Showing 30001 words to 33000 words out of 185502 words
*11*
Ko da Abba ya shiga gida kam ya kalli mama yace "Ina Mimi ne?"
Kallon Amir tayi sannan ta kalleshi tace "Tana gidansu Asma'u har yanzu."
Shi ma kallon Amir yayi yace "Je kira min ita."
Gyad'a kai yayi ya mik'e ya fita, 'yar kujerar robar da Amir ya tashi ya zauna yana fad'in "Bak'o na yi yanzun nan, kai uwata da kwashe-kwashe ake, ni ko a ina ta kwaso farin jinin nan? Yarinya kamar wata 'yar sarauta."
Wani murmushi Mama tayi ta saci kallonshi tace "Farin jini ko shirme, hauka ke damunta yarinyar nan."
Girgiza kai yayi yace "Harda farin jini ga uwata, ki duba ki ga ba dan bud'e mata ido da nayi ba da yanzu gidan nan bai zama dandalin tara kowane jahili da sakarai ba?"
Yar dariya tayi tace "Allah dai ya shirya mana ita."
Da fara'a ya amsa da "Ameen." D'orawa yayi da "Yanzu fa kam indai har ba zata saka shirmen nan da ta saka game da lamarin yaron nan Mas'ud ba, to Mimi kam ta dace da miji na gari mai hankali."
Cike da tsantsar damuwa Mama tace "Ni wallahi a tsayar da ranar aurenta shi zai sama min kwanciyar hankali, dan lamarinzamanin nan da rayuwar da Mimi ta saka kanta tana kayar min da gaba."
Jinjina kai yayi yace "Ai dai kin shirya aurar da ita ko?"
Sunkuyar da kai tayi ba tace komai ba, murmushi yayi yace "Indai har komai zai zo mana da sauk'i, to insha'Allahu auren uwata ba zai wuce wata d'aya da rabi ba, dan ni kaina bana son ganinta a k'yal-k'yal d'in nan, tun muna sanin inda take samu wata rana zata rufemu ta bai-bai, duk da muna shaidar halayenta amma ai yaro ka haifesa ne baka haifi halinsa ba."
Cike da tabbaci tace "Tabbas hakane, Allah ya mana jagora."
"Ameen." Ya fad'a a dai-dai sallamar Mimi da Amir a tare, amsa musu sukayi har suka zuba mata ido tana sunkuyawa tun bata k'araso garesu ba ta durk'ushe, kusan a tare suka saki murmushin jin dad'in yanda Mimi take matuk'ar girmama su, tunda tayi wayo ta mallaki hankali ta daina tsayawa a sanda suke tsaye, dukansu hakan na musu dad'i fiye da kima kawai dai basu tab'a nunawa bane, saidai kullum suna mata addu'ar Allah ya bata yaran da zasu mata biyayya ita ma fiye da yanda ta musu.
Cikin nutsuwa Abba dake kallonta yanda kanta ke k'asa yace "Mimi, kinsan wani yaro mai sunan *Ashfar*?"
Da sauri ta d'ago kai sai kuma ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Mama dasu Yaseen duk tintsirewa sukayi da dariya hakan yasa shi rarraba ido yana kallonsu, cikin had'e fuska yace "Wai lafiya dariyar ku kuma?"
Cike da kunya mama tace "Malam ai sunan ka fad'a ba daidai ba, ina kyautata zaton Ashraf ne ba Ashfar ba."
Sai lokacin shi ma ya ma kan shi dariya yace "To ni na sani ne, suna ne gashi nan dai idan uwaye suka saka ma yaransu."
Kallon Mimi yayi yace "Kin san shi ne?"
D'an sunkuyar da kai ta sake yi tace "E Abba."
Tsareta da ido yayi yace "Ya zo yanzu gidan nan, kuma izinin neman zuwa wajenki yake, shin kin amince da haka?"
Shiru tayi saida ya sake cewa "Kin amince?"
A hankali ta jinjina kai alamar eh, shi ma jinjina kai yayi yace "Shikenan tashi kije, zan d'anyi bincike a kan yaro na k'ara sanin halayenshi duk da dai d'an babban gida ne, gashi d'an manyan mutane kuma jinin malamai, amma ki sani uwata wannan karan ba zaki min iskancin nan ba, wallahi kika sa na shiga maganar nan kika sake kunyata ni Mimi sadakarki zan bayar."
A zabure ta d'ago tace "Sadaka Abba?"
Yatsina fuska yayi yace "K'warai kuwa, kina shakkar hakane? Ki jaraba ki gani."
Shiru tayi sai mama dake murmushi, tana so ta ce a bayar da sadakar ta ta ai zai fi, amma kunya da kuma girmama sunan sarakuwarta musamman da ya zamana a gabanshi take, Abba ne yace "Tashi ki shiga ciki."
Mik'ewa tayi zata shiga ya bita da kallo yana fad'in "Uwata ba dai zaki daina saka wannan sangen ba ko?"
Juyowa tayi ta durk'usa tace "Abba na daina fa, kawai idan zan shiga gidansu Asma'u ne ko aunty Maimuna nake sakawa fa."
Jinjina kai yayi yana kallonta ta mik'e ta shige d'akin kamar ta shiga taka rawa tsabar farin ciki.
*Yau* alhamis bbu karatu, hakan yasa tunda safe tayi shara da wanke wankenta ta kammala, tana idawa gaban mama ta durk'usa tace "Mama bani dala arba'in zan siyi k'osai da bredi nayi kari."
Wani murmushi Mama tayi tace "Ina ce jiya kinga tuwo aka dafa? Sannan kinga miyar da aka yi a matsayin mahad'in tuwon? Shi ne kike neman dala arba'in a hannu na?"
Girgiza kai tayi tace "Mimi idan ina da dala arba'in d'in da zan baki ai zan iya taimakawa mahaifinku ta hanyar yi mana cefanai me kyau muyi miya."
Wani huci ta sauke da tunanin mafita, ita fa tana da kud'in matsalar tambayar da zata sha yasa take b'oyewa, d'an kallon maman tayi tana karkare akaihunta dake jikin gajerun yatsunta tace "Mama to bari na ga ba zan rasa ba kam a jakata."
Mik'ewa tayi ta shiga ciro jakunkunanta masu kyau dake jikin hannun gado, zaune tayi ta shiga lalubarsu tana zazzagewa kamar gaske, Abba ne ya shigo da sallama d'akin suka amsa, shigowa yayi yana kallonta yana fad'in "Ke kuma lafiya? Me kike nema?"
Cikin ladabi tace "Abba dala arba'in nake fatan samu a nan."
"Me za kiyi da ita?" Ya tambaya kai tsaye, amsa ta bashi tana ci gaba da lalabawa da fad'in "Abba abun kari zan siyo."
K'uri ya mata da ido, duk da yasan halin Mimi tana da saka kanta a uku a wasu lamura, amma maganar tuwo kam tunda yarintarta ne bata son cin shi, shiyasa basa matsa mata da sai ta ci d'in, saidai yana tsoron yanayin rayuwa, baisan ina rayuwa zata kai ta ba nan gaba, ya zatayi kenan? Idan fa su iyayenta sun d'auka wani ba zai d'auki haka ba, laluba aljihunshi yayi ya ciro talatin yana fad'in "Karb'i nan, je ki siyo abinda zaki ci."
Kallonshi mama tayi tace "Bata kayi wai?"
Shiru yayi yana kallon mimi data mik'e da sauri ya ta d'auki hijab ta saka ta fita, k'arasa shiga yayi ya zauna bakin gadon da kyau yana fad'in "To ya zamuyi in ba'a bata ba? Ta fita waje ta nemo muke so? Ai kinfi kowa sanin bata cin tuwo, hakan ba dan d'aukarwa kai bane ko kuma k'arya, hakane take tun fil'azal."
Numfashi Mama t sauke tace "To yanzu daka bata su kana da kud'in ne?"
Girgiza kai yayi yace "Allah zai dubemu ya bamu wasu insha'Allah."
Jinjina kai tayi tace "Allah ya bud'a mana."
"Ameen." Ya amsa dashi kafin ya mik'e yace "Zan fita yanzu, insha'Allah zuwa anjima zan dawo na kawo muku abinda ya samu."
Nan ma jinjina kai tayi tace "Allah ya bada sa'a, Allah yasa a dace."
Amsawa yayi da ameen ya fita a gidan, kwanar daya shiga anan ya samu Mimi tsaye bakin kaskon mai suyar k'osan, murmushi ya saki ganin ta wani d'aure fuska ta dafe k'ugu, yasan saboda su Maryam da su Na'ima na wurin ne dan basa shiri ko kad'an. Har saida ya kawo daf da ita zai wuce ya kalleta yace "Mamana da an baki ki wuce gida kinji."
Sai lokacin ta farga dashi hakan yasa ta saurin sunkuyawa tace "To Abba."
Wucewa yayi ita kuma ta mayar da kallonta ga mai k'osan, su Na'ima kam bushewa sukayi da dariya har da tab'awa inda Maryam ke fad'in "Wa ya ga d'an k'wak'ur, dunk'ul-dunk'ul kamar zai shige a k'asa, a haka kuma aka haifffffffff..."
Saukar marin daya zauna a kumatunta ne yasa ta jan harafin na k'arshe, bata gama fahimtar me ya sauka a kan ta ba Mimi ta kuma kifa mata wani marin, tuni ta canza yanayinta daga nutsatsiyar nan zuwa mahaukaciyar k'arfi da yaji, dan kuwa bakin wuta ta jawo a cikin murhu ta shiga tik'awa Maryam tare da cakumar hijabinta. Cikin tashin hankalin samarin dake gefe zaune da kuma mai k'osan duk sukayi kansu, dan Na'ima na ganin haka ta daka da gudu ta shige wani gida tana fad'in ta kashe Maryam, da k'arfi Bello ya karb'i iccen hannunta daya rage babu wuta a jikinshi yana fad'in "Haba Mimi da hankalinki, me ye haka? Me ya had'aku?"
Kafin ta bashi amsa muryar wani saurayin ta daki ku'nuwansu yana fad'in "Inna lillahi! Ta kashe yar mutane fa."
Duk kallon Maryam sukayi da zafin duka da iccen wutar nan yasa ta fad'uwa a sheme, dan hijabinta ma duk yayi shaidar ya ci wuta, kafin ka ce kwabo wurin har an taru daddazon jama'a, yanda ake ta cacar maganar ana tuhumar Mimi yasa mai k'osan ne cewa "A'a fa! Domin Allah yaran nan basu da gaskiya, ba dan basu da tarbiya ba ai iyaye sun wuce gaban wasa, kuma hallitar iyayen Mimi ai Allah ne ya hallicesu haka, shi ne suka tsaya suna mishi dariya harda shak'iyanci saboda ya wuce ta nan, ni fa ban ga laifinta ba wallahi 'yar halak kenan."
Ruwa aka shafawa Maryam ta farfad'o tana fashewa da kuka da zagin Mimi tana fad'in sai ta rama, Mimi kam uwar k'asaita da isa da fad'in rai, a lokacin da kakar Maryam ta iso lokacin ta matso kusan Maryam d'in tace "Wallahi ba dan anyi gaggawar k'watarki ba, da sai na miki wanka da ruwan man nan, na kasheki na kashe banza wallahi."
Juyawa tayi ta shiga takawa da k'arfi har k'irjinta na wata nutsatsiyar kad'awa a cikin hijabinta, tsuguno tayi gaban farantin k'osan da aka kwashe ta jawo farar leda, a nutse ta shiga k'idayawa kanta k'osan har ta zuba daidai kud'inta, mik'ewa tayi ta kalli mai k'osan ta aje kud'in akan kujerar katakon ta tace "Ga kud'in nan, na talatin na zuba, ko d'aya ban k'ara a kai ba."
Cikin takon izza kamar wacce ta ci kwalliya ta shiga takawa har ta k'arasa gida ta barsu nan ana cecekuce, tana shiga hannayenta ta wanke sosai ta d'auki ledar k'osanta ta shige d'aki, yanayinta sam bai nunawa mama wacce wani abu ya faru ba, dan haka bata tambayeta komai ba sai kallonta da take jefi jefi tana cin k'osan da d'a-d'aya, hayaniyar Zara ta ji da alama dai biyota sukayi a kawo shedarta gida, dan har kukan Maryam take ji wiwi, a sauk'ak'e tayi murmushi tace "Hummm!"
Mama da taji abun a tsakiyar gidansu fitowa tayi dan ta d'auki murya, abun kamar wasa sai kuwa tsohuwar nan Zara ta d'aga musu hankali, dan ta dage sai an bi mata hakk'int dan an ga ita marainiya ce, in ba haka ba kuma zata yi k'arar Mimi wajen yan sanda. Mama baiwar Allah wacce da k'yar ma take kallon ciwon Maryam d'in dan doguwa ce ita ma ta shiga bata hak'uri da jajantawa ganin duk inda jikinta ya samu bakin wutar nan ya fara d'urar ruwa ya mata bororo, saida makwabta suka shigo suka tayata bata hak'uri amma fa ta ce zata jiran uban Mimi ya dawo saita nuna mishi abinda ta ma Maryam.
Duk hargagin da ake tana d'aki zaune tana jin su, Mama kuma kawaici ne ya hanata shigowa ta mataa magana, saida aka ci aka sid'e mama ta shigo tana k'are mata kallo, bata yarda ta d'aga kai ta kalleta ba, sai ma mik'ewa da tayi ta fito ta jefar da ledar k'osan ta d'ibi ruwa ta shiga wanka.
Saida ta gama ta shigo d'akin ta gama shafa mai ta jawo akwatin k'arfenta tana duba kayan da zata saka ta ji mama tace "Mimi kin kyauta yanzu?"
Ba tare data juyo ba tace "Mama, karki shiga zancen nan dan Allah, ba Maryam ba wallahi ko waye a garin nan ya nemi raina min iyayena sai na illatashi, saidai a kasheni ni ma."
Tsuru ta mata da ido tana kallonta ta mik'e tana k'ok'arin saka pant tana kare jikinta da zanin data d'aure k'irji, tsaf ta gama shirinta cikin doguwar rigar atamfa mai kyau, hoda kawai ta shafa da d'an man leb'e kafin ta kashe d'aurin d'an kwalinta, hijabinta ta d'auka bleue wanda ya dace da kalar atamfar ta saka takalmi masu kyau ta kalli Mama tace "Mama ni zan wuce, baki da sak'o wajen Iya?"
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, bata hanata fita ba dan duk alhamis dama ta kan je gidan kakarta data haifi mamanta ta wuni a can, ranar juma'a kuma ta kan yi wanki ne sannan ta shiryawa kayanta zamansu a cikin akwati, hakan yasa take da tsari a kan komai. Girgiza kai tayi tace "Ki gaida Iya, nima zan shigo gidan watakila gobe insha'Allah."
Jinjina kai tayi tare da d'aukar jakarta mai kud'i da kuma wayarta ta fita, unguwar kam tayi shiru a lokacin dan yara duk sun tafi makaranta, a nutse ta shiga takawa a k'afa dan ba nisa ne da gidan ba gaban islamiyarsu ne kad'an.
Tana k'arasawa gidan da sallama ta shiga a k'ofar tana fad'in "Salam salam, ina tsofaffin gidan nan wai? Har yanzu suna nan da ransu?"
Iya Delu dake k'ofar d'akinta zaune ne ta tarbeta da fad'in "Uwarki ma sai ta mutu ta barni ni da mijina."
Dariya Mimi tayi tana k'arasawa gareta tace "Haba dai Iyeye, ina kika tab'a ganin haka? Ai mutuwa dole ce ko?"
Takalminta silipas ta d'auka zata jefa mata daidai fitowar malam daga d'aki yace "A'a! A'a karki fara."
Da shagwab'a Mimi ta k'arasa gareshi ta rik'e hannunshi kan ta a kafad'arshi tana fad'in "Ranka shi dad'e ka gani ko? Na fad'a maka matarka bata so na."
Kallon Iya yayi yace "Ba sa茂 kin fad'a ba na gani da idona, ke dama haka kike mata?"
Kallon Mimi yayi yace "Amaryas ya kike so nayi da ita?"
Murmushi ta saki ta Iya tace "Kin gani ko? Ki bani hak'uri saina yafe miki, inba haka ba kuma zan sa mijina ya yanka miki ticket."
Dak'uwa ta mata tace "Kin jima baki saka d'in ba, dama fa ina cike da haushinki yarinyar nan."
Dariya tayi ta kalli malam tace "Malam wai dan ban mata wanki ba a ranar, kuma fa sai da taga nayi lalle kawai zata ce na mata wankin tsofaffin kayanta, amma ynzu ba gashi na zo ba sai nayi."
Murmushi malam yayi yace "Ai idan ma ba zaki iya ba ki bari idan na dawo na fansheki."
Girgiza kai Iya tayi tace "Kana iya wankin dama kake barina na wanke maka na ka kayan?"
Dariya sukayi sai Mimi da tace "To ai saboda aikinki ne dama, kuma lada kike samu."
"Fad'a mata dai amayata." Ya fad'a harda bata hannu suka tapa, lokacin kawai suka nutsu suka gaisa sosai tare da tambayar iyayenya, saida suka gamsu kafin malam ya musu sallama ya fita suka bishi da addu'a, saida ta ga b'acewarshi ta d'auke kanta tana tunanin duk yanda akayi shi ne ta yi, shiyasa ta zama doguwa a cikin iyalinta, dan ita dai shi ne dogo a cikin kakaninta, wacce ta haifi mamanta ma wadarce yar duk'ul, wanda suka fi mahaifinta ma dukansu gajeru ne. Dan kakanin na ta ma sun bata labari dalilin dagiya da kakanta yayi ya auri Delu (wacce ta ke bin maza uku ko sama da haka a haihuwa) yasa duk danginshi suka juya mishi baya, dan a lokacin ana canfa komai ne ana ganin aurensu ba alkairi bane, hakan kuma zai jawo musu gauraya zuri'a da masu gajeruwar hallitar nan, amma gashi suna zamansu lafiya har suka haifi yayar mamanta wacce uta ma haka take gajera mai sunan *Sahura* sai kuma *Shapi'atu* sannan mamanta ita ce k'ara.
Cire hijabinta tayi tana zaman kan tabarmar da fad'in "Iya me kika aje na ci ne gidan?"
Hararanta tayi tace "Komai, uwar kwad'ayi."
Turo baki tayi amma ba tace komai ba dan a lokacin tana jin wayarta na vibrations wacce ta kunna a kan hanya, jin shiru yasa Iya cewa "Bari dai na d'auko miki d'umamen tuwo, tunda na ga yau alhamis zaki zo na tanadar miki shi."
Dariya tayi tace "In dai tuwo ne Iya ki ci abun ki kam."
Dariya kawai Iya tayi ba tace komai ba, jim kad'an ta fito daga d'akin ta mik'o mata langar (kwanon samira馃槶馃槬 a da fa sai yar g芒ta ake ma jere da su, ynzu kuma yar gatar ma k'walele suke mata saboda tsada馃槣), karb'a tayi tana bud'ewa, da sauri ta kalli Iya tace "Iyeee! Iya dad'i kuka ci ne jiya?"
Zaune tayi tana murmushi tace "Gashi kuma ke ma zaki ci ba."
Aje kwanon tayi gabanta tare da saka hannu ta d'auko tsokar naman ta jefa baki, duk da girkin tsofaffi ne amma dad'in ma na musamman ne, dan daga jin d'and'anon zaka san a nutse aka yi aikin, babu k'arni ko kad'an saboda yaji kayan k'amshi ga kuma uwar daddawar da aka saka hakan yasa shi zama kamar naman kai.
Tsaf ta cinye naman tana jin kamar kar ya k'are kafin ta mik'e ta shiga d'akin, saida ta saka wayar a silent sannan ta shiga aikin gyarawa Iya d'akinta kamar yanda take yi a kowane sati, saida ta gama ta had'o kayan wankin ta fito dasu waje, sabulu Iya ta bata inda ta zauna kan kujera 'yar tsuguno ta fara wankin suna hira da Iya cike da armashi.
Haka ta wuni a gidan kakanin nata cikin farin ciki ba tare data amsa wayar kowa ba a wannan wunin, har bayan sallah magriba tana tunanin shiga d'akin Iya ta d'auki wayar ta duba sai kuma Iya ta zaunar da ita, wasu k'ullikan magani ta bata tana fad'in "Wannan mai duhun ki dinga wanka dashi, d'ayan kuma hayak'i zakiyi, sai d'ayan kisha a hura ko kunu."
Wani iska ta furzo tace "To fa Iya! Matsalata dake fa wallahi, da an had'u sai kin b芒 mutum wannan abubuwan."
Hannu ta kai kamar zata bigeta tace "Ke ni bana son iskanci, ke a yanda kike d'in nan kina ganin da ban jik'aki da wannan abubuwan ba da yanzu bakin duniya ya barki ne? Ko farin jininki kin d'auka haka kawai kika sameshi? To ni ce nan na shiga na fita tun kina k'arama na miki turaren farin jini."
Da mamaki tace "Yo Iye ina ga ma ke kika hallice ni haka ko?"
Duka ta kai mata hakan yasa ta tserewa a guje ta shige d'aki tana fad'in "To kaji Iya da rigima, Allah ya yi ni da farin jinina ki