu lafiya, har yanzu a kan shirye shiryen tafiyarsa nake."

Jinjina kai tayi tace "Allah ya sa." Da murmushi yace "Ameen, insha'Allah muna fatan haka."

D'an juyawa yayi ya kalli uwar d'akinshi, sanyin idaniyarshi abar k'aunarshi, murmushi suka sakarwa junansu kafin tace "Sheikh mun d'aga ma ka hankali ko?"

Girgiza kai yayi yace "Ba matsala, Allah ya bashi lafiya."

Ita ma a sanyaye tace "Ameen." Saida ya saci kallon Hajia kafin ya kalleta da kyau, da hannu da kuma ido da girarshi ya mata alamar "Ya ajiyata?"

Murmushi tayi tare da masa alama da motsa bakinta tace "Lafiya lau yake."

Lumshe ido yayi alamar jin dad'i, sunkuyar da kan ta tayi ita kam dan kunya, shiru d'akin ya d'auka na wani lokacin kafin Hajia ta kalleta tace "Ki tashi ku tafi gida tunda jikin nasa da sauk'i ko?"

D'an kallon sheikh tayi kafin ta jinjina kai alamar to, a hankali ya taka ya k'arasa daf da Asharf ya zauna bakin gadon, rik'o hannunshi yayi yana kallon kyakyawar fuskar Ashraf, duk da ba ciki d'aya suka fito ba amma yana bala'in son d'an uwanshi, sun shak'u sosai tun yana yaro, ladabinshi gareshi da kuma k'iriniyarshi suna birgeshi, kusan baya da aboki bayan yaron duk da kuwa ba tsaranshi bane, amma yanzu haka da zai samu sab'ani tsakaninshi da yayarshi na zaman tare, to shi yake ajiyewa tsakaninsu ya ja musu kunne.

Lumshe ido yayi kafin ya sake bud'ewa, addu'a ya shiga karantawa yana tofa masa kusan minti talatin, su kuma kallonshi suke dan bai d'aga murya ba bare su ji su amsa da ameen, dan haka suna ganin ya sakin hannun Ashraf suka amsa da "Ameen."

Mik'ewa yayi ya kalleta yace "Mu tafi." Kallonsu Hajia yayi yace "Saida safenku."

A nutse suke takawa masu tsaron na gaba shi kuma suna baya tare da ita, suna fita mai tsaron ya kama murfin mota zai bud'e mishi, d'aga mishi hannu yayi alamar a'a, dakatawa yayi ya koma mazauninshi, da kanshi ya bud'e mata ta shiga ta zauna kafin ya rufe ya zagaya d'aya b'aren suka bar asibitin.



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:49 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*3*


Kasancewarshi malami zai sa kayi mamaki idan kaga tabkeken gidan da mai gadi ya bud'e musu suka shiga, amma idan kasan margayi Alhaji Aliyu Sharif zaka tabbatar wannan ba komai bane, dan tsohon shahararren d'an kasuwa ne daya tara mahaukatan kud'i kuma ya mutu ya barwa magadansu, haka na su iyayen suma suka musu suka bar musu suka gaji nasu kason, haka kuma sheikh Abdul Waheed ba malamin ci da ceto bane, d'an kasuwa ne haka kuma a cikin gwamnati ma shi d'in mai bawa gwamna shawara ne akan harkar data shafi ilimi. Shigarsu k'ayataccen falon yasa yara tasowa da gudu suna musu oyoyo, da murna shi ma ya d'auki k'ananan yana rumgumesu a jikinshi, babbar cikinsu kam a hankalce ta k'arasa kusa da mahaifiyarta tana fad'in "Momy sannu da dawowa, ya jikin tonton?"

Da murmushi ta amsa mata da "Jikinshi da sauk'i, dan mun baroshi ma yana bacci."

Da nutsuwa yarinyar tace "Allah ya bashi lafiya." Da fara'a tace "Ameen."

Sauke yaran yayi yana kallon yarinyar yace "Uhm! *mamana* shi ne ko a kulani? Sai mamanki ko? To na yi hushi ma."

Dariya tayi ta matsa kusa da shi ta kama hannunshi tace "Abu, kayi hak'uri, ina tambayar jikin tonton d'ina ne."

Dafa kanta yayi yace "Ku masa addu'a kun ji, zai samu lafiya insha'Allah."

Da kai ta amsa masa tare da fad'in "Insha'Allah Abu." Murmushi ya mata shi ma yace "Masha Allah."

Kallon *Hafsat* yayi yace "Zan shiga ciki."

Da ido ta masa alamar "Ina zuwa." Wucewa yayi yana murmushi tare da cire babbar rigarshi irin ta malamai da bata da wuya sai hannaye kawai, kallon *Aisha* tayi tace "Eesha, ku je d'akinku ki taimakawa k'annanki su watsa ruwa su saka kayan baccinsu, dare yayi kin ji."

Da ladabi tace "To Momy." Kallon k'annanta tayi su uku tace "Muje."

Mai bi mata ne ya kalli uwar yace "Momy, amma ai ban da ni ko?"

Dariya tayi tace "Kai ai yanzu saurayi ne."

Murmushi jin dad'i yayi tare da wuce suka haye sama inda d'akunansu suke, mik'ewa tayi da k'yar saboda k'afafunta da suka kumbura sakamakon cikin dake jikinta na wata biyar ta nufi d'akin sheikh, falo ne mai zaman kan shi dake zagaye da litattafai na ilimi daban daban da littafi mai tsarki kala kala anyi jere dasu, kai tsaye d'akin baccin ta wuce ta samu har ya shiga wanka, zaune tayi bakin gadon ta d'aga muryarta tana fad'in "Shi ne ka shiga ka barni ko? Ai zaka koma ne dan da kan ka zaka min wankan yau."

Yana jin ta sai murmushi da yayi bai amsa mata ba, bai wani jima ba ya fito da rigar wanka a jikinshi, yana dariya, kama hannunta yayi yana fad'in "Muje na miki to, shikenan?"

Turo baki tayi tace "To me yasa zaka tafi ka barni?"

Murmushi ya sak茅 yi yace "A gafarceni to."

Murmushi tayi ita ma tace "To na gafarceka sheikh nawa."

Zip d'in rigarta ya ja zai cire tayi saurin cewa "A'a nagode, zan yi da kaina ai."

Lumshe ido yayi ya girgiza mata kai alamar a'a yace "Ki barni, ina so na samu ladar, zanyi koyi da annabina ne manzon rahama, yayi wanka tare da matanshi yayi raha da dariya dasu."

Jinjina kai tayi tace "To ai ni yanzu kunya nake ji, wannan abun fitowa yake sai nayi muni."

Dariya yayi sanda ya kalli cikin data nuna mishi, shafa kumatunta yayi yace "A rayuwar aure babu kunya tsakanin ma'aurata, karki manta addininmu shine addunin da yafi kowane kunya hasalima ya koyar da mu jin kunya, amma a bisa haka ya fayyace mana komai game da rayuwar aure da yanda zamu tafiyar da addininmu, manzon Allah (S.A.W) yafi budurwar data fara k'irgen dangin kunya, yanda take jin kunya ta kasa sakewa da mahaifiyarta ma, a cikin gidansu ta kan zama kamar marar gata ko bak'uwa, amma a haka ya warware mana addininmu, kama daga yanda zaka samu najasa a jikinka har zuwa yanda zaka tsaftaceta, saida ya fad'a mana, dan haka wannan cikin kar ya sa ki cuceni ko ki cuci kan ki, kin ji Hafsat."

Da kai ta msa alamar to, tana kallo ya cire mata kayan duk ya d'aure mata jiyoyin jikinta da k'aramin tambihinshi, hannunta ya ja zuwa ban d'akin ya shiga wankaceta soso da sabulu, saida ya gama mata suka fito, duk da d'akinshi ne amma a nan ya samu rigar baccinta ya saka mata, kwantar da ita yayi ya kalli fuskarta yace "Kiyi bacci kin ji, kin wuni ba kya jin dad'i yau hakan yasa na kai ki wajen Hajia, gashi alamu sun nuna a can ma baki samu hutu ba."

Murmushi tayi tace "To, kai fa?" Murmushi yayi shi ma yace "Zan kwanta, amma zan fara dubo yaran nan na gani."

Jinjina masa kai tayi ta bishi da kallo cikin doguwar farar rigarshi har ya fice a d'akin.



*Maryam*


Dake jiya saida Bello yasa yaran gidan suka cika musu kaf mazubin ruwa dake gidan yasa yau bata tsaya jiran ruwa ba, wanka kawai tayi ta shirya dan tafiya makaranta, fitowa tayi cikin hijabinta fari k'ar har k'asa rumgume da Alqur'aninta a k'irji, zaune tayi a kan tarmi tana kallon k'annanta dake cin d'umamen tuwo, yatsina fuska tayi tana ayyana ba zata iya cin shi ba, ta d'auko kud'in da mijin Maimuna ya bata Alhaji *Saminu*, idan ta je makaranta ta samu ko alala ta ci, fitowar mahaifinsu daga d'akin yasa ta saurin sauka daga turmin ta durk'usa kan ta a k'asa, saida ya tsaya gabanta cikin ladabi tace "Abba ina kwana."

Da fuska a washe ya amsa da "Lafiya lau Maryam, har an shirya?"

Jinjina kai tayi tace "Eh Abba." Kallon su Amir yayi dake cin abinci yace "Ku hanzarta to karku tsayar da ita."

D'an satar kallonshi Maryam ta yi a ran ta tana fad'in "Su ba yara ba ace sai na jera tare da su mun tafi?"

"Maryam." Mahaifinta ya kira sunanta, da sauri ta d'ago tana zuba mishi idonta, masha Allah, daga mahaifiyarya zuwa mahaifinta har k'annanta duk hallitarsu iri d'aya ce, dan kuwa mahaifiyarta ma har tafi mahaifin tsayi, dan shi ba zai wuce gwiwar Maryam d'in ba, k'annanta ma haka suke can cikin k'asa a haka kuma mai bi mata shekararshi goma sha hud'u, hakan yasa take matuk'ar kunyar tsayawa a tsaye idan iyayenta na tsaye, tana jin nauyinsu sosai da girmama halittarsu, shi ya sa bata iya tsayawa idan ba a hali na tafiya take ba. Cikin dattako *malam Adam* yace "Ku kula kinji, Allah ya tsare."

Jinjina kai tayi tace "To Abba, ameen." Kallon mahaifiyarsu yayi yace " *Rabi'a* zan fita, da wani abu ne?"

Shiru tayi kan ta a k'asa tana mai jin kunyar fad'a masa ba su da abinda zasu sarrafa da rana su ci, kunyar yaran yasa ta kasa yin maganar, lura da yayi yasa shi komawa d'akinsu, mik'ewa tayi ta bi bayanshi hakan yasa Maryam bin su da ido, saida suka b'acewa ganinta ta kalli k'annan nata, harara ta zabga musu tace "Wai sai yaushe zaku gama cin tuwon ne ku kuma? Sam ba kwa gajiya da had'iyar tuwo."

Tsaki tayi ta mik'e tsaye tana ci gaba da kallonsu, cikin sauri suka shiga turawa dan kar ta fara d'imarsu da k'ulli, suna kammalawa suka mik'e suka wanke hannayensu suka sha ruwa, daidai nan suka fito daga d'akin y'a nufi k'ofa uwar da duka yaran suka bishi da addu'a, yana fita suma suka bi bayanshi suka fita, suna gaba tana baya tana takonta a hankali a haka har suka k'arasa makarantar dake bayan gidansu.


*Asibiti*


Saida suka gama gaisawa ya samu kujera ya zauna yana kallon Ashraf dake zaune yana kurb'an shayi, murmushi suka sakarwa juna inda sheikh yace "Ya jikin na ka?"

Lumshe ido yayi yace "Jiki da sauk'i, ina so ma su sallami idan zai yiwu."

D'an hararenshi yayi yace "Gaggawar me kake? Wani abu kake shiryawa ne?"

Dariya Hajia tayi tace "Tambayeshi dai, ya manta jiya a some muka kawoshi nan."

Yanda ya tsareshi da k'ananan idonshi yasa Ashraf cewa "Shekh ka fahimta mana, zaman a nan babu abin da zai k'ara min ko ya rage min, na ji sauk'i kawai su sallame ni."

Rantsatsen rigarshi mai kama da alkyabba irin ta sarakuna ya d'an jawo daga gaba yana ci gaba da kallonshi, sanin ba zaiyi magana yasa Ashraf cewa "Wato kafi son nayi ta zama a nan ko? Saboda baka so na dinga zuwa gidanka ina damunka."

Murmushi yayi cikin taushin murya yace "Da zasu rik'e min kai d'in ai da naji dad'i, dan na gaji da zaryar da kake min a gida kullum."

Dariya Hajia da Ashraf suka yi inda ya kalleshi yace "To ba ga irinta ba, ni kam da zaka saka baki a sallameni, na rantse maka sai nayi budurwa gobe goben nan."

D'aga girarshi d'aya yayi kamar wani gogaggen d'an duniya tare da murmushin gefen labb'a yace "Da gaske?"

Saida ya had'e fuska yace "Ka sa a sallameni ka gani."

Cikin dariya Hajia tace "Sheikh kasa baki to, idan haka ta faru ai zan fi kowa farin ciki, watak'ila Allah ya dubeshi ya bashi lafiya sanadiyar auren."

Wata tattausar ajiyar zuciya ya sauke yana ci gaba da kallon Ashraf, d'an murmusawa yayi yace "Shikenan, amma idan sun ce da wata matsala ba zan takurasu ba."

Babu wanda yace wani abu har ya mik'e yana gyara babbar rigarshi ya fita, ya d'an jima kafin ya dawo musu da takardar sallama, Ashraf na murnar zai tafi gida sheikh na mishi dariya da fad'in "Kamar wanda ya aje mata hud'u."

Shi ma dariya yayi yace "Mata hud'u fa? Ai ni ra'ayina na yin mace d'aya ne, kuma ma me ya aikeni karambanin yinace hud'u? Bayan kai ma da ke ustazu d'aya gareka."

Wani k'ayataccen murmushi yayi yace "Ni ma ina nan ina nema, zan k'ara ne ai dan samun wannan tagomashin na masu mata sama da d'aya."

Da zolaya Ashraf yace "Kenan tare za muyi auren?"

Sake d'aga masa gira yayi wanda hakan ya zama jikinshi yace "Watak'ila."

Turo baki yayi yana hararenshi yace "Lallai ma sheikh d'in nan, wato zaka wa 'yar uwata kishiya kuma shi ne kake fad'a ma a gabana."

Wani murmushi yayi ya juya ya kalli Hajia dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login