Showing 39001 words to 42000 words out of 185502 words
ba tuwon suka dafa ba, sai kawai tayi murmushi tace "A gaskiya ba ma da tuwo, yau ba shi aka girka ba saboda zuwanka."
Da mamaki ya nuna kan shi yace "Ni kuma? Me yasa?"
Sunkuyar da kai ta sake yi ba tace komai ba, girgizz kai yayi yace "Maah, ni fa ke nake so ba matsayinki ko abinda kuka mallaka ba, rayuwar da kuke yi ita ke bani sha'awa kuma ita nayi niyyar farawa tare da ke, dan haka duk wata wacce kika san gwana ce ita a harkar tuk'a tuwo to zai fi kyau ki nemi kusanci da ita, dan a kowane dare na rayuwarki gidana shi zaki tuk'a min nayi ta sulmar kayana."
Kecewa tayi da wata siririyar dariya saboda maganarshi ta k'arshe, jinjina kai tayi tace "Ai ni ma na iya, na iya tuwon masara, tuwon hatsi, tuwon dawa dana shinkafa, sannan na iya na garin doya ma da kuma na semovita."
Jinjina kai yayi yace "Yawwa *maah le* ta, haka nake son ji."
Juyawa tayi tana fad'in "Bari na kira mama ku gaisa." Shiga d'aki, tabarmar dake jingine a farkon shiga ta d'auko mama ta kalleta da alamar tambaya, ita ma da ido ta amsa mata da "Shi ya ce na d'auko."
Saida ta juyo zata fito tace "Mama muje ku gaisa."
Sunkuyar da kai tayi ba tace k'ala ba, cikin shagwab'a tace "Mama muje, ko na ce ya shigo ne?"
Da sauri ta kalleta da mamakin wai me yasa wasu lokuta bata gane cewa tana jin nauyinta a matsayinta na babbar 'yarta ne? Girgiza kai tayi ta mik'e ta d'auki d'an gajeran hijabinta ta saka har k'asa, gaba take mama na baya hakan yasa sam bai kula da mutum a bayanta ba, saida ta duk'a dan shinfid'a tabarmar ya ga mama, har ga Allah tunaninshi bai bashi mahaifiyarta ma haka take ba, gashi fuskar maman ba wani tsufa ko dattijantaka, tarrr! Ya kalli fuskar mama da murmushi ya d'an d'ago hannunshi irin yana jiran ta k'araso d'in nan a cabke hannu tunda ga k'anwar matar da zaka aura. Mik'ewar da Mimi tayi ne ta juyo ta nuna mishi Mama tace "Ga mama ku gaisa."
Luuuuuu! Yayi ya sauke hannunshi tare da durk'ushewa yayi tsugunno irin na maza kan shi k'asa, gaba d'aya sai ya rasa bakin magana daya tuna yanda ya dinga kallon fuskarta, har fa yayi shigo dafa kan ta ya bata hannu su gaisa yace mata " *beby ya kike? Ya sunan k'anwar ta mu*?"
Lallai ashe da ya tabka kuskuren da har abada ba zai daina jin kunya ba, ganin ya kasa fad'an komai sai mama ce tace "Ina wuni?"
Da sauri cikin kunya yace "Ina wuninku?"
Da fara'a tace "Lafiya lau, an zo lafiya?"
"Lafiya lau, na sameku lafiya?" Ya fad'a kan shi a k'asa sosai, ita ma kan na ta a k'asa tace "Lafiya lau, ya mutan gida?"
Da fara'a yace "Lafiya lau, sun ce na gaisheku."
Da fara'a ita ma tace "Muna amsawa, a gaishe su sosai."
"Insha'Allahu zasu ji." Juyawa tayi tana fad'in "Allah ya shi albarka, a gaida 'yan gidan."
Saida y'a ji shigewarta ya sake d'ago kai, eh lallai Mimi baiwar Allah ce daya jarabeta ya cirota daga tsatson bayin Allahn nan.
Alama ta mishi da hannu ya zauna, saida ya cire takalminshi a nutse ya zaune tare da jingina a bango, d'aki ta koma ta d'auko duk abinda ta tanada domin shi ta kawo ta aje mi shi, cire takalminta tayi ita ma ta zauna kan tabarmar ta fara tsiyaya masa jus d'in, mik'a masa tayi ya karb'a yana murmushi yace "Nagode gimbiyar mata."
Murmushi tayi ita ma tana k'ara gyara zamanta irin na tsakiyar sallah (zaman tahiya), izinin shi ta nema ta zuba mishi abinci, jinjina kai yayi alamar eh, cikin nutsuwa ta fara zuba mishi farar macca da soyayyan nik'ak'en naman da aka nad'e cikin k'wai, sai soyayyen dankali da ta yi wa jus na mayonnaise da waken gwangwani.
Tura mishi tayi gabanshi ya gyara zamanshi yana fad'in "Da nasan wannan shagalin zan tarar ai da na taho da tsohuwar katifa ta."
Dariya tayi tace "Ka me da ita?"
Cike da zolaya yace "Da na ci nayi kwance mana."
Murmushi tayi ta girgiza kai tace "Gashi gidanmu baya d'aukar bak'on da baisan da zuwanshi ba."
Dariya shi ma yayi yanaa fad'in "Da alama dai baki son bak'o saboda karki raba shinfid'arki da shi, amma karki damu a gidana gadona zan ara miki kina kwana a kai."
Kunya ce ta rufe ta kawai ba tace komai ba, a nutse ya fara aika lomar abincin nan yana lumshe ido, da yatsa ya shiga nunata yana fad'in "Kar ki ce santi ne nake fa, dama ina so na tambayeki kalar kayan da zaki saka a ranar aurenmu?"
Waro ido tayi tana doka murmushi tace "To me kake kenan?"
Girgiza kai yayi yace "Na kare kaina tun kafin na yi magana fa."
Murmushi kawai tayi tace "Ka zab'a mana kawai."
Kallonta yayi yace "Kin yarda dani kenan?"
Lumshe ido tayi tace "D'ari bisa d'ari."
Jinjina kai yayi yace "Insha'Allah gobe zan turo d'an sak'o ya kawo miki wanda na zab'a."
Zaro ido tayi tace "Da wuri haka?"
Hararanta yayi yace "Ban gane da wuri ba? Wata d'aya ne fa, ni fa ranar kawai nake jira ta zo dan na gama komai, Maah kawai nake jira ta sameni gidana."
Sunkuyar da kai tayi cike da kunya, da haka suka ci gaba da hirarsu cikin farin ciki har yayi shirin tafiya, duk mik'ewa sukayi inda ya ce ta kira masa k'annanshi sannan ta fad'awa mama ya wuce, yanda ya buk'ata haka tayi dukansu tare suka isa har k'ofar gidan, saida y'a fara sallama da ita ya nuna mata cikin gidan yace "Koma ciki, nagode da rakiya."
Ba musu ba d'ard'ar tayi abinda ya ce, saida ta shigo kuma saita samu kan ta da tunanin wai ita ce yau namiji ba ubanta ba ya umarta haka, da yatsa fa ya mata wani fit fit koma ciki, murmushi kawai tayi tana fad'in "Allah kar ka kawo ranar da wani zai ramawa yan uwanshi maza abinda na musu, dan ba zan iya d'auka ba gaskiya."
D'aki ta samu mama ta shiga cire kayanta, Mama kam kallonta take har ta cire rigar ta saka riga da wando na bacci, tana idawa su Yaseen suka shigo da sallama da murna, duk gaban mama suka zube suna nuna mata ledar hannunsu, da sauri Mimi ta zauna gabanta ita ma ta jawo ledar ta shiga duba kayan, kayan k'walam ne sai turaruka da kuma kud'in daya zuba a ledar, d'aukar kud'in tayi ta ware jaka bibbiyu har guda goma ta ninkesu tace "Wannan na Abba ne."
Ragowar mama ta mik'awa tace "Mama ga na ki."
Kallonta su Yaseen sukayi suka ce "M没 fa aka ba, shi ne komai ba zaki bamu ba."
Harara ta dalla musu ta nuna Amir da yatsa tace "Daina kumburo min bakin nan kafin ka ji jini a ciki."
Kud'in data d'ora kan cinyar mama ta koma ta d'auka ta zagi jaka bibbiyu ta mik'a musu tace "Ku yi abinda zakuyi."
Farin ciki ne ya lullub'esu wanda ko dala biyar suka samu a hannu murna suke. Mama dai bata tanka musu ba sai al'ajabin lamarin Mimi, ta d'auka zata d'auki wani kaso a cikin kud'in ita ma, amma ba wannan ne gabanta ba mahaifinta ne yafi damunta, dama kuma ko bata cire mishi ba dole ita zata damk'a mishi, kawai ta bar ta tayi yanda take so ne, dan tsabar kawaici ko d'an abun tab'awa wata rana Allah ya hore Abba ya kawo indai Mimi na gidan ita ke rabawa.
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:52 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*14*
Washe gari tsaf ta shirya ta kama hanya zata fita Abba dake cin d'umame ya kalleta yace "Mimi."
"Na'am." Ta fad'a tana juyowa, saida taje daf dashi ta tsuguna kafin yace "Yanzu ba zaki fara jaraba cin tuwo ba? Ki gwada mana ko dan halin rayuwa."
D'an yatsina fuska tayi tace "Amma ba zan iya ci ba, idan na je makaranta na ci alala ko meat pae."
Gyara zamanshi ya d'anyi yace "Mimi, zan amince ki je gaida mahaifiyar yaron nan, amma abisa wani sharad'i."
Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar, d'orawa yayi da "Zan amince ne saboda sanin d'an wane gida ne shi, a sanina da iyalen Aliyu Sharif ba mutanen banza bane, mutane ne manya masu dattako, matsalarsu d'aya shine auren *k'warya* ta bi *k'warya* da suke yi, gaba d'aya ahalinsu sun dunk'ule sun zama d'aya saboda suna auren zumunci ne a tsakaninsu, idan har kika ga wani wanda ba daga cikin ahalinsu ba to tabbas akwai huld'a ta kasuwanci ko abinda yayi kama da haka, idan kika ga wanda ba ahalinsu ba kuma d'an talaka to rabo ne ya kai shi ahali, amma yana fuskantar tsangwama daga garesu da wariyar launin fata, a hakan ma dan akwai dattawan arzik'i da suke son dak'ile wanna' d'abi'a ta iyalin, saidai duk abinda aka ce maka mata sun rik'eshi da hannu biyu sai an sha wuya ake cin nasara."
Shiru tayi har saida yace "Abu na farko ina so ku min alk'awarin yin hak'uri da duk kalar tarban da kika samu daga danginshi, na biyu kuma kiyi hak'uri da duk irin wulak'anci ko cin zarafin da zai biyo baya, na uku shi ne ban yarda ba bayan gidan mahaifiyarshi da kuma yayarshi ki yarda ki k'ara binshi wani wurin ba, ko da hakan na nufin ki b'ata masa rai ne, sharad'i na gaba kuma shi ne dole sai in kin yarda zaku tafi da Asma'u ko d'aya daga cikin k'annanki dan su rakaki."
D'aga kai tayi ta kalleshi a ladabce tace "Abba, hakan na nufin tarayyata da Asas zata iya jawo cin mutumci kenan?"
Girgiza kai yayi yace "Ban da tabbas Mimi, amma daga gidan da kika fito da tsatson da kika fito nasan dole wani abu makamancin haka zai iya biyowa baya."
Girgiza kai tayi tana hawaye tace "Amma a dakatar tun yanzu, a dakatar kawai indai aurena da Asas zai sa a zagi hallitarku ko talaucinmu, bana son auren na fasa na hak'ura dashi."
Duk da mamaki suka kalleta sai Abba daya zura hannunshi ya dafa kafad'arta yace "Uwata, me yasa zaki ce haka? Kiyi hak'uri kinji, komai zai wuce kamar ba'a yi ba ai, abinda nake so ki sani shine yaron nan bai k'yamace ki ba duk da sanin wacece ke, dan haka kiyi hak'uri da k'alubalen da zaki fuskanta daga danginshi."
Ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana shashek'a tana jinjina kai alamar to, d'auke hannunshi yayi daga kafad'arta yana fad'in "To yanzu fad'a min wa kika zab'a dan ya rakaki?"
Cikin rawar murya tace "Zamu tafi da Asma'u."
Jinjina kai yayi alamar gamsuwa yace "To ki fad'a mata saita nemi izinin iyayenta ita ma sai ku tafi."
Tab'e baki Mama tayi ba tace komai ba, har zata mik'e yace "Gashi ke baki da waya, da gobe sa茂 ki je ku gaishe da mahaifiyar yaron nan."
Satar kallonshi tayi tana tunanin abinda ya fad'a, sai taji kunyarshi ta kama ta sosai duba da yanda take munafurtarsu haka, cikin ladabi tace "Abba dayake ina da lambarshi daya bani yace ko da ina buk'atar wani abu saina kirashi."
Zaro ido yayi yace "Amma dai ai baki kirashi ba ko?"
Girgiza kai tayi alamar a'a, jinjina kai yayi yana sauke b'oyayyar ajiyar zuciya yace "Yayi kyau, kuma idan kina buk'atar wani abun ki tuntub'eni zan miki."
Jinjina kai tayi alamar to, d'orawa yayi da "To ya za ayi ki fad'a masa?"
Jinjina kai ta sake yi tace "Zan kirashi ko da wayar Asma'u ne."
Da sauri ya girgiza kai yace "A'a karki kira, ki bari idan kika taso lokacin na dawo nima da rana saina baki wayar ki kirashi."
Jinjina kai tayi tace "To Abba, nagode."
Murmushi ya mata yace "Allah ya miki albarka, tashi kije."
Mik'ewa tayi ta fita a gidan tana share 'Yar k'walla da hijabinta mama na binta da kallo har ta b'ace ma ganinta.
*12:06*
Kamar kullum tafe suke tare da Asma'u cikin nutsuwa suna hirarsu, saida suka kusa k'arasowa gidan suka hangi gungun su Maryam tare da k'awayenta, tab'e baki Mimi tayi irin ko a jikina d'in nan, Asma'u kuma data lura da yanayin fad'a ne suke yasa ta kallon Mimi tace "Mimi dan Allah da manzonsa ki wuce cikin gida karki kula gayyar tsiyar nan."
A yatsine ta kalleta tace "Ke! Bana da lokacin wanda suka fi su aji ma bare kuma su karan kad'a miya."
Murmushi Asma'u tayi tace "Yawwa Mimi, rabu dasu kawai, kinsan fa amarya da tsautsayi"
Murmushi sukayi a tare, zasu wuce kawai suka zagayesu su shiga, wasu sun d'aure k'ugu wasu kuma da itace a hannu, Maryam fake shugabar ce ta tsaya gaban Mimi tace "D'aukar fansa na zo Mimi, dan wallahi dukan da kika min baki wa banza ba."
Wani luuuu! Tayi da idonta tare da jefanta da wani kallo sannan ta yatsina bakinta tace "D'aukar fansa? Da wannan zugar?"
Tsaki tayi tare da d'auke kai daga gareta, hannunta Asma'u ta kama tana fad'in "Muje ke."
Sak茅 tare gabansu sukayi Maryam na fad'in "Babu inda zata je sai jikinta ya gaya mata, idan sauri kike ki tafi."
Wani dattijo ne ya zo wucewa ya kalli yanayinsu yace "Kai! Me yake faruwa ne? Ba daga islamiyya kuke ba? Maza ku wuce gida kar kuyi mana fad'a a nan."
Gyara tsayuwa Maryam tayi tace "Ba ruwanka Baba kai dai yi tafiyarka kawai."
Asma'u ce tace "Wai ke Maryam me yasa baki da tarbiya ne? Yanzu wannan ba yayi sa'an babanki ba."
Tsaki tayi tace "Ke rufe min bakinki, ba dake nake ba."
Tab'e baki tayi ta sake kama hannun Mimi tace "Mu tafi Mimi, karki kulata dan Allah."
Cire hijabinta tayi ta wani jijjiga da fad'in "Ke babu inda zata je fa sai na..."
Muryar Alhaji Saminu sukaji a bayansu da fitowarshi kenan yana fad'in "Mimi lafiya?"
Duk kallonshi sukayi sai Mimi data wurga masa harara, juya baki Maryam ta fara yi tana fad'in "To fa! Ga kwarton na ta nan ya fit..."
Bata rufe baki ba Mimi ta kasheta da mari a hassale tana cin kwalar rigarta da fad'in "Kwarton wa? Wa kike had'awa da shi?"
Kacamewa sukayi duk su biyar d'in suka taran ma Mimi, Asma'u ma na ganin haka shigar mata tayi dan haka da gudu Saminu da mai gadinshi suka taho, haka ma yayan Asma'u daya fito yanzu sai wata mata da zata wuce ita ma, da k'yar suka rabasu su Maryam na ta aika musu zagi, a nutse Saminu ya kalleta yace "Haba Mimi, wannan ai ba girmanki bane fad'a a titi, me yayi zafi haka?"
Cike da fitsara Maryam tace "Ka fad'i haka mana saboda karuwarka ce, kun d'auka bamu san me ye tsakaninku ba? Ai ko kallon da take zuwa yi bana Allah da Annabi bane."
Da b'acin rai ya kalleta yace "Wai wace yarinya ce wannan fitsararriya marar kunya?"
Juya baki ta shiga yi kamar zata cira shi, yayan Asma'u ne yace "Jikanyar Kaka ce mana, tarbiyar da aka bata kenan zank'amar banza."
Shi ma harara ta wurga masa tana sake d'auke kan ta da gunaguni, Mimi dake hararenta ne ta nunata tace "Wallahi Maryam kika koma shiga harkata saina b'allaki, saidai kakarki tayi jinyarki."
A fusace tayi cikin gida tana sab'a kakarta a kafad'a, hakan yasa Maryam binta da shewa har da bubbuga bakinta tana fad'in "Yeeeeeehu! Ku duneta karuwa kawai, karuwar gida daga nan zaune, ita ke ciyar da iyayenta da kud'in iskanci, yeeeehu anji kunya dai, har wani felek'e ake mana wai ita zatayi aurean kawo kud'inta, shi ma baisan ragowar samarin unguwar nan zai kwasa ba."
A harzuk'e ta sake juyowa ta dawo kan ta da Sauri Asma'u ta rik'eta saboda ganin Abban mimi ya karyo kwanar layin, cikin jin haushi yayan Asma'u yace "Wai ke wace irin dabba ce? Wannan shi ne matsalar rainon Kaka kenan, mtssss?"
Abba na zuwa ya shiga bin mutanen wurin da kallon tuhuma musamman ma Mimi, da k'yar yace "Me yake faruwa ne?"
Asma'u ce tace "Abba wallahi su Maryam ne kawai suka mana taran dangi ni da Mimi."
Kallon Mimi yayi data sunkuya kan ta a k'asa yace "Shiga cikin gida."
Wucewa tayi tana kumbura hakan yasa shi kallon Maryam d'in dake fad'in "Dole ki shige mana anji tsoro, wallahi da sai mun miki terere a unguwar nan, kuma naje an fad'a karuwa karuwa karuwar gida."
Rintse ido Abba yayi yana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Sake bud'ewa yayi ya kalleta, Asma'u ce cikin jin haushi tace "Saidai in kece karuwar amma ba Mimi ba, banza jahila sai tsayin kawai babu lissafi."
A zabure tace "Ke rufawa kanki asiri, ai ke dama yar abi yarima asha kid'a ce, tunda duk h么tel d'in da za taje ke kika rakiyarta, sannan tana sammiki wani kaso a cikin kud'in tazubar d'in, gaba kad'an ke ma zata fara had'aki da alhazan birninta."
Wani mahaukacin mari Saminu ya kifa mata cikin b'acin rai yana fad'in "Ke ashe mahaukaciya?"
A hassale ya juya y'a kalli yayan Asma'u yace "Kai ina ne gidan? Yau sai kun bar unguwar nan fitinanniya kawai."
Wani kuka ta fashe dashi tana fad'in "Kaka, Kaka."
Ai kamar jira take ta kira sunanta ta fito ko mayafi babu tana fad'in "Waya tab'a min yar amanata? Wani tsinanne ya daki marainiyar Allah?"
Saminu ne ya nuna kanshi yace "Ni ne nan, wannan jikarki ce Iya?"
Saida ta kutsa ta kama hannun Maryam tace "Jikata ce? Me tayi ka daketa?"
Cikin bud'e baki da rashin wayo Maryam tace "Wai kawai dan na ce Mimi karuwar gida ce tana bin samarin unguwar nan, shi ne ya mareni a fuska yana zagina yana kirana mahaukaciya, kuma ai gaskiya na fad'a ko Kaka? Waye