Showing 60001 words to 63000 words out of 185502 words
na ganki cikin walwala."
Nan ma sake jinjina kai tayi alamar to, jinjina kai yayi shi ma yace "Zan wuce, sai jibi insha'Allah."
Jinjina kai tayi tace "Allah ya kaimu."
"Ameen." Ya fad'a yana juyawa, ita ma juyawa tayi ba tare data d'auki kayan ba ta koma d'aki, dan ita da sake karb'an abu a hannun wani kam har abada indai ba aure tayi ba, tana shigowa d'akin mama ta mik'e tana binta da wani kallo, yanda take ta b'oye hannayenta a hijabin ya dasawa mama alamar tambaya a game da ita, dan haka ta fizgota da k'arfi taja hijabin ta cire mata ta jefar, kallon hannayenta tayi tace "Me kike b'oyewa yanzu kuma?"
Saida ta durk'usa k'asa tace "Wallahi mama ba komai."
K'in yarda tayi da tsiya sunkuya ta saka hannu a k'ugunta tsakiyar siket d'inta, lalabawa ta shiga yi Mimi kam d'an kakkarewa take tana kallon Mamar, buge hannunta tayi tana fad'in "In kina da gaskiya ki bari na duba mana."
Da sauri ta d'auke hannayenta da tunanin mama ta gani ko ta samu rangwame, a tsawace ta kalleta tace "Mik'e tsaye, mai ladabin kunama kawai, kin iya sinne kai kina wani durk'usa mana kamar gaske."
K'are mata kallo ta shiga yi kafin tace "Zazzaga min siket d'in nan."
Cikin marairaicewa tace "Wallahi mama babu komai, mama me zai bani yanzu daga zuwanshi?"
"Ni ina zan sani? Ai kin fini sanin komai Mimi, dan yanzu ni tsoro ma kike bani." Cewar Mama tana ta lalabeta har cikin riga, saida ta tabbatar babu komai kafin ta tab'e baki ta juya ta fita, kayan da suka bari a tsakar gida ta d'add'ako da k'yar ta kawo ta aje, nuna mimi tayi da yatsa tace "Kuma ban yarda ko kallon ledojin nan kiyi ba har sai mahaifinki ya dawo."
Jinjina kai tayi alamar to tare da d'auke idonta daga kan ledojin, fita mama tayi a d'akin ita kuma ta gyara zama ta kifa kanta a cinyoyinta ta saka wani kuka mai ban tausayi, cajewar da Mama ta mata yanzu ta tsaya mata a rai sosai, daga shigowar Asas yanzu har tayi tunanin ya bata wani abu data b'oye? To me zai bata dan Allah? Shi fa ba haka yake ba, aure ne kawai a gabanshi ba shashanci ba, hasalima har yanzu babu wanda ya tab'a jaraba yi mata wannan ko da cikin wasa ne. Da wannan Mimi ta ci kuka ta gode Allah a wannaan wuni kam, ba aikin fari dan ko tsintsiya ta d'auka mama zata ce bata so ta aje, sallah kawai take mik'ewa tayi amma hatta da abinci mama bata ce mata gashi ba, sai yamma ne da taji yunwa zata kasheta ta d'iba da kanta cike da zulumin kar mama ta hanata shi ma. Gashi tun tana zuba ido ganin Asma'u har ta cire rai, kuma babu damar aiken Yaseen ko Amir su kira mata ita ko taji sanyi a ranta.
*Sheikh*
A d'aki ya sameta tana sallah isha'i da ta kubce mata har aka idar, zaune yayi bakin gado ya buga tagumi yana kallon enveloppe d'in hannunshi, abinda ya wuni yana damunshi ne ya sake fad'o masa a rai a daidai lokacin, idan ya tuna abun nan har ji yake kamar yayi ihu ko yaji zuciyarsa ta rage nauyin nan, saidai ina ba zai iya hakan ba, sai ma kama istigfari da yayi a zuciyarshi, har ta mik'e ta nad'e sallayar ta cire hijabi ta zauna kusa da shi bai lura ba, saida ta dafa kafad'arshi tana lek'a fuskarshi tace "Sheikh da tunani hakka?"
Da sauri ya kalleta yana murmushi, numfashi ya sauke yace "Kin idar ashe?"
"Na idar amma sheikh nawa ya tafi duniyar tunani." Ta fad'a cikin shagwab'a, d'an murmushi yayi yace "Ba tunani nake ba, akwai abinda nake yi ne."
Da mamaki ta kalleshi tace "Karatu kake? Ko wani sabon zikiri ne aka samu mai falala ba'a fad'a mana ba."
Dariya yayi tare da jawota ya rumgume yanda ba zai cutar da abinda ke cikinta ba yace "Sabo ma kuwa, yanzun nan na bincikoshi a wani littafi."
Cikin dariya tace "To fad'a min a kunne naji, dan kar iska ta d'auka ta fitar a waje."
Shi ma cikin dariyar tare da son kawar da abinda ke ranshi ya tallabo fuskarta da hannu d'aya yace "Wannan ai ko ido bana bari ta gani ba bare kuma kunne ta ji."
Daidaita bakinta yayi akan na shi ya had'e labb'ensu, a sauk'ak'e ya shiga paputukar neman kamo harshenta, cikin samun nasara ya shiga tsutsar harshen yana sake k'amk'ameta a jikinshi yana son zura hannayenshi cikin rigarta, da k'yar ta jawo bakinta tana mayar da numfashi da k'yar kanta a k'asa, sake tallabo kanta yayi yana son had'a ido da ita yace "Ba kya ra'ayi na ne?"
Da sauri ta kalleshi tace "Ni d'in? Haka ya tab'a faruwa ne?"
Mik'ewa tayi tana gyara rigarta tace "Kai ma ai kasan duk sanda ka zo min ina maraba da kai, kawai dai baka tab'a kirana bane a wannan lokacin."
Dariya yayi ya sake yin tagumi yana kallonta yace "To yau na kiraki, wannan ai shi ne hadisin da kike son sani, an fad'a min akwai samun nasara sosai a fad'an bayan sallah isha'i da magauta."
Dariya tayi tana girgiza kai tace "Ba sai an min wani wayo ba, kawai mutum ya fito fili ya furta abinda ke zuciyarshi."
Wani shu'umin kallo ya mata da k'ananan idonshi yace " *Sawwama*."
Cike da karsashi tace "Na'am yah sheikh."
Mik'ewa yayi yana aje enveloppe d'in yace "To na kiraki da k'arfi yanzu, za'a iya bani had'in kai?"
Yanda ya jawota a hankali ya had'a jikinsu tare da zame mata hannun rigarta yasa ta yin murmushi tace "Dole na mana, idan na k'i amsa kira na kwana ina shan mita ana min wa'azi a gida."
Dungure mata kai yayi yace "Iyeeh! Ni ne ma sarkin mitar kenan? Yanzu fad'an Allahn da nake fad'a ma ya zama laifi, shikenan zan daina daga yau."
Hafsat dai dariya kawai take yi har ya rage musu hasken nan mai k'arfi, saida ya kwantar da ita a nutse ya mata runfa yace "Me zaki bani tukuncin ziyarar da zan kawo miki yanzu?"
Lumshe ido tayi cike da k'aunar mijin nata tace "Me kake da buk'ata *shugaba na*?"
Saida ya waina ido alamar tunani kafin yace "Ki amince zaki tafi dani hutu k'asar waje na sati d'aya."
Murmushi ta saki tace "Na amince."
Sumbatar bakinta yayi tare da jawo musu babban bargo suka rufe rabin jikonsu. 馃槑(Sheikh ka ci gaba da zazzaga tsiyarka a nan, Asas ma lokaci ya kusa)
*Bayan kwana biyu*
Ba wani abunda ya zanca mata har yanzu, zaman shiru da kad'aici kawai take, ga makaranta da aka hanata zuwa bare kuma k'ofar gida, babban bak'in cikinta shiq ne yanda har yanzu Asma'u bata shigo gidan b芒 ita ma, sosai take buk'atarta take so suyi hira ko zata d'ebe kewa, amma ita ma shiru babu motsinta.
Tunda safe su aunty Sahura suka zo kamar yanda sukayi da ita, da k'yar Abba ya yarda su tafi tare dan cewa yayi saidai su tafi kawai, Shapi'a ce ta nuna masa basu son kalar da zasu d'auko mata ba, shiyasa yace su tafi tare amma fa karsu yarda ko daidai da shiga fitsari ban d'aki ta b'ace musu. Haka suka fito suna gaba tana baya dan kunya take ji ta jera dasu tunda ta fisu tsayi, su kuma akan tafiya suke bare ta durk'usa musu saboda girmamawa.
Haka suka je babbar kasuwa sukayi siyayya ta zab'i abinda take da buk'ata kafin suka juyo zuwa gidan har rana ta take sosai, taxi na aje su k'ofar gida ta sunkuya ta rik'e hannun Sahura cikin magiya tace "Aunty Sahura, dan Allah ku rakani na ga halin da Asma'u take ciki, kwana uku kenan ban ji motsinta ba kar a zo bata da lafiya."
Juyawa Sahura tayi ta kalli Shapi'a tace "Shiga da kayan ciki muna zuwa."
Jinjina kai tayi rumgumi kayan da k'yar ta shiga dasu ciki, su ma gidansu Asma'u suka shiga daidai da fitowar mahaifinta daga d'akin amaryarshi zai fita, saida Mimi ta duk'a tace "Ina kwana Abba."
Shiru yayi kamar bai ji ba sai ma gyara zaman hularsa da yake, mik'ewa tayi Sahura na gaba zasu k'arasa shiga ciki, cikin dakakkiyar murya yace "Dakata Mimi."
Tsayawa sukayi a tare suna kallonshi, sabo yasa saida Mimi ta k'ara durk'usawa saboda girmamawa tana saurarenshi, saida ya gyara tsayuwarshi da kyau ya shiga nuna mata da hannu yana fad'in "...
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:54 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*21*
"Mimi dan Allah ki tafi gida kinji, karki fahimceni ba daidai ba, ni ubane dole na so ganin 'ya'yana cikin kykyawan tarbiyar da za'a yi misali dasu, idan da hali dan Allah ki fita a harkar Asma'u, bana son k'awancenki da ita ko kad'an, dan in na bari kuka ci gaba da k'awance to ita ma tarbiyarta zata iya samun matsala, kuyi hak'uri kinji."
Yana gama fad'a ya sa kai ya bar gidan da sauri, Mimi data kasa tashi tana d'ora kalamanshi a mizani tana basu kyakyawan muhalli tana son ta tantance me yake nufi, bata samu sahihiyar amsar da take buk'ata ba Sahura ta fizgi hannunta da k'arfi suka fita a gidan tana fad'in "Aikin banza kawai, ka raba k'awancen mana sai me, da me take k'aruwarta dashi da yanzu hakan zai zamar mata illa? Mtssssss! Kawai mutane baku da lissafi kudai jiran tab'i kuke kuce dama kunyi zaton haka."
Suna shiga gida Mimi da gudu ta fad'a d'aki tana fashewa da kuka, da kallo mama da Shapi'a suka bita sai Shapi'a ce tace "Lafiya? Me aka mata?"
Tsaki ta kuma yi tana zama akan tabarmar ta fad'a musu abinda ya faru, da k'yar Mama ta had'e wani mak'ulloton abu a wiyanta na bak'in ciki tare da share zancen kamar bai dameta ba.
Sun jima gida suna tattaunawa da hira ta yan uwa tsakaninsu, sai kusan la'asar suka bar gidan, suna tafiya Mama ta sameta d'aki bayan sunyi sallama, kofi ta mik'a mata tace "Shanye wannan."
Karb'a tayi tare da kifa kanta ta shanye tas saboda zak'in da taji da kuma k'anshin karanfani, karb'an kofin mama tayi ta juya tana murmushi da mamakin yanda Mimi ta karb'i maganin nan ta shanye, duk da dai tasan akwai zak'in mazark'waila amma kuma ana jin d'and'aon sassak'en b'aure. Shi ma kuma yanzu Sahura ta bayar a dinga dafa maata tana sha zai mata maganin zafi da wanke mata dattin mara sosai kasancewarta mai son kayan da suka shafi yaji da maik'o.
*Sheikh*
Yau kam Allah ya nuna sun bar k'asarsu Niamey inda suka shiga air france wanda ya saukesu Paris cikin awa hud'u, taxi suka samu ta kaisu babban masauki dan huta gajiya, da kan shi ya kama musu lafiyayyen d'aki da rakiyar ma'aikacin hotel d'in suka isa d'akinsu, tare suka fad'a wanka tare da rama sallahr data kubce musu, suna idawa sukayi oder abincin da zasu iya ci, saida suka gama sun samu nutsuwa kafin sheikh ya kira Aisha da wayar daya bar mata, hira sosai suka sha da yaran har da Hajia ma wanda wurinta suke kafin suyi sallama, daga nan ganin babu lokacin sallah da zai riskesu sai suka shiga bacci a tsanake cikin kwanciyar hankali.
*Mimi*
Yanda ta k'urawa littafin idonta da suke taf da hawaye zaka san ba karatun take ba, tun yamma sheikh ya fad'o mata a rai, haka kawai ta samu kanta tana mai jin wata matsananciyar kunyar sake had'uwa dashi, daki-daki take tuna tun daga had'uwarsu har jiya, lallai tayi kuskuren yi mishi k'arya, me yasa tayi tunanin daga waya ne ba zasu sake had'uwa ba? Me yasa bata zama mai taka tsantsan ba? Yanzu gashi sun had'u a matsayin surukai, zata shiga cikinsu a yanda lokaci yake nunawa, shin wace irin rayuwa zatayi a cikinsu idan ta je? A hankali ta nisa tare da sauke numfashi a zuciyarta tace "Abdul Waheed ka zama mai hak'uri da manta baya kaji, dan Allah ka manta da komai ka yafe min."
Motsin da taji yasa ta d'aga kanta ta kalli Abba da mama dake fitowaa daga d'aki, tsaye Abba yayi a kan ta tare da mik'a mata kud'i masu yawa yace "Ki tashi kije yanzu ki kai d'inkin kayanki."
Hannu biyu tasa ta karb'a tana fad'in "Abba nagode."
Cikin had'e fuska yace "Ke dakata ba godiya ba, minti talatin na baki ki je ki dawo, kuma ga k'aninki nan Yaseen kuje tare."
Juyawa yayi ya kalli Yaseen yace "Kai kuma kaji da kyau, wallahi karka yarda ta baka tsoro ko ta zare maka ido tayi wani wajen, umarnina ne wannan dan haka kar ka bari ta firgita ka, ka tabbatar ka saka k'afarka a duk inda ta saka ta ta k'afar, ka ji da kyau?"
Jinjina kai yayi yace "Eh Abba."
Wani irin babbakewa taji zuciyarta na yi na rad'ad'i da zafin rasa yardar iyayenta, shikenan ta b'arar da kimarta a wajensu, sun daina yarda da ita kenan har abada? Mik'ewa tayi tana sakin murmushin da mai ido 'a gani zaka san kuka ne take dannewa, a kwana uku kawai idonta har sunyi fari fat, fuskarta kanta ta canza kamar ba Mimi sarauniyar adon nan ba. D'aki ta shiga ta d'auko wanda zata fara dasu ta fito, jiki a sanyaye suka kama hanya ita da Yaseen suka fita, Abba ma fita yayi zuwa masallaci dan lokacin sallah isha'i ya matso.
Hawayen da take tafe tana sharewa ya saka Yaseen kallonta yace "Mimi ki daina kuka kinji, Abba zai yafe miki kawai yayi hushi ne."
Saida ta sake share hawaye ta ja majina tace "Na sani Yaseen, amma dole nayi kuka saboda yanda nake ji a zuciyata, ka duba kaga yanda su Abba suka sauya min gaba d'aya."
Matsawa yayi kusanta sosai ya d'aga kai yana kallonta yace "Kiyi hak'uri kinji, bana son ganin kina kuka, kuma jiya da yaya Asas ya zo yace na fad'a mishi idan baki daina kuka ba."
Share hawaye ta sake yi tace "Shikenan na daina, karka fad'a masa kaji."
Da haka suka isa bakin titi ta samu taxi, duk da ba nesa bane sosai amma lokacin da Abba ya bata ba zai isheta ta tafi a k'afa ta dawo ba tare data sab'a ba, suna zuwa ana ta sallah isha'i a masalatai, cikin sanayya sosai suka gaisa da mai d'inkin har yana fad'in "Mimi manyan duniya kwana biyu ina aka shige? Nasan dai ba kya wata d'aya baki yi sabon d'inki ba, amma wannan karan naga har an share wata d'aya na biyu ya ci rabi, sai na fara tunanin ko aure kikayi."
D'an murmushin yak'e tayi cikin muryarta mai kama da wacce tayi mura tace "Banyi aure ba amma dai na kusa, dan yanzu ma kayan bikina na kawo maka."
Dariya yayi yace "Haba ko da na ce, ni kam wannan wane babban yaro ne haka Mimi? Wai kinsan da ranarki ta k'arshe a shagon nan kina fita wani Alhaji ya shigo yana tambayar wacece ke."
Cikin son kawar da zancen tace "Allah sarki, gasu nan kayan ina fatan dai zan samu a kan lokaci."
Kallonta yayi da mamaki yace "Mimi lafiyarki kuwa? Ko an miki wanka da ruwan lalle ne? A sanina dake rik'e k'ugu kike yi ki nunani da yatsa ki ce idan ban gama kika dawo sai kin wareni na zama zakka a cikin zarma."
Yar dariya tayi tana girgiza kai tace "Can ma ai k'uruciya ce."
Girgiza kai yayi yace "Ban yarda ba." Yaseen ya kalla yace "K'ane na wanene mijin da zata aura?"
Cikin murmushi Yaseen yace "Sunanshi Ashraf."
Cikin zolaya yace "Amma dai ustaz ne ko?"
Girgiza kai yayi yace "A'a, amma dai k'annin sheikh Abdul Waheed ne."
Zaro ido yayi kamar zasu fad'i k'asa ya d'auki ledar data aje yana fad'in "Ahh! An gama, Mimi bar d'inkinki an wuce wurin kawai, yanzu zazzago min yan uwan nima na soka aljihu."
Mimi dai banda murmushi babu abinda take yi, saida ya nuna mata sabbin d'inkuna a wayarshi ta zab'a kafin sukayi ciniki ta biyashi ta bar shagon da zuwan zata dawo nan da sati biyu kamar yanda ya mata alk'awari.
Har ta tsaya dan tare taxi sai kuma Yaseen yace "Haba Mimi mu tafi k'asa dan Allah, ni bana son shiga taxi nan da can kawai."
Kallonshi tayi tace "Ba zaka gaji ba?" Dariya yayi yace "Gajiyar me? Baki ga tare da Abba har sa茂 muje masallacin kaddafi sauraren wa'azin sheikh ba."
Numfashi kawai ta sauke tare da rik'o hannunshi suka shiga duba titi dan su tsallaka, da k'yar suka tsallaka suka d'auki hanyar komawa gida, suna tafe suna hira dashi jefi jefi, yana so ya k'wace hannunshi dan shi dai ba yaro ba, duka shekara uku ce tsakaninsu dan kaf Mimi shekararta *goma sha bakwai* ne a duniya, hakan yasa wani abun idan tayi shi har da wauta a ciki da zallar haukar k'uruciya, sam k'in sakin hannunshi tayi har suka kusanto unguwarsu.
Da gudun tsiya ya sha gabansu da motar ya ci birki, take gabanta ya shiga luguden daka dan in akwai wanda ta fi tsana ma a cikin tarikicenta to Muttak'a ne, tsaye tayi sunaa kallo ya fito yana washe mata baki, kallonta yayi ya kalli Yaseen, cike da rashin sanin darajar d'an adam da mahimmancinsu gareta yasa hannu ya shafi kan Yaseen yana fad'in "Kai me sunanka? Wannan kai haka?"
Da k'arfi cikin jin zafi ta buge hannunshi ta nunashi da kakkauren yatsanta tace "Karka sake tab'ashi, wai