Showing 165001 words to 168000 words out of 185502 words

Chapter 56 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

20 Dec 2024

521

mishi ba daidai ba.


*Mimi*


Sabo aka ce tirken wawa, rashin ganin kiranshi a wayarta, rashin jin muryarta uwa uba a kwana biyun nan da ta zama mai masifar son jin k'amshin turarenshi had'e da son taji tattausan hannayenshi a na ta hannayen, sai suka taru suka mata yawa kamar zatayi hauka, tsabar d'orawa kai damuwa daren jiya mafarki tayi da ita dai ba zata kirashi da mummuna ba tunda da mijinta ne ta ga suna wata kalar azababbiyar soyayyar data saka ta tashi a wani mugun kasalance jikinta yayi mugun nauyi ga kuma fitowar ruwan da suka sa dole wanka ya kamata.

*Kwana* na uku kenan yau ta tashi da wannan muguwar kasalar, haka ta zauna tana kallon Iya na kad'a miya zatayi d'umame, yar yaloluwar rigar jikinta mai k'ananan hannuwa duk sai ta ji ta mata nauyi, tagumi ta buga tana ci gaba da kallon Iya tana jujjuya wayarta.

Kallonta Iya tayi tace "Tunda kin tashi me zaki ci na samu yaro ya siyo miki? Nasan dai b芒 mtuwo kike ci ba ai."

Ba tare data d'auke tagumin ba a kasalance tace "Ki barshi kawai Iya, idan na tashi ci zan nema."

Da kulawa ta sake kallonta tace "Kunyi waya da mijinki kuwa? Tun shekaran jiya da Hajiar ta zo nan ta ce yayi tafiya."

Cikin turo baki tace "Ina kira ba'a samu, amma zan sake kira."

Daga haka Iya bata sake cewa komai ba ta ci gaba da aikinta, Mimi kuma wayarta take kallo tana d'an kai hannunta kamar zata danna lambarshi kuma sai ta dakata, ajiyar zuciya kawai take saukewa lokaci lokaci tana d'an tuna shawarwarin Rayya wanda ko jiya sun jima suna hira a waya, tunawa da wata shawarar ta saka ta mik'ewa da sauri ta shiga d'aki, kwance ribom d'inta tayi take gashinta ya zuba a kafad'unta, gyara zamanta tayi sosai ta d'an duk'o yanda gwiwan hannayenta ke kan cinyoyinta, hakan kuma yasa rigar matsewa sosai nonuwanta suka d'an turo gaba.

Saita wayarta tayi ta d'auki kan ta selfie tare da shiga lambar sheikh, turawa tayi bayan ta tabbatar ta kyab'e fuskarta irin zatayi kuka sannan ta rubuta daga k'asa _"Na fad'a maka baka so na, dubi yanda na rame saboda kewarka?"_

*Abuja*, a babban d'akin taro suke kowanensu da babbar riga da ruwa da lemu a gaban teburen suna ta ci gaba da tattaunawa musamman a game da harkar sabon tsarin kula da marayu, wayar dake kan teburi ne tayi zuuuuu! Alamar shigowar sak'o kasancewar idan yayi nesa da gida yana barin connexion a bud'e, ganin sunan wacce ya kwana uku yana marari da d'okin son ganin sunanta ya fito ne yasa shi d'an jan 茅cran d'in sama ya bud'e tsaron wayar, ko da ya shiga lambar da sauri ya d'aga kai dan ya tabbatar babu mai kallonshi.

Gyara zama yayi a kujerar ya tallabe hab'a yana k'arewa k'irjinta kallo da ya ga ya mishi wani kyau yayi mulmul da shi, wani k'asaitaccen murmushi ya saki yana girgiza kai ya furta "Ryam."

D'aga kan shi yayi ya mik'e daga kujerar yana kallon shugaban ahlul-sunna ya d'an mishi alama da kai da hannu, da ido shi ma ya amsa mishi dan ya fahimci zai yi waya ne mai mahimmanci.

Yana fita ya kirata hoto mai motsi (vid茅o call, appel vid茅o). Tunawa da maganar Rayya cewa _"Ke macece kuma kin riga da kin shiga gidanshi, wani sauran aji ya rage miki da zaki ja a gidan miji? Akwai lokacin da kina jan shi ma tsinkewa zai yi dan an riga da an gama da ke, ladabi da biyayya da kuma hak'uri sune zasu zama miki jigo a rayuwar zaman aurenki, akwai lokacin da zaki ja ajinki amma kuma akwai lokacin da dole ki sauke girman kai dan ke ce a k'asa da ke, musamman ma ke Mimi da kike auren shahararren mutum wanda a iya majigi kawai 'yan mata da zawarawa ke kallon fuskarshi suna jin ina ma zai zama na su, ki iya takunki Ryam ta yanda zaki san lokacin da zaki gasawa mijinki aya a hannu da kuma lokacin da zaki fi k'ank'ara sanyi a gareshi. Kamar yanda kike da abokiyar zama zai fi kyau duk tsanani sirrinki tsakaninki da mijinki ya dinga tsayawa iya falonki ko na sa, karki bari ko da wasa ta san bakwa shiri bare har ta kaiki ga daka yajin barkono, na haneki da haka Mimi ba dan na isa ba saidan jin dad'in zaman aurenki."_

Tuna wannan kalamai yasa Mimi d'aga kiran tana sake narkewa tana wani karairaiyewa, fahimtar yau bebyn rigima take ji kuma ta gama faranta masa rai da tayi abinda bai d'auka zatayi ba sai kawai ya shagwab'e shi ma kamar yaro yace _"Ni fushi nake yi ma, shi ne sai yanzu za'a tuna da ni?"_

Kamar wata jaririya haka tayi da fuskarta cikin murya mai d'auke da shauk'i da son yin kuka tace _"Ni ce ma na manta da kai? Abdul kai ne fa baka so na, me yasa kayi hushi dani?"_

Gyara tsayuwarshi yayi ya girgiza mata kai yace _"Ryam ina sonki, na fad'a miki haka har na kusa gajiya, ki yarda ina sonki mana."_

K'wallan da take rik'ewa ne suka taho tace _"Yaushe zaka dawo? Ina so na gan ka Abdul."_

Lumshe ido yayi ya k'urawa k'irjinta ido yace _"Ry..ammm!"_

A hankali ta amsa da _"Na'am."_

Bud'e idonshi yayi fes cikin na ta yace _"Ki rufe abubuwan nan...indai ba so kike...na miki."_

Zuba mishi ido tayi tace _"Me zaka min?"_

Cikin murmushi yace _"Na miki ciki mana."_

Rufe fuska tayi da tafin hannu cike da kunya, cikin murmushi yace _"Bud'e fuskar mana, ai babu kunya a tsakaninmu, ko kin manta ke d'in matata ce sirrina."_

D'an bud'e fuskar tayi amma ba duka ba ta kalleshi tace _"Ni dai ka fad'a min yaushe zaka dawo?"_

Sauke numfashi yayi yace _"Ryam yanzu haka muna zaman k'arshe, insha'Allah yau komai dare zan koma gida, dan na bar aikin al'umma a can hutu ne na nema."_

Da saurinta tace _"Tom, sai ka zo."_ Kashe kiran tayi irin kunya take ji fa, wata dariya ya saki yana girgiza kai yace "Watak'ila fa shirin tarbata zatayi."

Juyawa yayi zai koma d'akin taron yana fad'in "Ashe dai tana d'an hankali wani zubin."

K'arasa shiga yayi yana ta dariyarshi shi bai ma san yanayi ba, haka ya zauna da wannan yanayin har suka gama taron nan misalin 12:30 na rana, daga nan ma tare da sakataran (secr茅taire) k'ungiyar suka halarci wani wa'azi, haka dai suka kasance har sanda dare yayi suka rakashi filin jirgi suka d'aga.


*Tuni* Mimi bacci ya jima da d'aukarta a gadon Iya dan ba wani abun take yi ba, Iya ma dai har ta kwanta bacci ya fara d'aukarta taju gadon na zuuuu! Bud'e ido tayi ta daddab'a Mimi tana fad'in "Ke tashi, hala shegiyar wayar nan ce ta ki mai kukan raguna."

Da k'yar ta bud'a ido ta lalubo wayar tana fad'in "Wai ke Iya a dare ma masifa kike?"

K'ulli ta shirga mata a baya tana fad'in "Zan ci uabnki yanzu."

Mimi kam ganin lambar sheikh ce nutsuwa tayi ba tare da sanin tayi ba ma ta d'ora a kunne, shiru kamar babu wanda zai yi magana sai kuma yace _"Fatan kina cikin aminci?"_

Numfashi ta sauke sannan tace _"Um! Ba kayi bacci ba?"_

Murmushi yayi mai sauti kafin yace _"Um! Gani a k'ofar gidansu Iya na zo d'aukarki."_

Da k'arfi ta zabura tace _"Me?"_

A dak'ile ya sake fad'in _"E, ina jiranki yanzu."_

Da mamaki tace _"Amm..."_

Bai bari ta fad'a yace _"Ryam ina jiranki yanzu ki shirya ki fito, ba buk'atar sai wani ya rakaki, ni da ke ma mun isa."_

K'it! Ya datse kiran alamar ya gama magana kenan, da sauri ta sauka a gadon tana fad'in "Iya tashi, tashi tashi Iya."

Mik'ewa tayi zaune tana fad'in "Lafiya wai? Ke wannan akwai jaraba."

Tsaye tayi ta kalleta tace "Wai shi ne a k'ofar gida ya zo mu koma."

Da sauri ta sauko tana fad'in "Alhamdulillah, ka ga malamai magada Annabawa, haka ai shi ne daidai dama wallahi, maza maza to a tafi a bar min gidana."

Tale baki tayi tace "Eyeee! Wallahi Iyar nan ma dai, ba komai."

Zage doguwar rigarta tayi gaban Iyar ta shiga neman abaya a cikin kayanta, kawar da kai Iya tayi tana fad'in "Kai Allah ya shiryaki, bawan Allahn nan haka yake shan tab'arar nan iri iri a wurinki."

Ba tare data juyo ba tace "To me na yi kuma?"

Tab'e baki Iya tayi tace "Bakiyi komai ba." Murya k'asa k'asa kuma tace "Allah yasa ki je gabansa kina cire kayan ya tsala miki bulala a baya."

Kad'awa Iya d'uwawu tayi tace "Ba bakin ki ba Iyale."

Tsaki Iya tayi tace "Yar banza kinga yanda kika k'ara zama dumemiya kuwa?"

Saka doguwar rigar tayi ta saka kallabinta ta yane kan ta, turare ta d'auka ta shafe jikinta sannan ta tusa duk kayanta data barbaza ta rufe jakar, d'aukar k'aramar jakarta tayi da wayarta ta kalli Iya tace "To su Iya, a yafi juna kuma dan Allah, ni na koma inda na fito, idan Abba ya zo ki fad'a masa na koma."

Girgiza kai Iya tayi tace "Allah raka taki gona."

Waro ido tayi tace "Yanzu Iya ina ce wa na zo gidanki shan kunu amma kike min irin haka, shikenan zan je gidan Aunty Shafi'a kawai."

K'yaci Iya ta mata tace "Allah ya sawak'e min wahalar zan d'orawa kai na, ai can kuje ku k'arata."

Jan jakar tayi tana fad'in "Iya har da madara fa zan dinga sha a madadin kunu, baki so mu sha tare?"

Hararanta tayi sai kuma tayi murmushi ta girgiza kai irin ba magana kawai, dariya tayi tana k'arasa fita a d'akin tana fad'in "Iya dai baki yasan dad'i, to ki kula min da mai gidana idan ya dawo."

Da kallo ta bita har ta fita sannan tace "Allah ya tsare, Allah ya baku zaman lafiya, Allah k'ara miki farin ciki a rayuwarki."

Tana fitowa ta tsaya turus saboda ganinshi jingijine a jikin motar, cikin tak'on k'asaita ya shiga takowa gabanta, jakarta ya karb'a a hannunta ya jata zuwa bayan motar ya bud'e ya saka, juyowa yayi ya kalleta tana tsaye har yanzu.

Tunani take daga tsayen tare da hango yanda zata kwanta a k'irjinshi, wallahi har ranta take son taji ta shiga jikinshi tayi luf shi kuma ya sake rufeta da hannayenshi dake d'auke da babbar rigarshi, tan so ta lumshe ido ta ja numfashi sosai ta sake k'amk'ameshi. Amma wani abu d'aya shi ne daga ganinshi yanzu da yanda turarenshi ya daki hancinta sai taji tsigar jikinta ta tashi, wata kasala ta ji a take har saida ta lumshe ido saboda sanyayyen fad'uwar gaban da ta ji, haka kawai ta ji har wani abu yana tsikara mata a gabanta tare da jin wani mutsu mutsu kamar ruwa na zubo mata.

Gyara tsayuwarta ta sake yi ta matse k'afafunta wuri d'aya sai kuma ta ji tattausan hannunshi data kwana biyu tana mararin ya tab'a na ta hannun, janta yayi a hankali ya bud'e mata k'ofar ta shiga ta zauna, shiga yayi shi ma ya zauna sai lokacin ta tatbbatar tare suke da dreba ashe. Har suka d'auki titi babu wanda ya ce wani abu, saidai hannunshi dake cikin na ta har yanzu yana ta murzawa yasa gaba d'aya ya kashe mata jikinta, banda zubar abu a k'asanta babu abinda take ji, k'aik'ayi take ji jikinta na d'uka musamman ma k'asan dz kuma nonuwanta, lumshe ido take tana lashe leb'enta da take jin yana bushewa.

Sheikh da a hankali yake satar kallonta shi ma lumshe idon yake yana jin dad'in yanda yake tattausa hannun na ta mai tuwon gaske, saida suka yi nisa a hanya kafin ya d'an sunkuya kusan kunnenta yace "Kinyi kewata ne?"

K'ara rintse ido tayi sai taji kamar zata ce "Wayyo Allah na."

Sunkuyar da kai tayi dan ita kam wannan abu da take ji kuka ma yake neman sakata, murmushi ya saki na jin dad'i tare da kuma rusunawa yace "Ina kewarki."

Rawa bakinta ya d'auka hakan yasa ta d'agowa ta kalleshi da idonta da suka canza kala dan jaraba bakinta na hard'ewa tace "...



_Karku saka ran ganin rubutu gobe dan ina da abubuwa dayawa gaskiya._馃グ





*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*55*




Rawa bakinta ya d'auka hakan yasa ta d'agowa ta kalleshi da idonta da suka canza kala dan jaraba bakinta na hard'ewa tace "Ab..du...l."

Murmushi ya saki yana kallonta bai ce komai ba har suka isa gida, da kanshi ya bud'e mata k'ofar ta fito ya zagaya ya d'auki jakarta, tunkarar shiga falon sukayi yana fad'in "Da fatan ba zaki sake yi min yaji ba ko?"

Cike da kunya ta sunkuyar da kai sai kuma ta kalleshi tace "Indai Aisha ba zata daina min rashin kunya ba gaskiya..."

Kallonta yayi yace "Da matsala kenan? To indai Aisha ce kwantar da hankalinki, tana d'akin mijinta ita ma."

Da sauri ta kalleshi tana zaro ido tace "Aishar? Har..."

Sai kuma tayi shiru, jinjina kai yayi yana tura k'ofar falon a sanyaye yace "E, kwananta biyu d'akin mijinta."

Cak ta tsaya tana kallonshi da yanayin rashin jin dad'i tace "Amma kuma baka fad'a min ba, ban sani ba wallahi da na..."

Ajiyar zuciya ta sauke da rashin jin dad'i, murmushi yayi yana kallonta yace "Ba biki akayi ba, nasan kuma fushinki ba zai wuce ki ce baki zo biki ba, aure kawai aka d'aura a masallaci, ni ma bana nan akayi d'aurin auren."

Sallama yayi a falon a tausashe yana shiga gaba d'ayanshi, gaba d'aya k'ofar suka zubawa ido suna amsa sallamar da fara'a a fuskarsu, duk mik'ewa sukayi da sauri sukayi kan shi, Munzeer ya fara d'auka kafin Aswan ya rumgume shi haka ma Heezam, Hafsat ma a hankali ta k'araso tana kallon Mimi dake bayanshi tana amsa gaisuwar su Heezam da fara'a.

Tafukan hannayenta ta saka ta rufe fuskarta cike da raha tace "Har na ji kunya k'anwata, na ji kunyar ganinki ba tare da ni na je na taho dake ba."

Sai kuma ta bud'e fuskarta ta matsa kusan Mimi suna kallon juna tace "Amma kiyi hak'uri dan Allah, wallahi sabgar auren Aisha ne ta d'auke min hankali na."

Cike da dauriya da jin kunya ita ma ta d'an turo baki tace "Ni ai hushi nake daku aunty."

D'an waro ido tayi tace "Lahhhh! Me mukayi kuma? Ko da yake nasan muna da laifi, amma ki gafarcemu."

Takwaf takwaf tayi da fuskarta tace "Aunty auren Aisha fa akayi ban sani ba."

Sai kuma ta sunkuyar da kanta tace "Ko da yake laifi na ne, inda ina nan da anyi komai da ni ai."

Da farin ciki Hafsat ta rumgumeta a jikinta tana fad'in "Kiyi hak'uri Mimi, ranar ma sharrin shaid'an ne abinda ya faru, insha'Allah ba zai sake faruwa ba."

Cikin d'ari d'ari ita ma ta d'an shafa bayanta tace "Ni ma ki yafe min aunty wallahi nayi nadama."

"Ba komai." Ta fad'a tana d'agowa daga jikinta, Sheikh dake kallonsu cike da jin dad'i ne yace "Wato ni an wareni ko? Ko ganina ma ba'a yi."

Wani farrrr Hafsat ta masa da ido tace "To ina ta yar uwata ina zan dubeka sheikh."

Jinjina kai yayi yace "Uhum! Ni kuma da ba d'an uwanki ba ko?"

Murmushi tayi tace "Ranka shi dad'e barka da zuwa, an zo lafiya?"

Da murmushi shi ma yace "Lafiya lau Sawwama, ya gida da yara? Na bar miki ragamar komai a hannunki ko? Allah ya miki albarka ya ci gaba da baki ikon kula da gidan nan ko bayan raina."

Wani dammm! Mimi ta ji tayi saurin kallonshi, murmushi Hafsat tayi tace "Ameen ya Allah."

Murmushi ya mata ya kalli Mimi yace "Ki wuce ciki."

Jinjina kai tayi ta ja jakarta ta nufi na ta falon, d'an kallonta Hafsat tayi sai kuma ta dawo da kallonta kan Sheikh dake fad'in "Hajia muje a had'a min ruwan wanka ko."

Kallon yaran yayi yace "Zan shiga na fito sai m没 zauna da ku muyi hira."

Da ladabi Heezam yace "A fito lafiya Abie."

Saida suka nufi hanyar d'akinta cikin rad'a Hafsat tace "Yallab'ai, ina ga me zai hana ka je wajen k'anwata, kaga yau ta dawo ya dace ka zauna da ita."

Da mamaki ya kalleta yace "Ban gane ba? Kin manta kwananki ne? Ai ita tayi yaji ta bar gidan, hakan ba zai sa dan ta dawo ba na d'auki kwananki na kai mata ba."

Murmushi tayi tace "Ba haka nake nufi ba nima, nufi na na bar mata kwanan na wa, duba da yajin ma ai ni da 'yata ne silarshi."

Girgiza kai yayi yana wucewa da alamar bai fa gamsu ba, rik'o hannunshi tayi a marairaice tace "Dan Allah sheikh, wallahi na bar mata ne har cikin zuciyata."

Harara ya galla mata yace "To na fad'a miki ina da buk'atar wani abu ne a gurin wata? Bacci zanyi na huta gajiya malama, idan kwa'a dani ne ba zaki iya ba sai ki je d'akina."

Wucewa yayi ya barta hakan yasa ta binshi da kallo, girgiza kai tayi ita ma kafin ta bi bayanshi gabanta na fad'uwa tana tunanin ta yanda zata fara fad'a mishi bata sallah yanzu, a k'aida dama tana ganin jini take fad'a masa ko da baya gidan, wannan kuma an yi katarin baya gari kuma yau data kira dan ta fad'a masa sai layin ya k'i shiga har sai yanzu da ya zo, da a ce bata riga ta masa tayin kwana d'akin Mimin ba, yanzu idan ta fad'a masa sai ya ce dan tana so a dole y'a kwana a can ne.

Cikin kissa da salo take tayashi cire kayan tana ta langab'ewa tana son fara d'aukar hankalinshi zuwa kan ta kafin ta fad'a masa, tsura mata ido yayi yana kallo sai kuma ya saki murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login