Showing 15001 words to 18000 words out of 185502 words
lambar Muttak'a."
Yatsina fuska Salma tayi tace "Shi ne dama zai zo kika d'au wannan wankan?"
Kallonta tayi tace "Zaki d'aukeni hoto ne, idan ya kawo min wayar na ga kalata saina rik'eta na d'ora hotunan a statu na gaishe da mutane."
Girgiza kai Asma'u tayi ita dai ta zuba mata ido kawai, wayar Salma ta d'auka ta kira lambarshi da tasan ta saka sunan mace dan kar ta samu matsala da na ta alhajin ta kira, tana jin an d'aga ta mik'a mata wayar ta karb'a, saida tayi kamar ba za tayi magana ba kafin tace "Ina gidansu Salma, minti ashirin gareni na komawa gida, idan na tafi gaskiya ba zamu had'u nan kusa ba."
Da farin ciki yace "Gimbiya Mimi an gama, gani nan zuwa cikin minti goma."
D'inn? Ta yanke kiran tare da mik'awa Salma wayar tace "D'aukeni."
Sauka tayi daga kan gadon da take ta shiga snapchat ta fara d'aukarta, duk da rigar dake gareta haka ta matsa mata suka d'auka tare, Asma'u ma da k'yar ta iya tsayawa suka d'auka guda uku da hijabinta a jiki, har hoto mai motsi saida ta mata abun kamar na hauka ko gajiya basa yi. Tsawon mintuna suka d'auka saida ya kira yace gashi ya zo ta kallesu tace "Ina zuwa 'yan mata, ku tayani da addu'a Allah yasa IPhone zai bani."
Dariya Salma tayi tace "Zai zaki iya fasa mishi da kai da duk wacce ya baki idan ba IPhone d'in b芒 ce."
Dariya sukayi ita kam ta juya ta fita a takonta d'aid'ai, da kallo Asma'u ta bita tana jin ina ma Mimi zata kimtsu ta rumgumi halin da suke ciki, tana tsoron wata rana ta jawo musu abinda zai fi k'arfinsu, idan wani ya maka kyauta dan Allah wani ba haka bane, idan wani ya yafe maka sanda ya maka wani neman hanyar fanshewa zai yi, wani kuma zai iya bin kowace irin hanya dan ya fanshe wahalarsa a kan ka. Gata dai yanzu sun fito daga gidan babu kwalliya a fuskarta, ta zo gidan k'awa ta cab'a ado na d'aukar hankali, sassauk'ar kwalliya tayi amma da za'a tambayeka *wacece ita* sanda ka ganta a kan titi, ko shakka babu zaka ce k'aramar autar shugaban k'asar ne baki d'aya, sabida yanda kayan suka karb'eta ta haska tayi matuk'ar kyau, ka rantse da Allah yar babba ce zata je wani babban taro na manyan mutanen da ke fad'a aji a k'asa baki d'aya, amma kuma a gidansu nan suna can ta barsu sun yi faten tsakin masara da alaiyahu, ta tabbatar sanda Mimi ta baro gida basu da abinda zasu ci na gode da safe kawai, amma ita ba wannan ne a gabanta ba rayuwarta take yi mai cike da burirrika da saka kai a uku.
Gaba d'aya gigicewa yayi ya shiga sakin baki yana kallonta, a matsayinsa na sojan jirgi sai yaji ina ma wata 'yar hatsaniya ta faru a yanzu yanzun a layin nan, da zaiyi ram da ita ya saka a motarshi ya tafi da ita a zuwan cikin rububi ne na tashin hankali, kai shi a gaskiya zai iya rayuwa da Mimi ko babu aure, a yanda yake ji zai iya tarben tsinin wuk'ar da aka turo dan illata ta shi ya tarwatsa rayuwarshi, a kan baiwar Allahn nan zai iya yin komai. Hakan yasa bayan ya damk'a mata ledar mai kyau ya ciro kud'i yan jaka goma goma (Kwate馃槹 kin ga almubazzaranci) guda uku ya bata wai ya siye kwalliyar nan, bata yi k'asa a gwiwa ba kam ta sa hannu duka ta karb'a tana mishi godiya, yatsina fuska tayi saboda tsarguwa da kallon da yake mata na wuce k'a'ida tace "Ni zan koma ciki zamu tafi gida."
Tangale hab'a yayi yace "Mimi bana so ki tafi, kamar nayi ta kallonki."
Wulwul tayi da idonta tace "Sa茂 anjima, kaga idan mu kayi magriba za'a mana fad'a, kuma dan had'uwa da kai kawai na zo nan."
Jinjina kai yayi yace "Shikenan Mimi ta wa, sai anjima ba dan raina ya so ba."
Juyawa tayi zata koma cike da jin haushin Mimi ta shi da yace, tsayar da ita yayi yace "Mimi sai yaushe zaki bani dama na fito ayi maganar aurenmu?"
Juyowa tayi ba wani d'ard'ar tace "Sanda na shirya."
Marairaicewa yayi yace "Kamar yaushe kenan? Mimi ba kya so kiyi aure ne?"
Fuskarta a had'e tace "Ina so, amma ba yanzu ba."
Lura zaiyi magana yasa ta saurin juyawa tana fad'in "Sai munyi waya." Shigewa tayi ya bita da kallo har ta shige, d'an lashe leb'enshi yayi na k'asa daya bushe tare da shiga mota ya bar unguwar.
Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.
Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:51 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*7*
Tana shiga cikin sauri ta ciro kwalin wayar daga ledar, saida ta daka tsalle ta rumgume Asma'u tana murna ganin IPhone duk da k'aramar tashi ce, amma dai taji dad'i sosai da ganin wayar, Asma'u kam mamaki ne ya hanata magana sai kallonsu suna ta murna har da yin zaune tasa Salma turo mata abubuwa da dama har da hotunan data d'auka yanzu, suna idawa a gaggauce sukayi sallama da cewa sai sun zo ranar da za'a kawo kayanta, suna fita suka samu taxi ta nufi dasu unguwar yayar Asma'u.
Ko da suka je gidan basu wani jima sosai ba sai sak'on da Asma'u ta bawa yayar ta ta wanda uwar ta bata ta kawo sanda ta ji zasu taho, 05:50 suka baro gidan suka shiga takawa a k'afa dan isa bakin titi, dama idan aka kawoka ne kake samun mai kai ka har k'ofar gida, amma idan ba haka ba masu taxi basu cika kai kawo a layin ba.
Cikin fad'a Asma'u ta kalleta tace "Gaskiya Mimi kina ban haushi wasu lokutan, wai ke ba kya tsoron abin da zai je ya dawo ne?"
Yatsina fuska tayi tana d'an goge zufar data tsatsafo mata a hanci, kallonta tayi tace "Ba ma zaki kulani ba ko?"
Kallonta tayi ta sake yatsina mata baki tare da d'an mata gwalo ta sake d'auke kanta, jinjina kai tayi tace "Ba komai ki ci gaba, Allah na gani nayi iya k'ok'ari a kan ki Mimi, bana so k'awance na da ke ya zama irin k'awance da aka ambata ranar lahira mu had'u ni da ke muna zagin junanmu, ko kuma na rok'i da ki haska min gabana dan na tsallake sirad'i ko ke ki rok'i hakan, na fi so mu wuce a tare cikin aminci."
Wata bak'ar Prado ce ta sha gabansu ta tsaya wanda dole su ma suka tsaya cak, da sauri Asma'u ta rik'e hannun Mimi tana fad'in "Shikenan, Allah ya taimaku yasa ba cikin samarinki bane wani zai sace mu."
Kallonta Mimi tayi, saidai kafin tayi magana Ashraf ya zuro farar k'ararshi mai d'auke da takalmi k'afa ciki irin na matasan da suka san kansu wayayyu yan zamani k'irar polo, kafin suyi wani yunk'uri ya gama fitowa gaba d'ayanshi ya tura murfi da k'arfi ya rufe, a sanyaye ya shiga takowa gabansu yana cire bak'in glass d'in fuskarshi, gabanta ya tsaya cak yana mai k'arewa duk ilahirin jikinta kallo, faffad'an bakinshi mai d'auke da tsararun hak'ora ya bud'e ya nunota da yatsa kamar zai tsokale mata ido yace "Ke wacece da zaki wuce ta nan baki gaishe dani ba?"
Mimi da tun fitowarshi ta saki baki tana kallonshi, a take ta tambayi " *Wanene wannan*? Yaushe ya zo garin nan?"
Dan kam ita daga tsarinshi zuwa fatarshi da gyaran kanshi ya bayyana mata ba mai jin yaren hausa, zabarmanci, barbarci, tubanci, fulatanci ko buzanci bane, tunda take bata tab'a jin namiji ya birgeta a kallonshi ba sai yau, hasalima samarinta kallo d'aya take musu bata sake sha'awar kallonsu. Amma wannan sai take jin zata iya zaunawa tayi ta kallonshi ba zata k'osa ba ita kam. Sanda ya shiga nuna ta da yatsan nan a karo na farko a rayuwarta da taji a ranta zata shanye wulak'anci ta kuma had'e, dan wannan ba guy da zata ma rashin kunya bane, yanayinshi ma ya nuna mata zai iya tsinka mata mari, babbar asarar da zatayi kuwa bata wuce su rabu ba tare da yace yana son ta ba, dan gaskiya ita duk ajin shi da yanda ya birgeta ba zata tab'a sauko da k'anta k'asa tace tana son shi ba, ina! Ba zata iya ba, gwara idan sun rabu tayi takaicin rasashi a gaba kuma zata samu wani kamarshi ko wanda ya fi shi.
K'yasta yatsunshi yayi daf da fuskarta hakan ya sakata lumshe idonta da suka fara kawo ruwa sabida jimawa tana kallon abu d'aya, daidaita nutsuwarta tayi ta saka idonta a na shi sosai, hakan ya bashi damar sakar mata murmushi yace "Wasa nake miki, kin tsorata ne?"
Tarrr ta masa tana kallo inda a hankali ta shiga canza yanayin fuskarta daga shagala da mamaki har ta d'aure fuskar, kallo ne ta shiga yi masa irin na zuru d'in nan cikin jin haushi. D'an kallon Asma'u yayi da ita tayi galala take kallonshi yace mata "K'awarki bata magana ne?"
Da sauri ta zabura tace "Tana yi mana."
Kallon Mimi tayi ta sake jimk'e hannunta gam tana d'an motsa bakinta, a hankali ta sadda dubanta tayi k'asa da idonta tana sauke ajiyar zuciya, murmushi yayi mai sauti yace "Masha'Allah, dan Allah ya sunanki?"
Da sauri ta sake d'agowa ta kalleshi, dan Allah ya sunanki? Kamar wata 'yar talla ko kayan miya? Sama da k'asa ta harareshi tare da kaucewa ta rab'ashi zata wuce, da sauri ya sake tare gabanta yace "Dan Allah ki saurareni, ko na biyo bayanku ne har na ga gidanku?"
Asma'u ce tayi saurin cewa "A'a dan Allah ka rufa mana asiri, zaka sa a mana fad'a a gida."
Kallon Asma'u yayi yace "To in hakane ki sa k'awarki ta min magana mana."
Cike da tausayin kan ta ta sake kallon Mimi, numfashi kawai ta sauke dan bata ga abinda zaisa tayi maganar ba idan ba niyya tayi ba, sake matsowa yayi kusanta yana fad'in "Dan Allahana 'yan mata, ki taimaka ki fad'a min sunanki da unguwarku, nasan bai kamata na tsareku a kan hanya ba, amma babu yanda zan yi ne, ina ganinki naji zuciyata ta doka da k'arfi ta yanda ba zan juri ki sub'uce min ba."
Kallon Asma'u tayi ta mata alama da ido mu tafi, zata taka k'afarta yace "Ki fad'a min abinda zanyi mana da zai sa ki min magana, dan Allah kada ki bari ki kubce min *Naana*."
Kallon juna sukayi ido cikin ido, da sauri ta d'auke na ta saboda marayan kallon da yake mata, a marairaice yace "Ko sai na duk'a har k'asa ne?"
K'asa ta k'urawa ido ba tace komai ba, a hankali ya nemi zemewa ya durk'usa k'asa yana fad'in "Wannan ba kom..."
Ba ta barshi ya k'arasa ba tayi saurin kallonshi tare da fad'in "Maryam."
Da mamaki Asma'u ta kalleta jin ta fad'i cikakken sunanta yau ga saurayi, a iya saninta saidai ta fad'a maka Mimi amma ba zaka ji Maryam a bakinta ba. Mik'ewa yayi yana sakin murmushi tare da fad'in "Alhamdulillah, *Mimi*, suna mai dad'i."
D'an kumburo bakin da tayi yasa shi yin murmushi yace "Kina da aji, hakan kuma ya tabbatar min da na samu matar aure, fatana Rabbi ya dafa min kar ki k'i kulani a matsayin wanda zakiyi soyayya da shi ma bare aure."
Hannu yasa aljihu ya jawo tartsetsiyar wayarshi ya mik'o mata yana fad'in "Zan iya samun agajinki ta hanyar rattab'a min lambobin da zasu sadani da inda kike?"
Wani wallll! Tayi da ido tare da k'ura mishi ido, kunnenshi d'aya ya kama alamar ban hak'uri, fari tayi da ido hakan ya k'ara narkar dashi tare da fad'in "Ko na sake zubewa k'asa ne?"
Har yayi haramar zubewa k'asa tayi saurin fizgo wayar ta shiga saka mishi lambarta, mik'a mishi wayar tayi a hannu suna kallonshi ya saka suna kafin ya kalleta ya sumbaci wayar, irin kallon firgitarwar nan ta bishi da shi, shi kam murmushi yayi yace "Yanzu musaya ta fara shiga tsakanina da ke, a sannu sannu wata rana zamu gauraya mu zama babban iyali da zai tsiro da kyakyawa kuma hazik'an yara."
Kallon mamaki ta mishi shi kuma ko a jikinshi, saima rusunawa da yayi yace "Dan Allah zan iya saukeku inda zaku je?"
Asma'u ce ta girgiza kai tace "A'a gaskiya, an hanamu."
Kallonta yayi sannan ya kalli Mimi, cikin taushin murya yace "Hakan ne a ranki kema? Ba zaki shiga ba?"
A hankali ta lumshe idonta wanda suka sha mascara suka yi tsayi sosai alamar eh, jinjina kai yayi yana jinjina al'amarin wannan mai kama da jinin sarautar, idan da za'a barshi da hasashenshi sai yace 'yar k'usa ce a gwamnati sun samu matsalar abun hawa ne, dan duk da baya da sani akan suturar mata yasan kayan dake jikinta ba masu arha bane, ko da akwai mai arha to sai dai ko 'yan kunnenta dake k'anana sosai mak'ale a kunnen. Saidai a wajenshi kam ko ta kasance 'yar babba ko ta kasance 'yar takala wannan bai dameshi ba, tunda ya karyo kwana idonshi suka sauka a kanta ya ji zuciyarshi ta fizga a guje ta rakito duk wani abu daya shafeta ta killace da jin cewa zata dage a kan ta ko ma wacece ita.
Saida ya kalli k'wayar idonta ya daidaita gilashinshi da kyau ya manna mata shi a fuskarta, hakan kuma ba k'aramin kyau ya k'ara mata ba. Dariya yayi data fito da kyawunshi da kyau yace "Sai na kiraki, Mimi."
Da kallo ta rakashi sai Asma'u da tace "Dama kasan inkiyarta ce Mimi?"
Juyowa yayi yana shafa tarin sumar kanshi yace "Ban sani ba, amma duk mai sunan Maryam ina kiranta da Mimi, saboda sunan *mahaifiyata* ne."
A tare suka saki murmushi ita da Asma'u, haka kawai ta ji abinda ya fad'a ya sata nishad'i, da kallo suka bishi har ya shiga motar ya barsu nan tsaye. Kallonta Asma'u tayi sai taga har yanzu idonta na kan shi, da sauri cikin jin haushi ta cire gilashin daya saka mata tana fad'in "Malama ya tafi to sai ki kama bakin."
Da sauri Mimi ta kalleta sai kuma taja tsaki tare da k'watar gilashin ta saki murmushi ta kalleta tace "Dan Allah mutumin nan bai birgeki ba?"
Girgiza kai tayi tace "Ko kad'an, tunda saurayinki ne."
Cike da damuwa tace "Ke ba haka nake nufi ba, ina nufin tsarinshi, kalamanshi, kyawunshi da kuma yanda ya iya shiga zuciya lokaci d'aya."
Galala Asma'u ta kalleta tace "To fa, da alama wannan kam shi ne *zakaran* da ya zubar da 'yan maza warwas a wajen Mimi."
Kallon gilashin hannunta tayi ta sake mayar dashi ga fuskarta ta kalli Asma'u ta d'aga mata gira tace "Ya kika gani dan Allah? Ya min kyau?"
D'aga mata gira tayi ita ma tace "Kinyi kyau kam sosai."
Hannunta ta kama cike da jin dad'i suka fara tafiya tana fad'in "Asma'u a rayuwata ban tab'a tunanin zan had'u da irin wannan namijin ba?"
Da mamaki ta kalleta tace "Me yasa? Naga ai burinki kenan samun irin wannan namiji."
Saida ta saki hannunta tace "Hakane, amma ni ban tab'a tunanin zan samu kyakyawa haka ba ai, to wai wanene shi?"
Ta fad'a tana kallon Asma'u, tab'e baki tayi ta d'aga kafad'a tace "Ina zan sani, sai ki bari idan ya kiraki ki tambayeshi."
Wani murmushi ta saki tare da d'agawa wani d'an taxi hannu tana fad'in "Ba ni zan tambayeshi ba, shi ne zai fad'a min."
K'ala Asma'u ba tace ba har suka k'arasa kusa da mai taxi, saida ta kalleta tace "Gida muka nufa yanzu ko kuma dai kina da sauran gurin zuwa ne?"
Murmushi ta mata tace "Gida zamu koma mana ke ma, magriba ta kusa ai."
Girgiza kai tayi ta kalli mai taxin tace "Tallague."
Jinjina kai yayi alamar su shiga, bud'ewa sukayi suka shiga inda ya jasu, wayar ta ciro a jakarta ta shiga saitata zuwa yanayin da take buk'ata, saida ta tabbatar komai ya mata kafin ta ciro wani k'yalle a jakarta a hankali ta shige goge kwalliyarta na fuskarta tana kallon madubi, saida ta goge duka kafin ta kwance d'aurin d'an kwalin ta saka a jaka ta ciro hijabinta ta saka, sak yanda ta