Showing 141001 words to 144000 words out of 185502 words
tayi ta samesu suna ta labartawa Hafsat labarin abinda ya faru a islamiya, da gudu Munzeer ya tarbeta yana fad'in "Aunty."
Rumgumeshi tayi tana dariya tace "Munzeer an dawo?"
"E." Ya fad'a yana kallonta, kama hannunshi tayi tana kallon su Aswan da suke fad'in "Aunty sannu da gida."
Da fara'a tace "Sannu Aswan, Heezam, har an sauko?"
A tare suka fad'i "E." Satar kallon Aisha tayi da ita ma take kallonta, wucewa tayi tare da Munzeer d'akinta yana mata hirarshi ta yara, zaunar da shi tayi falo ta shiga ciki ta d'auko chocolat d'in da jiya suka siyo ta kawo mishi, da fara'a ya karb'a da hannu biyu yace "Nagode Aunty, Allah ya biya."
Da fara'a tace "Ameen yaron Abbanshi."
Mik'ewa yayi yace "Na tafi na cire kayan makaranta na."
Jinjina kai tayi tana kallonshi har ya fita a falon, aikinta ta shiga yi ta d'anyi goge goge ta saka turaren wuta dana tsintsiya, tana gamawa ana kiran sallah magrib da sauri ta shiga madafa ta duba tukunyarta, ganin komai ya daidaita ta kashe wutar suka zuba a kwanuka suka kai table kafin ta koma d'aki tayi alwala.
Kwalliya ta d'auka ta ban mamaki cikin doguwar rigar shadda ta kashe d'aurin d'an kwallin da d'azun nan ta kalleshi a YouTube, tana fitowa ita kanta sai ta ji kamar tana tsarguwa dan yanda suke kallonta jefi-jefi sai yasa ta ji d'ar a jikinta, haka ta samu wuri ta zauna suna kallon kallo ita da Aisha, sai Hafsat dake ta danna wayarta tana d'an hira da Munzeer.
Odar da akayi da kuma k'arar bud'e k'ofa ya tabbatar musu da sheikh na shigowa, suna zaune har saida ya shigo da sallama a bakinshi da alamun gajiya a tattare da shi, kusan a tare suka amsa mishi sai Hafsat da sabo yasa ta mik'ewa tana d'orawa da fad'in "Sannu da zuwa sheikh."
Da fara'a ya amsa mata da "Sannu Manga, ya gida?"
Da fara'a tace "Alhamdulillah, ya aiki ya fama da jama'a? Yau juma'a nasan ansha fama."
Murmushi yayi ya kalli Mimi da ita ma ta mik'e tace "Sannu da dawowa."
A tausashe ya amsa da "Sannu da gida."
Kallon Hafsat yayi yace "Gaskiya kam ansha fama, shiyasa ma na kubto da wuri dan na dawo gareku na samu nutsuwa."
Dariya tayi tace "Allah sarki, Allah ya k'ara maka lafiya jigonmu, wannan d'awainiya da kake Allah ya baka wanda zasu tallafeka sanda kake neman taimako."
Wani k'ayataccen murmushi ya saki tsabar farin ciki yasa shi jawo hannunta ya dafa kanta yace "Ameen ya Allah, Nagode sosai Hafsa, Allah ya miki albarka, ke ma kuma Allah yasa yaranki su zama masu jin k'anki."
Mimi dake kallonsu bata san sanda ta saki murmushi ba dan gaskiya sun birgeta, kuma yana daga cikin abinda yasa ta kasa samun k'ofar rainin a wajen Hafsat d'in shi ne, yanda ta ga shi kanshi wanda take zaune dominshi yana girmama matarshi, sannan ita kan ta matar ta rik'e girmanta kam, ko irin d'an kishinta ta k'i nunawa, shiyasa ita kanta sai taji Hafsat na mata wani kwarjini.
D'auke hannunshi yayi akan Hafsat d'in yana fad'in "Yaran nan basu dawo bane?"
"E, amma na tabbata suna kan hanya yanzu." Cewar Hafsat, jinjina kai yayi ya sunkuya ya d'auki Munzeer ya nufi d'akinshi yana fad'in "Bari nayi wanka na fito, ina fatan kun kammala abinci?"
Dariya Hafsat tayi tace "Amaryarka ta kammala maka komai, yau idan ka ci abincin nan sa茂 ka manta hanyar shiga d'akinka."
Dariya sukayi banda Aisha dake kumbura baki sai sheikh da yace "Idan hakane kuwa ya dace a had'ani da d'an jagora ai."
Zaune Hafsat tayi tana fad'in "Idan zaka biya ai ba matsala."
Juyowa yayi ya kalleta yace "Yanzu Manga a gidan nan ba za'a min alfarma ba?"
Girgiza kai tayi ta kalli Mimi ma data zauna tace "Ko kad'an, ban sani ba dai ko amarya zata iya."
Shigewa yayi yana fad'in "Sawwama Allah ya shiryaki."
Da k'yalk'yala dariya tace "Ameen malam." Yana shigewa ta kalli Mimi cikin rad'a tace "Mijinki fa yana son kulawa sosai, ki sameshi hakan zai faranta mishi rai."
Sunkuyar da kai tayi cike da kunya dan ita har yanzu jin abun take babba idan aka had'ata da shi matsayin miji da mata, d'an dukanta Hafsat tayi a cinya tace "Haba Mimi, tashi mana, wallahi zai ji ba dad'i, ki yarda da maganata, ina fad'a miki hakane saboda na sanshi sosai."
Jinjina kai tayi ta mik'e ta nufi d'akin na shi, hararanta Aisha tayi ta d'auke kanta, kallonta Hafsat tayi banka mata harara tayi tare da k'wafa ta jinjina kai alamar zaki sani, turo baki Aishar tayi tace "Kiyi hak'uri Amie."
A dak'ile tace "Hak'urin me Aish? Tunda kin gama rainamu ai shikenan sai kiyi, nasan dai burinki bai wuce ki ji ana fad'a a gari cewa Aisha yar malam ce ta k'i halin malam, na tabbata abinda kunnuwanki suke so su ji shi ne ke kamar ba 'yar sheikh Abdul Waheed ba saboda halayyanki."
Da sauri tace "A'a Amie, dan Allah ki daina fad'in haka, na tuba Amie ki yafe min."
Jinjina kai tayi tana d'aukar wayarta tace "In gaskiya ne abinda kika fad'a idan Mimi ta fito ki bata hak'uri, hakan zai sa na yarda gaskiya kike fad'a."
Kumburo baki tayi ta d'an jinjina kai alamar to, d'auke idonta Hafsat tayi daga kallonta, dan tana so dole ta ga canji a tare da Aisha, idan tace zata fito da kishinta ne yanda Aisha ke buk'ata gidan nan ba zai d'aukesu ba, idan ta ce zatayi kishi da Mimi ne to zata cinyeta ta had'eta. Amma duba da wasu abubuwq yasa ta d'auke kai da kawar da kanta, duk abinda zata gani yanzu tasan na d'an lokaci ne, a shekaru kamar na sheikh arba'in da bakwai zuwa da takwas ya samu yarinya kamar Mimi yar sha bakwai da zata shiga takwas, me zata tsammani dama? Idan ma baiyi rawar k'afa ba ai sai tace mijinta ba namiji bane, dan haka zata had'e komai har sanda ita ma zatayi cikar d'aki su zama d'aya, tabbata hakan zai sa ta tashi da riba biyu, ta farko shi ne daraja da mutumcinta basu zube ba a wurin mijinsu, sannan ita kanta Mimi ba zata samu k'ofar rainata ba, dan kuwa tayi 'ya da ita, miji da suka had'a ba zai sa ta rainata ba.
*Barkanmu da sallah yan Uwa.*
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:58 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*47*
Tana shiga ta sameshi yana cire kaya Munzeer kuma na gaban madubinshi da wayarshi a hannu, k'ura mata ido yayi har ta k'araso habanshi ta tsaya kanta sadde, shafa kuncinta yayi yana murmushi yace "Ryam kin ganki kuwa, a gaskiya kinyi kyau ba kad'an ba."
Cike da kunya da ladabi ta amsa da "Nagode."
Saida ya aje rigarshi babba daya cire ya sa hannu aljihu, kud'i ya d'ebo da shi kanshi baisan adadinsu ba ya kamo hannunta ya damk'a mata yace "Wannan tukuicin wannan kwalliyar nan, kuma a shirye nake na dinga biya kullum indai ba ayi wacce zata fi k'arfin aljihuna ba."
Murmushi tayi tana son zame hannunta tace "Nagode, amma ba sai ka biya ba, yabawa ma da kayi ya wadatar dan shi ne k'arfin gwiwar, zan iya siyan kayan da gumina ma indai zaka yaba."
Girgiza kai yayi yana dariya yace "A'a Ryam, ni fa ina d'aya daga cikin masu fad'a a waje a dinga yi wa mata kyauta musamman idan sunyi abinda ya birge, sai kuma ni na zama mai hannun jarirai a gidana? A'a wallahi baki isa ba."
Ya fad'a yana damk'a mata kud'in, karb'a tayi da hannun biyu tace "Nagode, Allah ya biya."
Da fara'a yace "Ameen."
D'an kallon Munzeer tayi dake ta tak'ular waya tace "Zan fita na barku ka shirya."
Shi kanshi dake akwai hirar da yake son yi da yaron sai bai hanata ba, da kallo ya bita ganin yar car da ita a fuska amma mazaunanta sai wani kad'awa suke, lumshe ido yayi ya girgiza kai yana d'an lashe leb'e.
Mayar da kallonshi yayi kan Munzeer da hankalinshi ke kan waya yace "Yau an fad'a min kun makara a zuwa makaranta da yamma? Me yasa?"
Zaro ido yayi ya kalleshi ya girgiza kai cikin muryar yarinta yace "Abie inji wa? Mun isa akan lokaci fa, a can mukayi sallah la'asar."
Murmushi ya masa jin ya amsa tambayar daidai ya d'ora da fad'in "To amma ai da kuka tashi an ce kun tsaya a hanya ko?"
Nan ma da sauri ya girgiza kai yace "A'a Abie, bamu tsaya ba, ka tambayi dreba kaji."
Jinjina kai yayi yace "To amma me yasa Aswan bai bayar da sallah ba yau a masallaci?"
A tsorace yace "Abie ya bayar fa, ka tambayi su Anas kaji."
Kallon tuhuma ya masa yace "Amma ba a gaban Heezam ya tsaya kula yaran unguwar nan dana hanashi ba?"
Turo baki yayi yace "Abie ba kulasu yayi ba, sun mishi magana sai shi ma ya musu saboda yace ka fad'a mana ba kyau wulak'anta mutum."
D'auke kanshi yayi yace "Me suka tattauna?"
Jim yayi alamar tunani sai kuma yace "Gaisawa ne sukayi sai kuma ya fad'a musu zai shiga majalisi, shi ne sai wani yace shi ma yana so ya fara karatu tare da shi."
Murmushin jin dad'i yayi yace "To me yasa yau a gidan akayi ta fad'a? Baka tsawatar musu bane?"
Galala ya kalleshi sai kuma yace "Abie yaushe?"
Kallonshi yayi yace "Kana nufin baka san lokacin ba?"
Girgiza kai yayi yace "Abie babu wanda yayi fad'a."
Kallonshi yaayi da zolaya yace "Halan yawo ka tafi?"
Girgiza kai yayi yana dariyar jin kunya yace "A'a Abie, ban fita ko ina ba."
Dariya yayi cikin farin ciki da jin dad'in babu abinda ya faru marar kyau bayan fitarshi, ban d'aki ya shige ya barshi da wayar a hannu yana ta latsawa yana buga game wanda dama saboda shi yake a wayar, shi ma kuma dan abune na wasa da ta wani fannin yana anfanar tunani da k'walwar yaro yasa ya barshi har yake bugawa lokaci lokaci.
Ya d'auki lokaci sosai kafin ya fito rik'e da hannun Munzeer, dukansu zaune ya samesu har su Heezam da basu jima da shigowa ba, gaisheshi sukayi su ma ya amsa da fara'a har da tambayarsu darasinsu sanda suke zama kan table, Hafsat da Mimi ne suka tsaya zasu zuba abinci Mimi ta kalleta tace "Aunty ki barshi ma zan zuba."
Murmushi tayi ta zauna tana aje plate d'in data d'auka, a nutse ta shiga zuba abincin ta fara ajewa gaban sheikh, kafin ta zubawa Hafsat da a lokacin ta kalli sheikh take fad'in "Sheikh gaskiya satin nan ina so na je na ga 'yata, wallahi kewarta hanani bacci take."
Dariya yayi yana kallonta yace "Kewarta na hanaki bacci ne jiya na sameki kina ta juyi akan gado?"
Dariya tayi tana rufe fuska da tafin hannu, jinjina kai yayi ya kalli Heezam yace "Ki shirya sai kuje tare da shi ya rakaki, idan kuma zaki je gobe to ki shirya mu tafi tare."
Farin ciki ne ya bayyana a fuskarta tace "Kai amma naji dad'i, zan shirya goben sai mu tafi."
Jinjina kai yayi yana kallon plate d'in gabanshi, shinkafa ce mai curry da jar miyar kaji, saidai yanda yaga naman a ido ya tabbatar masa da ya samu aiki mai kyau kuma zaiyi dad'i, ga k'amshin dake ta shiga hancinshi tunda ta aje gabanshi, kallonta yayi sanda take zuba wani a plate yace "Ryam."
A ladabce ta gaggauta kallonshi tace "Na'am yallab'ai."
Kallon plate d'inshi yayi yace "Da alama abincin nan ba zai isheni ba, a k'aro min gaskiya."
Dariya sukayi dukansu ban da Aisha da Munzeer dake cakalar waya, ganin Mimi bata ce komai bayasa Hafsat fad'in "Allah gafarta ka jira ka cinye na gabanka mana."
Kallonta yayi a marairaice yace "Na sani ne ba zai isheni ba, amma tunda kince haka shikenan."
Kallon Mimi yayi yace "Ki rage min saura kinji."
Jinjina kai tayi tace "Angama yallab'ai."
Aje plate d'in tayi gaban Aisha dan girma ne take bi wajen zuba abincin, d'an ture plate d'in Aisha tayi ta yatsina fuska tace "Na k'oshi ni."
Kallonta duk sukayi sai Mimi da tace "Kin k'oshi? Kin ci wani abu ne?"
Kumburo baki tayi amma ba tace komai ba saboda sheikh dake wurin, Heezam daya gama lura da kallon da sheikh ke ma Aisha ne yayi saurin cewa "Aisha ki ci abinci mana."
Kallonshi tayi tace "Na k'oshi na ce."
Hafsat ce tace "Ku barta mana, cikin waye? Dan kanta."
Kallonta Mimi ta sake yi tana k'ak'aro murmushi da tunawa da maganar Mama ta turawa Aisha plate d'in tace "Aisha ki ci abinci kinji, idan ni ce ba kya son girki na saina daina."
Cikin b'acin rai Hafsat tace "Ki daina kamar ya? Nan ba gidan mijinki bane? Ke da ita waye yake da iko a gidan nan? Ita fa kwana kad'an ya rage mata a gidan, ke kuma gidan mijinki ne da muke muku fata har mutuwa, shikenan saiki daina girki saboda ita, wacece ita? Kar Allah yasa ta ci mana taga idan wani zai daina rayuwa akan haka."
Sharrrr! Wasu hawaye masu zafi suka taho ma Mimi, dan wani iri take ji a zuciyarta kamar ta koma gidansu tayi rayuwarta cikin yancin, aje cokalin da take zuba miya tayi ta juya da sauri ta nufi hanyar da zata sadata da b'angarenta, tana shigewa ta fashe da kuka ta fad'a kan kujera.
Suma suna ganin shigewarta sheikh daya rasa me ke masa dad'i ganin abinda ke neman kunno masa kai ya kalli Aisha, a tsanake ya shiga kallon duka yaran sai kuma ya jawo plate d'inshi da kyau ya d'auki cokali yana shirin d'ibar lomar farko yana fad'in "Mu ci abinci."
Kallonshi sukayi duk sai suka tsargu, duk da basu san shi da duka ba amma sun san shi da fad'a, Heezam ne ya mik'e ya fara zubawa kanshi abinci hakan yasa Aswan jawo na gaban Aisha da tace ba ta ci. Kallonshi Hafsat tayi tace "Sheikh kuka fa take? Ka bata hak'uri dan Allah, karta damu da haukan yarinyar nan."
Yi yayi kamar bai ji ta ba ya lumshe ido yana fad'in "Gaskiya abincin nan yayi dad'i."
Cike da damuwa da kulawa Hafsat tace "Sheikh."
"Um." Ya fad'a yana kai wata lomar bakinshi dan ji yake kamar ya tsinke harshenshi, a sanyaye tace "Dan Allah kayi wani abu a kai."
Sake shareta yayi hakan yasa ta mik'ewa a hassale tace "Shikenan nagode." D'akin Mimi ta nufa dan b芒 ta hak'uri akan wautar Aishar.
Ko kallonta baiyi ba har ta shige, cike da rashin jin dad'i Heezam ya kalleshi a ladabce yace "Abie."
A k'asan mak'oshi yace "Ina ji."
Cike da tsoro yace "Dan Allah kayi hak'uri."
Kallonshi yayi da idonshi da suka fara canzawa alamar b'acin rai, aje cokalin yayi ya tallabe hab'arshi da bayan hannu yace "Hak'uri akan me? Wani laifi kukayi ne?"
Kallonshi Aisha tayi kamar zatayi kuka tace "Abie dan Allah."
Wani kallo ya wurga mata kamar zai had'eta, da nuna rashin damuwa yace "Me ye a ciki? Kuka ne take, ku barta tayi mai isarta ta k'oshi zatayi shiru dan kanta, idan kuma ta ji ba zata iya zama a haka ba ta tafi gidansu, iyakarta dai idan taje ta ce Abdul Waheed azallumi ne wanda bai san darajar aure ba, sai iyayenta kuma su ce ni d'in ashe dama tsohon banza ne da bai san mutumcin mace ba, sai mutanen gari kuma idan suka ji su ce ashe ni d'in babban mak'aryaci ne kuma mutumin banza wanda ya kasa tarbiya a gida, wanda yaranshi basu da tarbiya da sanin girman mutum, su d'ora da fad'in *dama ba'a aikin da abinda malamai ke yi, kawai kayi aiki da abinda suka fad'a maka*, shikenan idan aka fad'i haka? Kunji dad'i kenan?"
Cokalinshi ya d'auka zai ci gaba da cin abinci yace "Matata ce ita ma, ko bana sonta ba zan wulak'anta ta ba, ku kuma 'ya'yana ne da babu yanda zanyi na rabu da ku, tunda ba kwa so na da aurenta shikenan, ku fad'a min da bakinku yanzun nan sai na korata gidansu na ci gaba da zama da uwarku kamar yanda kuke buk'ata."
Heezam ne yayi saurin fad'in "A'a Abie dan Allah, ka yafe mana mun tuba."
Kallonshi yayi sai kuma ya mik'e ya bar wurin duk da kuwa yana son cin abincin sosai saboda yana jin yunwa kuma ya masa dad'i.
Heezam ne ya kalleta rai b'ace yace "Aisha kin gani ko? Kin ga kina so ki ja mana hushin iyayenmu ko? To wallahi ba zai yiyu ba."
Mik'ewa yayi shi ma ya bar wurin, Aswan ma harara ya galla mata ya mik'e yana fad'in "Ai gwara ma da zai aurar dake? Haka kawai zaki b'ata mana sunan gida."
Da kallo ta bisu baki sake sai kuma ta mik'e ita ma da sauri ta nufi d'akinta tana fashewa da kuka.
Hafsat na shiga ta samu Mimi a falon tana kuka, da sauri ta k'arasa tana fad'in "Subhanallah! Mimi kuka?"
Da sauri ta d'aga kanta tana share hawayen ta k'ak'aro murmushi, saida ta zauna kusanta suna kallon juna tace "Mimi kuka kike? Kiyi hak'uri dan Allah, wallahi ban san a ina Aisha ta d'auko wann..."
Da sauri Mimi ta rik'e hannunta data dafa kafad'arta tace "A'a aunty, dan Allah karki bani hak'uri, ba ina kuka bane saboda abinda Aisha ta yi, kiyi hak'uri idan na d'aga miki hankali."
A marairaice ta ci gaba da kallonta da tausayi tace "Mimi bana so mu shiga hakk'inki, ni kaina dake uwarta bansan a ina ta samo sabbin halayen nan ba, hakan yasa har na fara matsuwa a d'aura aurenta dan kar ta ja min wata maganar."
Da mamaki ta kalleta tace "Aunty Aisha dama aure zatayi?"
Jinjina kai tayi tace "E, ranar juma'a za'a d'aura aurenta."
Sak'e tayi tana saurare sai kuma tace "Allah yasa alkairi."
"Ameen." Ta fad'a a sanyaye, kallonta ta sake yi da kyau tace "Kin daina kukan yanzu?"
Jinjina kai tayi tana k'ara share hawaye