Showing 18001 words to 21000 words out of 185502 words

Chapter 7 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

482

fito daga gidan hakan yasa ta kallon Asma'u tace "Zasu gane wani abu?"

Girgiza kai tayi tare da juya mata baya tana kallon titi, tyab'e baki tayi tace "Asma'u kar kisa na fara tunanin ke 'yar bak'in cikina ce."

Ita ma juya gabanta tayi daga kallonta, a zaman kuramen nan suka isa gida, babu wacce tayi wa yar uwarta sallama kowace ta shiga gida dan suna da tabbacin zasu shirya zuwa gobe a makaranta.


*Sheikh*


Sauri yake sosai dan ya fita masallaci da sunyi sallah a d'ora karatu kasancewar masallacin na shi ne dake manne da gidan, haka kuma ga asibitinshi dake kallon gidanshi wacce yake d'aukar nauyin ma'aikatan ana duba mutane kyauta, kawai zaka ciri kati ne da d'an abun da baiyi tsamari ba, amma daga maganar rashin lafiyar da zata kwantar zuwa mata masu haihuwa da yara k'anana duk kyauta ake dubasu. Suna alwala amma ya cikashi da surutu, har suka fito daga ban d'akin dake cikin falon zasu fita yana fad'in "Ustaz kana ji na? Wallahi da gaske nake fad'a maka, dama na ce maka zanyi budurwa yau ba? To na yi yanzu aiki ya rage naka ka nemo min aurenta."

Hafsat dake jinsu tana neman tashi tsaye ne ta kalleshi tace "Wai auren wasa ne aka fad'a maka da za kace kayi budurwar yanzu kuma a nema maka aurenta?"

Da sauri ya kalleta yace "Aunty Hassy bari maganar nan dan Allah kada kisa mijinki ya baud'e min, wallahi daga ganinta tana da hankali da nutsuwa, wai kin ganta kuwa? Ga mugun aji yarinyar na tabbata ba kowa take kulawa ba."

Da sauri ya mayar da dubanshi ga sheikh zaiyi magana sai kuma ya yi shiru yana sunkuyar da kanshi saboda k'ura masa ido da yayi, a hankali cikin gyara ma hularsa zama da nad'in dake kanta na farin rawani yace "Kai yanzu har ka tabbatar da sahihancinta ne?"

A marairaice ya kalleshi yace "Allah kuwa sheikh, yarinyar daga ganinta sam alamunta da yanayinta ba suyi kama da na wacce zata iya cutar da kowa ba."

Juyawa sheikh yayi cikin takon hanzari ya nufi hanyar fita, da sauri shi ma ya bishi yana fad'in "Ustaz, indai kana so na kana son Hajia to ka nema min auren yarinyar nan."

Ba tare daya juyo ya kalleshi ba yace "Ta fad'a maka tana sonka ne? Ko kuma dole za'a mata?"

Da murmushi yace "A'a ba haka bane, dama amincewarka nake buk'ata kan zaka nema min auren na ta, idan na samu yarda daga gunka shikenan sai nayi yak'i dan k'wato zuciyarta."

A daidai zasu shiga masallack suna cire takalminsu yace "Allah yasa alkairi, zan nema maka auren nata idan nayi bincike na gane yar manyan mutane ce, akasin haka kuma zaka hak'ura da ita *Asas*, ka yarda?"

Jinjina kai yayi alamar to shikenan, shigewa sukayi cikin masallacin ana ta kiran sallah, lokacin tayar da sallah nayi ya shiga gaba dan jan su ba tare da mai jiyawar ba, da kan shi yake d'aga sauti yanda zai jiyar da kowa musamman daya zama ga lasipika.

Suna kammala sallah aka shiga shirye shiryen karatu, cikin k'ank'anin lokaci aka had'a komai kamar yanda aka saba inda masu d'auka ma ana watsawa a kafafen sadarwa da gidajen tv da redio kowa ya shirya. A nutse sheikh ya fara bud'e katarun da muk'addima kafin su tashi a inda suka tsaya. K'arfe 08:10 suka kammala dan ma an amsa tambayoyi kenan, yana mik'ewa zai fita yan agaji da masu tsaronshi d'aya daga ciki suka shiga kakkareshi suna son mutane su gyara ya wuce, gashi k'ofar da zata fitar da shi ta baya kuma mai sadashi da cikin gida ne, gashi kuma yana son fita shi kad'ai ba tare da 'yan koren nan ba. Sosai aka rufe hanyar fitar masu tsaro na ta k'ok'arin a bud'a hanya ya wuce, musamman matasa sune a sahun gaba kowa burinshi su gaisa wasu kuma takardar tambaya ce da su suna son sai sun bashi hannu da hannu.

Allah ne ya so shi ya rufe musu ido sanda ya kutsa ta cikinsu ya fice a masallacin ba tare da ma sanin jami'an ba, bai kuma tsaya komai ba yayi gaggawar fad'awa cikin gida, kai tsaye wajen motoci ya wuce inda ya d'auki wata jibgegiyar Honda crv ya danno hancinta waje sanda mai gadi ya bud'e mishi k'ofar yana bin shi da addu'a, har k'ofar gidan suka fito cigiya mmai gadi na fad'a musu sai hankalinsu ya kwanta tare da tunanin kuma ina ne sheikh zai tafi da baya buk'atarsu? A k'ofar gidan duk suka gyara tsayuwarsu da jiran ya dawo su tabbatar lafiya lau yake.


*Maryam*

Idar da sallarta kenan mahaifinsu ya shigo yana kiran sunanta, tasowa tayi daga kan tabarmar ta durk'usa kanta a k'asa tana fad'in "Abba gani."

Cikin fad'a ya shiga fad'in "Mimi me mahaifin yaron nan yake fad'a ne? Me ya had'aki da shi da suka ce sun hak'ura da tura kayan? Wani abu kika masa na rashin kunya ko?"

Girgiza kai tayi murya k'asa k'asa tace "Abba babu abinda na masa."

A tsawace yace "To me yasa suka ce sun fasa? Yace ke da kanki kika ce ba kya son shi."

Shiru tayi kanta a sadde ba tace komai ba, a zabure ya matso kamar zai daketa yana fad'in "Ba dake nake ba kina ji na?"

Da sauri ta d'ago tace "Abba ni bana son shi ne."

Baki sake ya shiga kallonta yace "Iyeeeeh! Ba kya son shi fa kika ce? Kuma kika kawo mana shi gidan nan har muka shiga maganarku."

Turo baki tayi tana kunkuni, da sauri ya k'arasa duk'awa ya d'auki takalminshi yana fad'in "Kinga 'yar butan uban nan..."

Da gudu ta shige d'aki tana fashewa da kukan shagwab'a, girgiza kai mamanta tayi tace "Allah ya kyauta."

Shi kam tsaki yayi tare da k'arasawa wajen Yaseen dake kwance yace "Har yanzu jikin nashi da zafi?"

A sanyaye ta sake tab'a goshin Yaseen tace "Da zafi malam, ko zamu kaishi asibiti ne? Ina tsoron zazzab'i wallahi musamman ma na dare."

A tausashe shi ma yace "Rabi'a ta ina zamu fara to? Abinda muka ci ma waccen ja'irar ce kika ce ta bayar da kud'in data samu a hannun yaron da muke tsammanin zai zama mijinta, yanzu kud'in taxi ma da zata kaimu asibitin kawai bana da shi."

Jinjina kai tayi kanta a k'asa, laluba aljihunsa yayi ya mik'o mata wasu canji yace "Kinga karb'i wannan, ba wa Mimi ta karb'o masa ko parac茅tamol ne ya sha zafin ya rage, bari naje gidan Iya Delu na ga idan malam na nan ba zai rasa wani taimakon da zai mana ba."

Hannu biyu tasa ta karb'a ta bishi da kallo har ya fita, a sanyaye ta k'wala kiran Mimi dake d'aki, tana fitowa da k'aton hibajinta fari na makaranta da tayi sallah da shi, kud'in ta mik'a mata tace "Inji mahaifinki ki siyo parac茅tamol a bawa Yaseen."

Karb'a tayi tare da komawa d'akin ta d'auko sabuwar wayarta da har yanzu bata bari kowa ya gani ba, ficewa tayi a gidan ba tare da ta kula kowa ba.


***************

Tsaye tayi bakin titin tana jiran shawagin ababen hawan ya tsagaita ta samu ta tsallaka dan ta isa ga mai shagon dake siyar da maganin, ta jima a wurin kafin tayi nasarar tsallakawa ta siyo ta juyo. Watak'ila Allah ne ya k'addara had'uwarsu, shiyasa ma ya fito shi kad'ai har ya buk'aci ruwa dan mak'oshin shi a bushe yake, gefe ya paka motar ya tsallaka titin ya siyo swan water, zai tsallako ya dawo ne ita kuma ta k'etara ta siyo maganin. Tunda ya ganta ya gane wacece, tsaf ya shaida kamanninta da ita ya had'u da ita na farko, babban abun da ya masa dad'i bai wuce ganinta da yayi a suffar daya fara ganinta a wurin sabkar nan ba, dan tun daga k'asa ya kalli k'afafunta da ake gani da k'yar saboda girman hijabin, gashi da k'yar take kallon gefe da gefe ba irin idonta a tsaye yake a kan titin b芒, dan har rintse ido take ko ta kawar da kanta idan wani abun hawan ya hasketa sosao. Hakan yasa ya ji cewa lallai 'yar babban gida ce (yar masu tarbiya).

Da kallo ya bita har ta wuce ta gefenshi ta siyo magani ta dawo bakin titi, yanzu haka tsakaninshi da ita bai fi tako biyar zuwa shida ba ya isar dashi gareta, amma tunanin rashin dacewar yi mata magana a kan titi, da kuma hangen ta yanda zata kalleshi yasa duk sai yaji gwiwarsa tayi sanyi. Amma dake zuciya da abinda take so kuma take muradi, sai yaji a ranshi ai kamar dama ce da zaka san asalin d'abi'ar dake lullub'e a cikin zumbulelen hijab d'in nan, hakan yasa shi takawa a nutse tare da d'an sakin jikinshi ya b'oye k'irarshi ta kakk'arfan dattijo har ya tsaya gefenta, shi ma kallon titin yayi cikin wata daddad'ar murya kuma sanyayya yace "Bayan nema miki amincin Allah, ko zaki iya kawo hannunki na k'etaraki?"

A hankali ta juyo tana yatsina fuska alamar za tayi halin na ta, amma ganin Sheikh Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif ya saka ta waro idonta tare da bud'e bakinta, murmushi ya sakar mata sanda suka had'a ido tare da cewa "Sannu."

Rufe bakinta tayi gam tare da yin k'asa da idonta, a hankali har ta sauke kanta k'asa tana d'an jujjuya kanta cikin siririyar murya tace "Assalama alaika, ina wuni?"


Da mamaki ya kalleta, mamakin shin bata ganeshi bane? Yasan dai fuskarshi ta gama garin nan da kewayenshi baki d'aya, ko baku da telebijin zaka iya ganinshi a telebijin d'in wasu, idan ba a nan ba kuma ga waya data game ko ina, wa'zinzikanshi masu tsayi da gajeru suna cikin wayoyin mutane dayawa, idan ka tara mutum goma zaiyi wuya ka kasa samun karatunshi a wayar mutum biyar ko ma sama da haka. Kowa yana son ya ganshi, kowa ya ganshi haba-haba yake da son su gaisa har su tattauna ko na minti d'aya ne, dan hakan ya zama abun alfaharin wani ko abun nishad'i.

Amma ita ta kalleshi da fari kamar zatayi mamaki amma kuma sai ta wani d'auke kai tace wai wani sannu a k'arshe. D'an d'auke kanshi yayi daga kanta ya kalli titi yace "Muje, karki yarda na barki a nan, hakan zai jawo miki kwana a bakin titin nan, ki saka k'afarki a inda na d'auke tawa."


Da sauri ta kalleshi da tunanin shi ne kuwa? To me zatayi? Tayi yanda yace ko kuma shi ma ta d'an gurza mishi ne kamar sauran? Wata zuciyar ce tace da ita "Malam ne fa! Kiyi yanda yace."

Sake kallonshi tayi ta kalli titin a hankali ta d'aga kan ta tana jinjina shi tace "...


Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.

Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.

Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.

_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._

_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_

Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ



*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:51 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.

Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.

Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.

_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._

_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_

Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*8*


Sake kallonshi tayi ta kalli titi a hankali ta d'aga kan ta tana jinjina shi tace "To."

Tana kallo sheikh ya fara kutsa titi a wani gadarance, motocin dake kai kawone suka shiga rage gudu wasu dan ganin mutum na wuce kuma ko kallonsu baya yi gabansa kawai yake kallo, kamar wutsiya haka ta ji tana biyarshi har suka k'etara, wani numfashi ta sauke tana kallon k'eyarshi, tana ganin zai juyo tayi saurin yin k'asa da kanta tace "Nagode, sai anjima."

Zata gifta ta wuce yayi saurin cewa "Dakata."

Cak ta tsaya amma kan ta a k'asa, dan fatanta d'aya ne su rabu ba tare da yace ga abinda tayi da bai kamata ba har ya shiga jawo mata ayoyi da hadisai, ita kam sauri take bare ta tsaya ta saurareshi. Hakan yasa ke iya k'ok'arinta wajen ganin ta sauke idonta k'asa karsu had'a ido, sosai take k'ok'arin yin sanyi har tana ta wasa da maganin a cikin hijab d'inta, ta nutsu sosai ta kuma bashi hankalinta matuk'a, ta yanda duk wanda ya ganta a lokacin zaiyi zaton ba ita bace, zaka d'auka tsuntsu ne a kan ta kuma aka saitata da bakin bindiga idan ya tashi a bakin ranta.

Ta b'angaren shi ma kallo yake sake k'are mata duk da dai yasan bai dace baa kan titi,saidai yana son sanin wata makama dazata isar dashi ga ahalinta, a lokacin da zai nemi aurenta garesu kuma shari'a ta bashi damar ya kalleta son ranshi dan ya tabbatar komai ya masa. A sanyaye cikin muryar nutsuwa yace "Ya sunanki?"

Saida ta gilgid'a kanta kamar k'adangaruwa tana sake kwantar da murya tace "Maryam."

D'an murmushi ya saki ya furta "Masha'Allah, *Ryam*, ina ne gidanku?"

A hankali ta d'ago ta kalli fuskarshi, amma sai taji kamar fuskar babanta zata kalla daga tsaye, sai kawai ta sunkuyar da kai tana jin gabanta na wani dum dum dum. A d'an kallon nan ta fahimci wani irin kwarjini da haiba dake tattare a fuskar mutumin, ashe dai yayi arha ne sosai da har suke iya had'a kallon fuskarshi a majigin wayoyinsu ko kuma telebijin, wani babban abu data fahimta a game da dattijon shi ne ma'abocin iya kwalliya ne, ko a wa'azi ka ganshi tsaf tsaf cikin d'aukar ado, yau kam data ganshi a zahiri saita sake tabbatarwa, gashi dogo da kuma wata murdadd'ar sura a cikin manyan kayan nan, uwa uba k'amshin da yake zubawa na d'aukar ran bawa ya killace shi, wani irin k'amshi ne mai k'arfi da sanyi ga mai shak'arshi wanda hakan ya tabbatar mata turare ne irin na manya masu tsadar nan.

Saida ta had'e yawu sosai kafin tace "Nan kwana."

Kallon hannunta yayi da tayi nuni dashi daga cikin hijabi ya kuma kalli kwanar, bai gane komai a kwatancen ba dan haka yace "Ya sunan mahaifinki?"

Da sauri ta d'ago kai sai kuma tayi k'asa da shi, cikin raunin murya da rawar murya kamar zatayi kuka tace "Dan Allah *Abdul* kayi hak'uri idan wani laifi nayi kar ka fad'awa Abbana, ka fad'a min ni zan gyara kuskure na wallahi, ba'a sani na bane nayi."

Rigiji-gabji! Shi dai da kan shi shine yau aka kira a gabansa da Abdul? Hakan ma k'aramar yarinyar daya tabbatar ko ta girmi Eesha shekarun basu wuce d'aya zuwa biyu ba, tun yana shekara ashirin da biyar a duniya ya rasa duk mutanen da zasu iya kallon cikin idonshi, a wannan shekarun na shi akwai masu daka mishi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login