Showing 27001 words to 30000 words out of 185502 words
wayar, karb'a yayi yana fad'in "Zan kiraki kinji sai m没 had'u."
Jinjina kai kawai tayi ta juya ta fita zuciyarta kamar zata fito tsabar b'acin rai da kuma shiga rud'u. Sai a k'ofar gida ta saka hijab d'inta ta k'arasa shiga cikin gidan, Abbanta ta samu yana cin abinci akan tabarma, saida ta durk'usa tace "Abba sannu da zuwa."
Da sakin fuska ya amsa mata da "Yawwa sannu Mimi, har kin dawo ne?"
Jinjina kai kawai tayi dan shashek'ar kuka ce a lokacin ta zo mata, mik'ewa tayi ta k'arasa shiga d'aki ta cire hijabinta ta fito ta d'auki buta tayi alwala ta koma d'akin, ko da tayi sallah isha'i daga nan kan dardumar ta kwanta tana jin kamar ta daka ihu ta d'urawa Saminu ashar, dan ya sakata yanayin da babu mahalukin daya tab'a mata irin haka. Da wannan tunanin bacci ya d'auketa duk da tasan za'a ta kiran wayarta, amma bata damu ba tunda saida ta kasheta kafin ta saka a akwati, dan samarin na ta ba lissafuwa suke ba tsabar yawansu, kowa shi dai yana son ta kowa son yake yayi hira da ita, wani lokacin bata san d'aga waya ne dan tana magana da wani kiran wani ke shigowa, haushin wannan k'arar d'in-d'in-d'in kuma bata son ta.
*Laraba*
Ranar yau ta kasance ta musamman a wurinsu saboda farin cikin abinda zai riskesu, musamman da sukayi waya da rana ya sak茅 tabbatar mata zai zo anjima, hakan yasa ta wuni cikin farin ciki da mantwaa da b'acin ran data kwana dashi, amma fa sam bata nuna mishi wannan haba-haban ba saboda ita ta tsani rawar kai ga namiji ma bare mace.
Tunda suka taso daga makaranta ta shiga sharar gidan tas, inda ta tura Amir a k'ofar gida tace ya share, dake lokaci lokaci ta kan yi haka sai Mama ba tayi mamaki ba, tana gamawa ta d'auki bokiti ta d'ibi ruwa a randa, d'aki ta koma ta cire kayan jikinta ta d'auro zani ta fito, duk'awa tayi zata fito daga d'akin a rashin kulawa yasa ta buga k'afarta a d'an dakalin dake bakin k'ofar, wata razanannar ihu ta saki tana kiran "Wayyo k'afata, mamana k'afata ta cire, wayyo Allah n..."
Tsawar da mama ta mata tana fad'in "Dallah yi wa mutane shiru uwar rakin tsiya."
Cikin hushi ta nufota dungui-dungui dan duba k'afar ta ta, d'an durk'usawa tayi tana kallon k'afar, wani dogon tsaki taja tana fad'in "Shirmen banza, ko gurjewa babu amma kike wa mutane wannan kukan."
Cikin kukan shagwab'a tace "Mama Allah da zafi, baki ji yanda na ji ba."
Juyawa tayi tace "Ai ke haka kike, da abunda ya kai na kuka da wanda bai kai na kuka ba haka kike, kina mace amma sai rakin sababi, dalilin da yasa kika yafe kitso kenan a rayuwarki, na ga yanda zaki rayu a haka."
Turo baki ta dinga yi tana mik'ewa ta nufi ban d'akin, dan gaskiya mama ta fad'a tana da jin zafi sosai fiye da kima, tana iya yin kwana tana kuka akan d'an abu da bai taka kara ya karya ba, uwa uba idan aka ce watanta yayi, har ta gama ba zaka daina ganin hawaye a idonta ba, shiyasa duk gidan basa fatan rashin lafiya daga gareta.
*Sheikh*
D'an murmushi ya saki dan lamarin na Asas kam ya fara bashi dariya, daga had'uwa da yarinya shekaran jiya duk ya damesu da zancenta, fatanshi d'aya a kan yarinyar nan ta zama ta k'warai, kamar yanda shi ma ya had'u da tashi a shekaran jiyar, a tare yasa a binciko masa komai a game da 'yan mata da sunansu ma ya zama d'aya, Allah yasa na gari ne da zasu zama abokan rayuwarsu, wannan shi ne burinshi.
Asas kam Hafsat yake kallo yana zuba mata zance da shirin tafiyarshi gidansu Mimi da zaiyi yanzu, hakan ne yasa *Abbakar* dake bi ma Eesha cikin ladabi yace "Amma dai tonton zan raka muje ko? Dan ina so na ga auntynmu."
A sanyaye sheikh ya kalleshi yana sakin murmushi, cikin fara'a Asas yace "Kana son ganinta kai ma? Ni kaina yaro a matse nake, amma kayi hak'uri idan na fara samun karb'uwa a wajen iyayenta yau, kaga jibi sai mu koma ka ganta."
Kallonshi sheikh yayi bai ce komai ba sai Hafsat da tace "Babu abinda zai sa ma su ce baka musu ba, zasu amince insha'Allahu."
Da zulud'i yace "Allah ya yarda aunty."
Wayar sheikh ce tayi k'ara babbar hakan yasa shi d'aukawa yana dubawa, mik'ewa yayi yana fad'in "Ina zuwa."
Fita yayi farfajiyar su kuma suka ci gaba da hirarsu cikin nishad'i, yana fita ya samu wani yaronshi da ake kira *Mudanseer*, hannu ya bashi sukayi musabiha kafin yace "Ya ake ciki? Ka kammala abin da na saka ka."
Kamar zai durk'usa ya sunkuya yana fad'in "An gama komai ranka shi dad'e, hak'ik'a a unguwar an bayar da shaida mai kyau a kan duka yaran, dan kusan kamar anguwarsu d'aya, wanda ya ban bayani a kan su ya fad'a min Maryam uku ke cikin layin, biyu 'yan mata sai d'aya k'arama, kuma duk kusan anguwar suna wannan islamiyyar ne dan ita tafi kusa dasu, a gaskiya dai babu wani b'atanci a kan duka biyun."
Lumshe ido yayi ya sauke ajiyar zuciya yace "Nagode."
Jinjina kai yayi yace "Sai dai kuma ranka shi dad'e d'ayar an fi kiranta da sunan Mimi, dan da k'yar aka samu wanda yasan asalin sunanta ma, an tabbatar iyayenta mutanen kirki ne, dan mahaifinta ma an ce yana zaune lafiya da kowa, d'aya Maryam d'in ce kuma a hannun kakarta tak ke wacce ta haifi babanta."
Wani murmushi ya kuma saki yana tunanin kenan wacce ke hannun kakarta ita ce Maryam d'in Asas, shi kuma ta shi ita ce ke gaban iyayenta, numfashi ya sauke ya sake bashi hannu yace "Nagode sosai."
Hannun ya bashi sukayi sallama ya fita shi kuma ya dawo falon kamar zaiyi tsalle dan murnan jin haka, dan shi yafi ma damuwa da Asas d'in saboda yanda ya ga ya zurma da yawa akan ta.
Shigowarshi shi kuma ya mik'e yana fad'in "Sheikh, ka bani wani wurdi nan na neman sa'a."
Yar dariya yayi ya girgiza kai yace "Bana da shi, ni ma nemanshi nake saboda abinda na saka a gabana."
Hannunshi Asas ya kama yana murmushi yace "Ya ustaz muje na ji to miye haka? Kar fa a zo kai ma yarinya ka samu zaka k'arawa yayata abokiyar zama kamar yanda kake fad'a."
Wata suka da Hafsat taji daga zuciyarta zuwa d'an cikin dake jikinta yasa ta saurin kallonsu tana mai tsaresu da ido, aje cokalinta tayi ba tare data d'auke idonta daga garesu ba, su kam juyawa sukayi suka fita sheikh na fad'in "Asas lafiyarka ita tafi damuna akan komai."
Suna fita farfajiyar ya kalleshi yana gyara tsayuwa yace "Sheikh nagode sosai da k'ok'arin da kake akan gaanin na samu lafiya, na tabbata Alhaji bai bar amanarmu a hannun da bai dace ba, Allah ya bamu ikon faranta maka kai ma."
Murmushi yayi yace "To miye a ciki? Mahaifinka namahaifina nono d'aya suka sha, mahaifina ne ya saki mahaifinku ya kama, duk abinda zan muku yan uwana na jini na yi ma."
Jinjina kai yayi yace "Hakane, Allah ya saka da alkairi."
Murmushi kawai ya masa yace "Saika dawo."
Jinjina kai yayi yace "Addu'arka fa sheikh."
Lumshe ido kawai yayi alamar to yana kallo har ya fita daga gidan a tsaleliyar hondarshi.
Duk da ba had'uwa zasu yi ba amma haka ta shirya cikin ratsatsen leshen da Mas'ud ya siya mata a lokacin sallah, wani irin kyau tayi duk da b芒 kwalliya b芒 ce tayi mai yawa, turare ma yau na musamman ta bud'e a kwalinshi, d'an k'arami ne mai masifar sanyayyen dad'i mai sunan *mukhalat* ta shafa, mayafinta ta d'auka ta ce wa mama zata shiga gidansu Asma'u, bata hanata ba dan tasan mahaifinta ma yana k'ofar gida a lokacin dan ko sallah isha'i ba a yi ba.
Tana shiga a soron gidansu Asma'u suka ci karo da yayanta da suke uba d'aya zai fita, tare gabanta yayi yana kallonta yana murmushi da fad'in "Mimi gari zaki tafi ne?"
Fuska a d'aure tamau tace "A'a, kauce min a hanya."
Wani murmushi ya kuma yi tare da gyara mata ta wuce ta barshi nan, tana shiga da sallama a bakinta, dayawa daga cikin mutanen gidan ne suka amsa har da Asma'u, idon kowa a gidan a kan ta yake yayin da suke shak'ar k'amshin tufafinta dana jikinta daya gauraye illahirin gidan, kowa zuciyarshi na girgiza tana jijjiga akan lamarin yarinyar. Mimi kam ko a jikinta sai ma hannun Asma'u data kama suka shiga d'aki tana fad'in "Wai ke miye haka? Dubi fa yanda kika yi wani gamin gambiza riga daban siket daban, a hakane zaki samu saurayi?"
Tsaki tayi sai Asma'u data fahimci yau kanta take neman juyewa kawai tace "Ina zaki je Mimi kikayi wannaan shirin haka?"
Murmushi ta saki tare da cire mayafinta ta aje akan gadonsu dake shirge da kaya tace "Ko ina, bana fad'a miki Asas zai zo wajen Abba ba, shiyasa na baro gidan."
Wani murmushi tayi ita ma tace "Allah dai ya nuna min Abba ya amince da Asas d'in nan ko hankalina ya kwanta."
Kallonta tayi tace "Idan Abba ya amince saina baki kyautar jaka goma."
Zaro ido tayi tace "Jaka goma fa? Ina ma laifin jaka guda."
Yatsina fuska tayi tana gyara zamanta da wayarta a hannu, bud'e tsaron wayar tayi ta shiga d'an daddanawa, hira suka dinga yi da Asma'u har aka kira sallah isha'i ta saka hijabin Asma'u ta kabbara sallarta dan da alwalarta dama, tana gama akan sallayar wayarta ta shiga vibration, d'auka tayi tare da sakin murmushi, Asma'u kanta murmushin tayi tace "Tunda na ke dake ban tab'a ganin an kiraki a waya kinyi murmushi ba sai yau, Asas kai d'an baiwa ne."
K'ala bata ce ba ta d'auki wayar ta d'ora a kunne, daga b'angarenshi yace "Maah, barka da dare."
A sanyaye cikin b'oye farin cikinta ta k'irk'iro muryar gajiya da kasala ta saka tace "Barka, ya kake?"
Da fara'a yace "Komai ba daidai ba daga yanzu har sanda zan k'araso gidanku mu tattauna da Abba."
A hankali tace "Uhumm!" A shagwab'e cikin sangarta ta autanci yace "Maamah, dan Allah ki tayani addu'a Abba ya bani ke."
Da mamaki tace "To wai me ye idan ka rasani, ka daina jin tsoron zai hana maka ni mana, ka sameshi kan ka tsaye kawai."
Saida yayi kamar zaiyi kuka yace "Shikenan to, amma Mimi ni kad'ai nasan tashin hankalin da zan shiga idan na rasaki."
D'an murmishi tayi tace "Ba zaka rasani ba insha'Allah."
A tausashe yace "Allah ya amince." Shiru ne ya d'an biyo baya kafin sukayi sallama a lokacin ya kawo daidai da kwatancen data mishi tunda rana.
Fitowa yayi daga motar yana gyara rigar shaddarshi gezna kalar ruwan k'asa mai duhu sosai wacce aka ma gajeren d'inki ya mishi kyau, saidai babu hula a kan shi sai gyaren kai irin na matasan zamani. Abba ne dasu Yaseen wanda yaji sauk'i suka jero sun dawo daga masallaci, ganin zasu shiga gidan yayi saurin matsawa yana musu sallama, Abba ne ya amsa tare da mik'a mishi hannu, lura d'脿 yayi irin hallitar Allahn nan ce ta gajerun mutane yasa Asas cikin ladabi yace "Dan Allah Baba gidan malam Adam nake tambaya?"
D'an juyawa Abba yayi ya kalli Yaseen da Amir kafin ya k'arewa Asas kallo, duk da shigarshi ta yi kama data wayayyun yara ce kawai amma kuma ta fito mishi da haibarshi had'e da kamala ta cikakken bafulatani, dan haka ya d'an saki fuskarshi yace "Yaro ni ne malam Adam a dai layin nan, Allah yasa lafiya?"
Tarrr ya sake zaro ido a kan shi, daga k'asa ya sake d'aukowa ya kalleshi, daga shi har su Yaseen d'in duk tsayinsu bai wuce zuwa cinyarshi dan babu wanda ya kawo k'ugunshi, har gwara ma Amir ya d'an fisu tsayi da kad'an.
Wani irin nauyi ne yaji tare da kunya sun kamashi, sai kawai ya tuna kalaman Mimi na safiyar shekaran jiya da take fad'in akwai baiwar da Allah ya ma iyayenta, shi ma idan ya gansu zai tabbatar da suna da baiwarsu. A take yayi saurin durk'usawa yana shafa sumarshi da fad'in "Ina wuni Baba."
Da murmushi Abba yace "Lafiya lau d'an saurayi, muna lafiya."
Gaisawa sukayi har saida Abba yace "Gashi kuma ban shaidaka ba? Daga ina haka?"
D'an d'ago kan shi yayi ya kalli su Yaseen, hakan yasa Abba cewa "Ku shiga ciki kunji."
Saida suka ga shigarsu kafin suka sake maido hankalinsu ga juna, a sanyaye cike da kunya yace "Abba dama mun had'u da Mimi..."
Tunda ya ji haka sai yace "Dakata samari, bari na kawo mana abun zama ko."
Cikin fara'a yace "A'a Abba da kun barshi, haka ma yayi nagode."
Gyara tsayuwa Abba yayi yana kallon sumar dake kan Asas yana fad'in "Dama mun had'u da ita ne, to na nemi na fara gabatar da kaina ne kafin na fara zuwa wajenta saboda a gaskiya aure ne ya kawoni ba wasa ba, shine na zo da kaina dan gabatar muku da kaina."
Numfashi Abba ya sauke yace "Yaro ya sunanka? D'an wane gida ne kai? Waye mahaifinka? Sannan me ce ce sana'arka?"
Ba tare da jin d'ar ba Asas yace "Sunana Ashraf Sabi'u, ni d'ana ga margayi Alhaji Sabi'u Aliyu Sharif Maina, ina zaune tare da mahaifiyata a unguwar Tchanga, sannan nayi karatu jarida ne amma ina kasuwa ne tare da d'an uwana sheikh wanda ya zama kamar uba gareni, dan gaba d'aya shi yake kula da harkar kasuwancinmu ni da 'yar uwata."
Jinjina kai Abba yayi yace "Masha'Allah, masha'Allah, yayi kyau haka, amma na ji ka ambaci Aliyu Sharif maina, kana nufin kai d'an uwan sheikh Abdul Waheed ne kenan?"
Da fara'a yace "Hakane Baba, mahaifinsa da mahaifina ciki d'aya suke fito."
Da farin ciki ba yace "Masha Allah, abu yayi kyau gaskiya."
D'an kallon Abba yayi yace "Saidai Baba akwai abu guda da ba zan b'oye muku ba."
Gaban Abba ne ya fad'i ya tsira masa ido, d'orawa yayi da "Baba shekara bakwai kenan da Allah ya jarabceni da wani azababben ciwon ciki mai tsanani, a duk shekarun nan mahaifiyata magani take nema min, amma insha'Allah komai ya kusa zuwa k'arshe dan yanzu haka muna ta shirin tafiya k'asar waje ne dan sama min magani."
Wata nauyayyen ajiyar zuciya Abba ya sauke tare da jinjinawa yaron sosai yace "Malam Ashraf wannan ai ba komai bane, ita larura tasan d'akin kowa kuma babu wanda Allah ya wuce ya jarabeshi da ita, Allah ya baka lafiya yasa a yi a sa'a."
Da murmushi yace "Nagode Baba."
Cikin murmushi da jin dad'i Abba yace "Masha'Allah, abu yayi kyau, Allah ya shi albarka."
Gyara tsayuwa yayi yace "Insha'Allah idan na shiga ciki yanzu zan tuntub'i yarinyar a kan maganarka, idan ta amince to fak'at, insha'Allah zan nemeka sai na maka bayani, bana da tamtama akan zuri'ar su sheikh, ina ji kai ma mutumin kirki ne kamar shi, ba zanyi bak'in cikin damk'a amanar 'yata ga wannan ahali ba."
Wuuuuu! Asas yaji kamar zaiyi kwasan karan mahaukaciya da Abba ya d'aukeshi ya goya, ko a haka aka tsaya yasan kam zai samu shiga da izinin Allah, dan haka bakinshi har kunne ya shiga godiya yana mishi addu'ar Allah k'ara girma da lafiya da d'aukaka da sauransu, Abba ma cikin farin cikin yau *uwar ta shi* bata yi masa jaye-jayen nan ba ya shiga shi mishi albarka, da haka suka rabu Asas ya d'auki hanyar gidan sheikh dan tsaigunta masa wannan labari mai armashi.
Mimi ma da tun tsayawar motar ta lek'o tare da Asma'u tsaf ta k'are masa kallo ta kalli Asma'u tace "Gaskiya guyen nan ya had'u, kinga wani mahaukacin shiri kamar yau ne d'aurin aurenmu."
Kallon Asma'u tayi ta kama hannunta suka koma ciki tana fad'in "Ai dole ma Abba ya amince, inba haka ba kuka zanyi."
Dariya kawai Asma'u tayi har suka shige d'akin suna yar hirarsu.
*Masha'Allah*
Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.
Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:52 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_